Sashe 25
Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba yace toni bani da kudi ma,
Bishira tace to kudin jiya da babana ya baka fa?
Umma tace fito dasu, yace umma dama fa kudin
sadaki ne ya biya min, kuma naba alhji karami
waliyyinta sai dai ki je gun shi ki amsa, tace don
kasan bazan tunkareshi bane shi yasa to tana
binka bashi, zaka chanza mata kayan daki, ka sai
mata zannuwa sannan ka bata jari, yace umma
banyi alkawari ba, in dai na samu kudi kuma ta
kwantar da hankalinta to xan mata, ya nufi daki
yabar su nan sunata zantukan su.
Lkcn daya
shiga gdn su umman shi, ummi tana linke kaya
tana sakawa cikin jaka, yana daga bakin kofa ta
dago ta amsa sallamar shi ta kalle shi, ya kalli
kayan sam zuciyarshi bata mishi dadi, ya nufi
wurin umma don yana son neman alfarma abar
ummi zuwa dan wasu kwanaki don yana so ya
dan gyara gidan, rashin galihun zai yi yawa, ba
lefe kuma gida ba gyara?
Yayi sallama suka
amsa, bayan ya gaishe su, ya dukar da kai yace
alhji dama nazo ne neman alfarma, suka ce
alfarman me?
Yace inaso ne kudan bar ummi
zuwa nan da sati daya, sannan na gyara gdn,
kuma nayi mata sabbin dinki, alhji yace ba kana
da fentin ba?
Kaje kasa a goga, sai ka biyo ta
kasuwarmu ka amshi zannuwa, abba yayi shuru
umma tace koda wani abu bayan nan?
Yace a'a,
umma tace to an daga maka zuwa gobe, yace to
umma da alhji nagode, ya mike ya zai fita, yace
am umma ummi tace zata je gyaran gashi, suka
yi dariya su kace ai wannan ikon kane, yace to na
tafi alhji sainazo kasuwar, ummi ta jera masa
kayan karin kumallo koda ya leka dakin sai tace
ya abba ka shigo ga break, yace ummi zanyi latti,
tace to da yunwa zaka tafi?
Yace akwai shayi a
can, tace come on ya abba zoka karya, ya kalli
agogo minti biyar gareni, ta dau copi ta tsiyayo
kunu ta mika masa, ya fara kurbar kunun, ta zubo
kosai a plate tarike a hannunta dauka kaci, ji take
tamkar ta bashi a baki, tsohuwa ta dago labulen
dakin, tace zura masa a baki za kiyi?
Ummi tace
kada ya kware tsohuwa, an hana yin magana in
ana cin abinci, toshuwa tace tafi can da cusa kai
ba kwarjini, abba ya dire kofi tareda mikewa yace
ummi saina dawo, ki bari da dare zan kai ki
gyaran gashi, yasa hannu a aljihu ya zaro yan
dari binbiyu guda biyar ya bata, tayi godiya ya
ciro dari yaba tshuwa yace yar sa ido kema kiyi
kotso da wannan, ta rike baki tana fadin wannan
yara da munafunci suke, ya fita yana murmushi
ummi tace a dawo lfy, ya sake waiwayo wa ya
kalli ummi, suka saki murmushi, 35. 64....
Tsohuwa da ke bin su da ido ta ce, "Kai ban
yarda da ku ba Takwara, dama can ke da me
sunan Malam soyayya ku ke? ---- Umma da ta
tsinci zancen bayan fitowarta daga dakin Alhaji,
ta ce "Ya a ka yi?" Ta ce, "Suwaiba ina ga
yarannan tuni kallonmu kawai suke.
Sai wannan
salo suke wa juna, sannan ga Takwara ciwon
barin gida shiru, ina ga dama ciwon nan na mai
sunan Malam ne." Umma ta saki dariya tare da
cewa "Allah yasa haka ne.
Ummi kam cikin daki
ta kule zuciyarta zallah dadi.
Misalin karfe biyu
Umma ta dan kishingide baya, ta idar da sallah,
tsuwar wayar da da Abba ya ba Ummi ajiya ce ta
farkar da ita.
Ta ce, Ummi me ke tsuwa a dakin
nan?
Wannan dai ba wayata ba ce.
Ummi da ke
tsakar gida ana mata zanan fulawa ta ce, Lah,
Umma Ya Abba ne ya bani ajiya.
Kila ma shi ne
ya kirata, ta dubi wadda ta yi mata zanen fulawar
ta ce Sabira don Allah shiga ki dauko min a kan
gado. 2missed call ta gani, ta ce kash!
Sai gashi
ya sake kira, kafin ta daga sai da ta leka dakin
tsohuwa ta hango ta kwance a gadonta.
Dama a
kofar dakin Tsohuwar take ta biyo inuwa ta daga
wayar tare da sallama, ya amsa cikin dokin jin
muryarta.
Ina ki ka shiga ne?
Ta amsa a can
cikin makoshinta, ana min fulawa a tsakar gida
wayar kuma tana daki.
Ya ce, Ok ana miki zanen
fulawar ne?
Ta ce an ma ganin har ya fara
bushewa ya saki murmushi tamkar yana gabanta.
Ana yi miki me kyau?
Ta ce, Eh yayi kyau sosai,
ya ce Good, zan dawo kamar karfe uku saboda
zan kwashe kaya za a yi fenti a daki, so kin ga
ba zan samu kai ki gurin gyaran gashin da wuri
ba. 65...
Don haka sai mu bar shi zuwa dare ko?
Ta ce, "To Ya Abba, ehm za a dafa maka wani
abu ne?
Dadi ya lullu6e shi amma saboda
burinshi na kimanta Bishira a idonta sai ya a'ah.
Na hutar da ke zan ci na Antynki Bishira,
maganar ta soki ran Ummi har ta kasa magana,
ya fahimci hakan don haka sai ya kawo zancen
da cewa sai nazo.
Ta tura baki tare da cewa
uhm, tana kashe wayar ta shiga kunkunan cewa
in yaso kaci abinci gidansu bana ta ba.
Tsohuwa
da ke sauraronta ta sheka dariya tare da cewa,
ba dai ke kin ce me sunan Malam ba?
Sai ma kin
je gidanshi yarinya ban miki baki ba amma za ki
raina kanki.
Ummi ta cafke cikin jin haushi ta ce,
wai to Tsohuwa da za ki ce na ce Ya Abba cewa
nayi ina sonshi?
Kuma da su Alhaji suka jona ni
da shi da naki har da ke za a dinga cewa ban yi
biyayya ba.
Tsohuwa ta ce, Raba ni da gulmarki,
kina sonshi ai ni ba yarinyar goye ba ce, kina
waya kina kashe murya, san nan ciwoce-
ciwancanki duk sun lafa.
Sai wannnan rawar kai
ki ke, to ki sani me sunan Malam dai ya aure ki
ne don dole, matar cushe kuwa ba daraja take
ba.
Ummi ta ce, "To nima dai ai ba sonshi ni ke
ba, ni dai tsohuwa don Allah ki daina samin ido.
Ta mike, Na ma bar miki kofarki.
Ta nufi kofar
dakin Alhaji tana kunkunai. 36. 66...
Sai dai duk
da haka kalaman tsohuwa sun tsaya a ranta,
matar cushe bata daraja, Ya Abba kan dole ya
aureta, lallai zancen tsohuwa abin dubawa ne.
Abba ya shigo gidan uku da doriya, tare yake da
yara guda biyu, dayan zai mishi dan face-face,
dayan kuma zai masa fenti.
Sune suka taya shi
kwasar kaya, bai samu Bishira a gidan ba, kila
tana gidan Ummanshi, ko makota.
Sun kama
aikinsu shi kuma ya shiga kicin don ya dan dafa
abinda zai ci.
Bishira gidan Anty ta tafi kuka take
wiwi wai ita fa ba za ta iya zaman gidan nan ba,
ta ce "Aunty Farida tunda kuna shiri da Baban
Walid ki ce masaya sawake min".
Anty Farida ta
tsura ma kanwarta ido, tausayin Bishiran ya
cikata.
Tabbas kishiya bata da dadi koda
mahaukaciya ce bare mai hankali.
Sai dai ita bata
da ikon da zata hana ayi kishiyar koda kuwa
mijinta ne ke son yi, don sunna ce ta mai tsira da
Aminci.
Bishira ta katse mata tunani da cewa,
dubi fa Anty hatta Dady yanzu yafi son Baban
Walid fiye da ni.
A gabana ya dauki kudi yaba
baban Walid, a halinni kara na kai a kar6ar min
'yancina, kuma Momy zata yi magana ya hanata
cikin tozartawa.
Hakan da Daddy yayi ba zubar
min da kima yayi ba, har da ita Momy?
Yaushe
Baban Walid zai sake ganin darajarta?
Anty
Farida ta sauke ajiyar zuciya, ta ce "Bishira Dady
bai zubar miki da mutunci ba, illa kara tarairayo
miki mutunci da yayi daga ke har Momy.
Kuma ni
ba zan ce mijinki ya sake ki ba, haka nan ba zan
ga laifinshi ba, domin aure sunna ce ta Manzon
Allah (S.A.W), sam ba zan yi fushi da wanda ya
raya Sunna ba, koda mijina ne.
Kiyi hakuri
kanwata koda bani da kishiya nasan akwai zafi,
amma kema kina da laifi, dube ki fa.
Yanzu
Bishira wa zai gan ki ya amince ke kanwata ce ta
hudu?
Zato za a yi ke yayata ce, kin saki kin yi
ragwaf, nonuwa har ciki haihuwa biyu jal, dubi
yanda tsabar datti yasa fuskarki da dokin wuyanki
zuwa bayanki duk kyasbi ya miki riga.
Da kin
zauna kusa da mutum wari ki ke tashi, hakora
sun miki yalo, kai mijinki fa ya yi kokarin ba
kowane zai dauki hakan ba.
Duk ba ki kalli laifinki
ba sai don ya kara aure yanzun?
Ina ce kwanaki
garin shegen gantalinki ne ki ka bar danki a gida
ya fada rijiya ya mutu?
To hatta Abban Nasir ce
min ya yi da shi ne ba zai yarda ba, saboda haka
ki dawo hankalinki ki zubar da kazantar nan ki
kama Ibadarki.
Bishira ba kya jin kunya a ce ba
kya sallah?
Kuma a tare da haka kina da wannan
kazantar ki ke kaurace ma shimfidar mijinki.
Kwanan baya ya kira ni a waya ya sanar da
nicewa kin ce min ina wari, don haka ni kuma na
ceya tafi gurin mai tsafta mai kamshi.
Shima fa
Anty magana yake dankara min don ba kisan
halinshi ba ne.
Anty ta ce, "Bishira kina cikin
hadari, ga kin sallah sannan ga kauracewa miji ki
kwana Mala'iku suna tsine miki.
To daidaita
sahunki, ga mijinki dan kwallisan dan Jarida mai
farin jini, ki kalli yanda in yana gabatar da
shirinsa yanda 'yammata kan kira su ce suna son
lambarsa.
Amma ke kina sakaci da shi, ki dubi
yanda wata mata ta kawo masa hari kwanaki da
a ce ya yarda ke ba za ki san kina da kishiyar
waje ba.
Ki shiga taitayinki zan dai miki taimako
daya in kinamince za ki natsu. 67....
Bishira ta
ce, Anty taimakon me?
Ta ce, "Zan samu Momy
su taimaka su canza miki kayan daki, sannan
Dady ya ba mu kujerar Makka ni da ke da Aisha.