← Book details Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 28

Sashe 22

Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace a'a ta farka
tun kusan karfe uku,koda fatima ta fada mata
yanda abubuwa zuka zama,tayita yan koke
kokenta,gaban abba yafadi****tabbas ummi ba
son shi take ba inba hka ba meye na kuka?

Ya
kalli inna bari in karasa,tace to kaje tshuwa na
ciki,a ranshi yace jaraba road,yasan dai ko yane
sai tshuwa tayi mishi surutu,yana tura kofar
tareda salama suka hada ido da ummi,sun kure
juna da kallo,kowanne nason ya fahimci ya dan
uwansa yadauki abin"tshuwa ta katse su dacewa
to zakin fama sai ynz kaga daman zuwa?

Ya
dubeta eh" ai eh ace?

To me kikeso ince,tace to
madalla ai na dade da sanin halinka,kuma da ace
iyayenku sunyi shawara dani lallai da baza suyi
wanna hadin ba Domin na tabbata kai zaka
karasa takwara don baka kaunarta, haushi ya
cika abba abba yana kallon tsohuwa yana tuna
amsar data dace da ita, ummi kuwa tsura mishi
ido tayi tana son jin me zaice,yace kamar kin
sani,tace ahaf shiyasa tausan yar nan kebani
tausayi, ta soma matsar ido,yace nima yakamata.
ki tausayamin tnda cusa min ita akayi,ummi
takoma ta kwanta lakwas tareda hakikancewabl
kalaman abba sako ne zuwa gareta,matar cushe
kuma bata daraja,to inaso kasan wani abu
guda,duk randa naji wani abu daidai da
wulakanci, toba kaiba har iyayenka saisun san
naje makura. 52..Dazun nake gaya masu basun
hada kai sun kulla auren nan ba,duk randa suka
kuskura sukazo min da batun warwareshi saina
basu mamaki,abba ya tabe baki tareda kallon
ummi wadda takasa jurewa tashiga rera kuka,ya
isa gaban gadon,"jikin ne ummi?

Tayi shuru,kinci
abinci?

Nan ma ta share,sai kurum ya nufi wurin
likitan zuciyarshi na kuna bako shakka kukan kin
shi ummi keyi,sun zo da likita ya shiga yimata
fadan kukan da takeyi,a cewar likitan kukan illa
ne ga lafiyarta,tshuwa ta kalli likita dan nan dole
ta koka a dauke ka ahadaka da wanda baya
kaunarka"abba cikin takaici yace subhanallla!

Don
Allah tshuwa kibarni inji da abinda ke
gabana,tace ina ruwana da abinda ke
gabanka,likita yayi dariya yace mama yakamata
ki koma gd haka,abba yace bari inkaita
indawo,tace ban binka da can dani kazo?

Abba
yace nahuta,likita yayi dariya,da kyar suka lallaba
tshuwa ta tafi da inna saratu,abba yaja kujera ya
zauna gaban gadon,bayan fitan likita Idanu ya
zuba ma ummi,godiya yake ma Allah a zucin shi
daya amsa addu'ar shi yabashi abar sonshi,itako
kai ta dukar a ynz takasa tantance kukan farin
ciki take ko takaicin kalaman ya abbanta?

Wani.

Dan zare dake jikin hijabinta take wasa dashi,a
zuciyarta kuma tambayoyi ne da fuska data jefa
masa su,ya katse ta kinci abinci?

Ta daga kai
alamun eh" yace to yakamata ki dangana da
kukan haka kisani ni kaina da ina nan bazan bari
su alhji su daura maki aure da wanda bakiso ba.
53..Da sauri ta kalleshi,yace. amma inkin yi hkr
zansame su zamu san yadda zamuyi,ta lumshe
ido a zuciya tace tab!

Ai rabamu sai mutuwa,zan
juri duk wani ki dazan gani daga gareka,ya
katsxeta kina zance a zuci fadi abnd kikeson
cewa,tayi tagumi tareda kallonshi,ya abba yakanfi
dacewa sa dan sanda ne ba dan jarida ba,sbd
yanada saurin nazartar mutum,to amma meyasa
yakasa gane tana son shi?

Yayi murmushi,zanso
inji abnda kikeb saqawa azuciyarki ko kinn samo
mafita ne? 29.

Zancan mafitar nan tana bata
haushi, don haka saita canza zancen da cewa,
tambaya zan maka guda biyu, ya dan yi shiru.

Nazari yake, wace irin tambaya zata masa?

Kila
zata tambaye shi ne ko zai amince ya sahale
mata auranshi, ya dubeta amsa daya zan ba ki in
kin yarda, ta ce To dama zance ne ya ka ji
lokacin da labarin sauyawar lamari ya zo gareka?

Ya kura ta da ido, ya tambayi kansa a zuciya, me
yasa take son ji@ yayi dan yake, yi tambayarki ta
gaba, ta tsura mishi ido.

Yanzun yaya za ka yi da
maganar Zainab?

Ya yi 'yar dariya, wacce amsa
ki ke so a ciki? da sauri ta ce ba ni wannan
amsar.

Ya ce, "Kiin manta ni mijin mace hudu ne?

Ta zaro ido kamar ya ya?

Ya yi kokarin danne
dariyarsa, sakamakon yanda ya ga ta zarana.

Ya
ce, "Ina nufin bayan Zainab har da wata, Ummi ta
hade rai sannan ta zame ta kwanta cike da dana
sanin tambayar.

Abba ya yi mamakin kishin
Ummi gare shi, ita da ba sonshi take ba?

Ko da
yake an ce mace ko bata son namiji in dai mijinta
ne ta tsani ta ganshi da wata.

Duk da haka ya ji
dadin yanda ta nuna kishinta a kanshi, da ya tuna
da Bishira ya ce tab, wata fitinar tana can tana
jirana yau.

Sam Ummi bata kara magana ba, shi
kam Abba waya ma yake tayi Inna Saratu ta
dawo, don haka ya mike ya kalli Ummi.

Zan tafi
ba tare da ta dago ba ta ce, sai anjima.

Ya tafi
yana waiwayonta bayan ya wa Inna Sallama.

Kin
shiga gidanshi ya yi sai kusan sha biyu a nufinshi
lokacin Bishira tayi bacci, sannan yaje ya sai
mata wayar da layi don yasan tana son waya.

Kudinshi kenan ma ya kwashe ya sai mata, bai yi
wani motsin kirki ba don kada ta farka, ya bude
dakinshi ya shiga ya fito yana jan ruwan wanka
kenan ta fito daure da zani a kirji.

Jikinta ko dan
kwali babu, gaban Abba ya fadi ta ce, "Munafukin
Allah, annamimi dama ashe abinda kuke shiryawa
kenan?

To ka sani dole kasa ke ni don ba zan iya
zama da Ummi ba, Allah ya kiyaye in hada miji da
wannan 'yar yarinyar, tunda kai baka ga ai baya
ba".

Ya sassauta murya, "Haba Bishira, wannan
abin fa Allah ya kaddaro za a yi haka, matar
murtum kabarinsa.

Ta ce, "To wannan ajalinka ce
tunda wancan ya ki shi ne kai a ka cusa maka.

Ya bar jan ruwan ya kama hannunta suka nufi
dakinta, tana ta masifa.

Ya ce, kibar maganar
yanzu dare ne duk makota suna ji za su yi, kuma
banga bain da zai sa ki daga hankalinki ba.

Kin
san dai ina sonki ko?

Ta yi shiru tana kallonshi,
ya ce ina zuwa.

Yaje dakinshi wayar ya dauko
mata, ga wayarki.

Ta ce, "Eh don ka toshe min
baki k? to bana so, ita wa ya san abinda ka sai
mata?

Ya ce, ya ki ke wannan maganar?

Ban sai
komai ba ko lefe ma tukunna.

Ta mike tare da
jefa mishi kwalin wayar, Ga tsiyarka nan
matsiyaci, dole ka saka min da haka, tuni a ka
gaya min tsiyar talaka na tafe.

Haushi ya kama
Abba ya dauki wayarshi ya tafi ya maida yazo ya
dau ruwanshi yayi wanka, yana jiyo kukanta da
duk zage-zagen da take yi.

Shi kam katifarshi ya
fada tare da rungume fito yana tunanin ranar da
Ummi zata maye gurbin filon. 30.

Har an tada
sallah a Masallaci lokacin da ya farka, ya jima
bai yi irin wannan baccin ba, da hanzari ya fito
ya nufi ban daki don alwala.

Abin mamaki Bishira
ce zaune kan kujera a kofar dakinta, matar da sai
ta kai takwas bata farka ba, amma yau bala'in
kishi ya hanata bacci.

Ta ce, "Eh na fito a ba ni
takardata na gama zama da kai, ko in da take bai
kalla ba ya ci gaba da abinda ke gabanshi, ya
nufi Masallaci yana jinta tana ina nan ina jira ba
zan zauna ba.

Haba, gaskiya naji na tsani
yarinyar ashe mijina zata aura, tsaki ya yi ya
bude gidan ya fice.

Har gari ya soma haske yana
cikin masallacin, tunanin zuwa gidan yake, daga
karshe dai ya fita da niyyar zuwa gidan
Ummarshi.

Wata zuciyar ta tambaye shi da cewa,
tsoron ta ka ke ji ne?

Kar ka zama soko dai a
gidanka.

A fili ya furta cewa, tunda na bita ta
lalama ta ki, bari in koma mata ta zafin, ida din
me?

Sai ya sauya hanya zuwa gida rai 6ace,
fuska daure ya shiga gidan, tana ta kai-kawo a
tsakar gida.

Ta dumfaroshi sai ka ce sabon
kamun hauka, daga ganinshi ta dinfaroshi.

"Ka
ban takardata ba ni ba zama da kai, tafiya zan
yi".

Ya harareta "Sai da takarda za ki tafi?

Lallai
ba ki ji tafiyar ba.

To ba zan bada takarda ba,
don ki sani, sai dai in kotu za ki kai can Alkali ya
baki".

Ta nufo shi da zummar shako masa kwala,
ya ce Kina ta6a ni sai na zane ki, in yaso ki tafi
da hujja".

Ganin yanda Abba ya bude mata wuta
sai taja baya, Ka isa ka zane ni, ai da ka san ka
dake ni, don ko sai ka sha dauri.

Ya nufi dakinshi,
wanka ya fito yayi sannan ya yi shirin tafiya aiki,
amma har lokacin tana nan, ga 'yarta ta tashi
daga bacci sai kuka take yi.

Ta dauke ta ta goya,
ta shiga dakinta can kuma ta sauke 'yar tasa
kaya ta fito ta dauraye fuska da kafa ta goya 'yar
tasa kaya ta fito taja kofar tana fadin." "Tafiya
zan yi".

Ta fito ta same shi yana goge gilashin
motarsa na gaba.

Ta ce, Tafiya zan yi sai an
kar6ar min hakkina".

Murmushi ya saki, sannan
ya kalleta, ta ina za ki bi in rage miki hanya?

Ta
dawo ta duki motar, Ba zan shiga wannan
gwanganin motar ba, kai ne bakon mota.

Kafi
kowa sanin daga gidan da na fito, ko motar zuwa
cefanen gidanmu tafi wannan tsarri.

Ya ce.

"Gurinki ko?

Ni ai bani da wadda ta fita tunda
bata gidan naku nike hawa ba.

Sannan kuma
tunda ba za ki zo in rage miki hanya ba shi
kenan sai naga sammaci.

Ya shiga motar ya
tasheta yayi gaba, ba tare da ya saurari abinda
take cewa ba.

Ta isa gidansu cikin tashin hankali,
Hajiya Zainu ta saurare ta tsaf, sannan ta ce "Kin
dai ga abinda a ke fada miki, kina ganin ba zai
faru ba ke so ya rufe miki ido, to yanzu an zo
gurin.

Bishira ta ce, "Ai na gane komai yanzun,
Momy nayi nadama.

Ta ce, "To zan tsaya miki
matsalata Babanku, yana nan a gari na kuma san
za su zo iyayen Abba.
Chapter 22 · 0% Book details