Sashe 27
Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bishira ta ce, Allah dai
yasa su yarda, Anty ta ce,"Za mu su yarda in
Allah ya yarda.
Ta dauko wasu kayan sawa da
sabbin kuloli ta ce ma Bishiran je kisa a motarku.
Abba ya ce, "Kawo in kai, Anty na gode sai
anjima, ta ce To Abba ayi ta hakuri".
Ya ce, Ba
komai, Insha Allahu.
Suka biyo shi a baya tana
kara jawa Bishira kunne kan cewa in har ta
kuskura ta ji wata magana ta 6ullo ta rashin
mutunci sai ta fasa tsaya mata a kan maganar
aikin Hajji ko Dady ya amince sai tasa ya janye.
71....
Sun shigo mata Muhibba tana baya tana
'yanwutsil-wutsil dinta tamkar kurame, haka suke
tafiyar.
Ta zaci su nufi gida sai taga sun nufi
cikin gari.
Bata tambaye shi ina za su ba, har
suka isa inda yayi parking ya dubeta, Madam ina
zuwa, hum kawai ta ce.
Ya bude baya ya dauko
Muhibba ya sa6a a kafada ya nufi shagon saloon
din.
Daidai lokacin sun kammala komai, Ummi ta
zari hijabinta da niyyar rufe kanta, Yagana ta ce
a'a kanwata bari ya gani don ya biya ni 'yan
kudina.
Abba bai zaci Ummi tana da gashi ba,
domin dai acikin Hausawa 'yan Arewa za a iya
saka Ummi acikin ma su gashi.
Yayi laya-laya a
dokin wuyanta baki sidik.
Yayi murmushi, lallai
kin gyara da kyau.
Nawa ne kudinki?
Ta fada ya
ciro ya bata, sannan Ummi tazari hijabinta.
Mamaki take, Gida ya koma ya dauko Muhibba?
Yamiko mata ita, Ga 'yarki.
Ta amsheta.
Yagana
tace, yarinyar tana kama da ku.
Abba ya ce, "Ai
'yarmu ce, suka yi mata sallama suka fito.
Ummi
da Bishira a tare gabansu ya fadi lokacin da suka
ga juna.
Bishira ta kauda kai yayin da Ummi taja
baya daga mazaunin kusa da direban da ta nufa,
ya bude mata baya ta zauna tana rike da
yarinyar.
Ya tada motar suka dauki hanyar tafiya
kowanne zuciyarshi da abinda take karantowa.
Ummi tunaninta Abba ya je ya zo da matarshi ne
don yanuna mata shi fa matarshi yake so.
Ita ko
Bishira nata ganin wulakanci ne na karshe da ya
dauko ta yazo da ita gurin wannan karamar
yarinyar.
Shi ko Abba addu'a ce a zuciyarshi
Allah ya hada masa kan matansa, sai kuma ya
soma tunanin ina zai soma zuwa?
Nashi ganin in
ya kai Bishira gida ya sauke ya tafi kai Ummi bai
mata adalci ba.
Amma ya kula Ummi tana fushi
kuma yaso ya lallasheta, yana cikin wannan
tunanin ya tuna dawayar nan.
Ya kalli wayar a
gefanshi.
Dan murmushi yayi da ya tuna lokacin
da ta dangwarar masa da wayar don ya ce ta
matarsa ce.
Yanayin yanda Ummin ke nuna
kishinta yana birge shi, koda bata sonshi tana
kishinshi sannan bata masa raini ko rashin
kunya.
Kofar wani gidan saida gasassun kaji da
ire-iren kayan kwalam ya tsaya.
Ya kalli Bishira
Madam mu shiga ko?
Ta ce, "A'a ni fa ba zan fita
ba, ya ce To bari in dawo, ya nufi ciki. 72..
Ta
waiwayo ta dubi Ummi, ta ce "Ba ni 'yata
fitsararriya.
Ummi ta mika mata tare da cewa
nima ai ba cewa nayi a bani ba, ta ce "Kar dai ki
min rashin kunyaki bar ganin an jona ki da mijina
ki zata za ki hada sahu da ni.
Ummi ta ce, "Sai
dai kada a kuma in dai batun hada sahu ne, kuma
ban damu don mijinki ba bai sona ba, tunda ni ina
sonshi.
Bishira cikin daga murya ta ce, oho?
Dama sonshiki ke yi?
Yanzun na gane da nufi aka
yi.
To ki sani kin sai ma kanki masifa da bala'i.
Ummita ce, "Kin ga bala'inki can, daga nan
batakara magana ba ta bar Bishira na ta masifa.
Tundaki ka za6i ki auri mijina zan shayar da ke
ruwan dana sani.
Sai kin gwammace zama a
kurkuku fiye da gidan mijina, daidai lokacin Abba
ya dawo da ledoji guda biyu.
Bishira bata yi shiru
ba sai zagin Ummi take yi,"'Yar iska, 'yar daba...
tsawa Abba ya daka ma Bishira, tare da cewa ba
ki ji kunya ba da ki ke zaginta amma bata kula ki
ba?
"Ta ce, "To ka ji abin da ta ce min ne?
Tsaki
yaja tare da daukar wayar da ta aje yasa a ledar
Ummi, sannan ya tada motar.
Kofar gidan su
Umma ya tsaya, Ummi wadda dama ta kosa tazo
gida, ta bude motar ta fada gida cike da takaici.
Ya kashe motar sannan ya dauki ledarta ya kalli
Bishira, Ina zuwa.
Kala bata ce ba.
Illa baki da ta
cije, kirjinta na yin wata irin suya.
Ban da tana
tsoron Anty kada ta fasa zuwa gurin Dadynsu da
tuni ta shago Ummi ta nadi 'yan kayanta.
Dakin
Umma ta shige, Ummar tana shirin fitowa Ummi
na shiga, ta ce kun dawo?
Ummin ta hadiye 6acin
ranta."Eh, mun dawo Abba a ya shiga gaida
Umma sannan ya mika ma Ummi ledar, gashi kin
manta Ummi ta amsa tare da cewa, an gode.
Umma ta ce, "Me ku ka siyo in ce dai ka sai ma
Bishira?
Ya ce, "Eh na sai mata, kaza ce fa
Umma ba wani abu ba".
Ta ce, "To shi ke nan
maza ka koma gurin su, yace "To.
Tana fita ya
kalli Ummi akwai waya a cikin zan kira ki, kuma
bana bukatar ki kashe min waya.
Ummi ta ciro
wayar da sauri, ta dibe shi ba wayar matarka ba
ce?
Ya ce, "Eh tata ce, ta mika mishi cike da
kunan rai, ga abinku ka kira ni da layin Umma.
Ya
ce, "Ke ce za ki cigaba da rike ma mata
tawayarta, ba tare da ya jira jin me za ta ce ba
yana murmushi, Ummi ta kasa gane cewa ita ce
matarta shi.
Ko kallon kazar bata yi ba illa dai
tayi duk wasu abubuwan da ta saba yi kafin ta
kwanta, sannan ta kunna wayar tana tsammanin
kira. 73.....
Shi ko Abba koda yazo Bishira tana
ta mitar don tsohon wulakanci an zo da ita an
shanya ta, bai ce mata kala ba illa dai motar da
ya tada suka nufi gida.
Gidan duk kaya saboda
bai maida ba da a ka gama fentin, ya dauki
tsintsiya ya share dakin, sannan ya shimfida
katifa ya fito inda take zaune bakin Rijiya.
Muhibba tayi bacci tana rungume a jikinta, ya ce
kawo ta, ta mike a fusace ta nufi dakin ba tare
data bashi 'yar ba.
Ya bi bayanta, so kurum yake
ya lallasheta ba wai don tsoronta ba sai don
tausayinta, yasan mata kan kishi za su iya yin
'yar karamar hauka.
Wasu ma sai sun yi babbar
kuma bai dace ana nuna kishinsa ba, shi kuma
yana nuna ko 'in kula a gare ta, gefen katifar ya
zauna ya lalubo hannunta ya rike cikin
nashi."Bishira!" ya ambaci sunanta cikin sanyin
murya, bata amsa ba kuma bata dube shi ba, ya
ci gabada cewa, "Bishira ban ga abin damuwa ba.
Ko damata uku a ka daura min aure da su bare
daya, inkin yi la'akari da irin son da nake miki ke
kin san Bishira ba kiyayya ta hada mu ba.
Kina
manta wannan ne?
Ta dago ta dube shi ta dan
soma saukowa, yayi murmushi har yau ban daina
sonki ba, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta turo
baki sai kace 'yar yarinya.
To ai na sha jin a ana
cewa so daya ne tak, ya cehaka ne, ta ce "To
tsakanin ni da Ummi wa ke keyi wa?
Da sauri ya
ce ke, ta ce Allah?Ya sake tausasa murya, haba
Bishira ya ki ke wannan zancen kema kin sani,
kuma don Allah na roki ki in muna tare ki daina
min zancen Ummi, ke kadai ce za6i na.
Bishira
taji dadin wannan kalamai, don haka sukaci
namansu suka kwanta, ya bukace ta a nan masai
da ta ce kaje gurin Ummin mana.
Ya ce, "Na ce
in muna tare bana son kina min zancenta.
Sai dai
in kina son ci gaba da horon daki ke min ne.
Haba Bishira, ko tausayina bakya yi?An fi wata
uku kina haramta min halas dina.
Kullum sai dai
ina azumi sai ka ce gwauro?
Yajawota jikinshi, ya
rungume da kyar dai ya samu yadan rage
matsala, sai dai ita ma ya lura tayi missing
dinsa.
Suna kwance har kusan sha daya saura
tuni ita tayi bacci, shi kam daman so yake tayi
bacci yakira Ummi.
Ya mike yaje yayo wanka
sannan ya nufi dakinshi.
Yaja katifarshi ya kai
dakin, sannan ya kwanta akai, ya kira Ummi
lokacin bacci ya soma figarta.
Ringing din ne ya
farkar da ita, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta
daga, kafin ta amsa sallamarshi sai da tayi wata
doguwar hamma.Ya ce, "Ke baccin ki ma ki ke
alhalin na ce zan kira ko?
Ta ce, "Amma ka san
bacci ba ya jira in ya zo,ni kuma ba zan iya yiwa
bacci gardama ba".
Ya ceto sarkin iya zance, yayi
nufin zolayar ta.
Yanzun dai na soma tunanin kin
soma sona, gabanta ya fafi, sam bata son ya
gano hakan yanzu.
Tafi son sai lokacin da shima
ya soma sonta.
Ya katse mata tunani, hasashe
na haka ne?
Ta ce, ko kusa, mene hujjarka da
fadin haka?
Ya gyara kwanciya.
Na farko naga
ana ta kishina, sannan tun da a kadaura aure da
ni sai ciwo ya kame kansa, kuma nalura kina ta
zumdin tarewa a gidana.Ya saki 'yar dariya,
yasan ya cika mata ciki da takaici, shiru tayi
nazari take wacce amsa zata bashi, ko dai wayar
zata kashe?
Tamkar ya shiga zuciyarta, sai ya
ce.... 41 Tamkar ya shiga zuciyarta sai ya ce,
"Koda wasakada a kashe waya.
Ranta ya sake
6aci, ta ce Ya Abba ka tafka kuskure da kayi
zaton ina sonka,sam ni bana wani kishinka.
In
don ka ce wayar matarka ce na ce ka rike abinka,
sanin kanka ne ba ma shiri da matarka, kuma duk
abinda ka ce nata ne dole na guje shidon ba zan
dauki wulakanci ba.
Batun ciwo kuma daka ce
tunda aka daura mana aure ka neme shi ka rasa
dama bani na dora makaina ba, kaima ina naka
hawan jinin ya tafi?