Sashe 24
Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya yi
murmushi, to shi kenan Umma da safe kafin na
fita zan nemo masu aiki ina da fenti da siminti
sai ayi 'yar kwaskwarima shi ke nan.
Dama ga
kudi nan da Mahaifin Bishira ya bani, wai dama
ya yi min alkawarin biya min sadaki. . 59...
Umma ta ce, "Yanzun Alhaji ya gama bani labari,
Mahaifin yarinyar nan mutumin kwarai ne, don
Allah Abba ka rike yarinyar nan ko don darajar
mahaifinta.
Ummi ta ta6a baki, kishi ya motsa.
Abba ya ce "In sha Allahu Umma nima abinda
nike dubawa kenan, ni ke hakuri da ita.
Ta ci
gaba da cewa, Sannan kada kaga Ummi yar
uwarka ce ka ce zaka fifitata, sam ba zan yarda
da haka ba.
Kayi adalci a tsakaninsu ka dinga
addu'a Allah ya hada maka kansu.
Ya ce, "In
Allah ya yarda Umma zan kula.
Ta ce, "To maza
ka tashi ka tafi gurin iyalinka.
Sam bai ma dace
ka fito ba, kamata ya yi a ce ka zauna gida ka
kara ba matarka baki, ya cee To Umma.
Ta mike
tana cewa, tashi maza.
Ya mike yana kallon
Ummi, yayin da ita kuma ta juya fuskarta cike da
6acin rai.
Ya ce, Ummi ki fa kunna in an kashe
injin?
Sam ba ta tanka ba don haushi, sai da ya
tafi sannan Umma ta dubi Ummi.
Ki tashi ki
kwanta don gobe ki tashi da wuri, kiyi duk shirin
da ya dace saboda babu daga kafa a tarewarki
gobe.
Ki ta fasha-fishenki ba zamu kuma yarda
da kalace-kalacen ciwonki ba, ta tafi abinta.
A
zaton Umma, Ummi tana fushin ba zata tare ba
ne, ita ko haushinta korar mata miji da Umma
tayi ya tafi gurin kishiyarta.
Koda ta kulle kofar
ba ta shiga uwar dakin ba, nan kan doguwar
kujeta ta mike abinta.
Jira ta ke a kashe Injin ta
kunna waya.
Abba ko kafin ya isa gida sai da ya
fita titi ya fanshi kaji guda biyu da madara mai
tsafta.I novels / ZURFIN CIKI book 3 part 8
ZURFIN CIKI book 3 part 8
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:37
Jira ta ke a kashe Injin ta kunna waya.
Abba ko
kafin ya isa gida sai da ya fita titi ya fanshi kaji
guda biyu da madara mai tsafta. 60...Sai dai
yana shiga gidan ya iske mahaifiyarshi da matar
tashi suna ta zage- zage.
Ya nufi gurinsu, Sahura
ta ce, Sai yanzun suka barka ka taho?
Ya ce,
"Umma dama ban dade da zuwa ba".
Ta ce, "Ina
ta aiken kazo ina nemanka shi ne ka 'ki zuwa
saboda ka maida ni 'yar iska ko?
Ya ce, A'a
Umma ba a fada min ba.
Sannan aiki ne yasha
kaina...
Ta ce, "Rufe min baki, ai baka daga kafa
da zuwa gun Suwaiba.
To saurare ni da kyau ka
ji, nazo ne in fada maka cewa ka rubuta saki ka
ba wannan 'yar iskar yarinyar.
Ya ce, Kiyi hakuri
Umma, ki bari sai a hankali.
Bishira ta ce, Umma
yana sonta fa, jin ku kawai nake.
Maganar Bashir
gaskiya ce da ya ce da shi a ka shirya hakan.
Umman Bashir ta ce, "Dama Abba kaima son
Ummi ka ke yi?
Ya ce, Umma ba zan ki Ummi ba,
in kun yi la'akari da kaunar da iyayenta suke
nuna min.
Amman wallahi ban san komai game
da auranmu ba, ta ce kana nufin kan dole a ka
daura muku aure ba don kana sonta ba?
Abba ya
yi dan jim, ta ce kai nake sauraro, don ta tafi sai
ya ce kusan haka dinne, itama kuma ba sona take
ba.
Umma ta ce, Ina ruwana da bata sonka, in
bata so iyayenta ai suna so.
Ni dai bukatata
yanzun kada ka bari ta tare, sannan ko kusa kada
taga fuska a gurinka. 33. 61...
Umma ta ce, "Ina
ruwana da bata sonka, in bata so iyayenta ai
suna so.
Ni dai bukatata yanzu kada ka bari ta
tare, sannan ko kusa kada taga fuska a gurinka".
Ya dan yi shiru yana tunanin wannan irin lamari a
zuciyarshi ya ce, bari kawai in lalla6ata, zan yi
yanda ki ka ce sai dai kuma in su Alhaji suka sa
kawo ta ni ba zan iya ja da su ba.
Sannann ke
kanki bana so a ce ke ki ka sa ni in ma Ummi
rashin mutunci, amma ki bar ni da ita in har ta
yarda ta tare a nan gidan.
Bishira ta ce, "Tab, ba
ko zata tare a nan gidan ba".
Umma ta ce "A'a ki
bari in sun matsa ta tare a nan din ta tare, gara
suna kusa muna kallon irin zaman da za su yi.
Can gefe ba sai su rinjaye shi ba".
Bishira ta ce,
"Umma na tsani shegiyar yarinyar nan ne, bana
son in ganta ko cikin mafarkina, bare a zahiri".
Sahura ta ce, "Bishira na ce ki nutsu ki bar komai
a hannuna, in ma zan hada da Bokaye ne ba
Malamai ba in sha Allahu sai kin dara a gidan
nan.
Ta ce, "To Umma, Sahura ta ce, Yauwa ke
dai ki zuba ido, Abba dai yana tsaye yana
kallonsu.
Sai lokacin yayi magana, Umma dare fa
yayi, ta ce to muga ledar hannunka, ya mika
mata.
Ta buda ta gani, "A'a kaza?
To ku zuba
min nawa".
Ya mika wa Bishira, Ki dibarwa
Umma.
Ya nufi dakinsa yana jin sallamarta tana
fadin ta wuce, ya fito ya ce "To Umma sai da
safe, ya rufe gidan ya koma dakinsa.
Da ya shigo
gidan ne da niyyar lallashin Bishira, amma yanda
abubuwan suka zama sai ya ji ba ma ya son
ganin Bishiran.
Zantukan Bishiran da na
Mahaifiyarshi sun saka shi cikin tunani, lamo ya
kwanta a kan katifa yana ta harsaso irin zaman
da za a yi a gidan.
Anya kuwa ba zai kama wa
Ummi haya ba?
Cak!
Hasken wutar dakin ya
dauke tare da tsayawar Injin.
A fili ya futa, Mai
ya kare kenan, sai da ya yi shirin bacci ya
kwanta tare da manne filo a kirjinshi, sannan ya
dauko wayarshi ya kira layin da ya hada cikin
sabuwar wayar da ya ba Ummi. 62..
Gabanta ne
ya fadi, lokacin da taga lambar Ya Abba suna
rawa a fuskar wayar, ta haddace lambobinshi tun
shekarun baya.
A fili ta ce, kenan ma ya hada
wayar ba yau ya soma hada ta ba, ta sake yin
lamo a kan gado tare da janyo filo ta manna a
kirjinta.
Ta daga wayar lokacin tana daf da
tsinkikewa, can cikin makoshinta tayi sallama.
Ya
amsa, tsigar jikinsa a tashe sakamon jin muryarta
tana ratsa jikinshi, ya ce "Ummi, ta ce Na'am Ya
Abba.
Ya ce, "Kina son ki tare goben?
Ta lumshe
ido, ba ni da za6i Ya Abba, duk yanda ku ka ce.
Dadi ya cika zuciyarshi.
To shi kenan ki tare
goben, zan yi parking tun Asubahi sai in sa mai
fenti yayi kafin in tafi aiki.
Ta ce, "Ba an ce in
mutum ya yi aure ana ba shi hutu ba?
Ya yi 'yar
dariya, "To ni ba ki ga yanda auren nawwa yazo
daga sama ba?
Amma duk da haka in na nemi
hutun za a bani, ta ce kayi aikin kama kawai ba
sai ka nemi hutu ba..
Ya katseta, "Don ba a sona
shi yasa ba a damu na amshi hutu ba?
Ta ce,
"Ba nufina kenan ba, naga kana matukar son
aikinka ne".
Ya yi dan murmushi "Kin dai
wayance kawai, to yanzun haka zaki tare babu ko
dan kunshi bare gyaran kai irin na Amare?
Koda
yake ba aure so ba ne.
Cikin muryar shagwa6a ta
ce, "Ya Abba ka daina, ya ce me zan daina?
Kana
cewa bana sona, ai kai ma ba ka sona...
Ya dan
yi shiru, yanda ta ke shagwa6ar ne ta tsuma shi.
Ya ce, ok, to goben sai kije ki gyaranki ko? ta ce,
"Umma ba za ta bari in fita ba, amma me yin
fulawa za ta iya ta mini".
Ya ce, "To ina ne a ke
gyaran gashin?
Ta ce, "Cikin gari ne, ya ce kin
san gurin?
Ta ce, "Eh, amma ban ta6a yi ba, ya
ce to ki bari zan shigo gidan kafin na tafi aiki zan
ce Umma ta bar ki, ta ce "To." Suka dan yi shiru.
Can ya katse shirun da cewa, "Me ki ke tunani?"
"Yaushe?" "Yanzun." Ta dan musukuta, "Ina
tunanin yanda abubuwan za su kasance gobe.
Yanda har za'a yi fenti, sannan a jire kuma in tare
duk a gobe".
Ya ce "Duk mai sauki ne, ni kuma
kin san tunanin da nake yi yanzun?
Ta ce, "A'a,
ya ce gobe kamar yanzun muna tare... da sauri ta
katse wayar, me Ya Abba ke son fada?
Ta kashe
wayar sannan ta kudundune.
Ita ma yanzun ya
jona mata wannan tunanin, a fili ta furta gobe
kamar yanzun me ya ke faruwa?
Shi kuwa sai ya
ji haushin kansa sakamakon furucin da ya yi har
ta yanke wayar, wani gefen kuma sai ya ga kila
don bata sonshi ne shi yasa har ta ji haushin
furucin nashi.
Kila ma yanzun tana can tana kuka
in ta tuna gobe tana gidansa, dare ya tsala amma
ya kasa bacci, don haka sai ya mike yayo alwala.
Sallah ya shiga don kara nuna godiyarsa ga Allah
da ya bashi Ummi tare da rokon Allah ya kimsa
mata sonshi, daga karshe ya roki hadin kan
matansa. 34 63..Yana wanka da safe ya jiyo
muryar mum dinsa harta zo gdn, a zuciyarshi
yace innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yana fitowa
tace wurinka nazo, Bashir yazo ya fada min cewa
yau za'a kawo fitsararriyar yarinyar nan ko?
Abba
cikin damuwa yace umma nima bansani ba, tace
munafiki kasani, bari kaji ko an kawota ko
magana bance ta hadaku da ita ba, kai in ma
kaje girin munafukan iyayen nan nata su ka ce
yau zata tare kace saika shirya.
Bishira tace
umma bazan yarda ta tare ba, bai sai min komai
ba, ya kalli Bishira to itama na sai mata wani
abun ne?
Sahura tace to ina ruwan wani da baka
sai mata ba?