← Book details Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 28

Sashe 19

Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yunkura zata tashi,
Ya abba zan tashi, ya tayar da ita zaune.

"Likitan
ya ce Alhamdulillah, Abba ya kalli likitan, ba
matsala kenan?

Ya ce, Ina zaton haka insha
Allah, Abba ya ce "Alhamdulillahi, ya jinginata da
jikinshi, sannu Ummina. 41....

Alhaji ya shigo
yana cewa, "Ina Abba ne?" ya ganta zaune a'a ta
farka ne? ya kama hannunta sannu uwata.

Ta
kalle shi.

"Ina Ummata?" ya ce, "Bari in kira miki
ita".

Yaje ya sanar da su, sun shigo da murna.

Sahabi ya iso gaban gadon.

"Sannu Ummi".

Ta
kalle shi sai ta kwantar da kanta a kafadar Abba,
"Ya Abba ina son in wanke bakina".

Ya ce, "To
bari in siyo miki Maclean din".

Ta ce, "A'a kada
kaje".

Ya gyara zama "To shi kenan." Umma ta
ce, "Me ta ke so?" Abba ya ce "Baki zata wanke".

Umma ta ce "Ai nazo mata da maclean da
burushin nata, don nasan ita gwanar wanke baki
ce".

Nurse ta kawo wani dan kwano na silba
Ummi ta wanke baki da taimakon Abba.

Likitan
ya ce, a bata tea mara zafi sosai, sannan a bata
magani.

Takaici dan'kam a zuciyar Sahabi, irin
wannan shigewa da Abba ke matar da zai aura
tayi yawa.

Kai shi fa wannan Yaya Abban bai
masa ba ma, don yana daure mishi fuska ko
gaida shi yayi d kyar yake amsawa.

Shi fa tun
ranar da a ka ce mishi Ummi ba cikinsu daya da
Abba ba ya ji ya tsane shi.

Umma ta ce, "Abba
an kira Isha'i.

Sahabi kaje kai ma ka huta yaran
nan tun tuni ya ke nan".

Abba ya kalle shi, "Ya
kamata ka tafi haka ko?" ya kalli Ummi sannan
ya dan rusuna "Sannu Ummi".

Ta ce, "Yauwa"
"Innata ta ce in gaida ki da jiki, ni zan tafi sai da
safe.

Me zan kawo miki?" Abba ya dube shi a
kule., "Don Allah Malam kaje ba za ta iya cin
wani abu yanzun ba".

Umma ta ce, "Abba".

Ya
kale ta, sai ta girgiza mishi kai alamun ya bari.

Sahabi jiki a sanyaye ya fice tare da cewa "Umma
sai da safe".

Ta ce, "To Sahabi, ka gaida Innar
taka".

Da ya fita ta kalli Abba "Wannan ba
halinka ba ne kada in kuma gani".

Ya ce "To
Umma". 23.

Su Alhaji sun yanke shawarar daga
auran Ummi a darua na Fati kawai, ita sati biyu
masu zuwa sannan ta murmure sai a daura nata.

Gidan su Sahabi sun ji haushi musamman
Innarshi, sun kashe dan abinda suka tattala don
bikin amma gashi an daga, su kam da an daura
auren in ta murmure sai a yi bikin.

Sahabi ya
shigo gidan ranshi a 6ace, ya kalli Mahaifiyarshi,
"Inna wai sun ki a dauram?" Ta ce, "Sun ki, dama
ai gaddamar dan yau ce.

Ban da shegiyar
gaddama ga 'ya can da a ka baka a daura ka
gaddame, to yanzun ina ranar abin da aka mana?

Gida duk dangi sun cika amma wai a daga biki,
mu kuma karamin karfi ne da mu, bare mu ce nan
da sati biyu zamu sake kashe kudi".

Sahabi ya
tuna abinda Abba ya masa a asibiti, shi ne dalilin
da bai sake zuwa asibitin ba, yaja tsaki.

"Kin san
Allah Inna ni kaina sai yanzun nake jin haushin
kaina da na ki amincewa da Badariyya.

Mu zuba
musu idanu in za su sake kawo mana cikas sai
kawai in koma gurin Badariyya." Inna ta ce, "In
da tun jiya kamin zancan nan da tuni yau ba a
fasa daura auranka ba an ma da Badariyya".

Ya
ce, "Kiyi hakuri Inna mu ga nufin su". * 42...

An
sha shagalin bikin Fati kuma an kaita gidanta.

Ummi jiki Alhamdulillah, Abba kullum in zai je aiki
sai ya biya.

Haka nan in ya dawo gida wanka
kawai zai yi ya tafi, wataran sai goma ko sha
daya.

Abokanshi suna ta zuba duba Ummi, ita
kanta da lokacin zuwanshi ya karato ta dinga
kallon agogo ke nan tana kallon kofa.

A zaman
asibitin nan Umma ta gama karantar su tsaf.,
matukar son juna suke yi, sai dai taji takaicin da
sai yanzun sonsu ga juna ya bayyana.

Lokacin da
ya kasance an riga an bada Ummi ga wani sai
dai ta ci gaba da addu'a Allah yayi za6i na
alkairi.

Bashir yayi murna da fasa auran Ummi,
dama a fasa gaba daya.

Yana fitowa dakinshi ya
ji Ummarsu tana cewa, "Kin san Allah Tasalla,
uwar yaron nan da zai auri Ummi zata ga bakin
ciki, don mallake mata da za su yi.

Tana ji tana
gani sai yanda suka yi da shi.

Kuma ba yanda
zata yi sai Allah ya isa".

Tasalla ta ce "Ban da
halin mutanan yanzun ba da sai na fada mata ba.

Kin san makotanmu ne ta baya, gashi su ba karfi
ba.

Sahabin ne fa ke rike da gidan, kin san shine
Babban a gidan".

Sahura ta ce, "Don Allah Tasalla
ki taimaka ki fada musu, don ko in har aka yi
auran nan in suna cin abinci sau uku ne a rana,
to za su koma dau daya".

Tasalla ta ce "Ai ko
zanje".

Tana fita Bashir ya dawo kusa da
Ummarsu ya ce, "Umma dama da kanki ki ka je,
saboda za su fi yarda tunda sun ga ke kina da
danganta da gidan".

Ta ce, "To in Babanku ya ji
fa?" Ya ce "Umma ai in kin fada musu ai kwa6ar
su za ki yi, sannan kada kije a kan lokaci, kije ana
gobe daurin auren".

Ta ce, "Saboda me?" Ya ce,
"Saboda su Alhaji Babban suji haushin rashin
fada musu da wuri".

Ta ce, "Haka za a yi, kuma
in an fasa Malamai zan shiga don a hanata auran
ma kwata-kwata".

Ya ce, "Kada kije wurin
Malamai yanzun tukun".

Ta ce.

"Ai dama sai an
natsa". * Abba ya fito cikin suit bakake, yayi kyau
matuka hatta takalminshi sawu ciki baki ne,
tamkar wani black America.

Igiyar wuyan ta
zauna tsam, sai kamshi yake.

Dakin Bishira ya
nufa ya daga labule, ta dago ta kalle shi yayi
matukar birgeta.

Tana alfahari da shi matsayin
mijinta, ya ce "Kin shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya
ce, "A'a, jiya fa na sanar da ke ki shirya da wuri
zamu je asibiti ki gaida Ummi".

Ta watso mishi
wani kallo uku saura kwata, tare da cewa "Ko
garin nan ba a sanyi ba zan fita gaida wata can
Ummi ba bare da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta
mike tsaye "Ciwo bai kai mutuwa ba, da mutuwa
ya yi tazo ta min gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke
Abba, da yake sarkin dankara magana ne, sai ya
ce "To ita ta kashe shi da zata miki gaisuwa?"
Ta kule da bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai
kasan ni na dora mata ciwon, don haka dole in je
gaisheta." Ya ja tsaki tare da cewa, ballahaza
wadda bata san mutuncin mijin auranta ba".

Ya
yakice labulen ya wuce yana jiyo ta tana cewa,
"Ba dai za ni ba ko me za ka ce".

Ranshi a 6ace
ya isa asibitin, Ummi na zaune kan gado ta kosa
Abbanta yazo, ko karyawa ta kasa yi, yana
sallama suka hada ido.

Nan ta ke ya ji ya manta
da duk wani bakin ciki da ya taho da shi, ya isa
bakin gadon fuskarshi dauke da murmushi.

Itama
murmushin take yi, ya ce.

"Ummi ya ya jikin?" Ta
ce "da sauki".

Ya Abba kayi kyau sai ka ce
Manajan Banki".

Umma ta saka dariya, shi ma ya
yi 'yar dariya, "To ko bankin zan koma?" Ta ce,
"A'a kafi kyau da dan jaridanka Ya Abba, balle in
kana turancinn nan a labarai".

Ya lakuci
kumatunta "Ko kwanwata?" Ya juya ya gaida
Umma, Umma ta ce "Ka zo katafi gurin aikinka
fa".

Ya ce, "Umma sai sha daya yau zanje gurin
aiki".

Ta ce, "Ni na ma kosa a sallame mu".

Abba
ya ce "Ai kila a sallame ku yau.

Likitan ya shigo
ne?" Suka ce "A'a.

Suna cikin karyawa Likita ya
shigo ya same su, ya kuma kafa mata dokokin
daina tunani, daina shiga duk wani abu da zai sa
ta cikin damuwa.

Rage shan gishiri tare da
samun isassen bacci, ya kuma gargadi su Umma
su dinga nisantar 6acin
Home / ZURFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 6
ZURFIN CIKI book 3 part 6
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:31
Rage shan gishiri tare da samun isassen bacci, ya
kuma gargadi su Umma su dinga nisantar 6acin
ranta. 26. 43...

ABBA Ya kwaso su ya maida su
gida, cikin satin Ummi ta murmure.

Sahabi na
zuwa sai dai da sun gaisa yake tafiya.

Mahaifiyyarshi ma tazo, amma Bishira da Sahura
ko le'ke, Bashir ma yana ta sintirin zuwa.

Ganin
haka Alhaji ya ci gaba da shirin biki, mutan kauye
dai dama an ce kada su dawo, Ummi dai bata
maida hankali ga komai ba.

Ta ce ma Umma zata
je gidan Fati, Umma ta ce To sai ki je gurin
Sahura ta kwatanta miki.

Abba ya same su suna
zancen, don haka ya ce ta shirya zai kaita ya
ajiyeta in ya tashi aiki sai yaje ya daukota.

Yanda
ta samu Fati da Angonta ana ta ji da juna abin
ya tsokanota, sai dai ta kasa ganin dacewar
soyayyar da Sahabi.

Da mijin Fati ya fita Ummi ta
ce, "Oh, Fati cikin kwana takwas dubi yanda ki ka
yi kyau".

Fati ta ce, "Amma ban rame ba?" Ummi
ta ce "Eh to, kin dan rairaye".

Fati ta ce, "Kai ai
dole, gaskiya ina koduwa, wallahi ba ya barina in
huta".

Ummi ta ce, "Da me?" Fati ta ce, "Dallacan
ki gane mana".

Ummi ta ce, "Wai da me?

Allah
ban gane ba".

Fati ta ce, "Ai ke sokuwa ce, gurin
kwanciya mana.

Ummarmu ta samu ta dirka min
kayan sha na mata, gashi nan nazo ina ta shan
wuya".

Ummi ta zaro ido, "Da wahala ne?" Fati ta
ce, "Tab, ai kin kusa kema za ki ji".

Tsoro ya cika
Ummi.

Ta ce, "Zan ce ma Umma ni dai kada ta
bani wannan kayan matan".
Chapter 19 · 0% Book details