← Book details Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 28

Sashe 17

Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta ce ni ko har addu'o'i zuwa girki
kala- kala ina koyo, Umma ba rannan nayi
dafadukan kwakwa ku ka ce ya yi dai ba?" Ta ce,
"To ki dai dinga daukan na kwarai kina yarda na
banza, Abba ya ce in haka ne d agaske zan samu
lokaci in zo ki karanta min in ji, ta ce "To." 27.....

Umma ta yi 'yar dariya ta ce, "Sai ka ce ba ka da
aikin yi?

Ya ce, "Allah Umma da gaske nake yi
don in ji wacce irin koyarwa suke yi, marubutan
ko ko sai shirme?" Kiran sallar Isha'i ne yasa
Abba mikewa, ita kuma Umma ta tafi kicin don
shiryawa su Alhaji Abinci.

Ummi kam sun bar ta
cikin takaicin tafiyar Abba don dai bata gundura
da shi. * Alhaji Ya kalli Umma, wai yau bikin
yaran nan saura wata nawa?

Ta ce, "Wata ko
kwana dai?" Yau saura kwana talatin da shida,
ban ga kana motsi ba?

Alhaji bikin nan zai
mamaye mu, ya ce "Yanzun ya za a yi da batun
kaya?" Ta ce, "Ni da cewa nayi ga Abba sai yaje
ko kuje ku za6a musu kaya masu kyau a siya,
kada a ba kafintoci in ba a yi sa'a ba har lokacin
yayi ba a gama ba".

Ya ce, "To zan sa shi ya tafi
da su kawai su za6a".

Ta ce, "Sai kayan girki na
dai sayi tukwane da risho, sai kuloli".

Ya ce, "Duk
da haka uwata zan sa ta za6i wasu kayan."
Umma tayi dariya tare da cewa, "Allah ya kara
budi, nan dai suka yi ta lissafin kudi.

Da safe
Alhaji ya kira Abba a waya ya sanar da shi cewa
ya dauki su Ummi suje su za6i irin kayan da suke
so, duk da cewa zancan ya doki zuciyarshi amma
ya ce "To." insha Allah zamu je, suka yi sallama.

Sam baya son ya ji batun auran su Ummi, baya
son rasata, kuma yana ji a jikinshi cewa zai same
ta. ** ** 28.....Yammacin ranar Asabar La'asar
lis garin yayi dan sanyi Abba ya nufi gidansu don
daukan su Ummi zuwa kasuwa.

Jikinshi sanye da
farin yadi mai shara-shara, har ana iya hango
fara kar din singiletin da ke ciki ta manne a
jikinshi.

Kamshin turarenshi ya cika dakin Umma
wanda ba shiga yayi ba daga bakin kofa suka
gaisa.

Ya ce, "Ummi su fito don Ummi ce ke
shiryawa tuni Fati ta fito, ya matsa kofar
Tsohuwa suka gaisa, sannan ya ce "Umma sai
mun dawo.

Ya nufi waje yana fadin su Ummi su
mishi sauri.

Sun fito za su duru a baya Abba ya
ce Ummi ta dawo nan gaba, ta zauna ranta
dagule don ita bata bukatar wani za6i tunda ba
wanda take so zata aura ba.

Haka nan ta
fuskanci Abba yau yana cikin wani irin yanayi,
kila daga gida aka 6ato masa rai, nata tunanin
kenan.

Shi kam takaicin zuwa za6on kayan ke
damunsa, ya kalli wayarsa da ke ruri ya daga,
Salis ya ce kana ina ne?

Ya ce ina nan
unguwarmu zan kai kannena ne za su za6i kayan
daki.

Ya ce, "Ta ina zaku bi?

Abba ya ce kai kana
ina ne?

Ya ce ina nan kusa da asibitin Malam,
bari in jira ka a jikin gidan man nan, Abba ya ce
"To." Salis ya kalli yarinyar da Abba ya ce Ummi
koma baya ya ce, "'Yammata sannunku, suka
gaishe shi ya yi murmushi ke ce Ummi?" Ta ce,
"Eh, ya ce ya su Umma?" Ta ce lafiya lau, ya
maida dubansi ga Abba wanda ke tuki cikin
nutsuwa ya ce, "Idris akan batun yarinyar nan ne
don Allah ka daure muje gidansu yau".

Gaban
Ummi ya fadi.

Abba ya ce, "Don Allah Salis ka
bar batun yarinyar nan, kai dai kasan halin da
nake ciki game da wata".

Salis ya ce, "Me yasa
ka amsa kana sonta, kuma har kana daga waya
duk lokacin da ta kira ka?" Abba ya ce, "Shike
nan za mu je da yamma tunda wancan na rasa
madafa".

Salis ya ce kuma fa da hakan zai fi
maka.

Ummi gashin jikinta duk ya mike, suna fitar
da zufa lumshi ido tayi luf a kan kujera ta kwantar
da kai, Salis ya waiwaya ya dubeta, yaya dai?

Ta
yi dan yake, "Ba komai." . 29....

Sun je gurin
kujeru da gadaje, Fati tayi ta ruwan ido yayin da
Ummi ta koma ta jingina a kujerar da ta zauna.

Abba ya dube ta.

"Ke wanne ki ka za6a?

Ita ta ce
wancan farin".

Ummi ta yatsina fuska, "Nifa bani
da za6i, duk wanda ku ka ga yayi".

Salis ya ce, "
Idris yarinyar nan ina zaton tana sonka, naga
tunda muka yi maganar zuwa gurin wata ta
canza yanayi.

Abba ya ce, "Kyaleta ba wani ya
dubeta ba, ke Ummi tashi ki za6a mu ji
farashinsu, sauri muke.

Ta ce, "Ya Abba cikina ke
ciwo, ka za6ar min don Allah".

Ya ce, "Salis ita
ma a bata farin kawai ko?

Salis ya ce, "A daukar
mata mai ruwan madaran, mai shagon ya ce sun
fi tsada, Abba ya ce ka daukar mata su.

Sun
koma gefen kujeru nan fa Abba ya ce dole sai ta
za6a, nan ma wanda ta za6a a ka ce sun fi na
Fati tsada, suka ji farashinsu su sannan ya ba da
wani abu suka tafi.

Ya sauke su a gida, Fati sai
ba Umma labari take yayinda Ummi ta shiga
kuka, Umma ta ce ke kuma lafiya ki ke kuka?

Ummi ta ce "Umma ni bana son in yi auren nan,
bana son in bar gida.

Fati ta ce, "Shi yasa naga
tun a gurin shagon kina ta 6acin rai?

Umma ta
ce, "Shirmen banza da wofi, sai ki tayi.

Ta fice,
Fati ta ce Ummi ke kin cika son damuwa.

Menene
na damuwa?

Kila ma kina nan unguwar.ovels / ZURFIN CIKI book 3 part 5
ZURFIN CIKI book 3 part 5
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:29
ummi sannu da zuwanku, nan sukayi masa
gaisuwa yace ummi kaisu ciki. 36..

Zainab tace a
ranta wato ma ummi yafara gani, a fallon su
umma suke don nan ta fara kai su, tace umma
wanan ce zainab, wannan kuma matar abokinshi
salis, umma tayi masu sannu da zuwa sanna tace
ummi ta kaisu dakin bishira, sun shiga sun yi
mata gaisuwa, bishira tace ke ko gaisuwa baki zo
min ba koda yake bai dame ki ba, ummi tace
nima ana ta zuwa min gaisuwan ne a gd, duk yan
dakin suka kalli ummi, sahura tace ke asuwa?

Bishira tace ita a mahaifiyar shi, ummi tace
zainab kuzo muje, tun daga lkcn zainab tasa a
ranta akwai matsala a wanan familyn din, basu
jima ba suka yi sallama, inda ummi ta rakasu
daga can itama ta wice gd, suna shiga soro
shima ya shigo yace badai tafiya zakuyi ba?

Ya
kalli ummi sun sha ruwa ma kuwa?ummi wadda
dama idanunta na kanshi ta amsa mishi da
idanu.

Yace yama akayi kuka gane gdn zainab
tace yaya salis ne yakawo mu, ya kalli matar
salis yace madam mun gode fa,tace bakomai
Allah ya jianshi, sam ummi batasan lokacin da
furucin ya fito mata ba, sai dai taji tace ya abba
duk ka rame baka cin abinci ko?

Shi kanshi yayi
mamaki don haka ya ya tsura mata ido, sai taji
kunya ta rufee ta saita kau da kanta daga
kanshi,don kada su zargeta.

Kayi hkr naji wani
malami yace duk wanda yaranshi kananan uku
suka rasu to zasu ceceshi ranar gobe.

Kaga ynz
kafara da daya,matar salis tace ai koma dayane
indai kayi hkr kayi tawakkali,ummi ta kalle shi
tace to kaji ma,yace ummi nifa tuni na
dangana,ta sake tausasa murya to meyasa baka
cin abinci?

Ya tausasa murya wadda dama take a
dusashe yace ummi inaci,tace ya abba baka fa
yin karya,yace to yau zanzo inci a gabanki, ya
kalli matar salis wadda ke murmushi, in naci a
gabanta saita yarda ko?

Tace tabbas! 37..Zainab
wadda takaici ya cikata tace da matar salis anty
nifa natafi, abba ya dubeta zainabu nagode ki
gaida su mama sai nazo,batare da ta tsaya ba
tace to, ummi ta musu sallama itama ta tafi gd.

Zainab ta dubi matar Salis bayan tafiyar Ummi,
ta ce, "Duk da son da na ke ma Idris din nan ba
zan aure shi ba".

Matar Salis ta ce dalili?

Zainab
ta ce, "Bana zaton ko matarshi ta gida da ya
aura ya aje yana sonta irin yanda yake son Umiin
nan".

Abin nasu yayi yawa.

Dubi yanda ya manta
da ni, ta ita kawai yake yi.

Matar Salis ta ce, kin
ji ki da wani shirme, ita da zata yi aure?" Zainab
ta ce, "Abinda ke tausar zuciyata ke nan in na
tuna cewa zata yi aure, amma kai naga ji ba zan
iya ba, haka suka tafi tana ta bai wa yarta
labarin yanda Abba ke ji da Ummi.

Kamar yadda
Abba ya ce zai zo cin abinci da dare yazo, Ummi
ta saka shi gaba wai sai ya cinye wake da
alayyaho da kifin da ta dafa masa.

Da kyar ya
cinye plate din farko ya ce "Ummi na koshi kin ji?

Ta daure fuska tana kallonshi, shi ma ita yake
kallo yana dan murmushi.

Ya ce, "Ina ma a ce
tun da da haka muka yi sabo, Ummin cikin
kwanakin nan kin lura cewa muna shiri".

Ta
harare shi, "Kana zaton na manta da irin dukan
da ka yi ta min ne?

Shi ma ya harare ta tare da
kwaikwayon muryarta.

"Kina tsammanin zan
manta da irin tsokanar fadanki ne?

Ko zan manta
da Suhailar Kaduna...?" Kafin ya rufe baki tuni ta
yi uwar daka da gudu, shi kam dariya yayi ta yi
yana cewa ki zo mana Ummi, kin fitowa tayi har
sai da ya bar gidan.

Duk lokacin da suka kasance
tare kowannan su yana mantawa yana da wata
matsala.

Saura kwana uku daurin auransu,
lokacin dangi sun soma zuwa, musamman 'yan
Zamfara.

Ummi da Abba hankalinsu ya kai
kololuwa gurin tashi.

Ranar ya ziyarci Zainab wai
ko zai samu 'yar nutsuwa.
Chapter 17 · 0% Book details