← Book details Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 28

Sashe 13

Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bashir bai daina cin
alwashin sai ya auri Ummi ba, dn haka kullum
cikin aiken kiranta yake.

Ban da haka ma ya
maida hnkl kan sana'arshi tunda ubansa ya mishi
gorin wa zai ba shi mata ya ki tsayawa sana'a
nashi ganin in ya rike sana'a r za a ba shi.

Abba
kuwa ya ji ya yi ma gidan wai don ya goge Ummi
a ranshi.

Anya "ZURFIN CIKIN nan zai kai su? .

Sai mu hadu a littafi na Uku don jin yadda za a
kare.

ZURFIN CIKI book 3 part 1
ZURFIN CIKI book 3 part 1
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:21
Na Halima Abdullahi K/Mashi 1...

Abba ya fito
cikin suit bakake, yayi kyau matuka hatta
takalminshi sawu ciki baki ne, tamkar wani black
America.

Igiyar wuyan ta zauna tsam, sai kamshi
yake.

Dakin Bishira ya nufa ya daga labule, ta
dago ta kalle shi yayi matukar birgeta.

Tana
alfahari da shi matsayin mijinta, ya ce "Kin
shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya ce, "A'a, jiya fa na
sanar da ke ki shirya da wuri zamu je asibiti ki
gaida Ummi".

Ta watso mishi wani kallo uku
saura kwata, tare da cewa "Ko garin nan ba a
sanyi ba zan fita gaida wata can Ummi ba bare
da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta mike tsaye "Ciwo
bai kai mutuwa ba, da mutuwa ya yi tazo ta min
gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke Abba, da yake
sarkin dankara magana ne, sai ya ce "To ita ta
kashe shi da zata miki gaisuwa?" Ta kule da
bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai kasan ni
na dora mata ciwon, don haka dole in je
gaisheta." Ahankali yake tukin, kira'ar Ahmed
Suleiman ce ke tashi wadda ya yi murya biyu
cikin sanyin murya.

Wayarshi d ake gefe ta soma
ruri.

Ya kali fuskar wayar, Hajiya Nina ce, don
haka ya ci gaba da tukinshi, kusan kira na bakwai
sannan ya daga.

Ta ce, "Lokacinka ne za ka iya
yin duk yanda kaso, amma kafin kazo hannuna
wacce shawara ka yanke?" ya ce, "Ta me?" Ta
ce, "Au, ka manta kenan?

To ba damuwa za ka
zo yau ne ko sai an dauko ka?" 2....

'Yar dariya
ta kufce masa, "Ki sa a dauko ni sai ka ce wani
karamin yaro?

In kin ci gaba da bibiyata za kiyi
nadamar hakan." Ta ce, "Ko kuma kai kayi ba, na
baka awa goma ka kawo kanka in ko ka 'ki, hum!

Za a kawo ka." Abba yaja tsaki "Yanda ki ke
zatona na wuce haka".

Ta ce, "Idris Aminu Idris
raina ya biya da kai, kuma dole sai na cimma
hakan, jarumtarka din nan ta sake bige ni, kasan
dalilin da yasa na ce nan da awa goma?

In ka
lissafa zai baka bakwai na yamma.

Daidai lokacin
da ake watso mana labarai ina kwadayin ina tare
da kai, lokaci guda kuma ina kallonka cikin TV
kana feso turanci, kasan ina son muryarka ga shi
ka gwanance da iya tsara turanci, sai ka ce
yarenka.

Kada in cika ka da surutu sai mun hadu
anjiman".

Ta kashe wayarta.

Abba yayi kokari ya
tsaida motar shi a gefen titi a hankali ya furta
"Allahumma ajir ni fi musibati..." ya kifa kansa a
jikin sitiyarin motar, yana tunanin wai shin ba za
ta sauya masa a halin da yake ciki ba?

Wata
zuciyar ta ce in tasan kana cikin wani halin ko?

A
haka ya isa gurin aikinsa, tunda suka shiga dakin
daukar labarai, abokanshi suka gane yana cikin
wani hali duk da bai kasance mai yawan magana
ba, amma yau ba kamar kullum ba.

Salis ne ya
kasa hakuri, don haka bayan an gama daukar
labarai da kyar sun je su yi sallar Azahar suna
zaune wata Bafulatana da ke kawo musu fura ta
kawo. 3.....

Dama shi Abba bai cika shan fura da
rana ba, yafi shanta da dare, don haka siyan
kurum yake yi.

Bayan yaje gida sai yasha, amma
ranar ya ce mata ta bar shi kawai, ta jiya ma
tana nan bai sha ba.

Da ta tafi Salis ya dube shi,
"Idris ba ka da lafiya ne?" Ya ce, "A'a me ka
gani?" Ya ce "Ba yanda ka saba ba, duk kwanakin
nan na lura kana cikin damuwa".

Abba ya dube
shi amma ai kasan nayi rashin lafiya ko?

Salis ya
ce dakata Idris kada kaga kamar na matsa maka
sai na ji cikinka, ko kusa ba haka ba ne.

Ni
mutum ne mai saurin karantar duk dan Adam din
dana zauna kusa da shi na awa daya bare kai da
na zauna da kai tsawon lokaci, muna kuma ci
gaba da zama.

Idris na fahimci kana da matukar
'ZURFIN CIKI' dalili kenan da yasa ban ta6a
damuwa da in tambaye ka matsalarka ba.

Sannan dalilin 'ZURFIN CIKIN' da naga kana da
shi ne yasa har kwanakin baya na kawo maka
matsalata da iyalina.

Alhamdulillahi ka bani
shawara kuma nayi amfani da ita, kuma naga ci
gaba, matsalolina sun ragu".

Abba yayi dan
murmushi.

"Wai kana nufin saboda ina da
'ZURFIN CIKI' ne kaga ya dace ka sanar da ni
sirrinka?" Salis ya ce "Kusan haka ne, don me
Zurfin Ciki ya iya hadiye magana, sai dai a ganina
zurfin ciki wataran zai iya fadawa halaka, ko
wata gagarumar matsala".

Abba ya dube shi,
"Wace irin halaka?

Salis ya ce, "Me zurfin ciki sai
ciwon zuciya ya kama shi yana muku-muku da
matsalarshi, wani ma har ya mutu da ita ba
wanda ya sani.

Amma in abu na cinka ka samu
wanda ka yarda da shi mai amana ka fada masa
zaka ji dan dadi".

Abba ya ce, "To kai tunda baka
da zurfin ciki, kenan bai dace ka ji matsalar ba?"
4....Salis ya tuntsire da dariya, "Ta nan ka 6ullo?

Ai dama ka sani ba ina son yabon kaina ba ne,
a'a duk surutuna nasan abinda nake fadi".

Abba
ya ce, "Salis na gode da kulawarka, matsalata ko
ka ji ta nasan shawarar da za ka bani bata wuce
ka ce in yi hakuri ba, ni kuma ba wannan ni ke
son ji ba.

Salis ba komai nake yiwa 'ZURFIN CIKI'
ba, yawanci in ina da matsala nakan tunkari
Ummata ne kuma ta warware min komai.

Saboda
na taso da wannan koyin da ta min, yanda na
shaku da ita ko su Alhajina ba mu shaku haka
ba".

Salis ya ce, "To me ya hana ka fada mata
wannan karon?" Abba ya ce, "Ba zan iya ba, sai
dai in za ka samo min mafita ban da hakuri, to in
fada maka".

Salis ya ce "In sha Allah ba za arasa
mafita ba".

Nan Abba ya bai wa Salis labarinshi
da Ummi tun farko har zuwa yau.

Salis ya
numfasa, sannan ya ce "Kaga illar 'ZURFIN CIKI'
ko?

Ummin ma taka ce amma kana nema ka
rasata, ai ba mafitar da ta wuce ka samu
Ummarka ko Alhajinka ka fada musu muradinka".

Abba ya ce, "Tabbas haka ce mafita, sai dai idan
na aikata haka abu biyu za su faru, na farko na
zubar da mutuncin Alhajina, domin babu girma,
sun ba da 'ya ba tare da wani dalili ba ya ce ya
fasa.

Sannan haramun ne neman aure cikin aure".

Salis ya ce, "Haka ne, to hakurin kawai zaka yi".

Abba ya ce "Ai mun yi ban da bada hakuri ko?"
Salis ya saki dariya, sannan ya ce "To kayi
addu'a".

Abba ya mike tare da fadin "Ka tayani
da addu'a".

Daga nan ya shiga dakin, Filin Don
Matasa na Hausa, don likkafar shirin tayi gaba
yanzu har na Hausa yana gabatarwa.

Kullum
sake kar6uwa shirin yake a gurin Jama'a.
5......UMMI Tana kwance kan doguwar kujera,
yau kwana hudu kenan bata saka Abba a idonta
ba.

Tamkar Umma ta san abinda ke ranta, sai ta
tsinkayi Umma na cewa "Yau kwana uku ne ko
hudu rabon Abba da gidan nan, sai dai ya kira mu
a waya.

Alhaji dai ya ce, yana zuwa gunsa
kasuwa".

Ummi ta ce, "Nima yanzun nake tunanin
haka".

Ta miko ma Ummi wayarta da ke gefenta.

"Lalubo min shi in ji".

Da ta soma /ringing/ sai ta
mika mata.

Ya dauka suka gaisa ta ce "Abba ko
dai na maka laifi ne?" Ya ce, "Umma me a ka yi?"
Ta ce, "Tsaf, ka dauke min kafa, wanda kullum
komai saurinka sai ka biyo".

Ya ce, "Ina nan
zuwa Ummata, kina raina duk inda nabi, harkoki
ne suka taru suka sa ni gaba".

Ta ce, "Ni kuma
sai na ke ganin kamar don ba mu dauki
shawararka ba ne ta game da karatun Ummi shi
yasa ka".

Ya ce, "Umma ba haka ba ne, zan shigo
da zarar na dawo".

Ta ce.

"To".

Sam shi batun
shi yayi ba, sai dai baya son yazo ya ga Ummi
domin da ya ganta yake neman kwanciyar
hankalinsa ya rasa na tsawon lokaci.

Amma
yanzun kalmar Salis ta karshe daya fafa masa da
za su rabu a gurin aiki ita yake tunawa.

Dafa shi
ya yi tare da cewa "Miste Man shawara ta
karshe, ka nunawa kanwarka kana sonta a fili".

Ya ce "Tab, wannan shi ne me wahalar ai,
furtawa Ummi kalmar so.

Zubar da kai kenan".

Ga shi ba sonsa take ba, duk yanda mace ke
girmamaka da zaran ka ce kana sonta shi kenan
ka zube a idonta.

Musamman in kai ke sonta ita
ba ta sonka, wata ma har da rashin kunya zata
tsula maka, a fili ya ce, "Ina, ai ba zan ta6a gigin
bari ta san ina sonta ba".

Daga kasan zuciyarshi
yaji an ce za ko ka sarata.

Sai da ya yi sallar
Isha'i sannan ya yi wanka ya saka kananan kaya,
ya fito da nufin gidan su Ummarshi.

Bishira ta
bishi da kallo, daga ganin fita zai yi ta fito da
saurinta tana cewa "Baban Walid!

Baban Walid!!."
Ya tsaya, ta dube shi "Ina za ka?" Ya ce "Gidan
su Umma".

Ta ce, "Ba wani gidansu Umma, kai
dai kurum tadi za ka je". 6....

Dariya ta su6uce
masa, sai da ya dara sannan ya ce "To in ma
tadin zan je ya za ki yi dani?".
Chapter 13 · 0% Book details