← Book details Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 28

Sashe 15

Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta mike zuwa wata durowa ta bude, dauri
uku ta dauko ta aje gaban madubi na 'yan dari
biyar-biyar sababbi dal!

Ta ce, "Wannan za ka
sha mai ne sannan kasa kati, kuma in ka kwantar
da hankalinka zan canja maka mota, zaka je
Makka. 11....

Sannan idan naga kana bin
umarnina zaka yi suna a aikin jarida fiye da duk
wani dan jarida da ka sani a kasar nan.

Kai zaka
taka duk wani matsayi da dan jarida ke takawa".
ta sake nufoshi da tausasa murya.

"In kabi yanda
nace ba kai ba sake kwana a talauci..." Ya
katseta da fadin, "In naki fa?" Ta hade rai tare da
zuba mishi ido, "Shima kallonta yake, sai a
lokacin ya ga tsufanta ya bayyana.

Ta juya mishi
baya tana 'yar tafiya, sannan ta ce "Am sorry to
say".

Ta juya ta dube shi "Za ka mutu".

Gabanshi
ya fadi, amma sai ya yi karfin hali ya ce "In na
mutu sai me?

Dama can mutuwa zan yi ko ba ki
kashe ni ba.

Kuma ni na san ba zan wuce iyakar
ajalina ba, murnata daya zaki sauke min nauyin
zunubaina".

Ta matso kusa da shi "Ka san
matasa nawa ke shiga malamai kawai don su yi
hulda da ni?

In ka dade muna hulda shi ne muyi
wata biyar, sau daya na rike saurayi har tsawon
shekara daya don yana da hankali".

A zuciyar
Abba ya ce "In fa na daka ta matar nan zan mutu
ban auri Ummi ba.

Sannan ba Allah a ranta bare
taji nasiha, yanzu bari yabi ta hikima".

Ya ce,
"Saboda me suke shiga malamai don suyi hulda
da ke?

Sannan daman duniya tasan ki kina
haka?" Ta ce, "Ko kusa, sun sanni a Hajiya Nina
sai in mutum ya zo ya ganni, in ya sanni to in bai
sanni ba duk daya.

Sudai burinsu kudin". 12......

Abba ya ce, "Nikam ba zan iya wannan huldar
ba".

Ta ce, "Kada ka bari taurin kai yaja ka
nadama irin wadda waninka ya ta6a yi.

In kana
da sha'awa in baka labarinsa don ya zamar maka
Ishara".

Shirun da Abba ya yi shi yasa ta ci gaba,
domin alamar yana son ji kenan.

Da a ce zan fadi
sunanshi zaka sanshi, wani malami daga cikin
Malaman garin nan, haka nan yanda na ganka a
TV kana labarai na kwadaita da kai, shima haka
na ganshi a TV yana wa'azi kuma zuciyata ta
yaba.

Na neme shi ya zo kuma shi na fada masa
ni ce Zabba'u ban 6oye masa ba.

Sai dai nuna
masa nai aikin rabon zakka zan ba shi, ma'ana
kudi ne masu yawa ban san yadda zan fidda
musu zakka ba.

Da jin haka sai ya taho, nan
dakin na kawo shi, sannan na fito mishi da
maitata fir! ya shiga jawo min ayoyi na numa
masa cewa ba zan hakura da abinda zuciyata ke
so ba.

Don ban ta6a 'kin cika mata burinta ba,
shi kuma ya fir ya ki ya nemi ya gudu na bashi
guri ya dan ci abinci na nuna masa mishi kuskure
ne ya ce zai gudu.

Don gidan nan duk masu tsaro
ne har da ma layin gaba daya.

Da sauri za a
kama ka a matsayin dan fashi, sannan in ka yi
kokarin shigo da jami'an tsaro lamarin to, zaka
kwana ciki.

Domin duk a hannunmu suke, amma
Ustazun ya ki shan ko ruwan gidan nan, gashi ya
min shame-shame zai mutu don yunwa.

Ba arziki
na saka aka fita da shi kuma aka kai shi gidan
karuwai a ka ba su na sakar musu kudi suka sa
shi a daki.

Nasa Malamina ya karasa min shi,
sannan na sa karuwan suka kira 'yan sanda kan
cewa ga wani ya zo gurinsu amma kwananshi ya
kare a nan.

To dama iyalanshi suna ta nemanshi
an sace shi nan fa suka dauke shi, na san yanzu
ka gane kowane Malami ne tunda labarin ya yadu
a cikin garin nan da ma wajen shi".

CIKI book 3 part 3
ZURFIN CIKI book 3 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:24
Abba ya ce "Lokacin da muke cin abinci tare,
Umma ta ce, lokacin da ka ke bata dai, Abba shi
ne ya fara baki abinci a baki. 20.....

Watanki
hudu, da kin hango shi za ki soma daga hannu,
Abba ya ce Umma na fa goya Ummi a bayana.

Lah, goyo?

In ji Ummi.

Umma ta ce, "Goyo sosai
kuwa, suka sa dariya, Umma ta ce, "Shi yasa in
naga yanda ku ke rashin shiri a tsakaninku
yanzun sai in ta mamaki.

Don tun ba ki fita a
tsumma ba Abba ke rainonki, tun ba ki fi wata
hudu ba, ki ka tantance muryarshi.

Haka nan
sunan shi ne ki ka fara iya fadi a duniya.

Abba
yana goya ki kin sha yi masa fitsari da kashi da
tumbudi, wanka da wanki duk Abba ya miki
Ummi.

In ko na aike shi ko zai tafi Makaranta to
sai da wayo da dabara.

Ke har an kai lokacin da
kin yarda in tafi unguwa in bar ki gurin Abba, in
ya dawo Makaranta tun daga soro zai soma miki
wakar da yake miki.

Ummin Abba da Alhaji,
Ummin Umma da Tsohuwa, da kin ji haka za ki
dibi rarrafe ki nufi gurinshi, kuma duk kudin break
dinsa zai debo miki tsaraba.

Umma na bada tarihi
Ummi ta zuba ma Abba idanu cikin wani irin
yanayi da ba zata iya tantance shi ba, shi kuwa
lokacin ne ya dawo mishi, ido ya yi dan murmushi
tare da cewa "Allah sarki da na tuna ranar da aka
yaye Ummi, Umma tayi dariya ta ce, "Ranar tare
kuka kwana kuna min kuka wai in yi hakuri in
baki nono".

Wata sabuwar kauna da so Ummi taji
ya rufe ta na Abba, har kwalla ta cika mata ido,
ta ce "To Ya Abba me yasa ka daina sona?" Ya
ce, "Ummi ban daina sonki ba, kanwata kiriniyarki
ce ta hada mu fada dama, yanzun kuma kin
daina ko?" Ta daga kai alamar eh, Umma ta ce
"Labarin yanda ku ka kaunaci juna mai tsawo ne,
kusan kullum sai mun yi labarin da Alhaji".

Ummi
ta kalli Umma shi ne ba ku ta6a bani labari ba?

Ta ce ba gashi kin ji ba, Tsohuwa tayi sallama,
suka amsa.

Ta ce, "Kai me sunan Malam me ya
faru da kai?

Nan ya warware musu komai, suka
yi ta al'jabi.

Umma ta ce "Ni 'yasu, yanzu haka
mata suka maida aure ba a bakin komai ba?"
Kuma ka ce matar aure ce, Abba ya ce dama z
aki san kowa ce ce za ki ji mamaki fiye da haka,
don dai kurum na rufa mata asiri ne in taci gaba
to can gabanta hadu da mai tona ta.

Su Alhaji
suka shigo da sallama, nan suma aka ci gaba da
jajanta batun, Alhaji Babba ya ce, "Babana ina ga
dai rahoto za mu kai gurin 'yansanda".

Abba ya
ce, "Alhaji tuni manyan shuwagabannin gurin
aikinmu suka shigo da hukuma, in Allah ya yarda
dolenta ta bar ni, Alhaji Karami ya ce, "Addu'a dai
ita ce z aka kara rikewa, Allah ya ja mana gaba".

Suka ce Amin. 21...

Ranar su Alhaji a tsakar gida
suka ci abinci anata hira, Ummi dai kallonsu take
yi amma zuciyarta na can duniyar tunanin labarin
da aka bata.

Ashe har yanzu Ya Abba na sonta,
Allah ya sa haka har yanzun.

Sai kusan sha daya
Alhaji ya matsa wa Abba ya tafi gida.

Abba ya ji
dadin hirar musamman in ya waiwaya idanunshi
suna kallon Ummi ta mai 'kuri da ido, Umma ta
ce, "Ka gaida 'yan gidan".

Ya ce "Za su ji, har ya
kai soro Ummi ta ce Alhaji da an raka shi kada a
kara sace shi fa, duk suka sa dariya".

Abba ya
dawo yana cewa, "Umma kun rage man fetur
kuwa?

Na san yanzu na gidan ya kare tunda ba
shi da yawa, bana son kuma sai na sake daukar
galan na fita".

Alhaji ya ce, "Na shigo da mai
dazu duba nan soro na aje shi, Ummi ta sake
cewa Ya Abba ka ce Alhaji su rakaka gida, yayi
'yar dariya kada ki damu Ummi, ina yin addu'a
Allah zai kare ni.

Yau kam Ummi ta dade bata ga
daren da farin ciki ya hanata bacci ba irin yau.

Haka nan shima Abba zuciyarshi fes Ummi ta
fahimci dama can santa yake, da alamu ba zai
sha wuya gurin shawo kanta kuma cikin
karammin lokaci. 11 HAJIYA NINA Ta kalli
matashin, sannan ta kalli jaridar hannunshi ta ce,
"Me ya'ki kai fa ba jakadan azriki ba ne, a duk
lokacin da na ganka sai gabana ya fadi,
musamman in kazo min da jarida".

Yayi 'yar
dariya "Hajjaju makatu sallah Makka Sallah
Madina, ni dai kin san ba ilimin nan gare ni ba, in
da z aki tsare ni in karanta ban iya ba, ni dan
sako ne.

Muftahu ne mai siyo duk wata jarida da
ya ga ta shafe ki, ta amsa ta bude cikin azama,
hoton Abba ta gani gabanta ya fadi, ta ce dan
jarida shege ne, yaron nan tallatani zai yi?

Ta
soma karanta labarin zufa tana karyo mata, har
ta gama.

Kafa kurum take karkadawa tana
tunanin abin yi, murna daya tayi da bai tona ma
duniya cewa ita ce Hajiya Zabba'u ba.

Amma duk
da haka ba zata bar shi ba, koda yake ta ga
manyan 'yan jarida na kokarin shigowa ciki, ta
kai hannu ta dauko daya daga cikin wayoyinta ta
danna kira. 22....

Jim kadan aka daga ta ce,
"Karamakallu barka da warhaka, ya amsa da
Ranki ya dade lafiya dai ko?" Ta ce, "Malam ba
lau ba, kana ji?

Ina yaron da nake baka labari
dan jarida?

Ya ce, Naji.

Ta ci gaba, Yaron nan
kaga yanda ya yayata ni a duniya?

Sai na koya
mishi hankali, da ni zai ja?" Malam ya ce, ya ma
ki ka ce sunanshi?

Ta ce Idris, ya ce To zan kira
ki anjima, kada ki dauki wani mataki tukunna sai
na gama bincikena duka.

Ta ce an gama.
Chapter 15 · 0% Book details