← Book details Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 34

Sashe 8

Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai tsaya ji komai ba yasa aka kame su aka kullesu har da abokan dady .
Kuma fur yaki yarda da duk wani ban hakurin da'ake bashi .
da'aka dame sa da magana ma yasa aka buga kara kotu .
To can ne ma ya kori ma'aikatan na har abada..
Sannan yabi didigi kowacce kadara dake garesu anan cikin company .
a karshe dama yasan ba komai ne zai dawo ba.
Amman cikin dari an samu kusan kashi tamanin da wani abu .

Teema ce tayi nouking kofar part din Abdullah ya bude .
tashigo da jug a hannuta ta same waje ta zauna sannan ta tsiyaya masa fresh miki ta bashi ya karba.
ita kanta teema yaga duk ta canza masa komai cikin tsanyi jiki take yinsa .
sai daya shanye .
sannan tace bros dama naxo ince maka ni zan rika kawo maka abinci da zaka ci.
da kaina zan dinga girka maka ina kawo maka saboda a gaskiya ban yarda da zaman su mama hafsa da faiza acikin gidan ba .
dan akwai wasu abubuwa da nake ganewa idanuna .
gashi Sam mami mai da hankali balle ta taka musu birki.
Abdullah bai ce komai ba sai dai ya amsa mata da kai.

itama tana gama fadar haka ta Mike har ta kusan kaiwa kofa sai Kuma ta juyo tace bros duk wanda zai kawo maka wani abinci byn ni ka barshi kawai .
ta juya shi daman baya iya cin duk abinci da,ake kawo masa .
saboda ba irin test din da yake so bane.
kwata kwata sai dai masu gyaran wajen su fita dashi .

Ya kalli agogo tara ta dade da wucewa yayi murmushin gefen baki Aisha tasan lokacin da yake bukatar fresh milk a dan zaman da suka yi tare.
bata taba bata lokacin bare ta manta.
a yanzu kuwa tunda maminsa ke shareshi wata rana salis ke siyo masa a waje ya Sha ya ci takeway ya kwanta .

Yayi shiru yana tuna yau kusan kwana talatin da shida da tafiyar dady iya kwanakin rabuwarsu da matarsa kennan .
ya Mike jiki a sanyaye ya shige ciki ya kwanta akan royal bed dinshi.
ji yayi gabadaya kwanakin ma kmr bayin su akeyi ba .
ya fada aransa a kalla yanzu za'a kuma ninka kwanakin sau biyu kafin yaji wani bayani daga gareta.
gashi su mami tamkar zasu sa ya gudu daga garin haka yake ji kansa.
Akan maganar auren faiza shi kam yace dasu suyi komai ba sai an nemeshi ba.
tunda da auren suke so ayi .
Amman shi kansa yasan yanzu ba wani auren da zai dauke shi da daraja byn na Aisha
sanda ya aure ta bata son shi ,shi kansa ya san da haka .
bata damu dashi kuma ba bata son wani abu nasa ba, Amman dan zaman da sukayi suka tare shiga ran juna ko bacci bata iyayi sai dashi.
nan take jikinsa ya sauya yarikece ita kawai yake kishirwa a halin yanzu, .
Gabadaya idanunshi sun gama canza kala sunyi jawur .
ya jawo pillow ya kankame ajikinsa yana shafa ahankali Amman bai daina jinta a sansar jikinsa ba .
barin da ya tuna yadda ta ringa rikita shi adaren da zasu rabu ,
Ko tasan zasu rabu ne yasa ta rinka masa abubuwa masu cracking brain .
ya Mike tsam ya shige bathroom .
ya sakarwa kansa ruwa ya dade tsaye ruwa na zuba kansa .
sannan ya fito Amman yana sake kwanciya sake jin ta biyosa ta manne akirjinsa ,.
Jikinsa ya dauki rawa ya runtse idanunshi ya kankame jikinsa waje daya yana surutai iri iri .
adaren dai yayi wanka ya kai sau goma .
dan ya samu saukin sha'awarta har aka fara kiraye kirayen sallah bai runtsa ba haka yakaraci haukansa shi kadai a adakin.
har sanda aka kira assalatu ya kara tabbatarwa kansa lallai so bala'in ne .
bai gane hakan ba a tun farko sai a yanzu

Basu da lecture yau Amman tun jiya da babanta ya sanar daita zance Aisha take tunanin can zata wuni.

dan haka tayi shirinta tamkar wacce zata je makaranta ta fice Abba ya gaya mata zance ne domin ko su mamanta bai bari sun sani ba .
Tana shiga gidan daita ta fara cin karo .
ta fito daga bandaki da buta .
suka sawa juna dariya Aisha har da dan kwallarta na murna ..

Sakina taja hannuta zasu shiga rufar inna .
Aisha tace shiga inna tana ciki ku gaisa tukun .
ni ina nan tana fitowa suka shige tsohon dakinta dake kusa da na inna wanda byn barinta gidan ya zama na usman.
Amman a yanzu ma duk da kayansa yana ciki anan din take kwana .

Sakina ta dubeta da kyau cikin sanyi jiki tace sister ya jikin naki Abba yace baki da lfy .
Aisha ta dan langwabar da kai tace to da sauki kennan sister .

daga can suka dan yi shiru sakina tace a she sister kun rabu da Abdullah kuma ?

duk son da yake miki Aisha tayi shr bata kalleta ba ta sake cewa me ya faru ne har haka da zafi har ya kai gayin saki .
Aisha ta kalleta tayi murmushi takaici tace haka Allah yaso zaman ne iya haka.
sakina tace haka ne Amma ba haka aka so ba.
abin ma har da abin alajabi wai sister ciki gareki ?
.. Aisha ta sake yin murmushi itama sakina dariya tayi .
tace koda yake ke ai kin haye kin cigaban arayuwarki .
tunda da wani zai samu irin taki .
ai da yayi tsalle da kukan murna "Aisha ta dan dago ta kalleta tana mamakinta .
eh mana sister dubi yadda kika zama ke kinganki kuwa .
kinga kyau da kika kara .
sai dai Yar rama .
itama ina ga ta rashin lfy ce.
na farko kennan kin auri miji mai kyau gashi zaki haihuwa da shi dan Abdullah ko daga nesa mutun ya hange shi .
dole ya tabbatar da kyaunsa .
kinga kuwa ina tabbatar miki danki ko "ya" zasu yo kama dashi .
Aisha ta kalleta sosai ita fa haka take kullum a na cikin magana daita yanzu nan zata subuce wani gurin tamkar Yar fari .
haka ta fada a ranta ahankali tace sister ke abinda Dame ki kennan ni ban Dame ki ba ko
sister?
Haka ranar da za'a tafi dani ma guduwa kikayi kika barni sai yau na sake ganinki .
gashi yanzu kinzo,
komai ma ciwo yake min Amman kina maganar wani abu na daban can .
sakina tayi saurin rike hannuta dukka tace sorry sister ayi min afuwa .

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 56-57

Da farko Kamar bazatayi laulayi ba, Amman kwanaki kadan laulayi yazo ya sata a gaba ko ruwa tasha baya zama acikinta.
gashi duk nisan abu idan ta kafa ranta shi zata dole taci dan idan bata ci ba sai taji duk cutar duniya kanta ta dawo ,.

kuma har dare bazata iya cin komai ba idan ba shi din ta samu ba wani lokaci har kuka take yi .

Gashi duk kinta da tunanin Abdullah sai da maraicinsa ya taba ta.
duk ta rame ta dashe tayi fari fat.
idan ta fara kakarin amai kuwa tamkar hanjinta zai fito.
magana ma wani lokacin da kyar take iya yin sa .
da kafar ta ma tafiya take dan yawancin duk unguwar an san da a yanzu tana gidan maganganu kuma iri iri bbu wanda baya tar dasu.

Ita sai daga bayan nan taji bayan tafiyar su da Abdullah.
dadinsa ya dauki nauyin hidimar makarantarsu yaya yusif da duk abinda zasu bukata.
akwai mutun na musamman da aka daura akan haka .
a yanzu haka akarkashin I M sidi magaji yaya Ali ya tafi NDA Kaduna ,.

sai gidanjenta wanda aka mallaka mata cikin sadakinta wanda tun bata dade da dawowa gida ba, da mlm abu yamata maganarsu .
Amman tace ita wlh gabadaya tabar musu Amman suna nan a rufe har yanzu ba abinda akayi dasu .
takardun ma suna gun alhaji aminu .
motoci kuwa ko yau suke so za'a kawo musu daga company dan haka duk wannan a idanun mutane suke har yau surutai ake a gari ballanantana da yanzu aka ga tana gida .

Aunty Maryam tazo da yammacin wata lahadi suna gaisawa da inna daga kitchen inna ta fito sai da ta samu gurin zama sannan take mata bayanin .
yawan zuwan da Doctor nan yake yi.
inna yayi shr tana sauraronta hade da kallonta aunty Maryam.
cikin tuhunna inna tace nifa abin har tsoro yake bani kullum ne sai yazo wai yazo dubiya ai ina jin kalla yazo gidan nan ya kai kusan sau talatin. Mlm ma da kansa abin ya dame shi .

Aunty Maryam ta dan langwabar da kai tace to inna yaya zanyi.
na rasa yadda zanyiwa doctor "can ma idan kinga yadda yake yi min sai kiyi mamaki "tun bana bi ta kansa har na hakura.
shi inna wai ita yake so da aure har cikin dake jikinta .
inna tayi murmushi kawai dan ita har yanzu ranta Abdullah take so da diyarta ,aunty tace baki ga abinda abun ya zame masa kmr wani ibada yazo kullum ya tambayi lfyr ta a gurina kafin ya fara aiki.
,har na rasa yadda zanyi da nacinsa .
inna tace haba nasan za ai haka abin yayi yawa fa da idan zaizo fa ke baki ga abinda yake tahowa dashi ba .
daga baya da muka fara fahimtar haka aka daina karba, aunty Maryam tace wlh ni kaina basan ya za a bullo abin ba ,.
gashi da bin diddigi maseefa ni fa kawai zuwa ya yi yace min wai kuna gaishe ni .
ban san ya'akayi yasan gidan nan ba ..
Chapter 8 · 0% Book details