← Book details Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 34

Sashe 18

Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Iya tunaninta yasa ne ayi musu iso kafin su shiga cikin gidan.
daga inda take tana hangensa yana magana da yahuza.
Amman bata iya jin abinda yake fada a saboda tana daf da inda injin yake faman aiki .
, Abdullah ya karaso ya bude mata kofar motar yana yi mata magana da kyar ta fito.
shi kuma ya hade fuska kmr da gaske tamkar bashi ne ke lallabata ba ,tana fitowa ta dan tsaya tana kallon tsarin gidan ahankali tace ina kuma ya kawota?
ita dai ta taba hange gidan gwana ta waje Amman bata taba shiga ciki ba.
dan haka tasan tun daga waje gidan ya tsaru iyakar tsaruwa fitilu ne suka haska koina kana Gani yadda wajen ya dau haske ,da duk kannin alamu ba gidan mutun daya bane saboda bangare bangaren da ta Gani .
ita tsoro ne ma ya kamata har gabanta yana dan faduwa .
shiyasa ta tsaya tana kalle kalle dan ta gane yadda gidan yake ,ita bata san inda Abdullah ya kawota ba.
dan haka ta dinga binsa ahankali ahankali har suka shiga part dinsa wani irin kamshi ne ya doki hancinta.
ba kamshin turare bane kawai naturaly ta saba jinsa a jikin da Abdullah , Abdullah ya waiwayo bayan ya rufe kofar bai tsaya wata wata ba ya kamo hannuta har ciki. Bedroom dinsa tana binsa a tsorace ,suna shiga ya janyota jikinsa...

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 68-69

Abdullah ya waiwayo byn ya rufe kofar bai tsaya wata wata ba ya kamo hannuta har ciki bedroom dinsa tana binsa a tsorace "suna shiga ya janyota jikinsa ya matseta a kirjinsa har tasa kara "yaki sakinta ahankali ya tura hannusa kasanta yana shafo cikinta sai alokaci ya dan ji tudunsa .
tun dazu dasu ke gidan Dr sagir yake ta kallonta Amman bai ga cikin ba hakan ne yasa tasa iya karfin ta" ta fizge jikinta daga gareshi.
ta watsa masa harara sai kuma ta fara kuka ,yayi murmushi ya jata ya zaunar daita a gefen gadon.
yace ina meyye haka hade da shafo saman kirjinta da sauri ta buge masa hannu tana turo masa dan karamin bakinta ta turo masa bazato taji bakinsa kan lip's dinta ya hade yasoma tsatsa kmr zai cire mata lip's ,sai da ya tsosa san ranshi sannan ya barta yana sauke ajiyar zuciya"ahankali yake tafiya da baya da baya har yabar dakin .

Yana fita tacigaba da dan kukanta wanda dagani duk na shagwabar ne . tana kallon dakin ahankali har idanunta ya sauka kan hoton data Gani a gefen gadon yasa ta dan fara gane kan abun .
hotonta ne wanda batama san ko wani iri bane " Amman dai ta san tabbas itace .

Abdullah ne yashigo da snacks a plate " ya koma ya kwaso kayan tea da flask , sannan ya duba store din shi .
ya ballo swan water da sauran lemuka guda uku saboda yaji Dr sagir yace ba'a son masu ciki su dinga shan tsanyi.
shiyasa bai debo a fridge ba ,ya kwaso yazo gabanta ya zube yana kokarin hada mata tea ta kalleshi tace Abdullah ina ne nan ka kawo ni?.
Yadda ta fadi maganar a natse" cikin mamaki yasa ya bar abinda yake ya kalleta.
sai kuma yayi murmushi yace gidanmu na kawo nan part dina ne ni dake ta zaro ido tana girgiza masa kai tace dan Allah kayi hakuri ka maidani gidanmu ni tsoro nake ji ta sake barkewa da wani sabon kukan "yayi murmushi
Yace me akayi kuma kike kuka nan fa gidanmu ne , mu kadai ne fa a gidan sai ma'aikata su mami basa nan sun tafi abuja bikin wasu neighbors dinmu shima dady dazu ya tafi daurin aure .
ta karkace kai tana kallonsa idanunta cike da Hawaye ya sake yin murmushi ya tura mata tea daya gama hada mata .
yace Aisha kici abinci Dr yace muna zuwa a nemam miki abinci kici tayi shr tana binsa da Idanu.
yadda tayi shr yaji har cikin ransa tayi mugun bashi tausayi .
ya mike ahankali yana murmushi yace ki sha tea bari nayi wanka rabona da wanka tun awanni tara har nasoma jin ba dadi ajikina.
bata kalleshi ba ballanantana ta amsa wanda shima yasan basamu zaiyi ba murmushi kawai yayi ya shige bathroom .
Tayi shr " wannan wacce irin rayuwa ce sukeyi ita da Abdullah kmr za'a yi kmr baza ayi ba "bata so bata so Abdullah ya sake dawo mata yasa ta a damuwa ta koina ta duba Abdullah ya wuce yadda take zato Abdullah na rayuwa anan Amman yake damuwa daita "da ta fito daga wannan lungun .

Bataso a kuma yin irin ta jiya gara duk yadda za'a yi ta lallabashi ya maida ita gidansu , idan ya maida ita kuwa da ikon Allah ta bar hannushi kennan sai dai ya nemi wata Aishar "duk ta gama tsara yadda zatayi idan ya maidata a ranta .
dan ita a yanzun duk da yace iyayensa basa gidan Amman ita gabadaya a tsorocr take dan alal hakikanin gaskiya tana mugun tsoron mahaifinsa kmr me .
gashi yau zata kwana a cikin gidan da take .
Bai dade ba ya fito kugunsa daure da white towel gashin kirjinsa na kwance suke luf luf luf dasu ga dan karami towel a hannunsa yana goge kansa zuwa tsantsar jikinsa .
Kallo daya tayi, masa ta dauke kanta daga gareshi dan bazata jure kallonsa haka .
"yazo har kusa daita yace "oh" my God this girl won kill me oooo Aisha har yanzu baki ci komai ba ya kalli agogo shadaya saura yace kalla Aisha a kalla kin yi awa takwas baki sawa cikin komai ba.
kina jin kuma abinda Dr ya fada .
Tayi banza dashi sai idanunta data zuba masa yayi dan murmushi iya bakinsa sannan ya zauna gefen gadon kusa daita ya ruko tafin hannuta yace please Aisha kiyi hakuri da komai kici abinci nan karki min haka kinji ta watsa masa harara hade da zame hannunta daga nasa .
tace ni na koshi ya dubeta dakyau yace Aisha yaro cikinki bashi da laifin komai ki tausaya wa bbyn mu dan Allah.
ni nayi miki laifi " to yaya zaki hukunta wanda bai san komai ba " idan kinci shima sai ya samu.
Suna nan zaune a haka har shabiyu ta kusa Amman bata da niyar cin komai.
Ran Abdullah yasoma baci yaji wani abu ya tsaya masa a wuya yana kallonta yana jin zuciyarsa na masa wani irin suya" tabbas Aisha bata sonshi tunda gashi bata son dansa.
ganinsa muddin bata ci abincin nan ba .
wani abu zai iya faruwa da yaron cikinta .
to abu ne idan akace maka na fari ne anfi rudewa akansa .
sai ya dinga ganin dan bata damu da shi bane shiyasa take son yarasa cikin ,.
shi kuma a halin yanzu ganinsa yake ba wata kadara da ya mallaka da ta kai cikin jikin Aisha
Ya dan kalleta a nutse take kuma fuskarsa ta canza .
ahankali yake magana Aisha na rokeki kada kiyayyata ta shafi dana shi bbu ruwansa bashi ya miki laifi ba.
In kin tashi yin hukunci ni nan zaki hukunta ya nuna kansa da yatsansa yana sake daure fuska.
maganar tazo mata a bazata kuma wani irin da sauri ta dago kanta ta kalleshi shima ita yake kallo sun dan jima suna kallon juna da kyar tasamu ta iya janye idanunta ta sunkuyar da kanta.
batayi magana ba still ahankali Abdullah ya zamo daga kan gado ya zube kasa gabanta .
tana dagowa afrigice ta gashi a durkushe da kofin tea a hannunsa yana miko mata .
taji kmr an zuba mata wani abu ne a jikinta ne. ita wacce da kmr Abdullah zai durkusa mata da sauri tasa hannu ta karbi kofin hannusa ta kai bakinta .
ta fara sha a lokacin guda kwalla ta cika mata idanu.
ya mike ya zauna yana miko mata snacks tana karba cikin sanyi jiki har yayi mamakin abinda taci" bbu wanda yayi magana acikinsu har ta gama ya kwashe kayan ya fita falo.
ya zauna kan kujera yayi shiru yana jin dacin abinda Aisha tamasa ya jima a gurin" sannan yaji abinda ke wuyansa ya wuce.
Yarasa me zai mata aduniya in akwai abinda yafi so da muradin kasancewa tare itace .
iya kokarinsa yana yi "akanta ya runtse idanunshi ya dade Zaune a falo bai shigo bedroom din ba .
Chapter 18 · 0% Book details