← Book details Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 34

Sashe 5

Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali ya sauke wayar a sanyaye ya dan kalli agogo dake gefen gadon sannan ya mai da kasa ya zubawa Tay's din dakin ido yayi shr yana tunanin maganar dady.
shine kake neman susuta kanka akan macce ,barin da ya tuna ma yadda Aisha bata wani son sa.
kawai mikewa yayi ya shige bathroom ya kunna fonfo dake manne cikin sink sai daya cika sannan gabadaya ya tura kansa ciki yayi dan Jim sannan ya dago yana maida numfashi ahankali ya kurawa kansa ido ta cikin mirrow din gashin kansa daya jike duk ya kwanto goshinsa ruwa na dinga .
idan Allah yakarbi ran Aisha shikenan baza ka sake amfanuwa ba kennan maganar data sake zuwa masa kennan.
ya runtse idanunshi sosai yana sakin numfashi ahankali ya furta alhamdulilllahi tunda Allah yasa Aisha ba mutuwa tayi ba .
ya sakarwa kansa shawa yayi wanka Amman har alokaci yana jin kadaicinta ajikinsa , ya fito yana goge jikinsa ya ya koma yayi rigingine da jikin gado ya zubawa celling dakin Ido ,duk son da yake mata idan wanda ya hallice tane ya dauketa bai isa yace komai ba,.
ya rufe idanunshi gam ahaka har wayar dady ta sake shigowa ya Mike zaune yana amsa wayar dady yace ina sauraronka .
Ahankali Abdullah yace kayi hakuri.
dady yace kai za'a bawa hakuri dan kai aka batawa.
Abdullah yayi shr dady ya sausauta murya ya kirawo sunansa yace Abdullah ba tun yau ba nake nuna maka mahimmanci idan wani damuwa ya sameka ka daina sa shi a ranka .
ka dinga barwa Allah komai inda ba haka ba zaka sa kanka a wani hali.

Abdullah tabbas nasan an bata maka tunda aka saka rabu da matarka an katse maka wani farinciki na rayuwa duniya.
ni nasan da haka to Amman karike aranka bbu wani dadi dayake samuwa batare da an Sha wuya ba.
kuma muddin kasan zaka samu wata rana dole zaka rasa .
Zuciyata ta amince maka da yarinyar nan Aisha.
dari bisa dari Kuma na amince ka zauna daita ko byn Raina , kuma ko ba komai wannan yarinyar diyata ce halak malak bazan so wani mugun abu yasame ku kai daita ba.
domin kuwa nasan adaidai wannan yanayin maimuna na can cikin bakin ciki da tashin hankali fiyye da wanda ka tsinci kanka ciki ..
dan haka Abdullah ina son ka daurewa zuciyarka na rashin matarka a kusa ka ajiye komai har sai na dawo.

ko inda take kada ka dosa hakan zai iya sa zuciyarka sake karyewa ko wani ban yarda ka tura ba.
har sai na dawo da kaina zan same iyayenta dan yanzu duk wanda za'a tura zasu ga an dauki auren wasan yara .

Amman bbu komai nasan maminka ni tabatawa bakai ba .
Saboda haka ka sawa ranka hakuri matukar Aisha rabonka ce.
gaba zaku sake zama ,ka maida hankali kan abinda nabarka dashi a game da ma'aikatan Abdullah idan ba'ayi da gaske ba company yana iya durkushewa a dalilin wannan satar.
Abdullah mutane nan so suke suga karshenmu Abdullah gashi bananan nasan zaka mayye gurbina har yafi idan ina nan.
dan haka Abdullah idan baka ajiye al'amarin Aisha a gefe zuwa wani lokacin ba zamu kwana aciki fa.
Abdullah ya jinjina kai ahankali yace inshallahu zan ajiye komai zai daidaita.
dady yace Mashaallah zan sake nemanka .
Ita kanta mami taga canji a ranar hatta kannensa yau sun dan sake dashi salis kuwa tamkar sallah haka yaji jin Abdullah yace zasu fita .

Amman daddare sai da Aisha tazo, ta hanashi bacci da tunanin halin da take ciki bbu yadda zaiyi da kaunarta ta zama naman jikinsa .

Wani tashin hankali da yazo masa nan da nan jikinsa ya dau rawa karfe biyu da mintina na dare ya lalubi wayarsa yasoma neman dady yaji duka wayoyin dady a kulle .
tunanin da fadomasa arai akalla dady zai yi wurin wata uku zuwa hudu kafin ya dawo , Kuma sai ya dawo zai je masa Biko AISHA .
to idan kafin lokacin suka aurar daita fa ?dan a wancan karon ma mlm abu cewa yayi zai aurar daita ga duk wanda yagadama.
Allah ya kiyaye to har dare ranar haka ya kwana yana surutai ba wanda yaisa ya aurar masa mata.
tashi ce shi kadai .

Da safe wayar dady nashigowa korafin daya farayi masa kennan dady ya danyi shr yana jinjina al'amarin Abdullah game da yarinyar .
sannan yayi dan murmushin yace to Abdullah a ganina duk maccen da,aka aura aka saka sai tayi idda kafin ta sake yin wani auren.
ma'ana sai tayi jini uku kennan kaga a kalla zai dauketa wata uku zuwa hudu ina ganin itama Aisha ai haka ne malam Abdullah dole sai tayi idda kafin suyi mata aure dan haka a tunani sai tayi idda itama ko ba haka ba ne .
Abdullah yadan sotsa keya kmr dady tamkar dady yana kallonsa yace haka ne .
dady ya sake yin murmushi to kaga kuwa har na dawo ..
Abdullah yadan janye wayar yayi .
yana murmushi dan gabadaya yagama rudewa gashi har yasa dady ya fahimceshi ya fada aransa .
Shima bangaren dady dariya yayitawa Abdullah .

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 51-52

Aunty Maryam na can bangaren aikinta ,inna ke sanarwa zance ciki da abinda ya kawo ciwon yayi tsanani , ta bar abunda take ta zubawa inna ido sosai , ahankali cikin mamaki tace innarmu cikin me Kuma har gabanta yana faduwa .
Inna bata bi takan tambayar da Aisha tayi mata ba tacigaba dayi mata bayanin yadda ake samun lalura iri iri na laulayin idan macce ta samu ciki ,
tayi shr tana ji Amman ba abinda inna take fada take fahimta ba , tunanin ta yana can wani guri. tashiga uku Kar dai Abdullah ciki ya bankamata ,sannan ya sakota.
tasan inna bata fadar abinda bata da tabbacin a kansa aunty ce tashigo tana surutai kai nima fa yau dole a daga min kafa nima mara lafiya ce dani .
Aisha ta kalli aunty Maryam ,inna tasan maganar zata mata dan Allah ta kwashe kwanuka ta fita wankewa har aunty ta zauna Aisha nabinta da idanu ahankali murya adashe tace aunty wai ciki dani ?
Aunty ta kalli yadda tayi maganar tace au ke tun jiya baki sani ba.
cewa nake kinji ne shiya bangaya miki ba.
to ciki ne dake bai kai wata daya ba .
nace ke Kuma irin naki laulayin kennan ciwon ciki da zazzabi ".
Kwalla ta cika a idanunta kafin kace me sai hawaye shar ...shar... aunt tace to mayye haka Kuma ke me son kananan yara.
gashi Allah ya kawo miki shine zakiyi kuka Aisha kuwa da zaune tamkar an dasata , bata sake cewa komai sai cigaba da kukanta take ita kadai tasan abinda ta tuna .
aunty ta matso kusa daita sosai tace A'a ai yanzu ba kuka zakiyi ba abinda ya faru yarigada ya faru,.
ta lafiyarki zakiyi da dan dake cikinki tunda ....Dr salim ne yashigo ya katse su ganin Aisha na kuka yasa ya ja ya tsaya yana kallonta can Kuma ya matso kusa da su yace yaya jikin ne ?
Aunty Maryam tayi dariya tana girgiza masa kai tace ko daya .
wai dan an gaya mata ciki ne daita ,shine take kukan dadi .
Dr salim ya kura mata Ido baya son har baya so daukewa daga kanta ,dama takasance matarsa aka Kuma sanar masa tana dauke da cikinsa da bai san irin gatan da zai nuna mata.
ba har sai shagwaba ta isheta," har sai da aunty takira shi sannan ya dauke idanunshi daga gareta".
da sauri ya kalli aunty yace ina tunanin irin su abinda dariya ne dasu. haka nake da wata kanwa itama ko bacci zatayi yara suka hanata duk girmanta sai kiga hawaye.
aunty tasake kwashewa da dariya tace kusan duk jirgi daya ya kwasosu kmr wasu kawaye shima dariya yayi sannan yace excuse me sister inason na dan ganki na mintina kadan "
aunty tace ba komai ta tashi tabishi sanda inna ta dawo itama.

Dr salim yace mijin Aisha ya jima da tafiya ne ko kuwa daman tafiye tafiye yake aunty tace A'a ai... Daman ba tafiye tafiye yake ba ..sai Kuma tayi shr .

Dr salim ya dan nakalci wani abu ,.
yace sorry ina son nasani ne saboda irinsu da yanayin da take ciki yanzu tana bukatar kulawa ma'ana dole takasance tana da wani a kusa daita da zai dinga lura da ita sosai.
musamman ita da cikin yazo mata a haka.
duk lokacin dataji ciwon ciki tana iya shan duk wani abu datasan zataji ya daina.
ya numfasa sannan yace to idan kuwa mijinta yana kusa shi zamu bawa matakan da zata kiyaye da irin abin dazata dinga Sha.
har zuwa lokacin dazata daina jin ciwon cikin .
Aunty Maryam tace ai da yake yanzu ma tana gida ne Amman ko ni ko inna duk wanda ka yiwa bayani ma za'a san abinda za'a dinga yi .
dr salim ya furzar da iska hade kurawa aunty Maryam ido dan ba abunda yaso ji ba kennan Kuma maganisa a kawai alamomin tambaya sosai a tare da bayaninta ,Amman bai son ya fiyye shishigi da binkice akan komai.
yana son yabi komai cikin tsari dan haka ya sake numfasawa yace shikenan .
Chapter 5 · 0% Book details