← Book details Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 34

Sashe 3

Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kansa mlm sai daya jinjina wannan sarkakken al'amarin wai Aisha ciki gareta ? Kuma har zuwa lokacin ita da kanta bata san da zance cikin ba ,.
bayan tafiyar su mlm sai ga aunty Maryam da mijinta aunty takawo musu abinci.
shima mijin aunty har ciki yashigo ya dubanta sannan suka wuce sai da inna ta matsa mata sosai sannan ta iya tsakutar abincin.
taci kadan tayi sallar ishai ta koma kan gado ta kwanta saboda har lokacin bacci take ji kwananta nawa rabon data tayi , ga shi sunyi mata allurar bacci .

Ko kadan batason zuciyarta ta tuno mata da Abdullah.
saboda tashin hankali kawai zuciyarta zata shiga ,sunansa ko wani abubuwa da suka yi a dan rayuwar da sukayi tare da juna .

Taki yarda ta tuna ko tayi tunani
Saboda yanzu hankalinta zai tashi tarikice, yayinda hankalinta da na iyayenta ne kawai zai tashi .
ta kudindine jikinta har kanta da bargo Amman sai ga Abdullah din har acikin bargonta yana shashafa mata jiki da kaiwa wuyanta sumba. domin a haka suke kwana ita dashi wai sai taji shi yana tayi mata rada a kunne yadda yasaba tasa hannuta duka biyu ta toshe kunnenta tana mai runtse idanunta gam.
Amman still bata fasa jin hannushi a tsantsar jikinta yana sarrafata ba kmr yadda yake manne mata a duk lokacin da suke tare .
Kawai taji wasu hawaye masu dumi nabin gefen fuskarta , ahankali take kukanta tana sake felling din tumin jikinsa yasan zai barta meyasa kullum yake mata hudubar da zata so shi , tabbas ita da kanta bata ja akan soyayyar Abdullah tasan zuwa yanzu son shi ne zai yi ajalinta .why why Abdullah why did you do this to me ?
meyasa sai da ka koyamin yadda zan soka sannan kabarni "meyasa ka cutar da zuciyar da bata san komai sai tsabar kaunar ka da tunaninka.ta takure jikinta waje daya wlh ina sonka ina sonka dan Allah kadawo gareni zuciyarta bazata iya hakuri rashinki ba tana sake jin Yadda yake yamutsa a bed ahankali tacigaba da kukanta acikin bargo batare da inna ta fargaba .

Dr salim ne ya shigo da kayan Niki Niki ya ajiye sanye cikin kananan kaya suka gaisa da inna har inna na mamakin siyayyar da yayo.
Shi kanshi Dr salim ya gano hakan a fuskar inna.
Dan haka nan da nan ya sauya dan karta dagoshi yace sister Maryam bata dawo ba kennan ?
inna tace ta dawo dazu Amman yanzu ina ganin Kuma sai gobe .

Dr salim yace ok to idan tazo ace gashi inji wannan likintan salim idris a bawa mara lfy inna tace madallah an gode za'a gaya mata.
cikin rashin kulawa sosai ya dan kalli gadon da Aisha ke kwance yace har yanzu mara lafiyar bata tashi bane ?

Inna ta dube shi cikin sakin fuska tace ta tashi tayi sallah har taci abinci bata dade da kwanciya ba.
ta kirawo sunanta bata amsa ba tace ina jin bacci ya Kuma dauketa .

Dr salim yace musamman saboda allurar bacci dake jikinta sannan yayiwa inna sallama cikin sanyi jiki ya fita .

Duk tana jin su bata ta amsasu gudun Kar su Gane kuka takeyi shiyasa tayi kmr mai bacci .

Dr salim idris da gangan yaki zuwa asibiti da wuri a washegari a dalilin shi yake son yacigaba da duba tafiyarta.
,dan haka ya kulle file dinta a office dinsa gudun kada ma a gano hakan ya hada tare da files din wasu marasa lafiyar hudu ya duk ya rufe a office.
dan haka har aunty ta iso shi bai karaso ba da kyar tasa ta gyara jikinta ta sauya kayan aunty da tazo mata dasu masu launin pink wanda suka kara fito mata tsantsar da kyaunta tamkar ranar bikinta .
fuskarta fayau babu make up Amman kallo daya zaka mata kaji tashiga ranka .
ita da kanta aunty Maryam sai da ta tsaya kallonta to ko daman cikin ne yasa tayi wannan shegen
kyau.
a haka tana kallonta Dr salim yayi sallama gabadaya suka amsa masa Amman banda Aisha dake zaune tana da yatsunta aunty Maryam tafara dariya tana gaishe shi hade da godiyar kayan da ta tarar. shima murmushi yake yayi yana gaida inna ya waiga inda Aisha take gabansa yayi mugun faduwa a yadda ya ganta shigar da tayi ta bugar masa da kwalkwalwa ,meyye ke shirin faruwa dani ne tambayar daya fara watsawa kansa kennan . ya kasan ransa kuma yace gata Kuma sanye cikin colour's din dana fi kauna a rayuwarta.

har yakai bakin gadon inda take bata dago ta kalleshi ba.

shi Kuma kallo daya yayi mata ya Gane I don't care ce .
yaji numfashinsa na kokarin sarkewa saboda dagowar datayi ta dan kalleshi yayi dan gyaran murya sannan yace sannu .
Bata amsa ba , Amman ta dai daga masa kai sai ma yarasa me zai ce mata.
kawai ya bude file dinta yarafa dubawa duk jikinsa yabashi har yanzu su aunty Maryam shi suke kallo aunty takaraso tace doctor ai naga jikin nata yayi kyau tun dazu wai ta matsu a tafi gida .

Yabar abinda yake ya dan kalleta fuska a sake yace yaya kike jin jikin naki ta kalleshi da tsumammu idannuta da suka kara birkitawa dr salim brain.
ahankali muryata a sanyaye tace ni na warke .
Gabadaya ma kennan ya fada a ransa ,yadda ta fadan kmr zata saka mishi kuka yaji wani abu na masa yawo ajiki .
ya saki numfashi ahankali yadda bbu wanda ya fahimci halin da yake ciki.
ganin ba zai iya cigaba da kasancewa a gurin ba.
yayi murmushi yace to kikara hakuri ki dai kara bari zuwa anjima sai a sallame ku ni zanje in duba patient ya fita .

A office dinsa ma dafe kansa yayi yace wannan wacce irin maseefa ce take son afka masa na son matar aure.
komai da yake tare daita hatta tsarinta shi yake nema a gurin macce da yake son mallaka.
jiya fa ko wadataccen bacci kirki bai yi ba a saboda matar wani .
ko kadan batayi kama da marasa kamun kai ba, dan haka zance ko cikin shege ne a jikinta ma bai taso ba .
musamman dayaga bbu wani daga hankali da family dinta sukayi da batun cikin ,idan kuwa yakasance shegene kuwa da shi da kansa zai fahimta a tsakaninsu abu biyu ne cikin daya da lura dashi lokacin daya sanarwa sister Maryam zance cikin ta dinga maimaitawa? Amman Kuma zai iya kasancewa ko saboda cikin fari ne me yuwa ko tayi saurin samu ne .
Shiyasa take dan mamaki ya sake numfasawa ya jingina bayansa jikin kujera yana jujjuyawa hade da rufe idanunshi ya dan langwabar da kai tamkar me jin yuwar daya rasa abinci ci kwana da kwanaki .
Ni na warke" ya tuna yadda ta fada me yuwa Kuma Yar auta ce shi yasa take a haka
kmr zatayi shagwaba.
ya hada hannuwansa guda biyu ya harde a kirjinsa yana tunanin mafita da kyar dai ya samu dan wani abin kamawa da zai tunkari sister Maryam dashi sannan ya Mike ya sake fita

Uhmmmm it's just the beginning oooooo

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ina, Mika ta'aziyyata ga faiza Anfa marubuciyar danfashi Allah ya jikan mahaifinki ya Kuma mai rahma yasa ya huta ya Kuma kyautata namu , Allah ya raya abunda ya bari yabasu hakuri rashi Ameen .

Page 45 -46

"Oh,oh ni hafsa ,Allah baki ga Yar yarinyar da Abdullah ya aura ba duka bata fi rahma ba ,inji cewar mama hafsa faiza tace Allah mama .

Yo ina takai cikar rahma sai kayan nonuwa da shegen idanu suna narai narai sai kace wata macijiya .

Faiza tace wayasani ma ko macijiyar ce,
Tarikide ta manne masa kinsa fa suna yin haka .

Mama hafsa Tace Ko daya, kinsa fa asalinsu fulanin dajin nan ne.

mama hafsa ta rage sautin muryata tace to komai fa ya gamu tun shekaranjiya yarinyar tana gidansu .

Faiza ta daka wani irin tsalle murna hade da rungume mama hafsa. Cikin rawar murya tace mama gaske kike ?

kina nufin Abdullah ya saki banzar yarinyar nan .
Zauna nan an gaya miki ni din ta wasa ce , ai tuni rauhanai sun gano sakin tun wajen duba gashi Kuma an yi shi,. Dan haka kishirya gobe gobe nan.
ki tafi dan nafison ayi abin da gaggawa tun kafin kinibabben wancan uban nasa ya dawo .

Haka kawai muda shan wahala wasu da jin dadi ai wannan ma bazai taba yuwa ba .
ai tun da mami ta lasamun zuma a baki naji nakasa hakurin kirasa Abdullah .
gara komai zai faru ya faru wlh.
da dai kirashi dadi yasake kama faiza .
Faiza ta tashi bbu kunya ta dinga tikar rawa tana juyi a gaban mama hafsa.
tace jaira tunkuna dai kibari kishiga daular Abdullah sai ki cashe yadda ranki ke so .
faiza tace ai wlh kodan kyansa kadai zan'iya aure shi ,
gashi namijin duniya tana magana tana girgiza jiki .
Ke matsa can wawiya banza ana maganar masu nauyi kina magana wani kyau.
ai idan bbu kudi ai ko shi kansa kyan baya wani tasiri ,.
faiza tace ai wlh dan dare yayi ne da yanzu zan tafi tunda kince ( boka dan ina da Kare) yace wuyarta a raba su ,idan aka rabasu komai zai daidaita .

Mama hafsa Tace haka yace Kuma bakisani ba har uwar ma a yadda ta nuna min sai yadda nace .
, dan haka banason abin yawuce wata daya ke Kuma kina shiga sai ki san yadda zaki mallaki dukiyar kinsa gidajen wannan ubanku nasa a market na siyar .
kinga sai amaida masa batare da ya ankare ba .
Chapter 3 · 0% Book details