← Book details Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 34

Sashe 17

Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sister tanemi da suna son suyi sallah.
ita sister din ce ta fara shiga tayi sannan da ta fito Aisha ta shiga ta lura da irin kallon da matar ke mata har jikinta ya dinga bata to ko ta taba saninta ne ?
A daki tayi sallah dan sister zahra ta rigada tafito tana karasowa falo Dr sagir yayi mata magana suka fito waje har Abdullah Dr sagir yayi mata godiya sosai yace zata iya tafiya abunta tayi shr Amman sai satar kallon Abdullah take ta dai .
ta amsa kawai har zatayi magana sai kuma ta fasa tayi murmushi tayi gaba.
tare suka dawo falon da Abdullah Dr sagir ya kalleshi yace Abdullah me yanmmata kennan kai farin jinin naka akansu yakare ne Abdullah ya kalli Dr sagir yace dan malam ban son iskanci kabarni da rikicen dake gabana Dr sagir yayi murmushi yace a to ni ina ruwa ita fa wannan sister din kai take so .
Abdullah yadan zungure shi yace hankali da bayanka dai Dr sagir yadan waiga kadan daidai lokacin da Aisha ke shigo falon ya juyo yace wuuuuuu... Ana kukan targade ....
Abdullah yace kawai kana neman karasani. sukayi dariya a tare .
tsoro frigice ne taji sun kamata alokaci guda sosai tasoma rikicewa har gabanta ya dinga faduwa saboda ganin su datayi tsaye suna dariya .
Ahankali tace gaskiya sun shammace ta dayawa .
duk a dabarbarce take Amman tayi yunkurin dakewa ta dan zauna a kujerar da tun zuwansu anan ta zauna tana dan dube dube.
su dukkansu ,zama sukayi Abdullah ya zauna kujerar dake kallon nata ya zuba mata ido "kyan da ta kara ya wuce yadda ya dinga kiyastawa ,.
komai ya canza a tare da ita har Yar kiba tayi me yiwuwa ko dan albarkar cikinsu ne yasa takara kyau .

Aisha kuwa tarasa a wani hali take ciki abinda ya kara tsorata sai yanzu ta lura da hoton dake jikin bango da kyau Dr sagir ne da matarsa sai dansu dan kimanin shekara biyu alokaci ma yana gidan kakaninsa .

Aisha ta dauke kanta karda dai rai na mata wayo za'a yi ta fada a ranta .

Dr sagir ne ya fara magana bayan matarsa ta ajiye musu abinci da lemon" yace madam kinyi shiru friend fa ke yazo ya bawa hakuri kuma ayi sulhu da juna .
Sai alokaci ta dan kalleshi Amman Sam taki amincewa idannuta ya hadu da na Abdullah tace da gaske ne dai abinda ta, zata.
ta sake kallonsu a yadda suke bbu yadda za'a yi ta iya tsallakesu ta shige batare da Abdullah yayi wani abu ba.
ita ko da matar Dr sagir za'a barta tasan baza ta koina ba.
kawai kallon Dr sagir take yana ta magana a ranta tace idan ba zasu barta ta tafi ba kuwa sai dai tayi ta zama anan Abdullah kuwa ko daga hannunsa baya iyayi.
duk wani halin da tashiga a yanzu yariga ya gane shi.
yana ji tamkar ya karasa ya tausasa mata halin da tashiga da kansa.
Dr sagir ya lura dashi sai ya dan share sannan ya mike yace yana zuwa .

Yana fita Abdullah yatashi ya koma daf da ita" inda take ya zauna har sai da ta dan kalleshi jikinsa a dan sanyaye ya kirawo sunanta bata amsa ba.
yarigada ya saba da hakan Amman yasan tana ji yace Aisha lokuta da dama abubuwa suna samun mutun iri iri ya zamo yawanci duk inda ya juya bbu dadi har ya dinga tsammanin ko shi kadai ne ba'a so ...
Amman duk wannan ana gwadawa ne a gareka a ga yadda zaka dauki al'amarin kafin daga baya alkhari yasameka.
ka dinga ganin kmr kai ake so.
yayi shr yana dubanta kanta a sunkuye yace Aisha a da ina tunanin rabuwar da tashiga tsakaninmu mun shiga wani tashin hankali ne na rayuwa.
na rabuwar kusanci da mukayi Amman tun yanzu na gane cewa ni kadai na shiga halin tashin hankali Amman ni din ma ga shi Allah ya wanke min da alkharinsa da ban taba samu ba sai a tare dake .

Kiyi hakuri dan Allah Aisha komai ya wuce shi kansa danmu sai yafi alfahari idan ya bude ido ya ganmu tare dashi
sai yafi yin farinciki .
har alokaci bata dago kanta ba hawayen takaici ne duk ya dameta a idanunta .
kawai Abdullah zai sake dawowa ya yaudareta tana zaman zamanta lafiya ahankali yasake kiran sunanta ta dago suka hada Ido ganin da yayi zatayi kuka yasa ya dada rikicewa ya kara matsota sosai kmr zai cire mata abinda ke damunta .
Matar Dr ta fito tana ganinsu haka da sauri ta juya ta koma .
su duka biyun suka bita da kallo har aka kira sallah magariba har sannan bata ce komai ba Abdullah kadai ke maganarsa ita taji ta hakura da abinda a kamata ya wuce har a cikin zuciyarta .
Amman ita kam bata kara yarda Abdullah ya Kuma yaudararta ta kuma komawa aurensa.
anan gidan sukayi sallar magrib har isha'i matar Dr sagir tayi saving dinsu abinci Amman shi Abdullah kasa ci yayi ganin har yanzu Aisha taki sakin ranta bare ita da tun lemun data dan kurba a tun dazu da suka zo da sister zahra.
har Dr sagir yana magana yace gaskiya Aisha abun naki zai zama da Kwara fa saboda bake kadai kike cin abinci ba idan baki ci ba na jikinki ba zai samu ba Abdullah ya kalli Dr sagir sannan ya juya kanta ya zuba mata ido yakoma kalar tausayi Dr sagir ya sake fita falon ya kara zama su biyu Abdullah yace Aisha tashi mu tafi na kai ki gidan inna.
Shr bata amsa ba sai daya sake dan matsota sosai yace kinga fa dare ya fara zamu takurasu .

Sai alokaci ta kalleshi itama tayi tunani haka tun farko ba dan zata takurasu ba ita ko akan kujera zata iya kwana. tunda dai tasan Abdullah ba zai barta ta fita ta je gida ba ..
da kansa ya nuna mata yes haka ne.
yace kinga damu zauna muna shiga hakkin wani gara mu tafi maganar ta dan shigeta dan haka ahankali ta mike.
ganin ta mike ne ahankali ya dan sauke numfashi sannan shima yamike yana kiran Dr sagir tare suka fito da matarsa da kyar Aisha ta kakaro murmushi karfin hali tayi mata sallama sannan tayi gaba abinta Abdullah kuwa suka jiro tare da Dr sagir hannunsu rike da juna suna magana da sauri Abdullah yakarasa ya bude mata kofar mota ta dan jima tsaye kmr mai tunanin kada tashiga. ganin dukkan idanunsu akanta yake yasa tashiga suka sake yin musabaha da Abdullah sannan da sauri ya zagaya yashiga dayan hannun ya tayar da motar Dr sagir ya sunkuya yana mata sallama Amman tayi banza dashi dan tasan duk dashi aka hada kai wajen rai namata wayo .

Ganin inda Abdullah ya tsayar da mota ne yatashi hankalinta ainihin gidansu na aure ne idan ba gezo idanunta kemata ba ai kuwa tana tabbatar da haka ta saka mishi kuka wato wani wayon ya sake mata ahankali tace ni gidanmu zaka kaini gurin innarmu haka kace .

Abdullah ya gyara parking ya juyo yana kallonta ganin ya tsayar da motar yasa tacigaba da kukanta .
Ahankali yace Aisha har yanzu baki hakura ba ?tace ni gida zaka kai ni sai da yayi wani tunani sannan ya rage murya yace kinga Aisha tunda kika baro gida na koma na gaya musu cewar zan biya na sauke ki dan haka duk su baba sun san yanzu kin gidana Aisha ta zaro masa ido tana yimasa kallon tsoro ya sake cewa kin san aurenmu ya maidu tunda nace na maidake yanzu matsayin matata kike .
Ai kuwa ta sake sakar masa wani sabon kukan tace ni bazani gidanka ba. ni gidanmu zani yayi shiru sannan yace to shikenan kiyi hakuri kiyi shiru .

Ta dan tsagaita kukanta yace kinga yanzu duk su inna su san muna tare tun karfe uku yanzu byn dare ya fara su ganmu mun koma musu .
me yuwa sun fara bacci baki ganin zasu dauka ko wani abun ne dan haka kiyi hakuri zan kai ki wani gida can ma gidan yan'uwane .
ki kwana inyaso Gabe sai naje na daukeki na kai ki gidan yafi muje musu da wannan daren.
tayi shr tana jinsa ya Kuma cewa kiyi hakuri muje can din duk gida ne a gurinmu shirun tayi ta sakeyi shirun da tayi ya fahimci ta amince .
Dan haka ya juya kan motar .

Masu gadin gidan suka bude musu get kafin ya karasa filin inda motoci suke yayi parking sannan ya dan kalleta yace ina zuwa ya fita can gurin masu gadi yana kiran yahuza ya karaso da hanzari daga inda yake dana tunda ya hango shi din ne yataso .
Abdullah yace yaje ya bude part dinsa .
,key din ya amsa da sauri ya tura cikin aljihunsa ya tafi ,. Abdullah na nan na jiransa har yahuza ya dawo ya Mika masa key ya karba yasa a aljihun wandonsa na baya.
Chapter 17 · 0% Book details