← Book details Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 34

Sashe 1

Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗
An dauko wannan littafi daga shafin www.hausanovels.com001.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348138892814

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.hausanovels001.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348138892814 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

AISHA A BAGUDO

Page 41-42

Jikinasa yaji a lokacin ya daina rawa sai babban dan yatsan kafarsa kadai ke motse .
ya dubi takardar gabansa ya dinga kallonta tamkar ma ba takarda ba.
yana jin hayaniyya akansa Amman baya gane abinda ake fada ba.
ya dauki Biro ya daura akan pepper sai ya tsaya shi kwata kwata bai san yadda ake rubuta saki ba .
Mama hafsa da ta fahimci haka tace sawa zakayi kai Abdullah ka saki matarka Aisha saki uku shikenan.
ka huta da jaraba .

Minal ce ta fado falon ta tana kallon inda yake zaune kmr gunki.
Byn tagama jin duk abinda su mami ke cewa.
ta tuna da maganar malamin dayake zuwa yana koyar dasu har gida a fannin addini yabata yi musu bayani game da babin aure da saki .
yace Allah da kansa ya halicci saki Amman baya sonsa mafi kysunsa ne ayi saki daya .
dan haka ranta dake mugun bace " ta isa gurinsa tace yaya ance ba kyau a saki macce saki uku .
saki daya ma yaisa dan haka ka rubuta saki daya .

Mami ta daka mata wata irin tsawa da frigita gabadayansu, dole ta bar falon .
da yake itace magana ta karshe da minal tai masa dan haka ya rubuta saki daya ya turawa mami takardar kusa da kafarta.
ya dafe goshinsa da kirjinsa lokacin daya ya fita haiyacinsa wani juwa yaki kansa nayi Amman yana nan a gurin bashi da niyar barin gurin .

Mami ta dauki pepper ta duba ta Gani tace ko rabin saki kamata nagode balle odindin daya.
Tace kana iya fita .
ta Mike tsaye itama mama hafsa ta karba ta Gani tace an dai rubuta sakin .
yanzu nan za'a kai mata mami tace yanzu kuwa tun dare bai mata ba aje akwana cikin duhu a gidan gyatumi tace eh .

Aisha na nan kwance yadda Abdullah yabarta Amman kmr anyi mata duka haka tarinka ji ajikinta da zuciyarta tamkar yadda ta ji a dazu.
ahankali taji karar mota bbu wanda ta bawa ranta sai Abdullanta ne .
ta danyi murmushin ta sake kudindinewa.
wai idan yashigo ya dauka tayi bacci ,.
Amman a yadda ta jiyo ana bude kofar cikin gidan ana shigowa da hargowa tasan bashi bane.
tayi sauri tashi ta zira rigar baccinta yayinda tarinka jiyo maganganu a falo ana hade kiran sunanta.
Yasa ta juya tana duduba gefe da gefenta ta wawuri wani zani da tayi wanka dashi dazu ta daura ta sanyo hijabin sallah ta fito .
Karo na farko kennan da mami ta taba ganinta .
a lokacin mami kmr ma ba a cikin haiyacinta take ba.
saboda tana son taga wacce mayyar yarinya ce ta kama mata ZUCIYAR Abdullah.
kawai taga fitowar AISHA.
ba haka taso ta ganita ba.
Yar yarinya Yar cikinta sai da suka kalli juna ita da mama hafsa .
akwai wani sirri dake jikin suruka da uwar miji wanda dukkansu sai da suka ji shi ajikinsu saboda shi dama namiji adan aka halicce shi daga jikin mahaifiyarsa byn wani lokacin sai ya koma jikin matarsa ..
to wannan sinadarin ma yayi matukar tasiri azuciyar kowanne su dan daga mami har Aishar haka sukaji .

Mama hafsa ma kanta saida ta Raina yarinyar tace ,"ho ni hafsa yanzu Abdullah kan wannan abar yake wani hauka da tashin kai .
ko me zai ci ajikin wannan "oho".

Mama hafsa Tace kinga ungo wannan kinji.
mijinki ne ya sake ki.
AISHA ta tsaya tana kallonta tana son manna mata hauka ta gane matar tun farko zuwan da suka yi gidansu.
mama hafsa tace karba ki duba mana kin tsaya kina bina da idannu .
idan kinga zaki iya tafiya yanzu to ga hanya nan a bude take idan kuma sai gobe ne ma duk daya.
Dan za'a kulle musu gida mami dake zaune kasa magana tayi.
AISHA tasa hannu ta karba takardar jikinta na rawa.
bata bude ba kmr yadda matar ta umarceta dan tasan haka din ne .
tunda ga mahaifiyar mijinta nan zaune .
Tana tsaye ta rasa abin yi ta sake ce mata ciki zaki shiga ki dauki abinda zaki dauka .
dan nasan kina fita zaki samu bus din zata kai ki wannan banzan lungun naku .

Ta juya ta shige ciki koda ta shiga din idanunta dishi dish bata ga wani abin dauka ba .
sai silifas din wanka tasako a kafarta ta fito.

minal ce ta fado .
kmr anjihota tace mata Aisha ki koma ki canza kaya ,
Aisha shr sai bin minal da idanu take minal tasake yin magana muke ki canza .
AISHA ta dan dube ta tace nagode minal bari naje kawai ahaka..

Minal tace to Amman...sai kuma tayi hade
saki hannunta ta shiga cikin dakin nata ta dauko hand bag dinta ta biyo ta dashi .
wanda a wannan lokacin har ta nufi get ,
minal tace direban dayakawo su mami yabita .
yakaita ka tabbatar ka kaita gida .
zaiyi magana ta nunashi da dan yatsanta tana huci tace wlh idan baka kaita ba idan dady ya dawo a bakin aikinka.

Tuni ya tsorota da maganarta dan yadda yakeji dadin aiki gidan idan ya rasa shi ai ji zai yi tamkar ya rasa ransa.
minal kuwa sai kwafa take tamkar dai yadda dady yake idan ranshi ya baci .

Dole tasa direba yabi bayan Aisha wanda har tayi nisa a tafiyar kafa .
Minal ta koma ciki ta riske mami tana kuka dama ita kadai ta biyo su
. ahankali tace mami meyasa kikayi haka byn kinsa kema kina da ya'ya mata , yanzu idan mu akawa haka wazakiji ....meyasa ma kike kinta byn ita din jininmu ce cikin sheshekar kuka ta juya ta bar falon mota tashiga ta tuka da kanta.
da hannuta da bai gama kwarewa ba.
dady ma ya hanata tuki Amman ba yadda taiya .
Da taimakon Allah tazo gida .
ita kuwa mama hafsa dadi goma da shirin kafin wannan gadddafin uban nasa ya dawo sai dai yatadda faiza a gidan haka ta rayawa aranta .

Koda ya sauketa da taimakon Allah tashiga lungunsu .
Amman tana shiga gidan ta yanke jiki ta fadi bbu wuta a garin lokacin.
ga sanyi kowa na ciki daki .
usman ne ya fara fitowa da kyandir yana haska jin alamun faduwa .ai kuwa
yaga Aisha kwance shame shame.
nan da nan ya jefar da kyandir din hannunsa yasa ihu .

Allah yasa kafin kyandir din yakara kasan ya mutu .
ya shiga kiran su inna kafin ma yayi wani yunkurin sai gasu gabadayansu banda aliyu har da mlm abu .
inna ta kamata agigice yayinda gabanta ke dukan tara tara suka dagata.
usman kuwa sai kuka yake yana kiran sunanta .
a dakin inna aka kwantar daita .
gabadayansu bbu wanda ya runtsa aranar.
Gashi taki yiwa kowa magana.
inna ce ta dauko rigarta ta sanya mata ganin yanayin ta jikinta ta bacci ce.
bata boye komai na jikinta ba.
sai da safe ne ma ya umar ya tsinci takardar sakin nata a zaure inda ta fadi .
Tun zuwanta sai yanzu aka fara gane kan al'amarin Amman har yinin ranar bbu wanda tayiwa kwakwarar bayanin abinda ya faru.
saki dai gashi nan a rubuce anyi shi.
mlm abu yake tambayarta itama iyakar abinda ta iya cewa kennan .
sakinta yayi bbu wani bayani data kara akan haka .
duk tsawon lokaci bbu wani mai cikakken sukuni a gidan.
mlm abu yace inda Allah ya rufa asiri shigar dare tayi bbu wanda yaganta da sun dada shiga uku ga masu zundensu sun siyar da yarsu .
Chapter 1 · 0% Book details