← Book details Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 34

Sashe 7

Zuciyar Masoyi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

faiza ta katse mama da cewa ni yanzu nafi so ayi abinda Abdullah zai dinga lashe ni tamkar dawisu saboda so shine kan gaba.
dan wannan jikin nasa idan ya kasance yana son mutun nasan zai sakaka ka more kuruciyyarka ka manta da kowa .
Mama ta zaro Idanu waje ka manta kowa fa najikince har dani ciki .
Faiza ta dan Susa kai ganin saba saiti . wayancewa tayi tace haba mama ai banda ai kece kan gaba in bake ai duniya zata min warbar kuno mama ta sauke ajiyar zuciya hade cewa abinda nake so naki kennan.
to kinga dama yau za'a gama abinda nasa ayi to kinga ko zuwa da yamma ne sai mutafi.
sai dai kuma idan duhu ne yayi .
sai mu bari sai gobe idan Allah ya kai mu .
ai baza mu tsaya kallon ruwa ba yanzu masha Kaye a gurin kwado suka sake kashewa faiza har jijiga jiki take zabar murna ...

Please kuyi manage da wannan kai ke ciwo😭😭😭

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 55

Bai san iya adadin cup din coffee da yaje sha a kullum kafin yabaro office.
Hotonta yana nan a bude a system dinshi ,shi ke tayashi hira da debe masa kewarta a duk sanda soyayyarta ta bijiroma masa , sannan yake samun ya gudanar aiyukansa .

Dady da kansa yace yadinga yin haka domin ya zama jarumi a office ko idan yana kallonta zai iya aiwatar da komai cikin natsuwa "batare da ansamu wata matsala ba .
Kiran dady ne yashigo wayarsa ya daga yana kallon hotota yasa hannu yana shafa beauty face dinta .
bangaren dady kuwa cewa yayi mhm Abdullah tell me tun safe zuwa yanzu sau nawa ka tuna Aisha?
Abdullah ya dan ciji karshen Biro da ke hannunsa yana tunanin. yayi dan yi murmushin takaici yace sau uku ne ma kawai.
shima sai yanzu dana bude system da rufewa nayi saboda ina son kammalawa da wani aiki ne .

Dady yace da kyau yarona kaga daga goma Sha ya fara raguwa gashi ya dawo sau uku .
Abdullah ya sake yin murmushin kadan dan shi kadai yasan halin da zuciyarsa ke ciki game da rashin matarsa ya dau cewa dady haka ne kawai ahankali ya sauke ajiyar zuciya sannan yacire white glass din dake manne da idaonsa.
ya jingina bayansa da kujera yana jujjuyawa ahankali manner da wayar a kunnesa yace dady akwai hanyar dana gano wacce tafi waccen saukin fahimtar komai ina ganin itace zata kawo karshen komai da muke bukata .
dady yace da kyau ina jinka Abdullah yace sai zuwa anjima idan na koma gida zan maka bayanin komai .
Da sauri dady yace shikenan sai ka koma din"Abdullah yace yauwa sannan yakashe wayar .

Yana juyowa ya sake ya zuba mata idanunshi yace kin gani ko Aisha komai na rayuwata ya canza, narasa farinciki da sukuni tun sanda kika tafi kika barni .
bana son a bani dariya saboda bana son nayi ,dariyar ki kawai nake so a tare dani .
gashi dady yace kada naje gareki ni Abdullah ya zan yi da rayuwata komai ya taru ya cakudemin waje daya.
rashin ki kadai ya isa ya tarwatsani .
shi kadai yake maganar shi tamkar wani zararre .
kawai idanunshi ya gane masa tana yi masa dariya ta cikin system dinsa.
ai ko yashiga danne danne a jiki yana sake neman ragowar hotunanta wai shi lallai sai yaga wushiryarta data yi masa dariya yanzu.
har sanda salis yashigo da coffee ya ajiye masa bai san wani duniya yake ba .
Sai can hankalinsa ya dawo jikinsa .
Gashi lokacin tashinsa ya kusa Amman baya kaunar abinda zai saya doshi gidan. sai yarinka jin gabansa na wani irin faduwa" tun kwana biyu da faiza da mama hafsa suka sauka a gidan,
yaji gabadaya baya son kusantar gida dan haka gurin Dr sagir kawai yace a wuce dashi dan shi kadai yake tayashi hirar Aisharsa in ba cin dady ya hana aje da tuni Dr sagir ya je masa gunta .
to zaune agun Dr sagir ne mami ta neme shi a waya" dan tasan lokacin tashinsa yayi daga office tashin hankali da mami ta sake jefashi da yaje kiran nata yafi wanda yake ciki a halin yanzu .
dan magana ce akan faiza ita dai lallai ita take son ya aura Kuma tana son ayi komai kafin dawowar dady .
Tana son faiza ta zama matarsa ta hakika .
mama hafsa dake kusa da mami ta kara tabbatar da hakan suke bukata ayi auren da wurwuri .

Abdullah ya zubawa maminsa ido shi kansa ya amince tun ba yanzu maminsa na matukar kaunarsa fiye da komai .
a tun sanda batun aurensa ya bulo ta sauya masa kar dai mami ta tsane shi ne ayanzu yaji gabansa yayi wani irin faduwa da sauri ya kauda wannan a ransa saboda dady ma ya hana shi ganin laifin mami yace yin haka bbu kyau .

Yarigada yasan halin dadinsa dan haka sai daya gama yi masa dukkan bayanin tsarin daya shirya game da masu son salwantar musu da dukiyar .
dady yayi shr yana jinjina kai yayi Ammanna da shirin Abdullah din.
da yaba masa Sosai da irin dabararsa a karshe har yayi masa godiya dasa masa albarka.
Bangaren Abdullah kuwa ba wannan ne a zuciyarsa ba .
dan haka yana gama jin dady shima ya dora akan sanar da dadinsa halin da'ake ciki na game da maganar auren faiza da ake ciki .

dady yayi dif ... Na wani lokaci wanda har Abdullah din yasake kiran sunanansa.
dady yace inatare da kai Abdullah ina jinka yadda Dady yaji aransa.
haka shi ma Abdullah din yaji.
dady yakira sunan Abdullah din rai a bace.
yace ka gane ko Abdullah duk abinda mahaifiyarka zata nema daga gareka kayi kokarin kaga kayi mata yadda take so .
kasan bbu abinda yafi uwa a nan duniya .
Allah (s w t) dan kansa sai da ya ambaci uwa uwa uwa har sau uku kafin ya ambaci uba sau daya.
Abdullah ya girgiza kai game da dan rufe idanunshi dady yace to kaga duk abinda zata ce kayi kai dai ka mata biyayya .
domin muma mun gama da iyayenmu lafiya.
jikin Abdullah yayi mugun tsanyi akan yadda Dady yace haka zaiyi Amman ana shi tunanin me yuwa a sanadin haka ya rasa Aisharsa na har abada.
saboda yasan muddin ya aure wannan faiza mutuwa zaiyi .
Tamkar dady yaji shi ya Kuma cewa kada Kuma kayi zaton aurenka da wannan yarinyar zai sa baza ka sake auren Aisha ba .
A'a kai namiji ne Shari tabaka damar auren mata fiyye da daya .
dan haka ka sawa ranka ko kayi wannan aure .
in Allah yaso Aisha zata dawo gareka kaji .
Abdullah ya amsa da to.

dady ya sake yin kasa da murya yace Abdullah na rokeka ka sausautawa zuciyarka damuwa nan kafin na dawo .
idan wani abu yasameka ban san yadda zanyi ba .
Bansa kalar halin dazan shiga.
sannan dady ya ajiye wayar ya jima zaube bai iya motsa jikinsa ba saboda bacin rai da yake ciki.
iyakar fushi yayi da mami sai a yanzu ya gano dalilin raba Abdullah da matarsa datayi.
ita ko tsoron alhakin yaron bata yi.
ko musu baya iya yi mata "tun bai kai haka ba Amman yau an wayi gari saboda wasu can masu kama kaman dagin ta raba danta da abinda ya kwalafawa rai .
ta batar masa da duk wata walwalarsa yake fada a ransa.
ba Abdullah din kadai ba hatta shi kansa abin kullum dashi yake kwana a ranshi .
gashi koda acikin hira taki yi masa zance idan sunyi waya .
shima Kuma ya dau alkawari ba zai fara sanar mata yasan da maganar ba.

Har ya kwashi mintina talatin da rabuwa da dady a waya.
Amman bai san cikakken tunanin da yake yi ba.
abubuwa uku sun taro sun cakude masa cikin kwakwaluwarsa.
Kuma duka atare suke tafiya ko wanne yana bukatar ayi solving dinsa.
Aisharsa auren faiza matsalar ma'aikata.
ya rike kansa da karfi dan kada ya tarwatse.
da kyar ya iya tuna dady yace ya dinga ya waita addu'a idan irin haka takasance dashi .
addu'ar yayi tayi har ya kara da sallah raka'a biyu a haka ya samu sausauci a zuciyarsa .
ko abincin daren ranar bai ci ba.
domin shi kansa abinci ma ba kalar raayinsa bane .
dan a Yan kwanakin mami gabadaya ta fita batun tattalinsa da abinda zai ci rawar jikinta akan faiza da mama hafsa kawai yakare .

Ko a washegari daya shiga gaisheta kafin fitar sa office .
karara mami ta nuna masa ita fa yanzu so take ya dauki duk abinda mama hafsa take bukata da mahimmanci tamkar ibadarsa data zame mata dole.
ya kalli mami kmr ya zubda kwalla dan takaici abinda tace.
Amman sai yace bbu komai duk yadda kike so haka za'ayi .
a hakan ya baro part dinta daidai zai fita falon ne suka kusan cin karo da faiza da sauri ya tunkudeta tun kafin takai ga jikinsa.
tayi taga taga zata fadi sannan ta rike bango ganin zai bar wajen ne yasa tayi saurin Sha gabansa ta tare shi wai tana son magana dashi kallon da yayi mata .
sai da taji shi har cikin hantarta .
nan tabi shi da ido har suka fice shi da salis .

Abdullah ya zagayowa mutanen su ta bayan gida ya kamo su ta inda baza suyi tsammaninsa ba.
mutun shida dama ake zargi sai gashi an kuma samu n mutun biyu a kasa.
takwas kennan abin mamaki sosai ragowar biyun din duk abokan dady ne na kud kud wanda yake ji dasu .
ragowar Kuma manya ma'aikatan company ne .
Chapter 7 · 0% Book details