Sashe 7
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Food is ready, maza ku zo ku ci kafin malamin lesson ya zo, ko kuna so ku yi latti ya yi muku bulala?"
Suka diro daga kujerar suka nufo abincin, Sulaiman ya zauna tsakanin Hadiza da Muniba, kafadun su na gugar na juna.
Ta sa murya ta ce,
"Fati!"
Ta fito sanye da hijab, da alama sallah ta idar, kallo daya Sulaiman ya yi mata ya dauke kansa, ya ci gaba da cin abincinsa.
Daga can bakin kofa ta tsaya ba ta karaso cikin falon ba, son addini irin na Fati yana matukar burge Hadiza ba kadan ba.
Ta ce, "Taho mu ci abinci in kin idar da sallar".
Ta yatsina fuska ta ce, "Na ci tun dazu, Alti ta zuba mini".
Don jikinta ya yi sanyi da hararar da Sulaiman ke zabga mata, bayan ita ko da gida da mota aka hada ta dama ba za ta ci abinci da shi ba, don ta ki jinin mutum mai halin GIRMAN KAI.
To a ganin ta halin Sulaiman kenan, babu wanda ke ganin walwalar shi sai 'ya'yan shi da matarshi, duk ilimin da ya ke takama da shi a ganin ta girman kai ba hali ne da ya dace da likita ba.
Ba ta san cewa shi ma bekenta yake gani ba.
Hadiza ta ce, "Don me ba za ki bari mu ci tare ba?
Kada ki sake yin haka".
Fati ta ce, "Haka nan na saba, ba zan iya cin abinci da mutane ba".
Sulaiman ya balla mata harara, ya dago a sukwane.
"Su waye mutanen?
Bakauya kawai, saboda ni ne ba za ki ci ba.
Na yi kama da rubabben saurayin ki ne?
Dube ta da Allah kullum da zumbulelen hijabi kamar takari, gara ma ki rage wannan zuhudun ko kya samu mashinshini, don duk mijin d aka bawa ke ko da sadaka ne an cuceshi wallahi wallahi, ko mata sun kare a duniya".
Fati ta harare shi ta zumbura baki kamar ta yi kuka, ta ce da Hadiza,
"Kina jin shi ko?"
Hadiza ta yi dariya ta ce, "Rabu da shi Fati na, ko shi din me zakiyi dashi?
Allah na tuba ko mutuwa nayi ai ya yi miki tsufa, me za ki ci da dan late thirty?
Sai yaro sabon jini kamar ki".
Daga Fati har Sulaiman, kalmar
mutuwa
da Hadiza ta ambatawa kanta, ta taba zuciyar su.
Sulaiman ya tsame cokali daga plate ya aje gefe yana bin Hadiza da wata irin harara da ita kadai ta san ma'anar ta.
Ita kuwa Fati ba ta kara tofawa ba, ta koma daki tana cewa cikin ranta;
kada Allah ya nuna min wannan ranar
., Yaya Hadiza sai dai ki yi min makoki, ba dai in yi miki ba
Kwana bakwai cif Sulaiman yana gida cikin iyalinsa bai je ofis ba, yana kula da lafiyar Hadizar sa.
Ta fuskar shan magungunan ta a kan lokaci, hidimar ta da walwalar ta, tare da ba ta karfin gwiwa na karbar rayuwa a duk yadda tazo, yana nuna mata kaddarar da ta same ta ba ta shafi ko kankani na daga soyayyar da yake yi mata ba.
Ta yarda, ta amince Sulaiman mai son ta ne, kuma irin mazan da da wuya a samu kamar su a wannan zamanin wajen rike alkawarin soyayya da sanin darajar diya mace.
A 'yan kwanakin ta kara samun karfin jikinta, don haka ta kirkirowa kanta abubuwan debe kewa da dama, wadanda a da ba ta da lokacin su, kamar karatun jaridu da mujallu,
Internet browsing
da kuma kasancewa full-time house-wife da 'ya'yanta suka kara shakuwa.
Abu na hudu da take ganin zai taimaka ainun wajen debe mata kewa shi ne, rubuta tarihin rayuwar ta a matsayin story-writing cikin harshen Hausa.
Wanda take so ta sanyawa suna
YAKANAH!
Da Sulaiman ya fahimci damuwar Hadiza ta ragu da 80%, sai ya samu kwarin gwiwa da jarumtakar fuskantar aikin sa.
Ya koma aiki ranar monday cike da tausayin Hadiza, yana mai tuno lokutan zirga-zirgar su cikin asibitin don ceton rayukan al'umma, da matsalar ta mai magantuwa ce ba ya tsammanin in zai rasa duk abin da ya mallaka zai gaza wajen nema mata magani.
A wani bangaren kuma yana tunanin shawarar su Dr.
Ruth ne da suka ce Hadiza za ta iya komawa aikin ta a haka.
Da ya tuntube ta, ta nuna ba ta yi na'am da wannan shawarar ba, don ba ta yanke kauna da rahmar Ubangiji ba, za ta zauna a gida ta yi zaman aure, wanda a da ba ta yi ba.
Ta ga shi kuma yaya yake?
Wace irin riba ce a cikin sa, tunda ta yi aikin, ta ga ribarsa da rashin ribar sa?
A wautar Hadiza, tunda wannan lalura ta same ta shikenan Sulaiman ya daina sha'awar ta, wato ya daina mu'amalar aure da ita, tunda ta nakasa, ba ta da abin da za ta ja hankalin sa.
Ba ta yi la'akari da cewa soyayyar ta a cikin jinin Sulaiman take ba, ba
a abun jan hankali ba.
Kwata-kwata sati biyu cur da fitowar ta daga asibiti, sai labari ya sauya, Sulaiman soyayya har ta fi ta baya, kamar wanda ya je ya kara yin course a kan (love-making) ga masu lalura.
Watakila da da hali da ya tsaga kirjinsa ya sanya ta a ciki, mai yiwuwa sannan ne zai zamo (contented).
Sai da komai ya lafa ya fahimci Hadiza kuka take, ba kuma kukan komi take ba,
.kukan rashin yarda da kai ne.
Amma shi duk sai ya rikice, kukanta da hawayen ta ba karamin daga mai hankali ya yi ba.
Ya tarairayo ta ya dora a kan kirjin shi yna mai shafar bayanta, cikin sassanyar murya yake tambayar dalilin kukan,
"Did I hurt you Hadizahh?'
Ta girgiza kai, cikin shesshekar kuka ta ce,
"Sulaiman kai ne???"
"In bani bane wane ne?"
Sai ta yarfar da hawaye da hannun daman ta, ta ce.
"Ni dai don Allah na rokeka, kayi min alfarma ka kara AURE!"
Sai ya janye jiki daga jikinta a hankali cikin mutuwar jiki da sagewar gwiwa,
"Kafin in baki amsa Hadiza, ko in bi umarnin ki, ina so in san mene ne dalilin ki na cewa hakan?"
Kai tsaye ta amsa.
"Saboda Hadizar da, ba ita ce yanzu ba, wannan nakasasshiya ce, ba ta cancanci wannan dimbin soyayyar ba".
Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskarta a dan hasken asubahi da ya soma keto shara-sharan farin labulen dakin, kamin ya yi murmushin takaici ya zauna sosai ya bata baya.
"Hadiza tafiyar ki ce ta sa na aure ki?
Ko ko yanga da kwarkwasa kika yi min na ji ina son ki?"
Ta girgiza kai, wasu tawagar hawaye na biyo idanunta.
"Babu ko daya.
Amma son da nake maka Sulaiman, ba zai barni in kware ka ba, idan ka ci gaba da zama dani ni kadai, na kware ka; a matsayin ka na lafiyayye kuma cikakken namiji.
Idan ka kara aure zan ji dadi, zuciyata za ta sake.
Akalla ina da tabbacin baka cikin kwaruwa, amma yanzu sai nake ganin, na kware ka........
I'm nothing but a burden to you.....".
Ya daga mata hannu ya ce, "Ya isa, ya isa Hadiza...." Ya ma rasa me zai ce don takaici, sai ya karkada kai ya fita ya bar mata dakin.
Kwanaki uku suna kan wannan takaddamar.
Hadiza ta dage ta ja tunga a kan bakanta, in ya yi fushi sai kuma ya sauko ya yi dariya don mamaki.
Yau Hadiza ke neman kai dashi.
Hadizar da ko kallonsa bata so mata su yi in ba bisa dole ba.
Ba ya son duk wani abu da zai bata ranta a dai wannan lokacin da yake angwancewa bayan shan jinya ta lokaci mai tsaho, da kuma yin la'akari da halin da take ciki.
Don haka a rana ta biyar da ya ga ba zai iya jure wannan horon da ta tsiri yi mishi ba, don ba shi da juriyar a wannan fannin ta inda take samun weakness din sa kenan.
Sai ya kama hannayen ta ya langabar da kai kamar karamin yaro, idanuwan nan sun juye sun rikide zuwa damuwa tsantsa.
Ya ce, "Hadiza na baki wuka da nama, ke ce mijin ke ce matar, ki zabo min duk yarinyar da kika ga ta dace dani, don bani da idon kallon wata diya mace, tun daga lokacin da Allah ya mallaka min ke......".
Ta cira kai a hankali ta dube shi, sai ya bata tausayi, don numfashi kanshi a wahale yake furzar da shi da sauri da sauri.
Ganin yadda jidalin ta ya ramar da shi kwanaki biyar kacal, sai ta kara jin tausayin sa.
Amma jan ajin mu na mata, sai ta balla masa harara wadda in ka lura ba komi ne cikin ta ba face tsananin son mijinta da matsanancin kishin sa, ganin daga karshe din kuma ya sauko ya bi ra'ayinta kamar yadda take so.
Kamar ta yi kuka ta ce,
"Nice ma zan nemo maka matar?
Ashe you are not serious
Ta juyar da kai, sai ga hawaye sharrr!
Sun zubo a kan kundukukin ta.
Kiris ya rage dariya ta kubce masa, amma ya danne kada ya kara laifi.
A gicciye ba tare da ya dube ta ba ya ce, "Wai ko a cikin student din ward din ku, irin 'yan yara-yaran 'yammatan nan?
Ko rikakkun 'yammatan likitoci irin su Dr.
Surayyah".
Haushi ya kama Hadiza, don ta lura ya mai da abin zolaya.
Ta yi shiru ba ta ba shi amsa ba.
Ya rungumota ta baya, ya dora kan shi a kafadun ta, yana sakin ajiyar zuciya mai nauyi.
A sanyaye ya ce,
"Ko kin daina sona ne Hadizahh?
Kike neman kai dani?
A da ko kallo na wata ta yi, kallon da bai yi miki ba, sai kin kwana bakya yi min magana, amma yanzu duk kin daga hankalin ki wai in yi aure.
Which means...... na gundire ki
. kina neman mataimakiya don ki huta
Ni ina ruwana da wasu kafafun ki tunda ba su nake aure ba?
Inda nake aure zam-zam yake.
Da aka yi accident din ma, kamar an kara masa armashi.
Kafafu?
Ni ba ina da su ba?
Kuma ba ina daukar ki dasu ba?
To meye damuwar ki?