Sashe 20
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
An ce mai da wawa, kulawar da take yiwa
yan shi ya taka rawa ba kadan ba, wajen sayo mata soyayya ta kwarai a zuciyar shi.
Kafin wani dan lokaci sun kimtsa tsaf suna falo suna jiran shi, ya fito cikin wagambari shudiya mai hasken sararin samaniya, wato navy blue, hannun shi na hagu daure da agogon RADO na bakar fata, haka takalmin da ke kafar shi wanda ya kasance budadde na fatar damisa.
Babu gilashi a idon shi sai fararen idanun shi ke sheki da daddadan kamshin
Chris Adams
da ya baibaye su.
Yaran suka nufi jikin shi, ya kama hannun kowannen su suka nufi harabar adana motoci, ita kuma ta koma kitchen ta juye dambun naman da suka yi gaba daya ta taho da shi don ta kai wa Inna.
A wajen shiga mota ne ake dirama, yana son ganin in da za ta zaba don zama don son sanin matsayin da ta aje shi, tunda
yar gaisuwar da ta ke mishi ma a darare ta hakura ta daina, tunda baya amsawa.
Ta bude gidan gaba su Munib suka shiga, sannan ta sunto goyon ta shiga baya ita da Alti.
Har suka hau titin Kabuga babu wanda ya yi magana, sai yaran da ke ta rigima a tsakanin su a kan jirgin sama mai batir na Munib da Muniba ta dage sai ta amsa.
Ita dai Alti shiru ta yi tana nazarin su, ga dukkan alamu kowannen su ya sauya, ya yi sanyi, amma an rasa wanda zai sauke ya bi dan uwansa.
Tana son ganin wanene zai yi jarumtakar tsaga billensa ya bi dan uwansa?
Wadannan ma
aurata suna ba ta dariya, ganin har ta cikin mudubi satar kallon juna suke, amma in daya ya kama daya sai a yi maza a fuske, a dauke fuska, wato babu shiri babu alaka.
Tafiya ta yi nisa a kan kwalta, barci ya fara daukar Alti, yaran tuni sun yi barci har Nana, ya mika hannu ya rage musu karfin na
urar sanyaya mota.
Kawai Sulaiman ya faka motar a tsakiyar daji, ya wani irin juyo ya dube ta, an yi sa
a ita ma a lokacin ta dago daga madara da take bai wa Nana, idanunsu cikin na juna, wani miracle ya yi aiki cikin
yan dakikai, ya haifar da wani al
amari mai GIRMA a zuciyoyin su.
Ji yake kamar yana yi mata kallon karshe ne, ya tuhumi kanshi da rashin sauke wani nauyi mai girma da Allah ya ce ya yi, ga shi har zai tafi, tafiyar da babu tabbacin zai dawo ko ba zai dawo ba, tunda rayuwar ba a hannunmu take ba.
Ya samu kansa da son tausasa mata, ko babu komi yana son goge mugun tabon da ta yi mishi a zuciyar ta.
Ya tabbata idan Inna ta san har zuwa yanzu bai kula ta ba, la shakka za ta dauki mataki, duk da ya san da wuya Fatin ta gaya mata, tunda ba ta da magana.
Amma in Inna ba ta sani ba ai Allah ya sani, kuma ba zai kyale ba.
Ya mika mata hannu,
Kawo ta in taya ki rainon
Ta galla mishi harara, sannan ta kara kankame
yarta.
Ya yi murmushi ya ce,
yar gaisuwar da kike min kin daina, why Fati?
Wannan karon ma ba ta yi mishi magana ba, amma ta tsuke baki ta juyar da kai.
Ya yarfar da hannu,
Tunda kin ki mu yi hirar bari mu karasa gaban Inna, watakila ita za ki yi mata bayanin dalilin ki na daina gaishe ni a matsayina na mijin ki da kuke kwana gida daya ku wayi gari cikin gida daya, zan gaya mata
yan ki kawai kika sani, amma ni kin daina shiga sabgata, kin mai dani saniyar ware, dan gyaran dakin da ake min tun daga ranar da kika yanke hannu kin daina.
Haka nan zan iya tunawa cewa, tun daga ranar ne kika daina gaishe ni
Nan ma shiru, kamar da dutse yake magana.
Haushi ya ishe shi ya fizgi motar.
Bai kara tsayawa ba sai a kofar gidan su cikin garin Bakori.
Malam Sulaiman na alwala a kofar gida lokacin da suka isa, ya soma maraba da
yan jikokin shi.
Suka dunguma suka shiga gidan tare, Inna na sallah lokacin da suka shiga falon ta, sai da ta idar ta shafa addu
a, sannan ne ta karvi Nana a hanun Fati, tana yi musu sannu da zuwa.
Alti tana daga waje, yaran ma Khalid ya shigo sun bishi shagon sa, falon ya rage daga Inna sai Malam, Fati da Dr.
Sulaiman, hira ce suke sosai a junan su, ba ta tsoma musu baki ba.
Can anjima ya dubi sashen da take ya yi mata wani irin kallo da ya sanyaya gangar jikinta, ya ce,
Na kawo karar Fati Inna, ta daina gaishe ni, ga shi ban san laifin da na yi mata ba, na tambaye ta ta yi min banza
Kunya ta kama ta, ta mike za ta fita Inna na ganin yadda ya bita da kyawawan idanun shi kamar ya fasa kuka, ta yiwa Allah godiya cikin zuciyar ta, ta tabbata Sulaiman ya fara son matarsa, addu
ar da ta ke kwana da yini tana yi ba ta fadi a banza ba.
Ta ce da Fati,
Koma ki zauna
.
Ba musu ta koma ta zauna, amma ba ta kara hada ido da kowa ba, ji take dama kasar ta tsage ta shige saboda kunyar da Baban Munib ya bata.
Inna ta ce,
Wai haka Fatima?
Malam kuma ya ce,
ah!
Fatima ba za ta yi haka ba haka kawai, kai dai ka san laifin da ka yi mata
Bai yi magana ba.
Inna ta ce,
Me ya yi miki Fati?
Na san ba shi da kirki
Da kyar ta ce,
Ni bai yi min komai ba, bana ganin sa ne
Inna ta ce,
Koma ya yi, ki yi hakuri kin ji Fati, komi na duniyar dan hakuri ne da yafiya (afuwa), kowa hakuri yake da abokin zaman sa, ta hakan ne za a ci ribar zama amma ba ta kullaci da rashin afuwa ba
Sai ta ga kamar Inna ta shiga zuciyar ta, da gaske ta kullaci Dr.
Sulaiman kullata mai yawa a kan abin da yake yi mata, duk da ta fahimci shi ma ya sakko yana son a shirya, amma ba za ta yarda a shiryan haka (so easy) ba.
Ya kuntata mata, ya cuzguna mata yadda harshenta bazai iya bayyanawa ba.
Wanda tun farko ya riga ya ce ba ya son ka, daga baya ya dawo ya ce yana son ka akwai dalilin shi na yin hakan.
Change happens only on reasons.
Amma ba za ta iya yin musu da Inna ba, don haka ta ce,
Na yi hakuri Inna.
Shima Allah ya huci zuciyarsa
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Munib da Muniba suka shigo, sai suka tsaya saroro suna kallon sa, sannan suka tafi da gudu suka rungume shi suka soma zubo masa hira.
Inna ta kawo mishi waina da taushe ta ji tantakwashi da lemukan zobo da na Aya da ta ke siyarwa cikin firjin da ya saya mata.
Fati ba ta shigo ba, tana gama wankinta ta shanya ta dau mayafinta jikin igiya ta gudu makota gidan wata makociyar Inna Goggo mai gyada.
Ba ta shigo gidan ba sai bayan azahar, lokacin shi da Malam suna kofar gida suna sallah da mutane.
Ta zaga ta bayan su ta shiga gidan ta shige uwar dakin Inna.
Ya dawo dakin Inna suna hira, shiru-shiru bai ga Fati ba.
Ya ce,
Wai yarinyar nan Inna gudu na take yi?
Ta ce,
Ni ina na sanar muku, ai kun fi kusa
Ya ce,
Tana ina ne?
Ta nuna mishi uwar dakin ta da dan alinta, ita kuma ta fita don ta dora sanwar dare.
Tana jin shi zai shigo ta yi linkim a gadon Inna, ita a dole barci take.
Ya karaso ya zauna a saitin kanta yana kallon kyakkyawar fuskarta ta dan hasken tagar Inna da ya ratso, babu wadatar haske a dakin don haka ya fiddo wayar shi yana haskata sosai.
Ta soma rikide mashi tana komawa Hadiza!
Kanshi ya dinga zagayawa jiri ya soma diban shi, a lokacin da ya soma romancing din ta da fuskar Hadizahh
Ta yi wani irin juyi ita a dole barci take, kamin wani dan lokaci al
amura suka rikice musu, tun tana pretending har al
amarin yafi karfin kawaicinta da juriyar ta.
Jin maganar Inna a falo ya sa ta daddage ta kwaci kanta, jikinta babu inda ba ya rawa saboda firgici da sabon al
amarin da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
Idanun shi a galabaice ya ce,
Haba Hadizah!
Don Allah Hadizahh.....!!
Wani haushi ya kama Fati, karona farko a rayuwarta da kishin Hadiza ya darsu a ranta, wato ma da sunan Hadiza yake alakanta ta, sannan ne zai iya auratayya da ita?
Za ta fita ya cafke hannun ta, ta wani irin juyo tana hararar sa.
Wai an ce aikin banza, harara a duhu.
Don kuwa bai gani ba.
Shi ma ya juyo kukan Nana da maganar Inna, don haka ya yi saurin sakin hannun ta, ta fita amma shi bai fito a lokacin ba, sai da ya daidaita kansa tukunna.
Sai dai fa shaddar Ghanilla baka wul duk ta yamutse.
Yana tsaye a falon Alti ta shigo suka gaisa, ya ce,
Goggo Alti sai ku shirya tafiya zamu yi
Ta ce,
To ranka ya dade
Fati ta kwakkwabe fuska ta ce,
Nifa Inna sai gobe zan tafi
Inna ta ce,
a, ga mijin ki ya zo tun daga wata uwa duniya ai wurin ki ya zo, yana bukatar kulawar ki, tashi ku tafi idan ya koma sai ku dawo, mu kullum muna maraba daku
Ba da son ranta ba ta tattara kayan su suka tafi.
Wannan karon ma a baya ta zauna ita da Alti, duk yaran har Nana suna gaba.