← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya ta ji dadin ganin su, fes dasu cikin koshin lafiya, wanda ke nuni da cewa babu abin da suka nema suka rasa.

Dr.

Sulaiman ya tsaya musu a kan komi.

Alti na tsakar gida, ita da Yaya suna daki suna hira irin ta da da mahaifi, ta ce,
Dazun nan nake ce da Sulaiman kun kwana biyu baku zo ba, ya ce karatu ne ya yi miki zafi ashe kuna tafe
Mamaki da haushi suka kama ta, wato yana kiran kowa har
yan shi yana kira a makaranta ofishin malaman su su yi hira ya ji lafiyar su, ita ce dai ba ya kira don har yanzu yana kin ta, don rannan Munib yake gaya mata wai Daddy yana gaishe ta.

Ta ce,
A ina ka ganshi?

Ya ce,
Waya muka yi a school
Sannan ga shi yau Yaya ma ta ce yana yi musu waya.

Duk inda ranta yake in ya yi dubu to ya baci, har Yaya ta lura kamar ta yi shiru tana tunani.

Ta ce,
Lafiya ko?

Ta yi saurin girgiza kai,
Babu komi
A dakin Baban su bayan sun gaisa, ta tambaye shi jiki ya ce ya ji sauki alhamdulillahi.

Sannan ya ce,
Fati har gobe ba zan daina sanya miki albarka ba, saboda yadda ki kai mana biyayya kika zauna lafiya a dakin mijin ki, duk da na san ba da son ranki aka yi auren nan ba.

Biyayyar ki da YAKANAH
. ni na gaya miki ba za su tashi a banza ba!

Allah ya baki
yan da za su yi miki biyayya fiye da yadda ki kai mana
Idanun ta suka cicciko, kamar ta gaya mishi cewa har yanzu Sulaiman ba ya son ta, da yana son ta da ya damu da lafiyar ta.

Amma ko ya take tsayin shekara guda bai taba cewa ba.

Idan kuma ta yi tunanin sauyikan da ta gani a tare da shi kafin ya tafi, sai ta samu kanta cikin rudu a kan al
amuran Dr.

Sulaiman, ta kasa tantance cewa yanzun yana son ta ko ba ya son ta?

You are darling!

Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi
Ta tuno kalaman shi ana i gobe zai tafi.

Gaba daya maganganun da suka yi a ranar take tunawa filla-filla, wadanda in aka auna su a ma
auni na hankali da tunani suna nufin Dr.

Sulaiman ya sauya muguwar fahimta da akidar shi a kanta.

To amma why yake kin neman ta a waya ko common gaisuwa ce su yi?

Me hakan ke nufi?

Babu wanda zai amsa mata tambayoyin ta sai shi.

To ina za ta gan shi?

Ta MAIRON HURE da ta ce,
He is far away.....
(Ya yi nisa).
****
Da la
asar sakaliya suka yi shiri suka nufi Bakori dukkannin su, za su yiwa Inna week end (hutun karshen sati).

Direba Malam Habu ne ke jan su, zuwa karfe shida na yamma suna cikin garin Bakori.

An yi sa
a Saude, Ruma da Anti Ramatu kannen Sulaiman duk suna gidan sun je biki sun dawo suka zarto wajen Inna.

Don haka falon Inna yau ya yi albarka, ya kauraye da hira.

Ita dai Fati ba ta magana illa in anyi abin dariya ta yi murmushi, suna son yarinyar sosai saboda sanyin ranta.

Anti Ramatu da yake sarkin barkwanci ce, ta ce,
Fati sai yaushe za mu zo suna ne?

Mun kosa fa Nana ta samu kani ko kanwa
Kunya ta kama ta, musamman da yake Inna tana wurin.

Ta rufe fuska da mayafinta, haka suka yi ta tsokanar ta su lallai suna jiran baby da Yayansu ya dawo.

Wayar Inna ta yi kidi tana neman agaji, Inna ta amsa cikin nutsuwa don ta gane lambar ta Sulaiman ce.

Bayan sun gaisa ya ce,
Hirarrakin me nake ta ji haka?

Ta ce,
Su Ruma mana, sun sanya Fati gaba duk sun hanata sukuni, gasu nan sun zo dukkannin su baka ga yadda Nana ta yi wayo ba
Ya lumshe ido yana sauraron Inna, amma bai ce ta ba shi Fati ba sai
yansa.

Sun dade suna ta shirmen su kamar ba kudi suke narkarwa ba, har gwalantun Nana an sanya mishi ya ji, sannan suka shiga gaisawa da kannen shi.

Ya ce,
Ina Khalid?

Inna ta ce ya je Malumfashi ta aike shi wajen Inna Atika kanwar ta.

Cike da kewa ya yi sallama da su, ya koma ya kwanta ya ta da kai da hannayen shi a rest chair irin kujerar nan da turawa ke sakawa da zaren roba da katako.

Ya mika hannu ga zungureriyar robar coca-cola ya daga, ya tashi zaune yana daddaka.

Sanyin lemon da karfin
gass
din shi na soya mishi makoshi, amma bai kula ba.

Ga wanda duk ya san Dr.

Sulaiman-Sulaiman a da, lokacin Hadiza, ya kuma gan shi a yanzu, to ba zai gane shi ba.

Gaba daya ya rame, ya kara yin duhu, sai dai hakan bai boye zahirin kyawun halittar sa ba.

Ba abin da ya sa gaba sai abin da ya kawo shi, sai dai hakan bai sa tunanin yarinyar ya barshi ya huta ko na second daya ba, kamar yadda ya yi tsammanin nisa da ita shi ne hanya mafi sauki da zai yaki kutsowar soyayyarta.

Ashe hakan tamkar zubawa wuta fetur ne?

Tunanin sa na cewa yin nisa da Fati shi ne babban makamin yaki da farmakin data kawowa rayuwarsa ashe ba shi ne maslaha ba.

Abinda bai sani ba sai bayan tahowarsa Fati ta riga ta yiwa zuciyar shi kamun kazar kuku, ta yadda dai-dai da rana daya tun tahowar sa zuciyar sa ba ta taba hutawa ko na dakika da tunanin ta ba.

Dr.

Smith ya iske shi a hakan, ya dade yana magana bai san yana yi ba.

Kafin dan lokaci ciwon ciki ya turnike shi, ya kama cikin ya soma juyi, sai ya fado bisa kilishin dake shimfide a farfajiyar wajen.

Da sauri Dr.

Smith baturen Chicago ne na asali, ya kama shi ya soma binciken abin da ke damun shi, tare da ba shi taimakon gaggawar duk da ya dace.

Bai samu kansa ba sai bayan awanni biyu, lokacin ciwon cikin ya lafa.

Ya sa ido yana kallon Dr.

Smith wanda ke shan lemo a gefen shi, shi ma kallon shi yake amma bai fasa shan lemon sa ba.

Ya mike zaune a hankali suna kallon-kallo.

Dr.

Smith ya dauke kansa ya ce,
A lokuta da dama bakar fata ku kan birge ni wajen rike amanar matan ku, mazanku da matan ku, da wuya daya ya ci amanar daya a cikin aure.

Wannan dabi
a ce mai kyau, in ka san ba za ka iya zina ba, me ya hanaka tahowa da matar auren ka?

Sai ka zauna kana tara abu har sai ya kashe ka a banza?

Ya aje tambulan din hannunsa ya dubi Dr.

Sulaiman sosai, ya ce,
Don me baka taho da matarka ba, alhalin gidan da aka baka yalwatacce ne?

Sannan dai-dai gwargwado ba za ka kasa rike ta a nan ba.

Tun wancan karon na gaya maka abinnan yana barazanar kwantar da kai, wanda in ka ci gaba da tara shi zuwa wani lokaci sai anyi maka aiki.

Duk me ya yi zafi?

Ka aika matar ka ta zo, mene ne wahala a ciki?

A sanyaye ya ce da shi,
Hadizah ta rasu!

Dr.

Smith ya ce,
Oh dear!

Tun yaushe ne?

Ya rausayar da kai ya ce,
For almost a year and a half kenan
Smith ya ce,
Why not ka kara yin wani auren Dr.

Sulaiman?

Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, har Smith ya kara maimaitawa.

Ya dago idanun shi da suka shagide ya dube shi.

Ina da wata matar Smith
To me ya sa baka taho da ita ba?

Ya yi murmushi ya ce,
Ba zan iya bane, saboda kanwar mata ta ce, auren hadin iyaye aka yi mana
Which means
.. baka son ta
Ko ina son ta ba zan iya hada jiki da ita ba!

Idan na yi hakan GIRMA NA ZAI FADI A IDANUN TA.

Ka gane, ina tattalin mutunci na ne, duk da Hadiza da kanta hakan take so kamin ta rasu, wato
yar uwarta ta maye gurbin ta, amma ni ba zan iya ba!

Smith ya ce,
Wannan shirme ne, baka da hujja kwakkwara.

Idan har kana son matarka ka aje girman kan nan ka daidaita da ita, domin kana zalintar ta.

Kana zalintar kanka.

Dubi yadda kake suffering (wahala) baka tunanin ita ma haka take, sai dai ta nuna kawaici?

In kuma baka son ta ne ka sahile mata ka ba wa iyayen ku hakuri, ba za ta rasa mai son ta ba, kai ma ba za ka rasa samun wadda za ka so ba.......

Ya yi saurin katse shi da cewa,
Babu saki tsakani na da Fati, har abada, babu.

Ko bana son ta balle halayen ta da nagartar ta sun sayo mata soyayya mai yawa a gare ni.

Hujjar nan dai da na gaya maka ita ce, wato tana ganin girmana bana so ta raina ni, bana so GIRMA NA YA FADI a idanun ta
Abin ma sai ya baiwa Smith dariya, ya murmusa ya ce,
Babu zancen raini a harkar aure, ka yarda dani Dr.

Sulaiman, ka daidaita da matarka don samun lafiyar ka da nutsuwar dukkanin ku, sannan da albarkatun da ke cikin aure.

Poor Fati!

Na tausaya mata, aure kusan shekara biyu ba ta san albarkar da ke cikin shi ba.

Wallahi ka yi a hankali, tun hakki bai kama ka ba
Da maganganun Dr.

Smith ya kwana, yana cizawa yana busawa.

Ta yaya zai doshi Fati da bukatar aure?

Gaskiyar Hadiza ne he is not taking things easy (ba ya daukar abubuwa da sauki).

Fati yarinya ce mai hankali da zuzzurfan sani a addini, mawuyaci ne ta raina shi don ya gyara rayuwar auren su.

Ya juya a hankali ya rungume filo, ya samu kanshi da flashing no Fati, cikin shekara daya da rabi da ya yi bai taba kiran ta ba, don ko abin ya ciyo shi ya dauko wayar zai neme ta fasawa yake yi.
Chapter 25 · 0% Book details