Sashe 16
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar da kika gaji, ki gaya min in maida ke gida, kina ji na?'
Cikin kuka ta daga mishi kai, ya saki kunnen ta ya ce, "To kwashe su a nan tun ban yi ball dasu ba, kema in babballaki". (Yana nuna wa da hannayen shi irin yadda zai babballa ta din).
Jikinta na kyarma ta kwashe ta yi kitchen dasu, ya ja tsaki "Tsuu
." A ranshi ya ce,
"Kai!
Inna da Malam sun takaice ni wallahi, me zan diba a jikin wannan fingi-fingin?" Ya yi ball da filon da yake kwance ya mike ya nufi (exercise area) din sa.
Fati bata daddara ba, washegari tunda ta tashi da asuba ba ta koma ba, kitchen ta shiga ta shirya kalacin funkason alkama da miyar agushi.
Wanda ta kwaba tun daren jiya.
Ta kara da Quaker oat da plantain soyayya ta aza a
master dining
din shi kamar yadda ta ga Hadiza na yi.
Da gudu ta koma daki ta kulle, yana fitowa zai fita rike da
brief case
ya yi tozali da sabbin warmers, sai kamshi ke tashi bisa dining din shi.
Da gaske yunwa ta gallabe shi, hanjin cikinsa har rawa yake.
Sai dai yana ganin idan ya ci ya zama sakarai tunda ga abin da ya ce da ita jiya, kuma raini zai gitta.
Don haka ya hadiye azababbiyar yunwar shi ya fice. yana shiga AKTH ya nufi gun cin abincin manyan likitoci na asibitin, can ya yi kalacin sa.
Sai dai a bakinsa babu dandano, don Hadiza ta riga ta sangarta shi da cimar Fati mai dadin da ba ya misaltuwa, ya kuma fi na Goggo Alti wadda a da yake ganin babu wadda ta kaita iya sarrafa abinci, musamman na Hausawa wanda ya fi kama mishi ciki kasancewar shi ma'abocin tara yunwa kafin ya yi quenching din ta.
Da ta tabbatar ya fita, ta fito ta bude ma
adanan abincin, babu abin da aka taba.
Bata ji haushi ba, ta tattara ta mikawa Malam Ilu bayan ta dibi iya wanda take ganin za ta iya ci, ta koma daki ta yi wanka sannan ta zauna cin abinci.
Tana kammalawa wayarta da ta sa a caji ta yi kara, ta amsa cikin kamilalliyar muryar ta, Inna ce.
Suka gaisa, sannan ta mikawa Malam Sulaiman shima suka gaisa.
Ya yi mata addu
a sosai, ya kara da cewa, ta jure duk wani rashin jin dadi da za ta fuskanta daga mai sunan shi, nature (halittar shi) kenan, fara nuna kiyayya ga abu kamin ya so shi.
Da yardar Allah watarana za ta tashi da riba.
Ranta ya yi fari, zuciyarta ta yi haske, a kalla ta san ta samu surukai na gari da ke son ta.
Ta kara jin karfin gwiwar son ci gaba da kyautatawa Sulaiman, ba don ya yabe ta ko ya so ta ba.
Ita ma ba son na shi take yi ba, sai dai ba za ta iya yin watsi da al
amarin shi kamar yadda ya bukata ba, saboda alkawarin da ta daukar wa Hadiza, ta tabbata sakayyar ta na wurin Allah.
Don haka ta mike ta nufi dakin shi don ganin ko akwai gyararrakin da za ta iya, cikin sa
a rufe kofar kawai ya yi amma bai sa key ba.
Ta murda ta shiga cikin sallama duk da babu kowa, wannan tarbiyya ce mai kyau sabida mala
ikun rahma.
Dakin babu kintsi, ko ina takardu baja-baja, gado a yamutse, kayan wanki a toilet fal cikin kwando.
A jikin bed side ta yi tozali da
yar uwarta tana murmushi.
Ta karasa ta dauki
frame
din hoton tana shafawa a hankali tana murmushi itama, hawaye fal idanun ta.
Ta maida shi mazaunin shi ta nade hannun riga ta soma gyara komai neatly, ta cire bed sheet ta canza wani.
Ta kunna A.C don dakin ya yi sanyi.
Ta koma toilet ta hau wankin da ya dauke ta har zuwa azahar, ta fito da kayan inda suke shanya ta shanya, ta wanke bandakin sosai da parazone, sai daukar ido yake, ta jawo kofofin ta fito ta soma aikin falo wanda babu datti sosai don su Inna sun tsaftace ko ina kamin su tafi.
Zuwa la
asar kayan sun bushe, sai tashin kamshin Dr.
Sulaiman suke kamar yanzu aka fesa turaren gidan (Chris Adams) ba
a sanya su a omo ba.
Ta yi shimfida a falo ta soma goge su da dutsen guga, ta kammala cikin dan lokaci, ta je ta jera mishi a wardrove ta kunna burner ta turare dakin da bandakin da touch me, sannan ta fita ta koma dakinta ta yi wanka ta kwanta tana hutawa.
Bai dawo gidan ba sai goma na dare, nan ya soma shakar daddadan kamshin amarcin da gidan ke yi, ya kara cin karo da sakon Fati a kan dining cikin wasu flasks din asu zabar kyau ba na dazu ba.
Wato yarinyar nan ba ta jin magana
Ya fadi a zuci.
Ya danna kai dakin shi, kamar ya sume don daddadan kamshin da dakin ke yi, da wata ni
ima ta musamman dake fita, wanda ya gauraye da rabar split mai sanyaya zuciya da kasalantar da gangar jiki.
Ya bude wardrove don ya sauya kaya, nan ma ya cimma sakon Fatima Ja
afar Mai-Yadi.
Ya girgiza kai ya ce,
Na san maganin ki tunda baki da zuciya
Washegari ma Fati ta kara yin kalacin kunun tsamiya dan leda, da poncake ta aza dining.
Yau ma da ya gani wucewa yayi yana girgiza kai, cikin ransa yake fadin.
Lafiya ce ta yi miki yawa kike losing energy din ki a banza!
Surely
yana bukatar abincin, amma girman sa da yake tattali a idanun ta ya hana shi.
In ya ci girkin ta ashe tana da amfani cikin gidan kenan, shi kuma so yake ya nuna mata da ita da babu duk daya.
Babu wani amfani da mace za ta yi masa tunda ya rasa wadda yake so, ya jure rashin Hadiza ma balle rashin cin abincin da yake so?
Haka suke ta gangarawa har tsayin sati guda.
Ranar lahadi yana gida, Mukhtar ya yi sallama ta hanyar danna kararrawa.
Ya tashi daga kan computer ya je ya bude, Mukhtar Ja
afar ne rungume da Baby Nanah, Munib da Muniba na biye da shi, suka rangada da gudu suka rungume mahaifin su.
Shi ma ya rungume su yana bin kowannen su da sumba, idon shi a lumshe.
Suka karasa cikin falon shi da Mukhtar, Mukhtar ya mika mishi Nana, ya karbe ta ya rungume yana sunsunar ta.
Sannan ya tsaya yana kallon ta, kamannin shi da ita har sun yi yawa.
Suka yi musabiha da Mukhtar, yake gaya mishi Inna ce ta yi waya ta ce a kawo su wajen babar su.
Ina Fatin ne?
Ko barci take?
Cikin dauriya ya ce,
Bari in duba
Ta fito daga wanka ke nan tana rufe kofar bandaki, karamin towell ne ta daura daga kirji zuwa cinyoyin ta, kanta cikin hular wanka, tana jona hand dryer don busar da gashin kanta da ya jike.
Ya turo kofar ya shigo, idanun shi suka yi kyakkyawan gani, shi kadai ya san abin da ya tsirga daga yatsar kafa zuwa zuciya da kwakwalwar sa, ashe model yarinya ce a cikin HIJABI?
Kallon second biyu ya yi mata ya dauke kansa, sannan ya juya da sauri cikin kakkausar murya ya ce,
Mukhtar ke kiran ki
Ta zubo doguwar rigar shadda
dark-bluesenegalese
ta dora da matsakaicin hijabi, ta tadda su a falon.
Ai kuwa su Munib suka yo tsalle suka yo kanta, har suna kokarin kada ita.
Itama ta rungume su, suka soma jero mata tambayoyi.
Anti Fati, Mummy ba ta dawo ba har yanzu?
Ina kika tafi muka daina ganin ki?
Nana tana ta kuka idan bakya nan, don Allah kar ki kara tafiya ki barmu
Ta ce,
Ba zan kara ba
.
Ta kamo hannun Muniba,
Ba inda zan je muna tare kun ji my kids?
Suka yi murmushi sannan ta karasa ta russuna ta gai da Yayanta, wanda suke ta hirar su shi da Sulaiman, ta nufi firjin kitchen ta kawo mishi lemon (Donsimon) da gorar ruwan (Eva) mai rangwamen sanyi.
Mukhtar bai dade ba ya yi musu sallama ya tafi.
Bayan ya karbi lambar Fati.
Tana so ta karbi Nana amma tana bisa cinyoyin sa, ta fara kuka don ta dade ba ta sha madara ba.
Dole ya mika mata ita, hannuwan su suka saka kara gogewa dana juna.
Wasu irin hannuwa gareta masu bala
in taushi kamar auduga, wadanda suka tada tsigogin jikinsa.
Ita kuma suka haifar mata da kasala irin wadda ta ji a ranar da hannun ta ya fara shafar nasa.
A hanzarce ya mike,
Oya kids!
Muje mu sha (Ice-cream)
Suka yi tsalle suka dane kafadun shi, Munib ya ce,
Amma har da Anti Fati za mu je?
Ya yi kamar bai ji shi ba, ita dai jakar kayan su ta dauka ta yi ciki da Nana a hannun ta.
Ya sunkuci yaran shi duka biyun a kowanne hannu daya du girmansu, suka yi waje.
Dama tana da tafasasshen ruwa cikin filas a kitchen, nan da nan ta dama madara ta soma baiwa Nana bayan ta sha iska.
****
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: 2
Karfe goma sha dayan dare garin Kano ya yi tsit, sai iskar hunturu da ke kadawa.
Malam Ja'afar ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida.
Zai gifta ta dakin Fati ya jiyo shesshekar kukan ta, ya dakata ya daga labulen yana kallon ta, tana zaune a kan darduma ta kunshe fuskar ta cikin hijabi sai kuka take.
Ya karasa shigowa cikin dakin ya ce,
"Fadimatu kukan me kike yi?"
A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur, sun yi luhu-luhu alamar ta yi kuka har ta gode Allah.
Malam Ja'afar ya zauna a wata 'yar kujera da ke dakin yana fuskantar diyar sa.
Nanah ta soma motsi alamun za ta tashi daga barcinta, ta soma rirriga ta.
Ya jima bai yi magana ba sai da Nana ta koma barcin ta ya ce,
"Gaya min damuwar ki Fadimatu, ni mahaifin ki ne".
Ta share idon ta da hankici, ta ja shessheka kafin ta ce,
"Baba babu komi".