← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 26

Sashe 12

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hadiza ta runtse ido hawaye na zirara, ta ce,
"Fati ina alkawarin mu?"
Cikin Kuka ta ce,
"Yana nan Yaya Hadiza".

Ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, duk su Malam Ja'afar na kallo, ta ce,
"Fati har da shi a alkawarin fa.........."
Ta yi sharbe ta yarfar da majina da hawaye ta ce, "In kula da shi kika ce?

Yaya Hadiza ai shi babba ne?

"Babba ba ya bukatar kulawa Fati
Ta ce,
"Ban sani ba".

Ta ce,
"To yana bukata, shi ma kamar Munib ne, bambancinsu shine shi Munib kulawar UWA yake nema, shi kuwa Sulaiman kulawar MATA yake nema..........".

Ta yi murmushi ta runtse idonta, cikin azabar da take dandana a kwakwalwarta.

Sulaiman ya russuna ya sumbaci goshinta, hancinta, bakinta da idanunta.

"You will get well soon Hadizah
, bana bukatar kulawar kowa sai taki, in ba taki ba na yafe, zafin ciwo yake sa ki yin irin wannan magana.........".

Ta girgiza kai tana kara manne hannun su cikin nata ta ce,
"Sulaiman-Fati............".

Dr.

Bunza ya karaso ya tura gadon da kanshi yana ta yiwa sister Magajiya fada.

Yaya ta karaso ta karbi 'yar da ke hannun Fati ganin tana neman kwala ta da kasa.

Dr.

Sulaiman ya mai da hannun shi cikin aljihu, yana so ya yi kuka amma idanun sun bushe kamar soyayyar gyada marau-marau.

Sai Malam Ja'afar ya iso gare shi ya kamo hannun sa suka zauna tare, yana cewa,
"Karbi 'yar ka sa mata albarka".

Amma Sulaiman ya ki, sai kirjin shi da ke ta kai kawo kamar zuciyar ta ballo allon kirjinsa ta fito.

Ana shigar da ita cikin computer don a yi hoton kwakwalwar ta kamin likitocin su san me za su yi a kai, ta soma wata irin jijjiga mai ban tsoro, kamin ta yi salati rai bakon duniya ya yi halinsa.

"Allah ya ji kan Dr.

Hadizah!"
Abin da dukkanin likitocin suka furta kenan, a lokaci guda suna share ambaliyar hawaye daga idanuwan su, tare da kai hannu su rufe mata idanun ta.
****
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Washegari da yamma sai ga Inna ta kara dawowa, Dr.

Sulaiman ya kawo ta, Hamza da Abdulyassar suka shigowa Fati da katon na madarar SMA, katon na diapers da himilin shopping na kayan masarufi da kayan biskit da choculate da su Indomie wanda su Munib ke zuwa makaranta da su.

Ta adana kowanne a inda ya dace, Inna ta ce ya je sai dare ya zo ya dauke ta.

A lokacin Malam Ja'afar ya iso da shi da Inna da Yaya suka kule a daki, suka sakayo kofa, me suka ce me suka ce oho, sun dai dade suna magana kafin ya dawo ya dauki Inna su wuce, kasancewar a gobe zata koma Bakori, ya biya ta Jifatu ya yi mata sayayya mai yawa kamar yadda ya saba, ita da Malam da sauran kannen shi, suka wuce gidan sa.

Inna ta tuka mishi tuwon semovita da miyar ganye ya ci, ta takura mishi ya bude wayoyinsa.

Yana budewa sakonnin ta'aziyya daga likitoci 'yan uwansa da sauran abokan arziki ya soma tittidowa cikin wayar.

Sannan ana neman shi a ofishin (Chief Medical Director) na AKTH ranar litinin.

Don haka yana kai Inna Bakori suka gaisa da mahaifin shi bai tsaya ba.

Da zai tafi Inna ta ce,
"Ni kuwa akwai wata magana muhimmiya da nake so mu yi, ga shi na ga alamar kana sauri".

Ya ce,
"Gaskiya kam ina cikin sauri, sai ko idan na dawo".

Ta ce,
"Shi ke nan Allah ya kiyaye hanya, ya kara maka hakuri da YAKANAH, ya shige maka gaba a kan al'amuran ka, ya yi maka musayan alheri".

Har ransa ya ji dadin addu'o'in Inna, wata nutsuwa ta kara shigar shi, son mahaifiyar shi ya kara shigar shi.

Ta ce,
"Ina so zuwa sanda za ka dawo in ga canji, kamar yadda ka yi min alkawari, in ganka a likitanka ba mai sunan Malam ba".

Murmushi ya yi, wanda rabon shi da yin shi tun wani karni can da ya shude.
****
Litinin, ya isa ofishin CMD, sun dade suna tattunawa a kan wani aiki na dashen zuciya da za a yiwa ministan lafiya.

Yana daya daga cikin likitocin da zasu gabatar da aikin.

Ya koma office dinsa ya daidaita komai ya ci gaba da aikin sa, cikin karfin zuciya da neman rinjaye a kanta.

Sai ya zamto yana jin dadin aikin sosai, don yana debe mishi kewa, yana hana shi zama shiru har maraicin matarsa ya gallabe shi.

Ya tarar da tulin ayyuka da yawa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya.

Ranar alhamis ya saci jiki ya je yayowa 'ya'yan shi siyayya ya biya ta makarantar su ya gansu, lokacin da aka fito cin abinci, a karkashin wani benci ya zauna ya rungume su suna ta labari, ya bude
kit-kat
yana basu suna ci suna yi mishi hira.

Tun suna damuwa da rashin Momin su har sun hakura sun dangana sun daina tambayar ta.

Munib ya ce,
"Daddy ba ka zo (prize giving) din mu ba, kowa Baban shi ya zo banda mu".

Ya kama kunnen shi cikin nunawa yaron amsa laifin sa, ya ce,
"I am very very sorry..... aiki ne ya yi min yawa.

To wa ya kawo ku?"
Suka ce, "Aunty Fati, ta yi mana kwalliya ta kawo mu".

Ya ce,
"Aunty Fati ta kyauta!".

Suka yi murmushi.

Ya ce,
"Next year ba zan sake ba".

Aka kada kararrawar komawa aji, suka fella da gudu suka nufi ajinsu, ya bisu da kallo yana murmushi cike da kewar su.

Hakan yake yi duk sanda ya samu sararin aiki, ya daina zuwa gidan don kar ya ga Fati, tana tuno mishi da wasu al'amura msu yawa a kan Hadiza.

Sannan ba ya son wata alaka take shiga tsakanin su, shi ma kuma bai san mai ya sa ba, ya danganta hakan da rashin haduwar jininsu na tuntuni.

Ita kuma ta danganta hakan da wulakanci da raina mata wayo, yana ganin ta kamar ba ta san abin da take yi ba, bayan in da wanda ya san ciwon kansa a duniya to ita ce.

Sai dai tsarin rayuwar su da ya banbanta, kowa da irin nashi tsarin rayuwar, sun dauki rayuwar bature mai zafi sun yafa shi da Hadiza, ita kuwa Lahira ta sani ita take wa tanadi, shiyasa yake mata wani gani-gani, don haka ita ma ta yi kamar ba ta san yana zuwa makarantar yaran ba, bayan kuma suna gaya mata.
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Ana i gobe sadakar arba'in din Hadizah, Malam Sulaiman, Inna Halima da Baffanin Sulaiman guda biyu, Malam Surajo da Alhaji Umar suka iso gidan Sulaiman a Kano, a daren suka bukaci ya kai su Karkasara.

In da ya ajiye su da daddare ya wuce asibiti, da cewar zai dawo ya dauke su.

Manya sun kule a falon Baban Hadiza, wato Malam Ja'afar suna magana ta gemu-da-gemu har da Yaya da Inna.

Yaya ta ce,
"Ni bana jin Fati sai shi Sulaiman, anya zai yi na'am da al'amarin nan?"
Malam Sulaiman ya yi murmushi ya ce, "Kune baku san Sule ba har yanzu, yana da wani hali tun yana yaro, abin da zai so sai ya fara kin shi tukunna.

Ga yadda mahaifiyar shi take bani labari, babu jituwa ko ya ya tsakanin sa da Fati, ita kuma ta kama kanta ba ta shiga shirgin shi.

Mu dai burin mu ku bamu hadin kai, Allah ya gani muna son zuri'ar gidan nan, muna son zumunci ya ci gaba da gudana kamar yadda aka faro.

Fati ita ta fi cancanta da ta rike 'ya'yan 'yar uwar ta, don a wannan zamanin da wuya a samu macen da za ta rike maka 'ya'ya har uku duk son da take maka.

Sannan mun yaba da hankali da tsarin rayuwar Fati, muna sa ran yara za su tashi da kyakkyawar tarbiyya har zuwa girman su.

Fati ba za ta dauwama a gida tana bautar 'ya'yan 'yar uwarta ba, dole watarana za ta yi aure.

Ranar da hakan ta faru ya ya Sulaiman zai yi da yaran nan?

Ga shi suna karatun su mai kyau a nan balle mu tafi dasu Bakori.

Fati ita ta fi cancanta da ta maye gurbin 'yar uwarta a zuciyar Sulaiman.

Don haka muna neman hadin kanku, yardar ku da amincewar ku Malam Ja'afar.

Shin an bamu Fati?

Da karfin mu muka zo, da sadakin mu a hannu, gobe muke so bayan an shafa addu'ar Hadiza a daura auren Sulaiman da Fatima".

Malam Ja'afar ya ce,
"Tun kafin ku yi wannan tunanin na riga ku yin sa, kun dai riga ni furtawa ne.

Tabbas duk matar da Sule zai aura nan gaba ta rike mishi marayun shi ba kamar Fati ba, wadda ta san ciwon su, tasan ciwon 'yar uwarta.

Sannan Hadizah ta yi wani abu a ranar da za ta koma ga mahaliccinta, wanda ya tsaya min a rai kwarai, ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, sai dai ban ji me suke cewa ba.

Fati yarinya ce mai biyayya, ba za ta tsallake umarnin mu ba, amma kamar yadda Sa'adatu ta ce ne, da kyar idan shi Sulaiman din zai amince.

Sannan ya wuce matsayin da za a ce za a yi mishi aure ba tare da sanin shi ba".

Alhaji Umar ya ce, "Ku bar wannan a hannun mu, kamar yadda Fati take mai biyayya, shi ma Sulaiman mai biyayya ne, iyayen shi basu taba saka mishi kara ya tsallake ba.

Ina da yakinin zai yi biyayya ga mahaifin shi, kuma a daren nan zamu sanar da shi ba sai gobe ba.

Ga sadaki naira dubu ishirin ga goro, daga aljihuna ni waliyyin sa.

Jikina ya bani alheri ne zamu kulla, don irin wannan auren na son zuciyar iyaye ba karamar falala ake samu a cikin shi ba".

Kowa ya jinjina kai.

Yaya ta ce,
"Nima a daren nan zan sanar da ita insha Allahu".

Da haka taron ya tashi, ya yi dai-dai da sallamar Sulaiman a falon, dukkanin su suka amsa fuskar kowannen su cike da walwala da annuri.

Malam ya ce,
"Faduwa ta zo dai-dai da zama kenan, ita ma Fatiman a kirawo ta".

Yaya ta tashi ta fita don kiran Fati.
Chapter 12 · 0% Book details