← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 26

Sashe 24

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tattausar muryar ta da nutsuwar ta na burge shi har bai son a daina hirar, ita kuma so take a gama, saboda yadda yake kara ruruta wutar son shi a zuciyarta
Nana ta yi motsi za ta soma kuka, dukkan su suka juya gare ta, suka mika hannu a tare don su dauke ta, nata hannun ya riga sauka a kan Nana, don haka nashin sai ya sauka a kan nata.

Dukkan su babu wanda bai ji a jikin shi ba.

Ta yi saurin sakar mishi Babyn, ta dunkule hannun ta.

Ya dauke ta ya kai kafadun shi ya mike tsaye yana safa da marwa da ita a dakin don ta koma barci, ya kasa fita a dakin Fati, mai wani irin sihirtaccen kamshi da ba zai ce na kowanne turaren wuta ne ba, haka nan gauraye da rabar A.C mai kwantar da hankali.

Dakinta ko tsinke babu saboda masifar tsafta.

Bai ki ba su kwana a hakan, yana jin sassanyan sautin ta mai motsa zuciya, ta yi mata rahma ko da ba da son ran mutum ba.

Ya kwantar da Nana cikin dan gadon ta dake kan gadon Fati, ya mika mata hannun daman shi, cikin sigar son a yi hannu ya ce,
Can we be friends apart from Yayan?

Murmushi ta yi, ta sarke hannuwan ta a baya,
a, ai ka ce ni kanwar ka ce wadda take zaman lalata kuruciya........

Daga yadda take furta maganar za ka karanci (bitterness) wato dacin da maganar ta yi mata a kan harshen ta da zuciyarta.

Ya ce a ransa,
Baki shi ke yanka wuya
.

Yana da tabo mai yawa a zuciyar yarinyar, wanda ke dakusar da karfin soyayyar sa da ta soma shigar ta.

Dole ya wanke kanshi, domin karfi da yaj Fati na neman zamowa wani bangare na zuciyar sa cikin dan kankanin lokaci.

Ya ce,
Mun yi magana a kan ALL the inconveniences, not SOME of the inconveniences, kin ce kin yafe su, amma why kike maida hannun agogo baya?

Sai ta yi murmushi, ita ma ta mika mishi tattausan hannun daman ta, suka sarke su cikin na juna.

Kowanne siririyar fatar bakin shi dauke da murmushi.

Dai-dai lokacin da suka ji kiran sallar asubahi a cikin kunnuwan su, a sannan ne suka mike domin haramar sallah cike da mamakin tsayin lokacin da suka bata suna hirar zuciya da zuciya (heart to heart talk).

Washegari ma bai samu zama ba, suna ta zirga-zirga a airport na booking jirgin tashin su.

Bai dawo ba sai dare, lokacin kafatanin mutanen gidan sun yi barci.

Bai nemi kowa ba shi ma ya ci abincin da suka aje masa ya yi wanka ya shirya ya kwanta, amma tunanin Fati ya hana zuciyar shi sukuni, yana so ya san halin da take ciki, yana so ya sake jin sassanyar muryarta da ke yi mishi yawo a kwanya, yana so ya sake jin taushin hannun ta, yana so....... yana so
...

Kai yana son komi nata!

She is indeed a blessing cikin gidansa da rayuwarsa
.

She is also a DARLING (abar so) farin cikin kowanne da namijin da ya san ciwon kansa.

Amma ba za a gane hakan ba farat daya, sai wanda ya yi zama da ita na tsayin lokaci ya nazarce ta, amma a fuska za a fassara ta da mutum mara son magana, kidahuma mai takurawa rayuwarta.

Sai an fahimce ta a hankali za a fuskanci halitta ce, wato nature.

Ya so ya je gare ta a wannan daren da ya zamo na karshe da zai dade bai ganta ba, su raya shi da hira ta fahimta kamar yadda suka raya shi jiya.

Wata zuciyar ta ce,
A kul!

Kama girman ka ka rike tsam-tsam kada ta ga weakness din ka
To kamun girman har yaushe ne?

Shi ma ya tambayi zuciyar tasa.

Tunda dai ba za a dauwama a haka ba, kuma ba zai taba sakin Fati ko ya yi mata kishiya ba, don bai da ra
ayin zama da mace sama da guda daya.

In haka ne dole watarana za
a aje girman a gefe a ranar da Allah ya nufa.

Shin ko yaushe ce wannan ranar?

Bai sani ba!

Fati ta riga ta kama zuciyar shi fiye da yadda biro zai iya rubutawa.

Tana shirya masa kalaci a dining ya fito, cikin shirin tafiya, duk ta yi sanyi ta zama cool.

Kodayake dama haka halittar ta take, amma na yau na daban ne, komai cikin sanyi take yin sa, amma na yau ya fi na kullum.

Ya tokare hannun shi jikin kofar dakin shi, dayan na zube cikin aljihu, ya langabar da kai yana kallon ta.

Jikinta ne ya ba ta ana kallon ta, don haka ta dago kai ta dube shi, sai ta yi murmushi ta sunkuyar da kanta,
Morning friend Fatima!!

Ya fada.

Tare da miko mata hannu, tana murmushi ta mika masa nata.

Ji take kamar in ya tafi shikenan ba za ta kara ganin shi ba.

Daga gaisuwar bai cika ta ba ya janyo ta a hankali ya rungume ta, ya sumbaci goshinta sannan ya cika ta.

Ta lumshe ido a hankali tana daidaita tunanin ta.

Wani abu na zarya a dukkan ilahirin jikinta.

Ya iso ga tebir ta karaso da sauri ta yi serving din sa, ya kama kasan hijabinta ya cire ya ajiye a kan daya daga cikin kujerun, ya ce,
A dinga ajiye shi a cikin gida, don a sha iska
Wata muhimmiyar kunya ta kama ta, saboda
yan kananan kayan da ke jikinta.

Kukan Nana ne ya cece ta daga kaifafan idon Sulaiman, don haka ta garzaya shi kuma ya fara cin abincin kamar bai taba cin abinci mai dadi irin shi ba.

Har karfe goma ya kasa fita, yana tare da
yan shi da Nana a cinyar shi suna ta bashi sautun abin da zai sayo musu yana murmushi yana rubutawa.

Abokan tafiyar shi sun yi waya har sun gaji, yana cewa,
I am coming
.. (gani nan)
.

Sai da Dr.

Khalil ya biyo bayan shi sannan ya mike, ya mika wa Fati Nana wadda kanta ke sunkuye.

Ya dago habarta da hannun sa, ta lumshe ido sai hawaye ya balle.

Ba sai ta fada ba ya san ko na mene ne, Fati ta kamu da ciwon da shi ma yake fama da shi, amma kawaici da alkunyar ta ya sa take boyewa.

Yatsun shi biyu ya sa yana goge mata hawayen, kararrawar da Dr.

Khalil ke dannawa ta sa dole ya amshi brief case din shi a hannun ta.

Da sassarfa ya juya ba tare da ya kara waiwayowa ba, da sanyin ido ta bishi har ya fice a falon.

Nana da ke hannun ta na ta kuka amma ba ta san tana yi ba, yara na ta yi mata magana, suma ba ta ji me suke cewa ba, ta tafi cikin duniyar kewa, shauki, bege da soyayya
mai wuyar fassarawa.

Idan wannan ita ce soyayya da Sulaiman ya dandana ta Hadiza, sai ba ta ga laifin shi ba na wulakanta ta a farko, don ba ta jin in ita ce ya mutu a yanzu za ta yarda ta kara yin wani aure a rayuwar ta, ko zata kara son wani, kwatankwacin wannan son na Sulaiman da take ji a zuciyarta, ruhi da bargon jikinta.

Ta kara tausaya mishi kwarai game da yadda ya jure da rashin Hadiza.

Idan haka rabuwa da masoyi yake, tana addu
ar Allah ya sa ita ma ya so ta ko da rabin-rabin yadda yake son Hadiza ne
****
BAYAN TAFIYAR SULAIMAN
Rayuwa ta yi zafi ga Fati, komi na yanayin rayuwarta ya sauya, ta zama calm mai yin komi cikin kokari, juriya, karfin zuciya da dauriya.

Soyayyar mijinta ta hana ta sukuni, hatta
yanta sun san Auntyn su ta sauya, ta rage zama da su, ta rage walwala, sai dai Nana kullum tana jikinta.

Ta sakar ma Alti ragamar komi na gidan, ta fiya kwanciya tsakiyar gado, rigingine da Nana a kan ruwan cikinta.

Ta rasa walwala da kazarniyar ta, komi ya fice mata a rai, mijinta kawai take so, wanda kuma ya yi mata nisan da ba za ta kamo shi a nan kusa ba.

Ita Alti sai ta yi zaton ciki ne, don haka take bata kulawa ta musamman.

Misali da yake ta rage cin abincin gidan, sai lemu da ruwa, sai take tambayar ta ko da wani abu da kike marmari in yi miki?

A lokuta da dama cewa take babu, in kuma akwai sai ta fada mata.

A daddafe ta zana jarrabawar JAMB.

Ba jimawa ta sake samun admission inda za ta karanci fannin da take so, wato Islamic Studies.

Idan direban yara ya kai su da motar da Dr.

Sulaiman ya bar musu, sai itama ya sauke ta a makaranta.

Kullum cikin zumbulelen hijabin ta har kasa, Alti kan zauna a kofar aji ta rike mata Nana, ko su zauna masallacin Ramat su jira ta ta fito lacca.

Karatun na taimakawa dari bisa dari wajen debe mata kewa da rage mata tunanin Dr.

Sulaiman din da take zaton zuwa lokacin ya manta da ita.

Don har yau da ya cika watanni biyar da tafiya, ko sau daya bai kira ta ba.

Kai tana jin ma ba shi da nomba din ta.

Duk sanda suka yi waya da Inna tana tambayar ta lafiyar ta da ta
yan jikokin ta, ba ta yin zancen Sulaiman, tana so ta tambayi Inna ko yana yi musu waya, tana kuma tsoron kada su yana yi musu ita ce ba ya nema, Inna ta yi mishi magana ya ce ta kai karar shi.

Don haka ta ci gaba da jurewa ba ta yiwa Inna zancen ba.

Shekarar farko ta kare cike da dimbin nasarori a gare ta, domin duk jarrabawar da ta zana ba ta faduwa.

Ta kare shekarar da maki mai daraja.

Nana ta yi bul tana gudun ta ko ina, ba ta taba sanin ba Fati ce mahaifiyar ta ba.

Ta shiga 200 level cike da karfin gwiwa, tun Alti na zuba idon ganin ciki ya bullo mata har ta gaji ta gane ba ciki bane.

A yau da suka tashi Karkasara suka wuce domin duba jikin Baban su da bai ji dadi ba.
Chapter 24 · 0% Book details