Sashe 6
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kadai ta san radadin da take ji a zuciyarta, ita kadai ta san azabtuwar da ruhinta ke yi, al'amarin ya shallake tunanin ta.
Ba ta yi tsammanin al'amarin ya yi kamarin haka ba, bata taba kawowa ba, spinal cord injury!
A gareta ita Hadiza.
Lallai dan adam ba a bakin komai yake ba.
Yau ne kake mai rai, gobe ne kake gawa.
Yau ne kake da amfani, idan Ubangiji ya so, gobe ne ka zama tarihi.
A rayuwar Hadiza ba ta taba tsammanin wata kaddara makamanciyar wannan za ta taba shafar rayuwar ta ba.
To ina ruwan Allah!
Ta bude idon a hankali daga runtsewar data yi musu, tana kallon iyayen ta da 'yan uwanta wadanda dukkanin su ke sharar hawaye, sai ta soma lallashin su cikin muryar ban mamaki, tamkar ba ita ba.
Ta fi su karfin zuciya, ta fi su tawakkali, ta fi su YAKANAH.
Ta karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu, tana fatan Allah ya sa hakan ya zamo kaffara a gare ta, in kuma jarrabawa ce ya sa ta cinye jarrabawar ta.
****
Dole kanwar naki, Sulaiman yana ji yana gani, da hannusa da kudinsa ya sayo ma Hadiza wheel chair ana i gobe za a sallame su daga asibiti.
Wani bigire na karshe da ko makiyinsa baya yiwa fatan ya hau.
Don duk raunin dake jikinta ya kame sai karfin jiki da dan abin da ba a rasa ba.
Yaya ta so Sulaiman ya ba ta Hadiza ta wuce da ita gida inda za ta fi samun kulawar iyaye da 'yan uwa, amma sai ya sa musu kuka.
Da me zai ji ne?
Da lalurar da ta kashe masa rayuwa, ko da rashin Hadiza a cikin gidan, wadda ta zamo wani bangare na rayuwar sa, kundin farin cikin sa, sannan barin jikinsa?
Dole suka kyale shi da matar shi, amma sun ce Fati ta koma gidan ta zauna tare dasu, don ta dinga taimaka masa kula da Hadiza, musamman kasancewar sa ba mazauni ba.
Sulaiman bai so ba, don shi tun fil'azal Allah bai sa mishi son Fati ba, saboda son da Hadiza ke mata.
Yana kishin Fati, a ganin sa Hadiza ta fi son Fati a kanshi.
Sannan zubin ta na zuhudu (gudun duniya) ya yi yawa, bai fiya son mutane irin ta ba, kasancewar shi (sociable).
A tsarin halittar dan adam (personality), tana cikin rukunin al'ummar da ake kira (introvert).
Ba ta iya hada ido da shi, kai da kowa ma, saboda kunya.
Da wuya ka ga hakoranta, sai dai in guri ya kure ta yi murmushi,
dimple
din da
cleft
su lotsa, wanda shi ne muhimmin al'amarin da ke daukar hankalin dubban maza a kanta, sai dai kuma bai isa ya tsallake hukuncin da Yaya ta yanke ba.
Haka Fati ta hado kayan ta tsaf, ta dawo gidan 'yar uwarta da zuciyar 'yan uwantaka.
Zuciyarta cike fal da so da kaunar 'yar'uwar ta da tausayinta, karatun da ta taso shekara da shekaru da burin yin sa, gashi ta samu, amma a yau ta sallama shi, ta jingine shi ta sadaukar da rayuwarta kacokam da lokacinta ga rayuwar, 'yar uwarta Hadiza.
Sulaiman ya ciccibo Hadiza ya fito da ita daga mota, Fati ta bude (boot) ta fiddo wheel chair a nade, cikin sauri ta warware, Sulaiman ya sanya ta a ciki ya tura a hankali zuwa cikin gida.
Fati ta fiddo kayansu daga cikin motar ta rufe motar, ta soma diban kayan daya bayan daya tana shiga dasu cikin gida.
Malam Ilu maigadi, ya yi sallama a falon, a lokacin Sulaiman na kici-kicin aza Hadiza a daya daga cikin kujerun falon, ba tare da ya juyo ba ya amsa masa.
Ya zube har kasa yana jajantawa iyayen gidansa kaddarar da ta same su.
Yana magana yana sharar hawaye, saboda yadda yake matukar kaunar Hadiza, saboda karamci da kyautatawar ta gare shi.
Haka Goggo Alti ta fito daga kitchen, ganin Hadiza yau nade cikin kujera sai ta fashe da kuka, Sulaiman ya yi saurin ficewa a falon ya dau mota ya fita don dauko yara a makaranta.
Hadiza ta dubi Alti ta yi dan murmushi, "Alti wane ne ya halicce mu?"
Ta ce, "Allah (S.W.A)".
Ta ce, "To kinga in haka ne ke nan bamu da iko da kanmu sai abin da ya ga damar hukuntawa a gare mu, mu kuma dole ne mu zamto masu godiya idan har muna so imanin mu ya cika".
Alti ta jinjina kai tana mai jinjina karfin imani irin na uwargijiyarta.
Hadiza ta juya ga Fati ta ce ta kai kayanta dakin ta, kasancewar a tsarin gidan likitocin babu wani extra room, ita za ta yi amfani da na Sulaiman.
Fati ta ce atafau ita dakin su Muniba za ta zauna tare dasu, ta kada ta raya amma ta ki, ta ciccibi jakarta ta yi dakin su Muniba d ita.
Fitar ta daga falon ke nan su Munib suka dira a falon, Baban su na biye dasu yana rike da jakunkunan su da food flasks din su.
Suka tafi da gudu suka rungume Mamarsu, Munib da yake shine mai wayo ya ce,
"Mummy yaya jikin ki?
Daddy ya gaya mana kin yi accident kin ji ciwo kina asibiti ana yi miki allura?"
Ya kai hannu ga tabon ciwon goshinta, "Sannu Mummy, kin ji?".
Ta shafa kansa ta yi masa murmushi bata ce komai ba.
Ita kuwa Muniba bin jikin Mummyn ta yi ta lafe kamar mage, dama ita ba ta fiya magana ba.
Zuciyarta kal da ganin mahaifiyarta da ta jima ba ta gani ba.
Munib ya soma jan hannunta wai ta taso suje su yi kwallo (ball) kamar yadda suka saba, Sulaiman ya kau da kai, bai son ganin wannan abin tausayi, ya mai da hankali ga lallatsa wayar sa, baya son su ga hawayen sa.
To ita ma Hadizar duk dauriyar ta sai da hawayen suka tsatstsafo, ta sa yatsun ta biyu ta dauke su, ta kama dukkan 'ya'yan biyu ta rungume a kirjinta.
Kukan zuci take wanda ya fi na fili soya zuciya.
Ta ce,
"Ku tafi wurin Anti Fati tana dakinku ku yi kwallon tare, har yanzu bani da lafiya".
Da gudu suka mike daga jikinta suka nufi dakin su suna murnar zuwan Antin su da suke tsananin so.
Alti ta yi sallama dauke da tray kanta a sunkuye, idonta cike fal da hawaye, muryarta a sanyaye tace da Hadiza,
"Na ce sai na daina daura abinci a tebir?
Hadiza ta yi murmushi mai hade da wani irin radadi a zuci, ta ce,
"Idan maigidan yana son hawa tebir din fa?"
Ta fada tana kallon Sulaiman.
Bai dago ya kalle su ba, haka bai tofa musu ba, duk da ya lura ta bakinsa suke son ji.
Alti ta ajiye katon tray a gaban Hadiza ta juya ta fita.
Tana ba da baya ya suri Hadiza a kafadar shi sai dakin barcin su.
A hankali ya sauke ta a makeken
family bed
din su, ya koma toilet ya cika baf da ruwa mai dumi, ya zuba dettol kadan ya dawo ya soma warwarewa Hadiza kayan jikinta, ya nade ta cikin towel ya sake sungumar ta ya yi toilet ya sanya ta cikin ruwan da ya hada.
Ita karfin Sulaiman mamaki yake bata.
Ya yi mata kyakkyawan wanka da kamsassan sabulun Zest, ya nado ta ya fito da ita.
Yawancin kayanta a dakin suke dama, don haka ya shirya ta cikin riga da wandon pakistan ruwan goro (orange), ya dauki (kumb) ya soma sharce mata gashin kanta da ya wanke da (head&shoulder) wanda rashin gyara kwana biyu ya sa shi duk ya cukurkude.
Ta ce, "Da ka bari Sulaiman Fati za ta yi min gyaran kan".
Bai saurare ta ba ya ci gaba da abin da yake, amma da a ce ta kalli fuskarshi a lokacin, data lura da yadda ya dan hada rai, saboda ambatar Fati da ta yi, wato ta fi son Fati ta kula da ita fiye da shi.
Ta yi murmushi ta ce, "Amma tunda ka hada ruwan wanka ka yi mai wuyar, zan iya wanka da kaina, sai Fati ta shirya ni koda yake ma zan iya shiryawa da kaina.......".
A hassle yace .
"Is o.k Hadizah, very o.k, ba tun yau ba na san kin fi son kanwar ki fiye dani.
In ba haka ba ni amfanin me ke gare ni?
Da ba zan kula dake ba a lokacin da kike cikin lalura?"
Ta kama baki, don ba ta ji dadin maganar shi ta farko ba, amma sai ta share ta ce, "Yau da gobe ne sai Allah Sulaiman
.".
Can kuma ta yi rau-rau da ido kamar hawaye za su zubo,
"Me ya kawo maganar na fi son Fati a kanka?
Ban ji dadin nagetive response din ka ba".
Ya ce, "To ai ke ce Hadiza da wani irin batu, amma ina so ki yarda da cewa, idan zan gaji da hidimar ki Hadiza, to zan gaji da hidimar kaina
Ta ce, "Amma Sulaiman......"
Ya kai hannu ya toshe mata baki, "Kina shakka da abin da na ce miki?"
Ba ta son jan zancen da nisa, har ya yi tsayin da zai zamo bacin rai, sai ta ce,
"Bana shakka Sulaiman, Allah ya bamu rai da lafiya".
Ya turo ta cikin kujerar ta suka dawo falon don cin abinci.
Munib da Muniba suka shigo, fes dasu cikin kaya 'yan kanti (pink colour) har Fati tayi musu wanka ta shirya su ta feshe su da turare.
Suka saki baki cikin mamaki, ganin Daddy yana tura Mummy cikin kujera mai tayoyi, abin ki da yaro, sai ba su kawo ma ransu komai ba, ko wani abu ne ya faru da Maman nasu, sun dauka haka nan dai yake tura ta don bata da lafiya.
Sai suka sa rigimar ta tashi suma Daddy ya tura su.
Haka Sulaiman ya sauke Hadiza a seater, ya dauke su su duka biyun ya aza a kujerar, ya yi ta zagaya falon dasu suna jin dadi, sai kyalkyatar dariya suke.
Hadiza ta juya ta dube su, ganin abin nasu ba na kare bane ta ce, "Oya!