← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 26

Sashe 18

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Ja'afar ya dubi Inna Halima ya ce, "Babu bukatar wata bidi'a, gobe Sulaiman ya zo ya dau matarsa da 'ya'yan shi su tafi, Allah ya yi musu albarka".

Fati da ke uwar dakin Yaya tana jin duk abin da ke faruwa a gidan, ta takure a bayan labule sai gursheken kuka take, goye da 'yarta sai makyarkyata take.

Ta rasa inda za ta sa ranta ta ji dadi, shin rayuwarta da wadda za ta je ta tarar wace irin rayuwa ce?

Shin meye makomar rayuwar ta?

Ta tabbata, kuma a ko
ina za ta yi rantsuwa a kan cewa Sulaiman bai son ta.

Takura mishi aka yi.

Yaya Hadiza ta dora mata nauyi, da kananan shekarun ta ba za su iya saukewa ba.

Amma in ta tuno nasihar da Baban su ya yi mata a daren jiya, sai ta ji sanyi a ranta.

Jin Inna na neman ta, ta yi saurin shigewa toilet.

Inna ta daga labule ba ta ganta ba, ta ce da Yaya
bata nan, watakil ta shiga bayi
Daga nan suka ci gaba da hira ita da Yaya a kan maganar lefe, ta ce za ta sa su Ruma su hado ko gidanta ne a kai mata.

Yaya ta kafe a kan cewa wallahi sun yafe, ko tsinken Sulaiman ba za su karba ba.

An riga an zama daya sai dai su bi yara da addu'a.

Amma Inna ta kudire a ranta sai an yiwa Fati lefe irin wanda ake yiwa kowacce yarinya budurwa.

Sai da su Inna suka bar gidan sannan Fati ta fito daga maboyar ta, makota na ta shigowa suna yiwa Yaya ta'aziyya da Allah ya sanya alheri.

Ta nufi dakinta ta shimfidar da Nana, sannan ta kwanta a gefen ta ba laka a jikinta.

Yaya ta shigo rike da kwanon silba da damammiyar fura mai sanyi, ta zauna a gefen ta tana kallon yadda duk ta zuge kwana daya kacal.

Ta ce, "Ungo fura tashi shanye ki bani kwanon".

Ta girgiza kai, "Bana son cin komi".

Yaya ta ce,
"Haka za ki daure ki dura, zama da yunwa da bacin rai ba naki bane, tunda dai auren nan an riga an daura ya kuma dauru, sai ki saki ranki ki watsar da duk wani tunani wanda zai hana miki kwanciyar hankali.

Karbi na ce".

Ta tashi zaune ta amsa, ta kafa kai tana sha tare da kokarin maida kukan da ya taho mata a dalilin furucin Yaya,
"Aure ne an riga an daura kuma ya dauru
.".

Wato dai da gaske ta zama matar Dr.

Sulaiman mijin Yayarta.

Sai da ta shanye furar ta share hawaye da 'yan yatsunta, Yaya ta ce, "Kukan dai?

Sai ki yi ta yi tunda kin ga shi zai fisshe ki.

Haba, ayi yarinya da shegen kuka kamar Muniba?

Yanzu ki tashi ki je ki yi wanka, ki sa kaya masu kyau ki je a wanke miki wannan dankararren gashin naki da yau kwana arba'in ba ki tsefe shi ba.

Ko ni uwar Hadiza ban takura rayuwata yadda kika takura taki ba.

Gobe za su zo su dauke ki, don Allah ki dan gyara kanki yadda za ki yi kyan gani, ki aje hijabin nan haka ki yiwa mijinki kwalliya.......".

Ai kuwa sai ta balle da kuka, "Ni wallahi ba inda za ni, ni wallahi bana son sa...........".

Yaya ta bige mata baki ta ce,
"Don Allah in an kaiki ki sha poison kema ki mutu, ba zan kasa rayuwa ba!!!".

Ta juya ta fita.

Ta tabbatar ran Yaya yai matukar baci tunda har ta yi wannan furucin, tana kuka ta taso ta biyo ta dakinta, tana zaune a kujera ta yi tagumi.

Ta zube a gabanta ta kama kafarta cikin rishin kuka ta ce,
"Don Allah Yaya ki yi hakuri ki yafe min, wallahi ba zan kara ba".

Ta ce, "Ni me ki kai min da za ki bani hakuri?

Ke aka yiwa laifi ke za a bawa hakuri.

Me kika fishi ko me kike takama da shi da za ki ce bakya son sa?

Ban da Allah ya kashe ya baki ai Sulaiman ba tsaran ki bane, ba za ki gano gatan da aka yi muku dukkanin ku ba sai nan gaba.

Wannan shi ne karshen kauna da za ki nunawa Hadizah, ki rungumi iyalinta a bayanta, sai dai in dama ba son ta kike yi ba........!"
Ta kara sautin kukan ta,
"Na tuba Yaya, na bi Allah na bi ku, na yarda zan zauna da Baban Munib ko ba ya so na.......".

"Shi ya ce miki ba ya son ki?

Bana son mummunar fahimta, ko bai miki son soyayya ta aure ba, yana yi miki son 'yan'uwantaka, wadda a hankali in kin sadaukar da kanki gare shi za ta rikide ta koma soyayyah!.

Sanda aka aura min mahaifin ku ban san shi ba, ban taba ganin sa ba.

Haka aka lullube ni aka kawo ni, ko sunana bai sani ba nima ban san nashi ba.

Amma kyautatawa da sadaukar da kai ya sa a yau ba abin da muke so da kauna sama da junan mu, har muka kai ga haifar ku daya bayan daya.

Kina gani har yau bai taba yi min kishiya ba, bai taba bata min rai ba sai bisa kuskure.

Bacin raina na nufin tashin hankalinsa, fushina na nufin tabarbarewar al'amuransa.

Ki yi auren BIYAYYA ba SOYAYYA ba ki ga wacce irin riba za ki samu a cikin sa?

Idan mun san babu riba ba zamu ba ki jarin ba".

Fati ta share hawayen ta, cikin zuciyar ta tana cewa, mazan da dana yanzu ai ba daya bane Yaya!

Balle wadannan da suka hantse cikin ilmummukan zamani masu gigitarwa, suka saba ganin mata iri-iri dai-dai da tsarin rayuwar su.

Ina zan iya burge shi balle har ya kaunace ni?

Ina zan iya mai da kaina irin Yaya Hadiza?
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Kayan cefanen su sun kare, ba ta san ya za tai ta gaya mishi ba, saboda irin yadda yake bi ya daure fuska kamar wani soja idan ya ganta.

Fati na mamakin wannan wace irin kiyayya ce Sulaiman yake mata ta babu gaira babu dalili?

Kamar ita ce ta kashe Hadiza?

Yana da wata kima a idon ta kasancewar shi wanda ya auri
yar uwarta da ba ta da ya ita a duniya, ya zauna da ita, ya rayu da ita cikin so da kauna da kyautatawa har ta koma ga mahaliccin ta, ba ta taba fadan laifin sa ko aibunsa ba, ko wani abu da ya yi mata na rashin dadi.

Sannan da kasancewar shi Baban
yan da take so sama da komi a duniya.

Idan ba zai so ta ba ai ta ci albarkacin Hadiza.

Amma yadda yake nunawa kamar ko a hanya basu taba hada wata alaka ba, idan ta biyewa wulakancin da yake mata ta ce za ta dinga bata ranta a banza, ita ce za ta cutu, ta dorawa kanta ciwon zuciya da hawan jinin da ko duba ta ba zai yi ba, balle ya rubuta mata magani.

Don haka ta debe tsoro da shakku, bayan sun dawo yana kwance a falo yaran shi sun baibaye shi suna ta yi mishi tadi, shi kuma yana aiki cikin kwamfutar da ke bisa ruwan cikin sa.

Ta lallabo ta fito uwa munafuka, tana goye da Nana ta rabe a gefe, Muniba ta taho ta zauna a cinyar ta.

Sai a lokacin ya ankara da shigowar ta falon, ya juyo da sauri kamin ta yi magana ya mike, ya aje computer a fusace.

Ta runtse ido tana jiran saukar mari a lallausan kumatun ta, ya ce,
t I warned you?

Idan ban neme ki ba ki daina zuwa inda nake?

Cikin makyarkyatar murya da gigicewa ta ce,
Ka yi hakuri, kayan cefane ne suka kare, sannan babu kayan abincin makarantar su Munib
Ya yi tsaki
Tsuuu!

Kamar ya tsinke harshen sa, ya ce,
Na ji shikenan ko?

Ta mike a salube gwiwa babu karfi ta koma daki, don ita ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata tsawa.

Su kansu yaran sun tsorata da tsawar da Baban su ya yiwa Antin su, sun yi zuru-zuru, suma ya nuna musu hanya ya ce su bita.

Da gudu suka tafi har suna faduwa, ya kashe komai ya fice daga gidan.

Washegari Alti ta dawo, ba karamin jin dadin dawowar ta Fati da yara suka yi ba, ko ba komai ta samu mai taimaka mata da debe mata kewa, don Goggo Alti mutum ce mai barkwanci da ban dariya.

Sai ga Malam Ilu yana shigowa da kayan abinci nau
i-nau
i.

Suka zaun ita da Alti suka gyara komai suka adana na adanawa a firij, suka markada na markadawa suka adana a
freezer
Washegari ta tashi da wuri da taimakon Alti suka kammala komi da wuri, suka shirya yaran da abincin su, karfe bakwai da rabi Babansu ya kwashe su ya wuce dasu, sannan ya dangana ga ofishinsa.

Kuma ranar ne su Yaya Haulatu kanwar Yaya da wasu daga aminan arzikin ta suka zo suka yi mata jeren kayan gado dai-dai karfin iyayen ta da dan uwanta Mukhtar.

Falon ba ya bukatar komi, masu gidan sun riga sun tsara abin su dai-dai da rayuwar su ta masu murza tsinin biro, sai ba
a taba komi ba, iyakacin su dakinta.

A kwanaki bakwai da Alti ta yi tare dasu, ta fahimci irin zaman kare da kyanwar da ake tsakanin Fati da maigidanta Dr.

Sulaiman.

A ranta ta ce,
Yarinya kyakkyawa kamar Hadiza, ga hankali da addini, ko meye nakasunta da Dr.

Sulaiman ya kasa son ta?

Ta ce,
Ko da yake so ba
a nan yake ba, abune wanda ke faruwa kawai a duk sanda ya so, ga duk wanda ya so, cikin iko da kudurar Allah.

A yau suna yankar alayyahu ita da Alti, domin yin miyar wainar masar dare.

Suka jiyo motsin shi yana shigowa kitchen din, tuni Fati ta soma makyarkyatar jiki, kan ka ce meye wannan wuka kakkaifa ta shiga cikin naman hannun ta.

Don ita ko gyaran muryar shi ta ji gigicewa take ta fita hayyacinta kada ya yi mata tsawar nan tashi mai dimauta ta.

Jini ya soma bulbula a dai-dai lokacin da ya idasa shigowa kitchen din.
Chapter 18 · 0% Book details