← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 26

Sashe 3

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Surayyar ba ta watsar da Hadiza ba, ta kan zo in ta samu sararin aiki kuma suna yawan yin waya.

Tayi-tayi Hadiza ta koma aiki in ya so sai Fati ta dinga kula da zirga-zirgar ta amma ta ki.

A ganin ta ita Fatin zaman ta kenan ba za ta yi nata auren ba?

Ko ko haka za ta karar da rayuwar ta wajen hidimar ta alhalin bata kai ga cimma komai a rayuwa ba?

Gara ita ta kai ga matakin da duk dan adam ke burin samu; tayi ilmi, tanada kwali, tayi aure, ta hayayyafa.

Don ta zauna gida a halin yanzu babu komi.

Amma Fati fa?

Ta ce, "Surayyah mune bamu gane ba, ko da yake mu namu aikin mai tushe ne daga addini.

Amma ba abin da ya kai mace ta zauna a dakin mijinta ta yi biyayyar aure dadi da kwanciyar hankali, amma ina amfanin da auren ki da mijin ki da 'ya'yan ki amma kin watsar dasu kin barwa mai aiki kullum kina titi, bayan mijin ya tsare miki dukkan bukatun ki na rayuwa?"
Surayyah ta ce, "Ke din ce dai kawai kin yi sa'a Hadiza, amma ba ko wadanne maza ne irin Dr.

Sulaiman ba".

Kishi ya motsawa Hadiza ta hadiye shi mukut, amma ta san Surayya gaskiya ta fada, Sulaiman is unique, akwai wani simpleness a tare da shi wanda maza da yawa basu da shi.

Hadiza ba ta samu kwanciyar hankali ba sai da Dr.

Surayyah Yahya ta kawo mata katin auren ta da Dr.

Bashir Bunza, cike da shakiyanci ta nunawa Sulaiman.

Ya karanta ya ciji yatsa,
"Shege Bunza, ya kasa ni!".

Ta kyalkyace da dariya ta ce, "Eh, to kai ne ka tsaya sanya".

Ya harare ta da idanun kauna, "Haka ma za ki ce?

Bayan ke kika kashe min gwiwa, ai da tuni na karkata hula nasa kai, wallahi da ni zan kasa shi".

Ta sake yin dariya ta ce, "Oho dai, sai abi wani sarkin ba Ado ba".
****
Asabar ce sassanya mai dauke da wani irin lullumi mai sanya nishadi a zukatan dan adam, ana saura kwana biyar a kama azumin watan Ramadan, kamar kowacce asabar din karshen wata.

Dr.

Sulaiman ya zuba 'ya'yan shi a mota suka nufi Bakori ainihin gidan iyayen shi kamar yadda suka saba, can za su wuni, wani zubin har yamma ko dare.

To yau ma hakan.

Gidan ya rage daga Hadiza sai Fati, don Alti ta je kauyen su Kukawa ganin gida za ta yi sati biyu tunda yaran ma cikin hutu suke.

Fati ta tura Hadiza kitchen kamar yadda ta bukata, ita tana girki Hadiza na mata hira.

Ta ce, "Fati yau shekara guda cur da faruwar al'amarin nan, nayi-nayi ki kara neman wani admission din amma kin ki, kina nufin haka za ki yi ta zama kina yi min bauta ni da iyali na ba karatu ba aure?

In don nice wallahi bana cikin matsala a halin yanzu I can take a good care of myself (zan iya kula da kaina) ko da a ce ni kadai ce a cikin gidan nan".

Fati ta sauke tukunya ta dora wata, ta yarfar da hannu don zafi.

Sannan ta dubi 'yar uwarta,
"Yaya Hadiza ba zan iya barin ki ke kadai in tafi makaranta ba, ko na tafi tunanin halin da kike ciki ba zai barni in mai da hankali a kan karatun ba".

Ta yi murmushi, "Cewa nake watarana aure za ki yi Fati?"
Nan da nan Fati ta yi kicin-kicin da fuska, ta juya mata baya ba ta ce komi ba.

Hadiza ta ce, "Ko baki ji ni ba?

Aure za ki yi Fati dole ba da jimawa ba, don haka ki tsaya ki gina rayuwar ki kamar yadda muka gina tamu, bana so saboda amfanin kaina ke in tauye ki.

Don haka na baki kwana biyu ki yi tunani, an fara sai da JAMB na wannan shekarar, don haka ki nutsu ki kama abin da zai taimake ki ranar da bani.

Duk wata kauna da dan uwa na gari zai nuna wa dan uwansa kin nuna min ita, sakayyar ki na wajen Allah.

Sai dai ba zan bari ki kari rayuwar ki baki dandani zakin ilimin ko auren da na dandana ba, dole in samar miki future kafin Allah ya yi hukuncin da ya so a kaina....".

Fati ta yi saurin juyowa ta dubi Hadiza, domin a da ta bata baya ne.

Ba ta gane abinda take nufi ba.

Hadiza ta yi murmushin karfin hali ta ce,
"Fati zan gaya miki wani abu, amma bana so ki daga hankalin ki.

Bani da lafiya Fati, amma don Allah ko Yaya ban yarda ki gayawa ba balle Sulaiman.

Fati na dade ina fama da ciwon kai wanda nake yi lokaci-lokaci, Sulaiman ya sani ina yawan fama da (migrain) amma bai taba zurfafa bincike ba, don ban taba gaya masa tsananin zahirin yadda nake jinsa ba.

Ba tare da sanin sa ba na je wajen Dr.

Bunza mijin Surayyah, da ke likitan kwakwalwa ne, cikin sirri ya yi min bincike mai zurfi inda ya sanar dani ina fama da kansar kwakwalwa (brain cancer)".

Fati ta zazzaro ido ta sulale ta zauna a kasa, ta kai hannu ta dafe kirjinta, sai ga hawaye suna shatata!

Hadiza ta yi murmushi ta matso da kujerar ta inda Fati take, ta dora hannu a kanta.

"A'a, Fati kada mu yi haka da ke, amanar rayuwata nake gaya miki, wadda bani da wanda zan bawa sai ke.

Ba wanda zan iya gayama wa sai ke, ciwon bai yi tsanani ba, kuma ina shan magani a boye, ko Surayya ba ta sani ba.

Fati abin da ya sa na gaya miki don ki tallafa min ne, Sulaiman likita ne wanda ke bukatar kwanciyar hankali don samun (confidance) wajen gudanar da aikinsa na ceton rayuwar al'umma, idan ya ji wannan maganar ba zai taba samun kwanciyar hankali ba.

Fati Sulaiman yana sona, sosai, irin son da zai iya bani rayuwar shi, bana son abin da zai dagula masa lissafi, ki rike min amanata, ki rike min 'ya'yana, ki basu tarbiyya irin taki kada ki bari Sulaiman ya tagayyara a bayana.

Ina son shi yadda yake so na, na so in ci gaba da rayuwa tare da shi, in ci gaba da haifa mishi 'ya'ya kamar yadda yake so, amma ban san ya ya Allah zai yi dani da rayuwata ba.

Ki rike min Sulaiman Fati... bana so rashi na ya tagayyara shi........".

Zuwa wannan lokacin duka 'yan uwan biyu sharbe suke, na hawaye da majina.

Girki yana ta kauri, amma ba su kula ba.

Fati ta rage sautin kukanta, ta ce,
"Shi brain cancer ba
a warkewa?"
Hadiza ta ce, "Ba a warkewa gaba daya, ko ya lafa zai tashi, amma ina kula da shan magani".

Fati ta yarfe hawaye ta ce, "Wannan ba abun boyewa bane Yaya Hadiza, ki daina fidda rai da rayuwa saboda ciwo.

Insha Allah ke za ki aurar da Munib da Muniba, ya kamata ki sanar da Dr. domin ya taimaka miki da addu'a, duk wani hali da zai shiga ai shi musulmi ne ya san duk son da yake miki ya san bai kai wanda Ubangijin ki yake miki ba.

If the condition become worse, ba tareda saninsa ba ba zai taba yafe miki ba.......!"
Hadiza ta yi shiru tana mamakin zurfin hankali irin na Fati, yarinya karama sai tunanin manya.

Ta ce,
"Zan duba shawarar ki Fati, Allah ya kara min YAKANAH, ya bawa 'ya'yana tarbiyya irin taki.

Ai dai za ki kula min dasu ko Fati?"
Cikin kuka ta ce,
"Yaya Hadiza ki daina yi min wannan maganar, bani da jarumtakar sauraron ta
Ta ce, "Na rantse da Allah idan baki yi min wannan alkawarin ba nima ba zan bi shawarar ki ba".

Cikin makyarkyatar murya ta ce, "Eh.......eh......na yi alkawarin zan kula dasu!!".

Ta ce, "To nima zan bi shawarar ki, amma ba yanzu ba.

Tashi sauke tukunyar can tana kauri".

Ta share idonta ta mike ta sauke, ilahirin jikinta sai rawa yake.

Ta kashe komi ta maido Hadiza falo, ta yi dakin su ta rufe ta fada kan gadon su ta soma girka kuka.

Ta ga kukan ba zai amfane ta da komai ba, sai ta je bandaki ta dauro alwala, ta shimfida sallaya ta soma sallah, a kowacce sujjadarta tana yiwa Hadiza addu'ar Allah ya ba ta lafiya.

Wayar Hadiza ta yi kara, a lokacin tana bisa sallaya tana azkar, don haka ba ta daga ba har ta tsinke.

Sai ya yo text, ta dauka ta duba.

Sulaiman ne yake gaya mata suna bisa hanya har da Inna Halima za ta zo ta duba ta kuma za ta ga likita, don haka a gyara mata daki don za ta kwana biyu.

Hadiza ta ji dadin zuwan Inna, domin Innar Sulaiman mutum ce har mutum, ma'abociyar raha da sanin mutunci.

Don haka ta kira Fati a waya ta ce ta kara yawan abinci da ta aje a falo, ta kuma canza shimfidar gadon dakinta, don kullum a gyare yake Fati ba ta wasa da tsabtarsa.

Tara na dare dai-dai suka shigo, Inna dauke da Muniba da tayi barci a kafadunta.

Hadiza da Fati suka yi mata sauka ta ban girma.

Sai lokacin kwanciya ne aka kai ruwa rana da Inna, don ta ce ba za ta zaunawa Hadiza a daki ba, sai tare da 'yan jikokinta, dole suka kyale ta.

Duk juyin da Inna Halima ta yi a wannan dare, Fati take gani a kan sallaya, ta yi sallah, ta yi lazimi.

Da asubahi kuwa ta soma rero (Suratul Yaseen) da sauti irin na Abdurrahman Sudaith.

Kai ka ce daga masallacin Madinah aka kunno karatun.

Saida tayi sallar asubah sannan ne ta dan samu barci.

Karfe shida ta fada kitchen ta soma aikace-aikace, Inna na hankalce da damuwar da yarinyar ke ciki, ta rasa abin da ke damun ta kankanuwa da ita haka.

Bata uhm bata umhumh.

Lokaci lokaci tana sanya gefen hijabinta tana dauke hawaye.

To haka a washegari ma, har cikin kitchen wannan yarinya ba ta rabo da hijabi da carbi, tun tana burge ta har ta koma bata tausayi.
Chapter 3 · 0% Book details