← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 26

Sashe 17

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya jima yana kallon ta, sannan ya yi murmushi ya ce,
"Kina tuhumar mu da yi miki auren da baki so, auren mijin 'yar uwar ki.

Ki yi hakuri, alheri muke nufin ku da shi, ba za ku gane ba sai nan gaba, idan kun gano gatan da muka yiwa rayuwar ku".

Fati ta yi shiru tana sauraron Baban su, ta ga cewa wannan ita ce damarta ta karshe, daga gobe za a zarga mata igiyoyin wanda ta tabbatar ba ya son ta.

Ta kai kanta kasa tana kuka sosai, ta ce,
"Ku yi min alfarma Baba, Baba baka taba sani in yi wani abu na shallake maganar ka ba, amma a wannan karon, ina so ka duba hujjojina.

Baba Dr.

Sulaiman ba ya sona, Baba Dr.

Sulaiman ya fi karfina, bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa.

Baba Sulaiman ba zai taba son wata ba, bayan son da yake yiwa Yaya Hadiza.

Baba kune baku sani ba, amma Dr.

Sulaiman tun fil azal ya tsane ni, ban san laifin da na yi masa ba.

Ban taba gaishe shi ya amsa ba, haka bai taba duba na a matsayin jinin Hadiza ba, balle ya yi la'akari da wannan ya kaunace ni.

In dai don 'ya'yan shi ne ai nima 'ya'yana ne, zan ci gaba da rike su ba sai na zama matarsa ba".

Ya ce,
"Amma za ki zama matar wani ko?

Kuma babu wanda zai aure ki da zugar 'ya'yan Yayar ki?

Da
yar uwarki ta damka miki amanarsu?

Na ji hujjojin ki Fati, na kuma yarda bazaki yi mun karya ba, amma nima ina so in tambaye ki.

Wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya kaita ga matakin zama matar babban likita irin Sulaiman?

Tana 'yar talakawa kuma mace kamar ki?"
Babu dogon tunani ta ce,
"Ilimi".

Ya ce,
"A ina ta samu?"
Ta ce,
"Fita ta yi ta nema".

Ya ce, "In haka ne ke mai zai hana kema ki fita ki nema?'
Ta ce,
"Ba zan iya irin nata ba!"
Ya yi murmushi ya ce,
"Duk ilimi sunan sa ilimi, balle ilimin ki ya fi na kowa, yafi na komai, ilimin Alkur'ani ne da ke wanda ya kunshi dukkan rayuwar duniya da lahira baki dayan ta, ke din nan ba abar wulakantawa ba ce 'yar baiwa ce, mahaddaciyar Alkur'ani, wallahi-wallahi a rayuwar duniya da lahira ba za ki tozarta ba.

Sannan don kina gaishe shi bai amsa ba, sai ki ce ba ya son ki?

Me kika yi masa?

Mutum ne mai kyakkyawar zuciya, shekaru dai-dai har bakwai da nayi tare da shi ban taba ganin wata halayya ta banza a tare da shi ba.

Tunda ya auri 'yar uwar ki ba
a taba jin kansu ba, ba ta taba yin yaji ba, ba ta taba kawo karar shi ba.

Sai ki yi tunanin me Hadiza ta yi ta samu wannan mafificiyar soyayya a zuciyar mijinta, tunda kin zauna da ita, kema ki kwatanta ko ba duka ba, ki gani idan ba za ki samu ba?".

Ta share ido ta ce,
"Baba ai ni gani na yake 'yar kauye, ga shi ni kuma ba zan iya yin irin rayuwar su ba.

Mai ya sa ba za ka gane ba?

Banida abinda zan burge shi da shi.

Don Allah Baba ka aura min ko wane ne, komi yawan matansa da yawan shekarun sa, na rantse zan zauna da shi, amma kada ka kai ni inda ba zan yi kwarjini ba, inda za a wulakanta ni, inda ba za a so ni ba
Ya yi murmushi ya ce, "Babu inda zan kai ki sai gidan SULAIMAN!

Na kuma tabbatar miki ko a yanzu bai son ki, watarana na zuwa da za ya so ki.

Kamar, ko ma fiye da yadda yake son 'yar uwarki.

Daina kukan nan kada ya haddasa miki ciwo, a duk sanda ki kai sujjada cikin sallolin farilla ki ce, "Allah ka sanya soyayyata a zuciyar mijina".

Za ki sha mamaki Fadima, ki sanyawa zuciyar ki salama, shi da yake namiji bai bijirewa iyayen shi ba sai ke?

A'a kada mu yi haka da ke Fadimatu, na san ki, na san halin ki, na tabbata ba za ki bani kunya ba.

Ki yi min alkawarin za ki zauna lafiya da mijin ki, ki yi min alkawarin za ki yi mishi biyayya, ki yi min alkawarin za ki ba shi soyayya irin wadda shakikiyar ki ke ba shi, ki yi min alkawarin ba za ki taba kai karar shi wani waje ba, ke ko mu din nan ban yarda ki kawo karar shi gare mu ba, balle iyayen shi.

Duk abin da ya yi miki na rashin dadi ki yi hakuri, ki yafe mishi cikin zuciyar ki, ki yi mishi uzuri.

Wannan halin YAKANAH kenan!

Sakayyar ki na wurin Allah!!".

Tana kuka sosai ta ce, "Na ji Baba, kuma na yi maka alkawari".

Ya dora hannu a kanta,
"To Allah ya yi miki albarka, ya ba ki juriyar rike 'ya'yan ki, ya sa suma mahaddata alkur'ani ne kamar ki.

Tashi ki dauro alwala ki ci gaba da neman yardar Allah da yardar mijin ki".
****
Dr.Sulaiman yana tuki amma hankalinsa ba ya jikinsa, in banda tafasa babu abin da zuciyarsa ke yi, amma kamar wanda aka dinkewa baki ya kasa ce da iyayen shi komi wadanda ke ta hirarrakin su a kan karamcin iyayen Hadiza.

Har suka iso gida ya kai su bangaren da ya tanada don bakin kwana, wanda ke daga wajen gidan.

Inna kuma ta wuce dakin da yake na Hadiza.

Ya fada toilet ya yo wanka, yana alwala cikin sink sai jini ya balle mishi ta hanci.

Haka ya tsaya yai ta kwararar da habon (nasal bleeding), yana bin shi da ruwa yana wucewa.

A duk lokacin da yake cikin takurar zuciya habo yake yi, ya soma yiwa kanshi taimakon gaggawa har jinin ya tsaya.

Ya fito
bed room
din su wanda ya zama kaca-kaca saboda rashin gyara, ya dauko wata rigar barcin Hadiza ya kwanta rigingine, ya dora rigar a kan fuskar shi yana shakar kamshin Hadizah na dindindin na turaren 'escada-sentiment'.

So da kaunar matar shi ke dawainiya da shi.

Ya lumshe ido ya shafo makwancin ta, katon fili ya yi mishi sallama, wasu irin dumammun hawaye, suka mirgino ta gefen idon sa.

A sannan ne tunanin shirmamman auran da za a yi mishi a gobe ya dawo mishi cikin kwanya, Eh!

Shirmamme mana, don bai dauki wannan auren da sunan aure ba.

Amma a yadda Inna da Malam suka sanya ransu da zuciyar su a auren nan in ya ce baya yi ya tabbata zai bata goma ne daya ba ta gyaru ba, don za su yi fushi da shi, sannan kuma ba za su fasa ba.

Don Malam bai yin magana biyu, sannan ransu za ya baci, kuma ba za su taba shiryawa da shi ba.

Don haka maganar ya je ya ce da Inna bai yarda ba, ko bai amince ba, kamar yadda zuciyar shi ke ta kimsa mishi ba ta ma taso ba.

Illa ya zuba musu ido su yi yadda suke so.

Sai dai ya san yadda suka kawo yarinya, haka za su zo su dauki abar su.

Shi mijin mace daya ne a duniya da lahira (Hadizah).

Bayan ita bashi da sauran bukatar komi daga kowacce diya mace, balle kanwarta duk da Allah ya halarta, amma ai da kunya, ya hada rayuwa da kanwar Hadiza, balle wannan yarinyar da bai san irin ta ba, sannan Allah subhana bai halicci zuciyar sa da kaunar ta ba.

Ba kilin (clean) ba isasshen wanka a jikinta, balle aje ga ado irin na 'ya'ya mata.

Kullum cikin tsummokara!

Yo tsummokara mana?

Kyawun surar ta ya tashi a banza tunda ba ta san yadda za ta yi ta gyara kanta ba.

Shi duk ma ba wannan ya dame shi ba, kawai ranshi baya son Fatima Ja'afar, duk da kasancewar ta kanwar Hadiza.

Jikinsa ya sha ba shi akwai wani al'amari mai GIRMA tsakanin shi da yarinyar, tun daga sanda ya fara ganin ta, cikin kwayar idanunsu wani
chemistry
mai girma ya afku rana ta farko da ya ganta matsayin kanwar Hadiza, amma bai taba kawowa cewa aure ne ba.

Yadda Fati ta kwana ido biyu, haka Dr.

Sulaiman ya kwana ido biyu, kowannen su zuciya na zugi.

Sai dai ita Fati ba ta kin al'amarin musamman in ta tuna da alkawarin da ta daukar wa 'yar uwarta.

Damuwar ta shi ne Sulaiman ba ya son ta, da dan karen tsoron zama dashi dankare a zuciyar ta.

Shi kuwa tunanin yadda zai yi ya tsallake auren yake ba tare da ya batawa iyayen shi ba, ya san a sake dai bai isa ya ce ya saki ba.

Daga karshe ya yanke wa kansa shawarar da yake ganin ita ce za ta fissheshi.

Don haka ya dan samu sa'idar da ya kwanta ya runtsa idon sa.

Kwanciyar sa ke da wuya aka soma kiraye-kirayen sallar asubahi.

Ya dauro alwala ya gabatar da raka'atainil fijri, kamin ya dora da farillar.

Ya yi addu'o'in shi ya koma ya kwanta.

Zuwa bakwai ya tashi ya feso wanka ya debi koriyar Getzner sabuwa kar sai sheki take, ya fesa turare ya zuba hular kube, ya fito kamar saurayi dan shekaru ashirin da bakwai, ba za ka ce shi ne ya aje su Munib ba, zuciyar shi wasai da hukuncin da ya yankewa zuciyar shi.

Ya fito ya janyo kofar ya iso falo, nan ya tarar da Inna ta hada musu kalaci, kunun gyada da dafadukan taliya, kasancewar a gurguje ta yi don dai ya samu ya ci wani abu kafin ya fita.

Ya je ya shigo da su Malam suka yi kalacin gaba daya.

Daga nan suka nufo Karkasara.

Kofar gidan Malam Ja'afar ya cika makil da jama'a wadanda suka zo addu'ar arba'in din Dr.

Hadiza, aka rarraba pieces *na alkur'ani aka yi mata sauka, aka yi addu'o'i na musamman.

Daga nan kafin mutane su watse, waliyyai suka gabatar da daurin auren Dr.

Sulaiman Sulaiman Bakori, da Fatima Ja'afar Mai-Yadi, a kan sadaki naira dubu ishirin kacal.

Mutane suka yi ta mamaki tare da sanya albarka, domin an yi koyi da fadar ma'aiki (S.A.W).
Chapter 17 · 0% Book details