Sashe 23
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga wannan mataki ne mutum zai kasance cikin mutane
yan kadan wadanda suka samu yardar Allah tare da kusanci da shi.
YAKANAH ita ce kofar da ake bi ta cikinta zuwa wurin da baiwar Allah da rahamar sa suke muhimmancin YAKANAH ga musulmi kamar kwatankwacin bargo ne a cikin kashi.
YAKANAH tana a matsayin bargo na Ibadah, kuma sauran ayyuka suna a matsayi na kashi.
Bayin Allah wadanda ake kira
zahideen
masu cike da da
a da tsantsenin duniya, tare da
nasiqeen
masu sadaukar da rayuwar su domin bautar Ubangiji, dukkannin su suna ji da wannan baiwa ta YAKANAH.
Bayin Allah masu YAKANAH basa yin maganganu barkatai, basa yin tsegumi ko wata muguwar magana a game da wani a bayan idanun sa, su kan fadi abin alheri ne a game da shi.
Ba sa shiga sharo ba shanu, kuma zuciyar su fes take.
Ta kuma nisanta da miyagun dabi
u, kamar hargowa da JI DA KAI.
Wato kirjin irin wadannan bayin Allah garau yake.
Duk maganar da irin wadannan bayin Allah masu YAKANAH suka fadi, ta dace dai-dai da abin da suka yi, suka kuma yi imani da shi.
Basu da wani abu da za su boye a zuciyar su domin kada wani ya sani, wato basu da wani mummunan abu a tare dasu.
Bayin Allah ne masu zallar gaskiya da rikon ta, wanda duk ya yi hulda da irin su zai ga cewa basa fafutukar neman kuskure a kan wani, maimakon haka, a shirye suke wajen neman kuskure daga wajen su, wato a kan kansu.
Basa yarda su zauna tare da (marada) (masu kawo tsegumi).
Don haka
yan uwa musulmi mu yi damara da kokarin kasancewa cikin bayi masu YAKANAH, mu rike addininmu, mu kama Alqur
anin mu, mu suturce jikinmu, mu tsayar da sallah domin samun dacewa a duniya da lahira.
Kamar jarumar wannan littafi, Allah ya bamu iko amin summa amin.
Takori
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Yakanah
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Tana ganin sanda sulaiman ya saki wata boyayyar ajiyar zuciya.
Inna ta ce,
To Allah ya yi muku albarka
Ya gyara zamansa cikin nutsuwa yace,
Inna dama na zo in yi muku sallama ne
Cikin mamaki ita da Malam suka hada baki suka ce,
Zuwa ina?
Fati kuwa zuciyar ta ce ta buga, irin bugun da ba ta taba yi ba.
Ya soma yi musu bayanin course din da aka zabe su su goma shi da abokan aikinsa na shekaru biyu a cikin jami
ar Chicago din Amurka.`
Amma tare za ku tafi da iyalinka bakidaya ko?
Malam ya tambaya.
Ya ce a ransa,
An yi ba
a yi ba kenan!
Fatin yake gudu, Fati yake son tserewa, Fatin yake so yayi nisa da ita, Fatin yake son yiwa kandagarki daga son kutsowa cikin rayuwarsa da karfin gaske, bai shiryawa hakan ba, bai taba mafarkin kasancewar hakan ba, kada ta rushe masa plan din rayuwa, in ya dauke ta suka tafi me aka yi ke nan?
Bonono rufe kofar da barawo?
Duk da shi ma ya soma kalubalantar kansa da ganin wautar sa na tsallake abinda rai da zuciya suka soma so da gangan, wai don kada GIRMA YA FADI!
Ya ce,
a, za su zauna ita da Alti saboda yara suna zuwa makaranta
Malam ya ce,
Kun yi shawara ne ta yarda za ta zauna?
Bai iya karya ba, kai tsaye ya ce,
a, bamu yi zancen ba
Ya ce,
To sai ku yi shawara a tsakanin ku can, in ta yarda za ta zauna din shikenan, mu
yan sanya albarka ne
Ba su taho ba sai yamma lis, kamin su iso gida har an yi kiran isha
i, kasancewar duk a koshe suke, Inna ta cika musu ciki da dambun shinkafar ta mai dadi, basu shiga kicin ba kowacce ta nemi makwancin ta, yaran ma sun nabba
a a dakin su, shi kuma ya juya asibiti.
Fati tana shiga daki ta kwanta rub da ciki, da filo a karkashin ta cikin wani mawuyacin hali na soyayyar Baban Munib da ke cin zuciyarta.
Ta kai hannu ta dafe kirjin ta wanda ke bugawa da-sauri-da-sauri da haruffan SU-LAI-MAN a kowacce dakika, zai tafi ya barta, bayan ya gama da farauto zuciyarta, ya kimsa mata soyayyar da ba ta san iyakacin ta a zuciyar ta ba.
Ya warware duk wata nutsuwa da tunanin da ke tare da ita, ya mamaye 80% na zuciyarta.
Ya haifar da wasu al
amura masu girma a gare ta da ba ta san ya ya za ta yi dasu ba.
Jin tafiyar shi take har ruhi da bargon jikinta, Fati tace wai maiyasa wasu mazajen suke haka ne?
Idan sun san sun kimsa maka soyayyarsu, sai su nemi gudu su barka da jibgin abar ka?
Wasu hawaye suka zubo, maimakon ta share sai ta tara hannu tana tarar saukar su a kan tafukan ta.
Ba ta ji motsin bude kofa ba sai alamar zaman mutum a gefen ta, kafadunsu suka gogi na juna, ta yi hanzarin juyawa, Dr.
Sulaiman ke kallon ta da murmushi.
Ya sanya hannu cikin aljihun bakin jeans da ke jikinsa, ya zaro hankicin sa ya mika mata, ta jima ba ta karba ba, daga karshe ta karba ta share ambaliyar hawayen ta.
Ya mika mata hannu alamar ta ba shi abinsa, sai ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kai ba tareda ta bashi ba.
Ya ce,
Bani mana?
Ko kukan bai kare bane?
Ta tsuke fuska, ta tsuke baki, ta hade girar sama da ta kasa.
Ya yi murmushi ya sa hannu cikin hannunta ya dauke hankicin sa, kadan ya rage ta sume da hucin sassanyan numfashin sa ya doki fuskar ta, kamshin jikin sa na fizgar ta, da wata itin fizga mai karfi, kamin ta farfado daga shidewar da ta yi na wucin gadi ya fice a dakin.
Zuwa can kuma ya dawo da takardu a hannun sa, sai dai wannan karon ya janye murmushin da ke kan fuskar shi, ya zauna dab da ita cikin kakkausar murya ya ce,
Me ya sa ki kuka?
Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, zuciyarta na ci gaba da azalzala da azabar soyayya, wadda ke linkuwa a bayan kowacce dakika.
Jikinta ya soma rawa, tana son cewa ya tashi ya ba ta waje ta samu iska amma ta kasa.
Kallon ta yake yana (observing) da i
do, da zuciya.
Gaba daya yanayin ta ya sauya, ya nuna wata mace da ke azabtuwa da soyayya da sha
awar mijinta mai yawa.
Amma kawaici da kau da kai ya rinjayi komi, ya tabbata idan ya tafi ya bar ta cikin wannan halin, Allah ba zai yafe mishi ba, amma tunanin Hadiza ya danne komi.
Tattalin girmansa da mutuncinsa a idanun yarinyar ba zai bar shi ya aiwatar da abinda zuciyoyin su da gangar jikin su ke so ba, idanun shi a juye yake kallon ta, gangar jikin shi babu inda bai kaduwa.
Ya soma kokarin saisaita kansa, in azabar soyayya ce ai ya fita dandana, ba tun yau ba.
Ya janyo brief case ya fiddo daurin kudi masu tudu
yan awolawo ya ajiye a gefen ta, sannan ya mika mata form din JAMB Online.
Ta dan ware ido tana kallon sa da alamar jin dadin hakan sosai a kwayan idanun ta, ya kawar da fuskar shi gefe ya ce,
Zan bude maku account da skyeBank in Allah ya kai mu gobe, in na wajen ki sun kare kuna da bukata sai ku je ku diba.
Akwai sabon direba na aje muku duk inda kuke son zuwa ki kira shi a waya ki gaya masa, ni zan tafi jibi insha Allahu sai Allah ya nufe mu da dawowa.
To amma Fati, ba zan samu ko da kalmar Allah kiyaye hanya ba, daga Fatin da ba zan kara gani ba, sai bayan wasu shekaru har guda biyu?
Hawayen ya kara zubo mata, ta yi saurin sharewa da bayan hannun ta.
Ya tsura mata ido analytically, can kuma ya ce,
Girl, ina so in san damuwar ki
.., Akalla ko ban yi miki maganin ta ba, ina da shekarun da zan ba ki shawara a kanta.
Ta bangare na dai duk hanyar da nasan zan bi in gyara kuskure na nabi, amma kin ki bani hadin kai I do not your thoughts.
Not even a single word from you, you are indeed a nice person!
Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi!!
Ta yi hanzarin dagowa ta dube shi, kallon ta yake ta cikin kwayar idon shi, da wani lallausar murmushi makale a gefen bakin shi.
Gaya min mene ne damuwar ki Fatima?
A hankali ta ce,
Babu
Ba kya bukatar komai?
Nan ma ta ce,
Eh, Allah ya kai ku lafiya!
Ya ji dadin addu
ar da ta yi mishi, sai dai ba irin wannan rabuwar yake so su yi ba, ta rashin dadin zuciya.
Ta ki sakin jiki dashi ko yaya ne.
Ya kama tafin hannun ta ya rike cikin nashi,
Ba za ki gaya min abin da ke sanya ki kukan ba?
Ta ce a ranta,
Za ka yi min magani ne?
Magana ta yi a zuci, ba ta san ta fito, ta shiga kunnuwan sa ba.
Idan ina da shi me zai hana in yi miki?
Ta ce,
Bani da damuwa, ba sai mutum yana da damuwa yake yin kuka ba, wani zubin mutum yana yin kukan, don ya ji dadin ransa
Ya yi murmushi a kaikaice ya lakaci kuncin ta da dan alinsa,
Mu kwana lafiya, amma ina rokon ki duk wasu inconveniences ki yafe min su!!!
Ta lumshe ido kafin ta ce,
Babu wani inconvenience game da kai a tare dani, kada ka manta ka ce ni kanwar ka ce.
Idan Yaya Mukhtar ya yi min laifi zan kullace shi ne, ko zan kasa yafe mishi?
Ya yi kirr!
Da ido yana duban ta da wani irin sassanyan kallo.
Kalmar
Yayan
sai yau bata yi mishi dadi ba kamar ba shi ya jaddada ta ba.