Sashe 22
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta rufe ido tana dariya, shima ya san bazata iya ba, har a gobe halayenta na kawaici da alkunya basa canzawa, sai shi ne ya karaso ya rungume ta tsantsan a hankali, yana fada mata kalaman da suka zama sirri ne a tsakanin su tana ta sakin murmushi.
Cikin ranta addu
a take Allah ya barta da SULAYMAN dinta, ya dorar da rayuwarsu cikin daukaka da soyayya, kamar yadda ta faro, har zuwa ranar da suka daina numfashi.
*** ***
SHEKARU GOMA SHA BIYAR A GABA!
Taron rantsar da sabbin ministoci da mai girma shugaban kasa President Umaru Musa
Yar Aduwa zai gabatar a yau a hotel din NICON NOGA, har da babban likitan zuciya da kasarmu Najeriya ke tanka how
da shi, wato Dr.
Sulaiman Sulaiman Bakori, wanda aka rantsar a matsayin Ministan Lafiya na kasa baki daya.
Ranar Litinin, ashirin da shida ga watan Maris, na wannan shekarar.
Dr.
Fatima Ja
afar, H.O.D Islamic, a jami
ar Abuja, cikakkiyar mace
yar kimanin shekaru talatin da bakwai da haihuwa, uwar
ya biyar a halin yanzu, in ka hada da manyan
yan ta Munib, Muniba da Nana Khadija sun zama su takwas kenan.
Tana sanye da bakar abaya kirar Bahrain da mayafinta, hannunsu sakale dana juna suka isa ga mazaunin su, daukacin Ministocin da ake shirin rantsar wa suna tare da matansu da rakiyar
yansu, to haka suma, Muniba, Nana Khadija, da Ja
afar.
Ya yin da suka baro Mufida, Mufid da Ibrahim da dan autan su Abdulhak a gida, cikin kulawaar tsohuwa Alti.
Bayan mai girma shugaban kasa ya rantsar da Ministocinsa, aka zarce da gagarumar walima.
Ba su baro dakin taron ba sai dare, suna kan hanyar isowa gida wayar Munib ta shigo, wanda ke can kasar
Srilanka
yana karatun harhada magunguna.
Munib Ya ce,
Daddy kun manta dani, ko waya an fi sati ba wanda ya yi min.
Yanzu nake jin abin alheri a BBC, congratulations Daddy!
Ya ce,
Kwantar da hankalin ka Munib, zirga-zirga ta hana mu neman ka.
Ina mai yi maka albishir da cewa, muna tafe dukkanin mu cikin satin nan, sai ka tanadar mana better
Ya yi ihu ya ce,
Allah Daddy da gaske?
Fati ta amshe wayar ta ce,
Amma sai in point din ka na wannan semester ya kai CGPA 4.00, if not, babu wanda zai zo
Ya ce,
Wallahi 4.60 ma na samu Mummy
Ta ce,
Ah, lallai Babban Yaya ka gama min komai, zuwan kowa ya zama dole, tunda duk muna cikin hutu
afar ya amshe wayar ya ci gaba da ba shi labarin duk shagulgulan da ake yi a yau.
Munib ya ciji yatsa ya ce,
Ayya!
Na yi missing
Daga nan sai Muniba, ita kuwa Nana ta ce, ba za ta yi magana da shi ba tunda baya yi mata waya sai budurwar sa kawarta Naina.
Daddy ya harare ta ya ce,
Bana son sakarci, shi ba shi da wata budurwa dan makaranta ne
Ta ce,
Amma yake yi mata waya yake yo mata tsaraba in zai zo?
Ya ce,
Ba kanwar shi ba ce?
Ke ba ya yi miki?
Ta ce,
Wallahi Daddy nata ya fi yawa, har da kati an rubuta I LUV YOU
Fati ta tintsire da dariya, shi kuma Dr.
Sulaiman sai ya rasa ta cewa, yaran zamani sai a barsu, da wayonsu ake haifar su.
Ya dubi Fati da wani irin sassanyan kallo,
Momin yara, wai da gaske ne Munib yana da budurwa?
Ta rausayar da kai ta ce,
Shirmen Nana ne, Naina Bunza, tana da shiga ran kowa sosai ba Munib kadai ba, suna shiri da Munib sosai sabida kokarinta.
. (Diyar Dr.
Surayyah).
Ya ce,
Ba zan yi mamaki ba in son nata yake, ai jin kanshi yake matured (balagagge) kamar kowa
Dariya ta kama Fati, sai da ta murmusa sosai.
Sun isa gida yara kowanne ya kama harkar gabansa, ya cacumi Fati su kai sama ana biyan bashin soyayya, wadda hidimar kwana biyu ba ta bari ba.
Suka ci gaba da amsa sakonnin taya murna da fatan alheri daga
yan uwa da abokan arziki, har tsayin sati daya.
Ranar juma
a jirgin MEA International ya tashi dasu zuwa Srilanka, har filin jirgi Munib yaje ya taro su, ya dauki Abdulhaq ya rungume suka karasa zuwa makarantar su bayan sun yi booking din hotel din da za su sauka.
Farin cikin Munib ba sai an fada ba, ya rasa inda zai sa iyayen shi da
yan uwan shi.
Dr.
Sulaiman ya yi bincike sosai kan karatun shi, ya yaba sosai da hazakar da yaron ke nunawa.
Kwanan su uku suka wuce Saudiyyah suka yi Umarah, sannan suka dawo gida.
Da albashinta da ta ke tari, da kuma taimakon Dr.
Sulaiman, Dr.
Fatima Ja
afar, ta bude makarantar Islamiyya ta yara maza da mata a nan Abuja, da aka sanyawa suna NANA HADIZAH ISLAMIYYAH.
Haddar Alkur
ani mai girma ake yi tsantsa, sai sauran littattafan addini irin su Ishmawi, Bulugul Maram, Sirah, Hadith, Al-Akhdari, Fikh da koyar da harshen larabci.
Ana zuwa daga karfe biyu na rana zuwa shida na yamma.
Ba ta da abin da za ta ce da Dr. kuma Minista, Sulaiman dan Sulaiman, sai godiya da addu
ar alheri, domin ya gama cika mata burinta na son yada ilimin Alkur
ani da hadisi, kamar yadda ta ke buri.
Ya lullube ta da duk wasu alhairori na rayuwa, ya lullube ta da so da kauna.
Gaskiyar Babanta ne; Alqur
anin ta ba zai bari ta tozarta ba!!!
Ta san Sulaiman ba ya son ta ya aure ta, kuma ba zai taba son wata diya mace kamar yadda ya so Hadiza ba, amma tana tantama a halin yanzu, idan son da yake mata baiyi kunnen doki da wanda ya yi wa Yayarta Dr.
Hadiza ba.
A alfarma ta soyayyah, ta san ba ta cancanci Dr.
Sulaiman ya so ta a wancan lokacin ba, amma ya so ta saboda hakuri, juriyar ta da YAKANAR ta.
Ya so ta sabida kyawawan halayenta.
Mene ne YAKANAH?
Nayi tattaki har gidan Dr.
BAKORI na tambayi Malamarmu, Dr.
Fatima Ja
afar Mai-Yadi.
Ta yi murmushin ta mai motsa zuciya tace.
Takori ba ki san Yakanah ba?
Na ce,
Ina zan sani Fati?
Sai ku malaman addini
Ta yi murmushi ta ce,
Nima daliba ce SUMAYYAH!
Sai dai in sanar da ke dan abin da na sani a dalibtaka ta
Na ce,
daure ki sanar dani Aunty Fati, komi kankantar sa.
Domin al
umma zasu so su san me ita wannan kalma ta YAKANAH take nufi?
Faty ta yi murmushi tana dubana ;
MECE CE YAKANAH???
Ita YAKANAH ba kasaifai ake ganin ta a wajen yawancin mutane ba, YAKANAH ita ce take daukaka darajar mai yin Ibadah, ta kai shi wani matsayi na daukaka a wajen Allah.
YAKANAH ita ce tushen dukkanin aiyuka na gari, wato daukacin ayyukan kirki suna fitowa ne daga cikin ta.
Mutum mai YAKANAH shi ne mai yin babban jihadi ko gwagwarmaya da kansa wajen watsi da abubuwan da rai da zuciya ke so, saboda neman yardar Ubangiji, da neman dadin falalar sa, tare da nuna biyayya a gare shi.
An ambaci irin wadannan mutane a cikin Alkur
ani mai girma, kamar cikin suratul Al-Imran (3:17) Al-Nisa
i (4:25, 127-128), Fussilati (41:34) da sauran su.
Irin wannan babban jihadi da kai ana yin sa ne tsakanin mutum da zuciyar sa (Nafs Al-Ammara), domin sauya ta ya zuwa (Nafs Al-Lawwama), sannan ya zuwa zuciya madaukakiya (Nafs Al-Mutma
innah).
Saboda haka madallah da ita wannan baiwa ta YAKANAH, domin tana kai masu yin Ibadah zuwa ga matakin shiga cikin rukunin salihai wadanda a koyaushe suna masu yin godiya a kan dukkanin abin da ya zo musu daga Allah.
YAKANAH it ce kololiyar taqwa wato tsoron Allah.
Takwah kuma ita ce mai kore tsoron haduwa da Allah (wanda ba ya jin kunyar ubangijinsa kuma mai sabon sa, shi ne mai zama cikin fargabar haduwa da Allah).
Daya daga cikin ma
anar YAKANAH ita ce, ka dinga kallon kanka a matsayin kai ba kowa bane a cikin jama
a, kuma kowa ya fi ka, saboda haka YAKANAH tana nuni da rashin kasancewar mutum cikin halin GIRMAN KAI!
Misalai: Idan ka kasance mutum ne kai mai YAKANAH ta gaske, a duk lokacin da ka gamu da wani mutum wanda baka san shi ba, komi lalacewar sa, sai ka ce da kanka a cikin zuciyar ka.
Watakila matsayin wannan mutum a wajen Allah ya fi nawa
Idan kuwa ka gamu da yaro kankani, sai ka cewa kanka,
Ka ga wanda ba ya sabon Allah, ni kuwa ina yi
Idan kuwa ka gamu da wanda ya girme ka, sai ka ce,
Ka ga wanda ya jima yana bautar Ubangiji tuntuni kafin ni
Idan kuwa ka yi kicibus da mutum mai dimbin ilimi, sai ka ce,
Ga wanda aka yiwa baiwa da abin da ni bani da shi, domin ya fi ni ilimi, kuma yana aiki da ilimin sa, amma ni ko ya ya dai?
Idan kuwa ka yi karo da jahili, sai ka ce,
Dubi wani yana sabon Allah cikin rashin sani, ni kuma ina yi cikin sani.
Ga shi kuma ban san yanda karshen sa zai kasance ba, kuma ban san nawa karshen ba.
Ko me zai zama a nan gaba?
Allah shi ya fi kowa sani
Idan kuwa ka gamu da kafiri, sai ka ce da kanka,
Wa ya sani?
Watakila nan gaba ya musulunta kafin ya mutu, kuma wa ya sani ko ni kuma in mutu a kafirce?
Ire-iren wadannan maganganun gaba daya suna nuni da halin mutumin da YAKANAH da tawali
u suka baibaye shi, yake kuma cikin hali na binciken kansa a koyaushe.
Dalilin irin wannan tunani a zuciyar wannan bawan Allah shi ne, yana cikin yanayi na rashin yarda da kansa.
Tare da rashin tabbas game da abin da zai abku wajen haduwar sa da Allah.
Ire-iren wadannan tunani kuwa suna nuna karfin imani ne da dogaro da Allah madaukakin sarki wanda shi ne tushen kaskantar da kai.
A kowanne lokaci idan bawa ya kaskantar da kansa, Allah zai kare shi daga masifu, kuma ya ba shi sirrin
Ikhlasi
Wato nacewa da son bin hakikar gaskiya a dukkannin al
amuransa na yau da kullum.