← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 26

Sashe 26

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Yau dai ya tabbatarwa kanshi Fati ta ci kwallon, ta yi winning a kansa, ta kayar dashi warwas, duk da tana kidahumar ta.

Kenan a so mutum, soyayya ta gaskiya ba ya nufin a nuna tsiraici, ko abubuwa na jan hankali.

Halin mutum shi ne jarinsa,
yammata sai ayi hattara!
****
ana kwance a gadon bonon Inna, lokacin da wasu lambobi rankacau suka shigo cikin wayar ta.

Ba a jima ba sako ya shigo.

Ni na san ni mai laifi ne, amm ina neman afuwar ki kamar kullum.

Fati, zan samu?

Ta maimaita sakon ya fi sau hamsin, babu wanda ta sani a kasar waje sai mijinta Dr.

Sulaiman.

Ta mike ta yi sujjada ga Allah da ya karkato mata da zuciyar abin sonta, cikin addu
in da take kwana da yini tana yi.

Amma ba ta ba shi amsa ba, don ta dade da sanin shi hawainiya ne canza kala yake yi.

Tana tsoron kar ta kara sakin jiki da shi ya zo ya sake guje mata kamar baya, bayan ta sakankance da shi ta amshi ban hakurin sa da soyayyar sa.

Tun yana sauraron amsa har ya koma ya jingina da balcony na harabar flat din shi.

Ya kira wayar har ta gaji ta tsinke ba ta daga ba.

Ya san Fati ta yi fushi!

Haba!!

Ai ko shi ne, shekara guda da rabi ba kwana guda da rabi ba.

Sai dai ya san sanyin halinta, da wuya su yi arba ya ba ta hakuri ba ta hakura ba.

Hankalin sa ya tashi sosai,
Wallahi ka yi a hankali tun hakki bai kama ka ba
Ya tuno kalaman Smith, kirista ma kenan, balle shi da yake a cikin musuluncin sa.

Inna na tuyar masa, Fati na wankin kayan Nana a jikin famfo, sanye take da riga da zani na atamfa (super) ruwan ganye.

Ta makala dan karamin hijabi iya kafadun ta.

Babu wani make up a fuskarta, sai tsabar kyawun halittar tsurar sa.

Nana na gefe ta yi fes cikin fararen suwaita da (mini skirt) kanta ya sha ribbons da rufaffen takalmi da socks a kafarta, tana ta wasa da Saddika
yar Anti Ramatu.

Khalid ya soma shigowa da wasu firda-firdan jakunkuna, can kuma sai wani kamshi da ta dade da sani na turaren
Chris Adams
ya bakunci hancinta, kamin ta gama tantance abin da ke faruwa ta jiyo
husky
muryar Dr. na Hadiza suna gaisawa da Malam a soro.

Ranta ya yi fari, duk wani kunci da ke cikin zuciyar ta sai ya yaye, ta tabbata ya kasa hakuri ne da yin biris din da ta yi da shi, shi ne ya taho, ba zato ba tsammani.

Ba ta fasa aikinta ba amma kar ki so ki tona zuciyar ta, da soyayya ta yiwa illa mai yawa.

Ji ta yi kamar an dauke numfashinta, tana shirin faduwa a gindin famfon, ta yi sauri ta kama kan famfon, harshen ta na addu
ar neman nutsuwa daga rabbil izzati.

Karasowa ya yi gindin famfon ya yi tsuguno a gaban ta, ya leka fuskar ta yana murmushi.

Ta gan shi ya yi kyau, amma ya rame, fatar shi ta kara taushin gani a ido, ya zama cool kamar ba shi ba.

Ta yiwa Allah tazbihin kasancewar ta matar Dr.

Sulaiman-Sulaiman Bakori, domin ba ba kowadanne maza ne irin Sulaiman ba, ko da ba ya son ta ai ya damu da ita, tunda fushin ta ya tunkudo shi har inda take.

Ya mika hannu ya dauki Nana yana sumbatar ta, fuskarta babu fara
a ta ce mashi,
Sannu da zuwa
Hararar ta ya yi,
Bana son sannun ki, rike abin ki
Inna ta fito daga cikin kitchen bakinta ya kasa rufo, suka wuce dakin ta yana dauke da Nana wadda ke ta kukan ya sauke ta don ba ta san shi ba.

SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
e30e75a2bdfa44daab315761930dba81
Chapter 26 · 0% Book details