← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 26

Sashe 15

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo daya za ka yi mishi ka tabbatar da cewa har yanzu mutuwar matar shi ba ta gama dukan shi ba.

Ta juya suka koma ciki, suka zauna a falo.

Ta ce, "Ka kara YAKANAH Sulaiman, a kan wadda kake da ita.

Ka rike Fatima da amana, domin amanar ce a hannun ka.

Jiya baka je ka ga ya take ba, ya ta zo, meye matsalar ta balle lafiyar ta.

Sannan yanzu ma ka fita ba tare da ka neme ta ba
Ya yi shiru kansa a kasa, a gaskiya!

An takura rayuwar sa, an kakaba masa abin da bai san ya zai yi da shi ba.

Ba ya jin ko sautin shi zai iya bai ma Fati.

Amma Inna gaskiya ta fadi, dole ya dinga bincikar lafiyar ta.

A sanyaye ya ce, "Ki yi hakuri Inna, insha Allah, zan kula".

Ta ce,
"To Allah ya yi maka albarka".

Ya ji dadi har kokon ransa, ya ce,
"Za ku jiranin in je in dawo in kai ku?"
Ta ce, "A'a, ka maida hankali kan aikin ka.

Ga Jibril zai kai mu, sai mun yi waya, Allah ya hada mu da alheri".

Ya zaro kudi cikin aljihun sa ba tare da ya kirga ba ya mika mata, "Sai a ba Jibril ya sha mai".

Ya sake zaro wasu, "Wannan kuma sai a rabawa su Ruma, karshen watan nan zan zo insha Allah in abin da nake jira ya fito".

Ta ce, "Meye abin da kake jira?"
Ya yi murmushi kadan,
"Sai na zo din dai Inna".

Bayan fitar sa ta shiga dakin Fati, ta tarar da ita ta yi wanka ta sauya kaya, cikin doguwar riga kirar Omman ruwan makuba, ta makala dan kankanin hijabi fari iya wuyanta, fuskarta sumul babu ko tabon pimples ko daya, sannan babu wani make-up amma ta yi kyau sosai.

Akwai wata boyayyar kauna da Inna Halima ke yiwa Fati, wadda ta dasu a ranta tun daga lokacin da ta fara zama da ita daki daya, ta fahimce ta, ta fahimci akidar ta.

A wancan lokacin ta ce a ranta, ina ma ina da wani babban da in aura mishi Fati ko ya samu tabarrakin da ke tattare da ita, Khalid bai isa aure ba.

To ashe dukkan su rabon Sulaiman ne, haka Allah ya tsara.

Ta zamo daga gadon ta russuna tana gai da Inna, ta kama hannun ta suka zauna a gefen gadon tare, ta ce,
"Mun kwana lafiya Fatima?" Ta ce, "Lafiya kalau Inna, ya ya gajiyar ku?" Ta ce, "Gajiya ta bi lafiya Fatima, mu za mu wuce Bakori, sai kuma Allah ya hada mu cikin alherin sa".

Idanun ta suka yi rau-rau kamar za ta yi kuka, Inna ta ce, "A'a, kada mu yi haka da ke, mun yi waya da Alti tana nan dawowa karshen wannan satin, ba za ki zauna cikin kadaici ba.

Sannan ungo wannan".
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Ta mika mata kwalin karamar waya kirar Nokia, ta ce "A hade take da caji da komai har layi an sanya, jiya na aika Jibril mijin Ruma ya siyo, duk wata matsalar ki kada ki nemi kowa ki neme ni.

Sannan kada ki ji shayin gaya min komai wai don ina uwar Sulaiman, dukkanin ku 'ya
yana ne, baki da wata damuwa?"
Cikin nishin kukan da ke son ya balle ta ce,
"Dama........dama ina so a karbo min Nana ne".

Inna ta yi shiru kamar tana tunanin wani abu, can kuma ta ce, "Ki dai yi hakuri zuwa rana
i ta yau din, ko kin manta ke AMARYA ce?

Ki huta kwana bakwai, ki kula da mijin ki.

Rana ita yau za a kawo miki 'ya'yan ki dukkan su.

Allah ya yi muku albarka kan biyayyar da ku kai mana, kuma ya sa 'ya'yan ku su yi muku fiye da ita.

Kada ki yi wasa da GIRKI Fati, domin shi ne mafi saukin hanyar isa ga zuciyar miji.

Na barku lafiya".

"AMARYA!

AMARYA!!"
Fati ta maimaita kalmar Inna.

Bayan fitar Innar.

Sannan ta koma ta kwanta rub da ciki a kan katifar ta
I'm not a bride Inna (ni ba amarya ba ce Inna).

Ita amarya cikin farin ciki take, cikin sa take kwana, cikin sa take wayar gari, cike da soyayyar mijinta.

Amma ni yaya na kwana?

Kwana na yi cikin suyar zuciya da tunanin 'yar uwata abar sona, wadda take min soyayyar da babu mai yi min ita a duniya, in ka cire iyayena.

Bana kin sa shi yake kina, a kan laifin da ban sani ba.

Ban san so ba balle in ce bana son sa.

Amma ni meye laifina a kan auren da nima ba so nake ba?

"Kulawar MATA yake nema
..".

Ta tuno furucin karshe na Hadizah.

To ga ni na zama matar tasa Yaya Hadiza, wace irin kulawa kike nufi in ba shi?

He is old enough ya kula da kansa, wanka zan mishi ko pampers zan cire masa?

Goyon shi zan yi ko feader zan ba shi?

Ban san wacce irin kulawa kike nufi ba.

Ta kai bayan hannu ta shafe hawayen ta, banda GIRKI kamar yadda Inna ta ce, in za a kashe ta ba ta san wata extra kulawa ta daban da mace ke yiwa miji ba.

Sannan ba ta iya shisshigi da cusa kai a inda ba za ta yi kwarjini ba.

Bayan tafiyar su Inna gidan sai ya yi shiru, babu sauran wani mahaluki in ka dauke Malam Ilu dake can bakin
gate
yana gadi, an bar ta daga ita sai halinta.

Ji ta yi kamar an kawo ta kabarin ta, ta yi kuka ta yi kuka har ta gode Allah.

A karshe ta tattara komi ta mikawa Allah, ta jawo kular da Inna ta ajiye mata ta debi abinci tana ci.

Ai ba ta tashi jin tsoro ba, sai da karfe tara na dare ya yi, Fati ba ta taba kwana a gidan da babu mutane ba, ta tabbatar ita kadai za ta kwana a wannan katon gida, don tuni ta san Dr.

Sulaiman ya saba aikin kwana.

Jikinta ya soma mazari kamar ana kada mata gangi, ta daddage ta takure a can karshen katifa ta kudundune cikin bargo tana dakacen ina ma ita ce ta tafi, Hadiza ta zauna, ko babu komai Hadiza ta fita bukatar rayuwar.

Na farko tana aikin lada, ta hanyar ceton rayuwar mata
yan uwanta.

Na biyu tana da 'ya'ya tana kula da tarbiyyar su da rayuwar su, na uku tana da mijin da ke son ta suke rayuwa cikin so da kaunar juna.

To amma ita fa?

Babu sidi babu sadada.

Ba ta kai karshen tunanin ta ba ta ji karar fashewar tangaran a kitchen, wannan ya tabbatar mata ba ita kadai ce a gidan ba, to wane ne?

Ta san dai ba maigidan bane, don shi in ya dawo karfe shida ba ya kara fita sai takwas, ba kuma zai dawo ba sai past ten sai dai in yana da aikin kwana.

Ta ji dan tsoron ya ragu, ko ba komi tana da confidence na cewa akwai mutum cikin gidan ba ita kadai ba ce.

Ta mike ta fito ta nufi kitchen, wanda ba ta zata ba shi din ta gani, ya tara hannu cikin famfon sink yana wanke jinin da ke bulbula daga hannun sa, ga kuma kwai yana ta kauri a kan cooker.

Ta karasa da sauri ta sauke, ta kashe gass din.

Ta dauki tsintsiyar laushi ta soma tattare fasashshen tangaran din, kafin ta farga ya fice a kitchen din yana ta disar da jini a kan tiles.

A take ta hada wani kwan ta soya masa, ta juye a farantin tangaran ta debi
cake
samosa da spring roll cikin firji ta dumama a microwave , ta tafasa ruwa nan da nan ta juye a karamin tea flask ta kwasa ta yo falo don ta bashi.

Ya tada kai da karamin filo yana kwance a tsakiyar kilishi, sanye da fararen riga da wando na barci marasa nauyi, har yanzu dan yatsansa bulbular da jinni yake, amma bai damu ba, kamar ba jikinsa ba, ta zo gaban shi ta russuna ta aje mishi, sannan ta sanyaya murya ta ce,
"I'm sorry!".

Bai kalle ta ba, haka bai amsa ba kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta a gun ba.

Kai bangaren data ke ma bai kalla ba.

Ta mike za ta koma daki cike da tunanin hannun shi da ke ta kwararar da jini, amma matsayin shi na likita bai yi wani kokari ba ko yaya ne don dakatar da gudun jinin ba.

Ta san da Hadiza tana nan Allah kadai ya san irin gigicewar da za ta yi, sannan za ta sa mishi magani ne ta daure, sannan ta yi ta jinyar ciwon har sai ya warke.

Hakan ya taba faruwa da ya sharce babban dan yatsan sa garin ferar tuffaha, irin wannan kulawar kenan Hadiza ke nufi ta yiwa mijinta?

Da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.

Aka ce wargi ma wuri shika samu; ko fuska babu, ba ta son tuno yadda ya yi da fuska kaman an aiko mishi da manzon mutuwa lokacin da ta shiga kitchen din.

Ba ta kai ga shiga daki ba ya yi mata wata irin tsawa wadda ta gigita ta, ya ce,
"Ke!"
Ta juyo da sauri.

Ya ce,
"Zo ki batar min da wannan shirgin naki a nan, na ce da ke ina bukatar taimako ne?"
Jiki na rawa ta dawo ta russuna za ta dauke, ya kama fatar kunnuwan ta da riko mai karfi, ta sa kuka don azaba.

Ya ce,
"Daga yau sai yau kada ki kara shiga shirgina, ko me za ki ji na yi kada ki zo inda nake, tunda ban neme ki ba.

Na yi kama da saurayin ki ne?

Be careful ni Yayanki ne, mijin Yayarki, Hadiza.

Idan kin manta in
tuna miki.

Tun da kin yarda a kawo ki ki yi zaman 'ya'ya ki lalata kuruciyar ki a banza, to ki yi ta yi.
Chapter 15 · 0% Book details