Sashe 13
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana yiwa su Munib shimfidar kwanciya goye da Nana, Yaya ta yane labulen dakin ta ce,
"Fati kin kwanta ne?"
"A'a, ina harama dai".
"To biyo ni dakin Malam yana son magana da ke".
Ta sauke goyon ta zurma hijabin ta, ta bi bayan Yaya har dakin Malam.
Ta sha mamakin ganin taron dakin har da Baban Munib, wanda ke can sunkuye da kai a gefe.
Ta yi sallama cikin sassanyar muryar ta dukkan su suka amsa, ban da Sulaiman wanda ya fara shan jinin jikinsa kan wannan taron domin shi aka yi.
Jikinsa ya yi sanyi, gaban shi ya soma faduwa, haka nan gwiwoyinsa ya jisu kamar an rarrade su da murfin kwano.
Ta samu gefen Inna ta zauna, ita ma jikinta ya soma kyarma don ba ta son a tirke ta a cikin mutane.
Iyayen dai na duban su suna nazarin kowannen su, sun fahimci dukkan su a firgice suke, amma firgitar ta fi karfi ga Sulaiman.
Wannan taro na mene ne?
Malam Sulaiman baya shiga kankanuwar magana.
Sai da suka tabbatar sun dan samu nutsuwa sannan Malam Sulaiman ya dubi dansa ya ce,
"Mai sunana wani abin alheri ne za mu yi maka, da fatan za ka karba hannu bibbiyu".
Bai yi magana ba, amma ya dago ya dubi mahaifin sa.
Ya ci gaba da cewa,
"Muna kara yi muku ta'aziyya, sannan muna so ku sani cewa, duk abin da Allah ya tsara akwai hikimar yin hakan a cikin sa.
Mun zauna mun yi tunani, mun yi shawara mun yanke cewa, Fati za ta maye gurbin 'yar uwarta a gare ka, ku ci gaba da raino da tarbiyyar 'ya'yanku kamar yadda mahaifiyar su ta fara yi musu, kuma 'yar uwarta ta karbe ta.
Allah ya riga ya hada mu, zuri'a ta hada mu.
Don haka Sulaiman bana son ka da wani aure in dai ba jinin gidan nan ne ya kare ba.
Za mu yi alfahari daku idan kuka taushi zuciyoyin ku kuka yi mana biyayya.
Allah zai nunawa Hadiza har cikin kabarin ta cewa, ke Fati kin rungumi iyalinta, kin rungumi mijinta baki bar rashin ta a rayuwa ya tagayyara su ba.
Sannan kai Sulaiman Hadiza za ta yi farin ciki idan har ya zamto ka rungumi amanar rayuwar 'yar uwarta ta hanyar aure, wadda kowa shaida ne kan bata da kamarta, muna neman hadin kan ku, shin za mu samu Fatima da Sulaimanu?"
Da a ce Malam Sulaiman ya lura, da ya ga irin jibin (zufar) da ke ambaliya a fuska da jikin Sulaiman, yayin da gudun jini ya katse a jikin Fati, idanuwanta suka juye suka kada suka yi jazur, hanjin cikinta ya dunkule waje daya ko dan yatsanta ta kasa dagawa balle ta motsa bakinta.
Tana addu'a cikin zuciyarta idan mafarki take Ubangiji Allah subhana ya yi gaggawar farkar da ita.
Sai dai a bangaren shi Sulaiman, ya so a ce shi da iyayen shi ne kadai su kai wannan maganar, da a take zai ce dasu idan kasa da sama za ta hadu bai amince ba.
To an ce wai ko mutuwa tana kunyar iyaye, balle iyayen Hadiza?
Ya zai yi ya iya ya budi baki a gabansu ya ce baya son jinin Hadiza?
Shi tunda ya rasa Hadiza bai kara tunanin nan gaba zai kara yin aure ba, bai kara tunanin wai yana da future ba, balle ya yi tunanin yin aure.
Kuma a rasa wadda za a aura masa sai wannan yarinyar da bai san a matsayin da ya ajiye ta a zuciyar sa ba.
Duk da yadda take hidima da 'ya'yansa, Fati ba ta taba burge shi ba, Allah bai sa masa kaunar ta a zuciyar sa ba, sannan kuma wai auren ma daga yin arba'in din Hadiza?
Sannan da shakikiyar ta?
Fati ba ta taba burge shi ba balle ya so ta, bai taba tunanin irin ta a matsayin matar shi ba.
Ya ya ma za ai wannan kidahumar yarinyar 'yar sakandire ta maye gurbin Hadiza?
Ta ya ya mahaifan shi suke tunanin zai iya rayuwa da kanwar Hadiza?
Ya yada girman sa ya yi mu'amalar aure da ita?
Kwarai ya fahimci abin da Hadiza ke nufi tsakanin shi da Fati a ranar da Allah zai dauki ranta, amma (he is sorry to say) ba zai iya cikawa Hadiza burinta ba.
In don 'ya'yan shi ne a ba shi abinsa ya rike ko ya bai wa Inna, karatun nasu a birnin Kano ba dole bane, ba sai an makala mishi auren da bai san ya ya zai yi da shi ba.
Malam Ja'afar ya ce,
"Duk kun yi shiru, ko da yake shirun alamar amincewa ne, To ku tashi ku je Allah ya yi muku albarka, dama mun sanar daku ne kada sai gobe ku ji an daura aure ku ce ba a sanar daku ba.
In kuma akwai mai magana to ya yi, a shirye muke da mu bai wa kowannen ku hakkin sa".
Inna tana murmushi ta dubi Sulaiman ta ce,
"Ni na san mai sunan Malam ba zai ki abin da muke so ba".
Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya nemi duk wata hujja da zai bayar ya neme ta ya rasa.
Zuwa lokacin Fati ta mike za ta fita, juwa na kwasar ta, da dafa bango ta samu ta bar falon.
Ta yi dakinta ta dauki 'yar jaririyar ta wadda ke ta tsala kuka a dalilin ta manta ba ta sa mata gidan sauro ba ta fita, sauro ya hana mata barci.
Shi ma bai yi magana ba yana jin su suna ta kida suna rawar su na addu'o'i, sa albarka da fatan alheri a gare shi.
Gwiwa a salube ya fito jikin mota ya baro su suna ta sallama.
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Yaya ta yi murmushi irin na manya wadanda suka san cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, sarai ta gane abin da Fati ke nufi; Hadiza 'yar gayu ce, kuma wadda ta gogu cikin zuzzurfan ilimin boko, ita kuwa 'yar Islamiyyah ce, wadda Allah da Annabi sune kawai a gabanta, wato dai ita 'yar Arabiyyah ce wadda ta horu ta goge cikin ilmummukan addini daban-daban da fadin Allah da manzonsa.
Wadanda 'yan bokon irin su Sulaiman ke wa kallon 'yan kauye, wannan banbancin a farrake yake.
Ta ce,
"Fati kowacce mace da kika gani da kissarta aka haife ta, sannan kowacce da yadda Allah ya halicce ta.
Sai dai ra'ayi da akida sun banbanta.
Amma fa duk sunan su daya (MACE), kuma abin da ke jikin wannan shi ne a jikin waccan, ba wadda ta fi wata a matantakar sai dai ko kazama da mai tsafta.
Fati ke mai tsafta ce, har a makaranta tun daga firamare har sakandire an fahimci tsaftar ki an kuma sha baki kyauta a kanta.
Wannan kadai kika rike jigo ne a gidan aure, kuma ya ishe ki ki yaki zuciyar kowanne da namiji ba Sulaiman kadai ba.
Kamar yadda kika ce baki da abin da za ki burge Sulaiman sai in ce a'a, Fati kina da shi, HANKALI da sanin CIWON KAI sune manyan halayen da ke burge namijin da ya san ciwon kansa irin Sulaiman ba kyale-kyalen mace ba.........".
Fati ta dago ido tana kallon mahaifiyar ta,
"Yaya kina nufin Baban Munib bai fi karfina ba?"
Yaya ta yi murmushi a karo na uku, ta ce, "A doke kam idan za ku gabza ai ya fi karfin ki, amma a zaman aure bai fi karfin ki ba.
Tunda kema mace ce kamar Hadiza, kuma a hakan da kike ba sai kin yi wata kwarkwasa ko kwalisa Sulaiman zai so ki ba.
A'a, maintain your own qualities (rike taki sigar) kada ki aro wadda ba taki ba don ki burge.
Kwalisa, kwarkwasa da yanga ba sa burge namijin da ya san ciwon kansa, sai hankali, nutsuwa, kamewa, ilimi da sanin ciwon kai.
Wadanda dasu ne Hadiza ta samo zuciyar Sulaiman ba appearance (kamantuwar ta ba).
Saboda haka Fati ki kwantar da hankalin ki, ki yi biyayya ga mahaifin ki, Alqur
anin ki, ba zai bari ki tozarta a rayuwa ba
..!!".
Ta mike ta na murmushi cike da jin dadin kalaman mahaifiyarta, ko ba komi ta bata kwarin gwiwa cewa, itama mace ce kamar sauran mata ba mata ta rako duniya ba kamar yadda Sulaiman ke cewa.
Ta cire mata inferiority complex din da ya bi ya addabe ta, har ta ji za ita iya jure duk wani hali da za ta tsinci kanta ko da a ce hasashen Yaya ba su zamo gaskiya a kan nata al'amarin rayuwar ba.
Da kanta Yaya ta zaunar da ita a gabanta, ta sa kibiya ta tsefe mata gashin kanta da ya yi masifar dauda ya duddunkule saboda rashin gyara har tsayin kwanaki arba'in da biyar.
Fati sai yawan gashi amma babu tsayi irin na asalin Kanawa, sannan ga shi da karfi kamar reza, sabida ba ta taba shafa mishi relaxer ba, da za ta shafa mishi din da ya mike ya zama mai ban sha'awa.
Fa'iza ta yi sallama ta shigo tana cewa, "Wai da gaske ne abin da nake ji?"
Ta tsuguna ta gaida Yaya ta amsa.
Fati na hararar ta ta sake cewa,
"Don Allah Yaya da gaske ne?
Yau an daurawa Fati aure?"
Yaya ta yi murmushi ta ce,
"Eh, haka Allah ya nufa".
Ta ce,
"To, Allah ya sanya alheri".
Yaya ta ce, "Amin".
Fa'izah kawar Fati ce, tare suka yi makarantar kwana a G.G.C Kano, kuma gidansu nan cikin layinsu yake babu nisa zuwa gidan su Fati.
Yaya ta ce dama yanzu zan tura Abdulyassar ya kirawo ki, ki zo ki raka ta wajen wankin kai, na san in na bar ta a haka za ta tafi gidan mijin.
Daga nan ku biya ayi mata kunshi".
Fa'iza ta ce, "Gaskiya kam, kawo in karasa mata tsifar".
A daren sai ga kannen Dr.
Sulaiman da wata kanwar Inna sun kawo akwatuna hudu shake da kaya, ga shi ba su gayawa Yaya za su kawo ba balle ta tara masu karba.