Sashe 19
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alti ta ce,
Ya salam!
Kin gani kin yanke, na yi na yi ki daina amfani da wannan wukar kin ki, ta fiye kaifi da yawa, sannan gaki da saurin gigicewa
Ya ji hankalinsa ya tashi ganin yadda jini ke gudu amma ba ta dago ba.
Ta dukar da kai ko motsi ta ki yi.
Ya basar Ya ce,
Babu sauran ruwan roba ne Baba Alti?
Firjina babu komai, sannan ina jin kishi
Ta mike zuwa store ta dauko mishi katon na FARO ta dawo, ta kama hannun Fati ta ce,
Babu kananzir balle in sanya miki, bari a daure da tsumma
Ta tsaga zanin ta tana kokarin daure mata.
Ya kalle ta a kaikaice ta kasan ido ya fita, zuciyar shi babu dadi, don ya tuno yadda ta nuna damuwa ranar da ya yanke nashi hannun.
Mamaki ya kama Alti, ashe Baban Munib ba shi da kirki?
Matarka ta yi irin wannan yanka amma ko kallo ba ta ishe ka ba?
Tana daure mata Fati ta fara kuka yankar ta fi karfin daurewa da tsumma.
Alti ta biyo shi, ba ya falon yana dakin sa.
Ta tura Munib wanda ke ta wasan game cikin computer ta ce ya kirawo Baban shi.
Jim kadan suka fito tare shi da Munib, yana rike da gorar ruwan yana sha.
Cikin takaici ta ce,
Zan kai Fati asibiti ne
Ya sunkuyar da kai duk jikin shi ya yi sanyi, ganin bacin rai kwance a fuskar tsohuwar da bai taba ganin bacin ran ta ba tsayin shekaru shida da suka yi tare da ita, ya dukar da kai sosai ya ce,
Bari in diba ciwon nata
Ya koma daki ya dauko first aid box ya same su a kitchen din, jinin na ta zuba har yanzu.
Sanye yake da brown getzner ta sha dinkin Mohammed wanda shi ne dinkin sa kawai, ya russuna dai-dai inda take sunkuye, ya kama hannun ta.
Wani sanyi ya tsirga a zuciyar ta.
Dago idon nan da za ta yi sai idanun su cikin na juna, wadannan kwayan idon na Sulaiman suka birkita ta, kamar yadda suke birkita zuciyar duk wata lafiyayyar macen da ta san cewa akwai tsokar zuciya a tare da ita.
Amma ga shi Sulaiman, gani yai ta rikide mishi ta koma Dr.
Hadizah
Wannan yankar sai an yi dinki
.
Ya fadawa Alti.
Cikin sanyin murya ta ce,
Ai shi ya sa na ce muje asibitin
Ya ce,
Ba damuwa bari in dinke mata
Ya fara da yi mata allurar
anaesthesia
, sannan ya fara dinkewa.
Idanunta a rufe ba ta bude ba har ya gama.
Bayan ya gama ci gaba ya yi da rike hannun bai saki ba, ita kuma ba ta sani ba cewa ya gama ko bai gama ba.
Alti ta yi saurin fita ta bar kitchen din.
Ya soma samun wani sassanyan sauyi a tare da shi, ya dinga hango rashin kyautatawar sa na tsanar jinin Hadiza da ba ta tsare mishi komai a rayuwa ba.
Auren su da aka yi ya tabbata ita ma ba da son ranta a kai ba, soyayyar Hadiza da ta yi mishi yawa, ita tasa yake kin kowacce mace.
Ita kuwa Fati ba zai ce ga dalili ba.
Ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai, ina ruwan shi da tsarin rayuwar ta?
Tunda ba a goshi zai lika ta ba?
Ya soma kokarin goge muguwar kiyayyar da yake yi mata ta hanyar baiwa zuciyar shi uzuri iri daban-daban ga duk muguwar hujjar da ta kawo.
Sai dai muhimmin abin da iyayensu suka hada wato AURE da mu
amalan auratayya, baya jin zai taba iya yin shi da wadda ta zamo kanwa ga Hadiza.
Duk da ba haramun bane shi kam ya haramtawa kansa, an halicce shi kadai don Hadiza, kuma har ya koma inda Hadiza take ba zai kara mallakawa wata diya mace soyayyar shi ba, babu gurbin da zai iya jogana son wata.
Sai dai shi kansa yana mai kalubalantar tunanin sa na cewa zai iya dauwama a haka ba tare da mace ba, kasancewar ta wani bangare na rayuwar dan adam, da kuma ganin tun ba a je ko ina ba ya fara kwana cikin halin ha
i.
Dole ya dau matakin da zai kawo karshen duk wannan, wato ya yi nisa da Fati, tun YAKANAR ta, kyautatawar ta, hakurin ta da juriyar ta basu ciwo galabar tattaurar zuciyar sa ba.
Jin ya yi shiru ba ya dinkin kuma bai saki hannun ta ba, Fati tayi saurin bude idon ta, suka yi ido hudu da Sulaiman dan Sulaiman da Inna Halima.
Ashe haka Baban Munib yake da kyau?
Ban taba sani ba?
Fati ta ce a zuciyarta.
Ina ma a ce yanda yake da kyan nan haka zuciyar shi take da kyau?
.
Zuciyar ta kara tambayarta.
Ta samu kanta cikin wani sabon yanayi da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
A wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar kowannen su, daga Fati har Sulaiman babu wanda ya runtsa, soyayyar junan su ke neman samun muhalli a zuciyar kowannen su.
Amma sun sa kafa suna fatali da ita da gan-gan, don a ganin kowannen su bai dace ba.
Sannan ita Fati ta riga ta yiwa Dr.
Sulaiman mummunar fassara zuwa na makiyinta, mai nuna mata kiyayya karara, kiyayyar da babu wani mahaluki da ya taba nuna mata a rayuwar ta.
Don haka a kan me za ta so shi in ban da sharrin zuciya, don haka take ta ciccijewa, ita lallai karya zuciyar ta take yi ba son shi take yi ba.
Shi kuma a can nashi bangaren, Sulaiman, ya kasa sukuni, ya kasa runtsawa ne a dalilin abubuwa da dama na yarinyar a yau da suka fizge shi.
Ga dai kamannin Hadiza, sannan ga wasu (extraordinary qualities) da ya lura dasu a dan zaman watannin da ya yi tare da yarinyar.
Don haka ya kwana cikin yiwa kai da zuciya hisabi, don tantance al
amarin da ke shirin faruwa da shi a kan Fatima Ja
afar Mai-Yadi.
Sakamakon ba mai saukin fadi bane a gare shi, halayen ta da yakanar ta da juriyar ta wajen yin abubuwan ta don Allah ba don ya yabe ta ko ta burge shi ba, sun taimaka kwarai wajen sayo mata soyayyar dole, wanda ke nufin Fati ta yi nasara kenan a kansa?
Shi kuma ya fadi game din da suke bugawa. (He is the loser, and she is the winner!
Idan ya yi sake hakan ya bayyana gare ta shikenan za ta raina shi, GIRMA YA FADI!
Ya manta cewa a magana ta aure babu raini tsakanin mace da mijinta.
To amma ina zai kai jin kan?
Na tunanin kankanuwar yarinyar da yake rainawa ta yi winning a kansa?
Don haka tunanin sa na ya yi nisa da Fati, don gudun RAINI ya kara kamari a tare da shi.
A kwanakin da suka biyo baya, duk hanyar da ya san za ta hada shi da Fati a gidan yana kauce mata.
Ita ma Fatin hakan, tun daga ranar da ta yanke hannu, ga shi har ciwo ya kame.
****
Basu Kano ba su Abuja shi da wasu daga cikin likitoci
yan uwansa, suna fafutukar
visa
zuwa jami
ar Chicago domin halartar wani kwas na shekaru biyu a kan dashen zuciya (heart transplantation) da
federal government
ta tura su.
Ko Inna ba ta sani ba, sai da ya gama dukkan shirye-shiryen sa, shi lallai dole yana yaki ne da zama da Fati kada soyayyarta ta rinjaye shi, shi ya sanya ya sanya kanshi cikin
yan tafiyar, don da babu yadda shugaban su bai yi ba ya shiga cikin tawagar amma ya ce a
a, duk da matukar bukatar shi da kwas din da asibitin ke yi, don haka da ya zo da kansa ya ce zai tafi, ba karamin jin dadi shugaban su ya yi ba.
Suka fara shirye-shirye, har zuwa yau da Allah ya nufa suka kammala, sai tafiya kwanaki uku masu zuwa.
Ya cimma su ita da Alti a kicin don su nan ne ofishin su, suna ta suyar dambun nama.
Ya hada giran nan sama da kasa lokacin da idanuwansa su kai arba da na Fati, ita ma ta hade tai murtuk kamar ta ga mala
ikan daukar ranta, wannan gigicewar da take yi in ta gan shi yau ba ta yi ba, s
akamakon jimawa da ta yi ba ta sanya shi a idon ta ba.
A can wani gefe daga karkashin zuciyar ta, wani sanyi ne ya sauka a zuciyar ta wanda ba ta san dalilin shi ba.
Hakika ta azabtu da rashin ganinsa a dan tsakanin, saboda yadda ganin sa ya zame mata SANYIN IDANIYA, yake gusar da duk wani bacin ranta, yake rage mata zugin rashin
yar uwarta da ke cin zuciyar ta, duk da rashin alherinsa gare ta kuwa.
Babu ko tantama ta fada a
soyayya,
a inda take da yakinin cewa ba za a taba son ta ba, in haka ne zuciyar ta ta gingimo mata babban aikin da ba ta san ya za ta yi da shi ba.
Yana duban sashin da Fati take kasa-kasa ya gaida Alti, sannan ya dauke kanshi a sashin Fatin, ganin yadda ta yi murtuk da fuska.
Ya yi murmushi ya ce da Alti,
Ku yi shiri zan je in watsa ruwa mu wuce Bakori yanzun nan
Alti ta ce,
Allah ya sa lafiya?
Ya yi murmushi ya ce,
Lafiya kalau Goggo Alti, yara sun kwana biyu basu ga Inna ba, suna ta tambaya ta
Ta ce,
To bari mu yi sauri mu karasa
Taso ta ce da shi,
Har da Fati?
Ta ga wannan ba abin da ya shafe ta bane sun fi kusa, wai harshe da hakori.
Ita ma Fatin da ba a ce da ita ba kawai sai ta hau shiri, domin tana son ganin Inna ainun.
Ta zuba Abaya kirar Kuwait, ta kawo katon hijabin ta har gwiwa ta zuba.
Bayan ta shirya yaran dukkanin su, ta fi son ta goya Nana, maimakon ta yi ta rike ta a hannu ko a kafada.
Har Sulaiman kan yi mamaki ya ce a ransa, ita wannan ba ta gajiya da goyo ne?
Duk sanda zai ganta goye da Nana zai ganta.