Sashe 14
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kama baki ta ce, "Yanzu Allah sai da aka takura Sulaiman da yin lefen nan yana fama da halin da yake ciki?"
Ruma ta ce,
"Ai babu komi, abune da idan ba mu yi ba, ba zamu ji dadi ba".
Yaya ta ce,
"To Allah ya amfana, ya sa an yi a sa'a, ya kuma tabbatar da alherin da aka kulla, amin".
Fati kwana ta yi sallah, in 'yar ta yi kuka sai ta dakata ta kula da ita har ta koma barci, sannan ta ci gaba, Cikin sujjadarta tana mai rokon Allah koma mene ne zai zo cikin rayuwar ta ya zo mata da sauki.
Washegari ko tsakar gida ba ta leko ba, don gidan ya cika da 'yan uwan Yaya da dangin Malam, saboda kowa da Hadiza a zuciyar sa babu wanda yake yin hayaniya.
Karfe uku na rana Fa'iza ta kawo mata kayan da za ta sanya, wani leshi mai taushi ruwan zuma da kananun stones da ta kai Diallo (Zoo Road) aka yi mata dinki express, amma ya yi kyau sosai, ya amshi dan karamin jikinta.
Fati siririya ce, kuma ba ta kai tsayin Hadiza ba, komi na halittar ta (natural) kamar fata, gashi da hakora yiri-yiri, kuma farare kal wadanda ba ta wasa da kuskure su da listerine (mouth wash) a duk lokacin da ta goge su.
Shiyasa suke farare tas, kamar kankara
A can gidan Sulaiman shi ma cike yake da nashi 'yan uwan, suna ta gyare-gyare, suka gyara gidan tsaf, dama tuni an kwashe kayan Hadiza har gadaje da (wardrove) an balle an fitar dasu an kai gidansu.
Malam Ja'afar ya ba da daki guda aka kulle su, Inna tasa aka sayo katuwar katifa aka aje a dakin da a yanzu ya zama mallakin Fati kamin a yi mata jere.
Kai!
Rayuwa!!
Ran dan adam ba a bakin komai ba, kowa ganin al'amarin yake kamar almara, masu yiwa Hadiza addu'a na yi, masu kokawa na yi, masu korafin anyi gaggawar yiwa Sulaiman wani aure na yi.
Amma a bayan idon Inna, don kowa ya san irin son da Sulaiman yake yiwa Hadiza.
Shi kam bai ma gidan yana asibiti tun safe, ya kama wayoyin shi ya kulle kada Inna ta neme shi.
Don a daren jiya ta shaida mishi wai shi zai je da kanshi Karkasara ya dauko Fati da yara, shi kuma ya kudire in har shi zai yi hakan, to wallahi sai dai idan ba za ta zo gidan ba.
Zuwa karfe hudu ran Inna ya soma baci da rashin samun Sulaiman a waya, sai dai ta yi mishi uzri.
Ta sani sarai sun takura shi, wanda su sun tabbatar abin alheri suka yi, sun gyara zumuncin su da iyayen Hadiza, sun kawo wadda za ta rike 'yan jikokin su da gaskiya, sannan sun aura mishi mai kama da Hadiza, kuma shakikiyarta.
Akwai gatan da za su yi mishi da ya wuce wannan?
Ta kudurce a ranta za ta tsayawa Fati da addu'a da yakin zuciyar Sulaiman har sai ya so ta kamar yadda yake son 'yar uwarta.
Don haka sai Inna Talatuwa kanwar Malam da su Ramatu ne suka taho dauko amaryar a motar mijin Ruma, don motar shi da ita ya fita, ta Hadiza tuni an sayar sai ta amfanin gida rufe cikin tampol.
Cikin girma da mutuntawa aka basu amarya.
Yaya ta ce a bar mata yaran bayan sati daya za a kawo su.
Ruma ta ce,
"Yaya baki yiwa Fati nasiha ba".
Ta yi murmushi ta ce,
"Duk nasihar da zan yi mata na yi mata jiya, Allah ya sa ta je a sa'a".
A dakin Malam Ja'afar kowa ya fita ya bar su, ganin irin kukan da Fati ke yi kamar ana zare mata rai sai zuciyar shi ta motsa.
Ya ce,.
"Fadimatul-Zahra'u, ki daina kuka, ban aurar da ke ba sai a hannu na gari, hannun dana san cewa ba zan taba yin dana sani ba".
Har aka iso gidan, wanda ba bakonta ba ne tana tauna maganar Babanta, me ya sa Yaya da Baba suke son Dr.
Sulaiman har haka?
Me ya sa kowa ya budi baki kyakkyawan kalami yake yi a kanshi?
Me ya sa ita ba ta ganin kirkin nashi da nagartar tashi?
Kenan ita kadai yake yiwa rashin kirki, to laifin me ta yi masa?
Babu wanda zai ba ta amsar sai Sulaiman din kansa, wanda ta tabbatar har abada ba za ta ji amsar ba in har sai shi din ne zai amsa mata.
Inna ta tarbe su ta rungume ta, ta kama hannun ta har dakin da a yanzu ya zan mallakin ta, ta aje ta a bakin katifa.
Fa'iza da Karima kawayenta na gefen ta, wannan ya shigo wannan ya fita, amma ita tunanin ta ya tafi ga Baby Nanah wadda ta baro a wajen Yaya, ta shaku da yarinyar sosai ta yadda har take mantawa cewa ba ita ta haife ta ba, ta alkawartawa ranta za ta roki Inna ta karbo mata ita gobe ba za ta iya yin kwanaki bakwai ba tare da ita ba.
Zuwa karfe goma na dare gidan ya yi shiru, masu tafiya sun tafi, masu gajiya sun kwanta barci.
Su Fa'izah duk sun tafi, Inna ta shigo dakin rike da kulolin abinci guda biyu, ta ce,
"Kin yi barci ne Fati?'
Ta mike zaune rike da carbi a hannun ta, ta ce, "A'ah".
"To tashi ga abinci ki ci, tun dazu na so in kawo miki na san ba za ki iya ci cikin mutane ba".
Ta mike zaune ta karba, jellop din cous-cous ne wanda ya ji kayan lambu a filas din farko, sai farfesun kayan ciki da ya ji kayan kamshin gargajiya a daya filas din.
Inna da kanta ta zuba mata ta soma ci.
Inna na kallon ta cikin tausayi, ganin yadda take cin abincin hannu baka hannu kwarya.
Allah kadai ya san tun yaushe rabon ta da abinci, mai yiwuwa tunda aka yi mata zancen aure da mijin Yayarta.
Ta gama ci ta kora da gwangwanin fanta, ta koma ta kishingida Inna ta yi mata sai da safe ta kwashe kulolin da plate din da gwangwanin fantar ta fita.
Karfe daya na dare Dr.
Sulaiman ya shigo gidan, ya tabbatar zuwa yanzu dai kowa ya kwanta balle a dame shi.
Yana shiga dakinsa ya danno kofa ya murza key, hoton Hadiza cikin dan kankanin
frame
da ke kan
side drower
na gefen gadon shi ya yi mishi sallama, tana murmushin ta ni'imtacce cikin farar shirt din calvin-klien wato C.K.
Ya zare falmaran din suit din shi ya zare tie ya fada a kan gadon, ba tareda ya cire takalmi da safar kafarshi ba, ya fizgo hoton ya rungume a kirjin shi, ya yi magana cikin muryar kuka,
"Why do you leave me Hadizahh
.???
Mai ya sa kika boye min cewa kina da brain cancer?
Likitancin ki bai gaya miki cewa babu ciwon da ba shi da magani ba?
Hatta kanjamau ana nan ana kokarin nemo maganin ta.
Mai ya sa baki jira ni mun tafi tare ba?
You left me incomplete, shattered
Ya mirgina ya kara rungume hoton ya feso wani irin huci mai zafi.
Da gaske Allah ba ya barin wani don wani, na tabbata da ba zai dauke ki ya barni ba.
Ya za ai a ce na zama mijin kanwar ki?
Wannan cin fuska da cin amanar soyayya har ina?
Ba za a yi ta dani ba!
I am for Hadizah only
.!!
Zan jira wa'adina Hadiza in iske ki acan mu ci gaba da rayuwar mu a inda babu mutuwa
. balle ta sake raba mu
Ya lumshe ido, hawaye suka mirgino, ya budesu a hankali ya kai
frame
din ga siraran lebban sa, ya yi masa sumba mai tsayi da zurfi, kafin ya yi masa murmushi ya ce,
"I love you HADIZAH
.Cikin kowanne hali INA SONKI HADDIZAHH!!!"
****
Masoyan Hadizar na da yawa, domin ita ma a can, Fadima, a dai-dai wannan lokacin, goshinta na gaban mahalicci, cewa take.
"Ya Allah!
Ka yi rahma ga baiwar ka Hadiza, ka yalwata kabarinta da haske da kamshi, ka yaye mata duhun kabari, ka shayar da ita ruwan Alkhausara, ka bani juriyar cika alkawarin ta duk da na san ba abu ne mai sauki ba
Kafin gari ya yi haske tuni Dr.
Sulaiman ya fice, sai karar motar shi Inna da ke lazimi ta jiyo.
Ranta ya baci sosai, ta dauki waya ta yi kiran sa, anyi sa'a wayar na bude ba shi kuma da hujjar kin amsa kiran Inna.
Yana amsawa ta ce,
"Dabbobin da ke cikin gidanka za su koma makyankyasar su, sai in ce Allah ya hada mu da alheri".
Kafin ya yi magana ta kashe.
Ya juya wayar a hannun sa, "Dabbobi?
Dabbobi?
Su waye dabbobin?
Eh, dole ta kira kanta dabba a gidansa, tunda har za ka iya fita tana cikin gidan ba ka gaishe ta ba".
Jikinsa ya yi sanyi, a hankali ya yi round ya juyo.
Lokacin da ya iso gidan har sun faka kayan su suna sawa a motar Jibril mijin Ruma, tana kokarin fitowa yana kokarin shigowa suka yi karo, karaf, ya yi saurin ja da baya.
Ya ce, "Inna ki yi hakuri in je in yi signing yanzu sai in dawo in kai ku".
Ta harare shi ta ce,
"Ai ba kai kadai ke da mota ba, tunda ka iya ka kwana cikin gidan ka wayi gari ka fice ba tare da ka binciki halin da muke ciki ba ai dabbobi ka dauke mu.
Ni matsa ka bani hanya bana son motar taka".
Ya soma magiya,
"Ki yi hakuri Inna, mu koma ciki mu yi magana, wallahi dama ban yi niyyar dadewa ba zan je ne in dawo kuma ban san yau za ku koma ba".
Ta balla masa harara sai kuma ya ba ta tausayi.
Wanda ya san Dr.
Sulaiman a baya, ya kuma ganshi a yanzu, zai yi wuya ya shaida shi in ba ya yi masa farin sani ba.
Duk da ya aske kasumbar da ta cika mishi fuska, hakan bai voye muguwar ramar da ya yi ba.
Ita kanta muryar shi ta canza ta zama mara amo, kamar ta mai fama da mura.
Dara-daran idanunsa sun zurma ciki.