Sashe 11
Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce, "To Allah ya sauwake, ke kuma Allah ya ba ki ladan hidimar da kike yi da 'ya'yan ki, ya sa suji kan ki kamar yadda kika ji kan su, ya kai rahama kabarin mahaifiyar su".
Ta ce,
"Amin Baba".
Shi ma Sulaiman da ke can daki yana jin su ya ce "Amin".
A zuciyar shi.
Malam ya daga labulen ya ce, "A'a!
Ashe Inna ce, barka da zuwa kin sha hanya, ya ya aka baro Malam?"
Ta amsa, suka ci gaba da gaisawa suna hirar 'yan jikokin su, tare da kara yiwa juna ta'aziyya.
Malam Ja'afar ya dubi Sulaiman sosai ya ce,
"Ina maganar aiki ta kwana?"
Ya yi shiru kanshi a sunkuye, can kuma ya ce,
"Zan koma gobe insha Allahu".
Malam ya ji dadi, ya kara mishi da nasiha mai sanyaya zuciya.
Ba su baro gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan Inna da Yaya sun yanke shawarar yaran za su ci gaba da zama a nan saboda ya fi kusa da makarantar su.
Har za su tafi ya dubi Yaya fuska ba walwala ya ce,
"Duk abin da ake bukata Yaya, don Allah a gaya min".
Yaya ta yi murmushi ta ce, "Me ake bukata ban da madara?
Bayan ita babu abin da zai gagara da izinin Allah".
Ya ce,
"Duk da haka ina son sanin sauran abubuwan da ake bukata, ai ragi-ragi ne".
Ta ce,
"To ka tambayi Fati".
Ba don ranshi ya so ba ya nufi kofar dakin nata.
Ta goya Nanah tana jijjiga ta, wannan karon babu hijabin a jikinta, kwayar idanun su ta hadu, ya yi saurin dauke kansa don gani ya yi kamar Hadiza, hatta digon tauwadar Allah da ke kan tsinin hancin Hadiza akwai shi a tsinin hancin Fati.
Zuciyar shi ta yi wani irin mummunan bugu, don gani ya yi tana rikide mishi Hadiza sak, kasancewar bai taba ganin ta babu hijabi ba.
Ya tsaya daga bakin kofar hannun shi duka biyu zube cikin aljihu.
Da kyar yake magana kamar an tilasta mishi, ba tare da ya kara kallon ta ba.
"Na tambayi Yaya abubuwan da yara suke bukata, ta ce in tambaye ki?"
Kanta a kasa ta ce,
"Sai ko pampers da madara".
Ya ce,
"Bayan su ba wani abu?"
Ta ce, "Eh, amma malamar su ta ce akwai prize giving day ranar asabar kuma ana son iyayen yara su je".
Sannan ta dauko report card na yaran na wannan zangon ta mika masa.
Garin karba hannayen su suka gogi juna, sannan suka kara hada ido a lokaci daya babu wanda bai ji a jikin sa ba.
Ita tsoro ta ji, shi kuma ji ya yi kamar hannun Hadiza.
Bai ce komi ba ya karba ya sanya a aljihun shi ba tare da ya duba ba, bai kuma ba ta amsar zai je ko ba zai je ba ya fita.
Ya tadda Inna har ta fito suka tafi, ya bar Fati cikin tunani.
Ta zauna a gefen gadon ta, ta sauko Nanah wadda ta samu barci ta rungume cikin hannayen ta, tana tunanin me Hadiza ke nufi da ta ce ta kula da Baban Munib???
..Munib kulawar Uwa yake nema, Sulaiman kulawar MATA yake nema
Ta tuno kalaman Hadiza.
To ai ita ba matar shi ba ce, ba gidansu daya ba, ta ina za ta kula da shin kada rashin Hadiza ya tagayyara shi?
Wannan baudadden mijin nata dake yi mata kiyayya maras dalili?
In har Hadiza na nufin ta auri mijinta ne wanda ba ta fito baro-baro ta fada ba, sai hannunka mai sanda da ta yi mata, ta hada ta da wani al'amari da ba zai taba yiwuwa ba.
Ba ta fata, kuma kada Allah ya tabbatar ta yi tarayya da Hadiza a kan abin da take so, ta tafi ta bari ba don ba ta so ba, sai don hukuncin Allah wanda ya fi karfin dan adam ya yi jayayya da shi.
Hakika ta dauki alkawarin da ba ta san yadda za ta yi ta sauke shi ba.
****
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: ****
Inna ba ta koma Bakori ba sai bayan watanni biyu, lokacin laulayin Hadiza ya ragu, tana yi mata dabaru irin na manya har ta samu sauki.
A lokacin cikin ya shiga wata hudu, sannan ne laulayin ya tsaya.
Sannan ciwon kanta ya jima bai tashi ba, saboda Dr.
Bunza ya sauya mata magani, Fati ce ke zuwa ta karbo ba tare da sanin Sulaiman ba.
Ganin ciwon ya dade bai tashi ba sai Hadiza ta watsar da shawarar Fati ba ta gayawa Yaya ba, shi dama Sulaiman tuni ta binne shi ya kuma yarda cewa migraine take.
Cikin Hadiza wata bakwai, ya fito ya yi tororo kamar watanni tara.
Haka za ka ganta fus!
A cikin wheel chair tasa cikin a gaba tana kallo tana mamakin sarautar Allah, wanda ya ga damar ta haihu a cikin halin da take ciki.
So da kulawa wurin Sulaiman kamar ya yi mata nakuda.
Watan Aprilu ya kama, wanda ya yi dai-dai da EDD din ta, cikin dare wani azababben ciwon kai ya tashe ta, ta soma bubbuga kanta a jikin gado, kafin a yi haka ta yi dogo suma jini ya kece kamar da bakin kwarya.
Duk wani kokari da zai iya shi ne kiran Dr.
Abdullahi ko Dr.
Surayyah a waya, amma hannun shi ya kasa kama wayar saboda dimaucewa.
Sannan shi ya manta kansa balle ya yi tunanin wane irin taimako zai iya ba ta komai kankantarsa, a matsayin shi na cardiologist wanda kuma ke da general knowledge a kan komai.
Sai ya sunkuto ta ya nufo harabar gidan, ya shimfidar a bayan mota.
Malam Ilu ya wangale mishi
gate
ya fita, cikin ranshi yana cewa kai wannan yarinya kina cikin jarrabawa kala-kala, Allah ya baki lafiya.
Da taimakon innalillahi........ da yake ta ambato ya samu nutsuwar da har ya iso AKTH, aka karbe ta a bangaren ta wato dakin haihuwa, su Dr.
Surayyah, Dr.
Abdullahi suka rufu a kanta, ba ta san inda kanta yake ba.
Suka soma ba ta duk wani taimako da ya dace don ta haihu da kanta kamin su yi bincike a kan wata matsala daban da suka hango wadda da alama dadaddiya ce.
Amma duk iya kokarin su sun tabbatar da ba za ta iya haihuwa da kanta ba, don haka suka miko mishi takardu don ya sanya hannu a shiga da ita tiyata.
Da kyar yake iya sarrafa 'yan yatsun shi a lokacin da yake rattaba hannun, zuciyar shi ta riga ta bushe da tashin hankali.
Yana tsaye aka turo ta a kan gadon daukar marassa lafiya zuwa dakin tiyata, bai yi tunanin gayawa kowa ba sai da safe, kasancewar ba shi da nutsuwar yin hakan.
Da ya ga wannan ba za ta yi mishi ba, sai ya nufi ofishinsa ya murda kofar ya shiga, ya jingina da kofar ya soma tunanin wasu al'amura da ya lura Hadiza na boye mishi, da yawan waya da take yi da Dr.
Bunza na mene ne?
Sannan da kwayoyin maganin da ya gani a leda babu suna babu takardar su a karkashin gadon su.
Ya yi wani irin huci mai zafi,
"Akwai wata matsala wadda da alama dadaddiya ce".
Ya tuno furucin Dr.
Abdullahi.
A sukwane ya bude kofar ya fita ya nufi ofishin Dr.
Bunza a Neurolgy.
Dr.
Bunza na rubuce-rdubuce a file suna hira da Dr.
Karaye, Dr.
Sulaiman ya bankada kofar ofishin ba tare da ya yi sallama ko neman izinin shigowa ba, ya kai wa Dr.
Bunza shaka ya ce,
"Gara in kashe ka, kafin ka kashe ni
Dr.
Karaye ya soma kokarin kwatar Dr.
Bunza wanda ya sha shaka matuka, duk idanun sun yo waje.
Ya ce,
"Ba zan cika shi ba, sai ya gaya min abin da ke damun matata, da magungunan mene ne yake dirka mata?"
Dr.
Bunza ya ce,
"Ka yi hakuri Dr.
Sulaiman mu yi maganar cikin nutsuwa".
Ya samu ya sake shi da kyar ya koma kujerar sa yana gyara wuyan rigarshi, yayin da Sulaiman ya yi mishi kerere a kai, idanun shi a jujjuye, shi dai kawai so yake ya ji mene ne matsalar Hadiza?
Dr.
Karaye ya ce,
"Ka yi hakuri ka zauna Dr.
Bakori, Dr.
Bashir ba zai cuce ka ba
Ya juyar da juyayyun idanunsa a kan Karaye,
"Akwai wata cuta wadda ta wuce wadda ya yi min?
Matata na dauke da cuta shekara guda amma bai taba gaya min ba?
Ya biye mata suke yi min rainin hankali, na yi kama da wanda bai je makaranta bane Dr.
Karaye?"
Dr.
Bunza ya ce,
"Ba haka bane Dr.
Bakori, ina bisa aikina ne, akwai sirri tsakanin likita da petient din sa, wannan shi ne hujja ta.
Sannan Dr.
Hadiza na da tata hujjar, ta boye maka cewa tana da (brain cancer) don samar maka da kwanciyar hankali, ta ce idan ka ji babu kai babu sauran kwanciyar hankali, kuma nima na yarda you are not taking things easy (ba ka daukan abubuwa da sauki).
Ka bini a hankali in maka bayani".
Ya kunna computer inda (record) din Hadiza yake yana nuna masa yadda ciwon ya ci karfin ta a yanzu, da irin taimakon da ya ba ta.
Shi kan sa Bunza sai da ya yi hawaye balle gogan, wanda gudun jini ya katse a jijiyoyin jikinsa.
****
Karfe shida na safe Dr.
Surayyah ta fito da jaririyar da aka cirowa Hadiza, kamar ta daya da Baban ta kamar ya yi kaki ya tofar, har duhun kalar nashi ne.
A lokacin ne jama'ar gidan su Hadiza suka iso, Dr.
Surayyah ta sanar da su.
Fati karfe bakwai na safe ta iso asibitin, ta baro yaran da Alti ta zo a (keke-napep).
Dai-dai lokacin da aka turo Hadiza za a mai da ita ICU, ya yi dai-dai da sanda Surayyah ta mika mishi jaririyar ya ki amsa, sai Fati ce ta amsa.
Za a wuce da Hadiza ta rike hannun sister Magajiya ta rada mata cikin nishi,
"Ina son yin magana da su
..".
Don haka sister ta dakata.
Sulaiman da Fati suka garzayo gareta, kowanne ya fita hayyacinsa.
Fati rungume da jaririya tsantsan tana ta tsala ihu.
Itama Fatin Kukan take.