← Book details Yakana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Yakana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranshi ya ce,
Tunda na rasa Hadiza ai ba abin da ba zan gani ba, ga shi na zama direban Fati ina ji ina gani
Har suka isa gida babu wanda ya ce da dan uwansa uffan, don babu fuska a wurin Fati, fushi take sosai kan biris din da ya yi da ita tsayin shekara guda da doriya.

Sai shi da Munib suke ta hirar su, Alti na mamakin wadannan ma
aurata da ba ta san yaushe za su saduda su san Annabi ya faku ba.

Ba ta san kuma laifin na wane ne a tsakanin su ba.

Suna zuwa gida ta dauko makullin dakin sa ta shiga ta soma gyara, duk da dama a gyare yake, domin duk bayan sati biyu take shiga ta share ta gyara ta wanke toilet.

Shi kuma da ya ajiye su fita ya yi, bai dawo ba sai karfe goma na dare.

Ya yi wanka ya yi excercise ya zuba pajamas da turaren shi na kullum, amma a yau sai ya samu kansa da karawa da
Boss-Intense
, ya cakuda da
far away
.

Sannan ya kara da
Gio-Gio Armani
Ango sosai.

Mai ji da koshin lafiya da kuruciya, wanda Allah yayiwa duk wata ni
ima ta rayuwa.

Ya tadda Fati a dakinta, ita ma lokacin ta yi wanka tana busar da gashin ta da hand dryer, cikin wasu tausasan nighties, masu shara-shara, ya kashe dirayar ya ajiye a gefe, cikin kunnuwan ta yake rada mata.
..Ki yi hakuri mana Fati
..don Allah ba don ni ba
Ta ce,
Da aka yi me fa?

Ya ce,
Rashin kiran ki a waya, ba haka kawai bane ina da hujjoji na
Cikin raunin murya ta ce,
Kana da hujja sosai, hujjar baka damu dani ba, kana kiran kowa ban da ni, ba sai ka yi haka zan san cewa baka so na ba, lika maka ni aka yi.

Tuni na kwana da sanin wannan......

Hawaye suka balle mata.

Ya juyo ta da sauri suka fuskanci juna, sanyin numfashin su na dukan fuskar kowannen su.

Ya ce,
Ni na ce da ke bana son ki?

Baka fada ba amma ka nuna mini, ka nunawa zuciyata.

Tunda har ka iya ka yi shekara baka nemi jin lafiya ta ba, saboda ni kadai ka tsana a duniya, a kan laifin da ban sani ba
Ya yi murmushi sosai ya ce,
Dole sai ta bakin ki zan ji lafiyar ki?

Ina ji a bakunan da ba za su yi min karya ba.

Maganar lika min ke aka yi, sai in ce MADALLAH da wadanda suka lika min ke, yaa ke ma
abociyar YAKANAH!.

Domin na hadu da alhairori da yawa a tare da auren ki.

Ki yi min afuwa Fatima kamar kullum, ban san ki da kullaci ba, saboda ke na jingine komi dake gabana na zo, kada ki sagar min da gwiwa, saboda in gyara zaman mu, in gyara kurakurai na.

Na tabbata Hadiza ta tafi;
She is my past
... and you are my present.....!!!

Haka ya ci gaba da kalallame ta da kalami masu dadi, har ya samu ya karbi abin nan mai matukar daraja daga gare ta.

Ya rungume ta tsantsan yana fadi a ranshi,
Yaya, (Sa
adatu) ta haifi
yan baiwa
Albarka da addu
a, hadi da godiya mara iyaka Fati ta samu daga Dr.

Saiman har ta gode Allah.

A bisa yanayin daya risketa.

Idan aka ce mata wani abu mai kama da MAFARKI to wannan ranar ce.

Ranar da bata taba mafarkin gani cikin mafarkanta ba.

It
s a dream that comes true.

Bata jin akwai wani sauran buri da ya rage mata a rayuwa bayan na cikawa da imani da dorewar wannan
indescribable moment
har karshen rayuwarta.
****
Kwanaki biyar din nan da yayi bai zuwa ko
ina sai barzar amarci, har Fati ta saba, duk da tana matukar cin kwakwa, tana galabaita matuka da wannan sabuwar rayuwa data samu kanta.

To abin ne an tara shi fal, tsawon shekaru biyu ba kadan.

Albarka kam tana shan ta, ya soma tunanin yadda zai iya komawa ya bar Fati, saboda yadda ta zamo wani bangare na gangar jikinsa, zuciyar sa da ruhin sa gabadaya, ga shi suna tsaka da karatu balle ya yi mata visa in ya so yaran a kai su wajen Yaya.

A gobe ne zai tashi zuwa Lagos, daga nan ya bi jirgi mai zuwa Chicago.

Fati tana hada mishi kaya, duk jikinta ya yi sanyi saboda mugun sabon da suka yi cikin kwanaki shidda kacal, sannan ga wata iri kewa na cin zuciyarta mai wuyar bayyanawa.

Ya fito daga wanka yana tsane kanshi da karamin tawul, jin kansa yake wani sabo, fresh, kamar yanzu aka bare shi a leda.

Tunda ya samu ya sauke al
amuran da suka takurawa zuciyar shi da lafiyar shi.

Inda zai iya maida Fati ciki, da watakila ya yi hakan ya sanya ta cikin ya gudu da ita.

Abin alfahari ce ga duk namijin da Allah ya baiwa, ya gode Allah da bai bi son zuciyar shi ya bijirewa iyayen shi ba.

Ya tabbata da tuni yazo yana nadama.

Nadama mara amfani kuwa.

Ta mika mishi wasu kayan barci
yan Indonesia marassa nauyi, ta ci gaba da hada sauran.

Ashe hawaye take zubarwa shi bai sani ba, ya sanya kayan barcin, ya zauna a gabanta ya janye jakar kayan da ta ke hadawa, ya kamo dukkan hannuwanta biyu ya rike cikin nashi.

Haba Fati!

Ai sai ki karya min gwiwa, ku yi shiri ke da Nana ku raka ni har Lagos, sai in sanyo ku a jirgi ku dawo.

In kin yi kuka ke da kike da ababen debe kewa (
ya) ni kuma in yi ya ya?

Kamar yau ne za ki ga na je na dawo, mai da hawayen nan maza-maza bana son ganin su
Ta ja shessheka tana kokarin mai da hawayen, daga nan kuma aka koma aikin lada, mai gigitarwa.

Karo na farko da Fati ta taka matattakalar jirgi a rayuwarta.

A Lagos sun jima suna tsimayen lokacin tashin jirgi me zuwa Chicago, yana ta tausar ta da kalami masu dadi kamar ba Dr.

Sulaiman ba, da cewa; ta kula da kanta, karatunta, da
yanta.

Suna daga mishi hannu ita da Nana ya bi matattakalar jirgin da sauri, ba tareda waiwaye ba, ya tabbata zai yi kewar su.

Karfe biyu na rana nasu jirgin (Bell-View) ya dawo dasu gida (Kano).

Malam Habu ya debe su a Airport.

Tun tana damuwa da rashin Sulaiman har ta saba, ta sanyawa ranta salama, musamman kuma da yake duk dare suna tare a waya, ta maida hankali kan karatun ta da rainon
yan ta.

Shekara kwana ga mai yawan rai, Dr.

Sulaiman-Sulaiman Bakori, ya gama course din shi cikin nasara da shi da sauran likitoci
yan uwansa.

Aka yi mishi sauyin aiki da karin girma zuwa babban asibitin koyarwa na Abuja, a lokacin Fati na mataki na uku a jami
a, dauke da tsohon ciki na haihuwa yau ko gobe.

Zuwa wannan lokacin Fati ta gama mallake komi na Sulaiman, da da
arta, halayen ta da addinin ta.

Ita ce matar shi mafi kusanci da shi, sannan kawar shi abokiyar shawarar shi.

A gefe abin so da kaunar shi.

Iyayen na matukar alfahari da wannan aure da suka hada a bayan ran marigayiya Hadiza, wadda har gobe, jibi, har gata basu daina yi mata addu
a ba.

Kuma tunaninta bai taba gushewa daga zuciyar kowannensu ba.

Dr.

Sulaiman yana Abuja, sai week end yake zuwa musu, sai ko in duk sun samu hutu suma su ke bin shi Abujan.

Ranar wata litinin kwana daya da tafiyar Sulaiman nakuda ta kama Fati, suka nufi asibiti ita da Alti, yaran duk suna Karkasara.

Kafin magariba ta haifi sankacecen danta mai kama da Baban shi har farcen kafa.

Sai waya Dr.

Surayyah ta yi mishi cewa baby ya iso.

Sai ga shi a washegari kamar an jefo shi, ya tadda Fati da baby a
aminity
, sai dai dakin cike yake da
yan uwanta.

Sai daga nesa yake jifanta da murmushin
bani da abin da zan gode miki
Ita ma murmushin take masa da su kadai suka san ma
anar abin su.

Ba da son ranshi ba Yaya ta wuce da ita gida inda za ta yi wanka, don Alti an aiko mata rasuwar danta a kauyen su Kukawa, don haka za ta tafi a washegari.

Dakin ta na da Yaya ta gyara mata suke wankan, Munib dan kankanba ya kasa sukuni saboda ya yi kani namiji dan uwan sa.

Bini-bini zai ce a ba shi ya dauke shi, ita kuma Fati ba ta gajiya da mika mishi shi.

Kawarta Fa
iza ta zo mata barka wadda ita ma an yi auren ta tuni, suka wuni sur suna hirar bayan rabo, don Fati ta zamewa Fa
iza abin sha
awa ganin yadda ta yi kyau ta kara girma, yanda duk wanda ya dube ta duba daya zai tabbatar tana da kwanciyar hankali a gidanta.

Sabanin ita da kishiya ta sa ta gaba, ta hana ta zaman lafiya.

Fati na tausar ta tare da ba ta shawarwari na gari.

Ranar suna yaro ya ci sunan Malam, wato Ja
afar.

Malam ya roke su kar su boye mashi suna su kira shi da Jafarun shi.

Juma
a yamma lis, Dr.

Sulaiman ya iso Kano daga Abuja, kai tsaye gidan surukan sa ya fara dosa.

Bayan motar shi dankare da himilin tsaraba, Yaya ta yi mishi shimfida da sabuwar tabarma, ta sunto baby da ke bayan ta ta mika mishi.

A lokacin Fati ta fito daga bandaki, ta yi daurin kirji ta rufu da tawul, ta sha dukan ganye, jikin nan ya kara zama fresh, fatar nan ta kara zama mai taushin gani a ido.

Ta kasan ido ya dube ta, sai ya ga duk ta canza mishi, ta kara zama yarinya danya sharaf.

Da alama ba ta da damuwa, sun barshi da kadaici, sai fama yake da biro da takarda.

Yaya ta shige kitchen ta barsu, ai kamar jira yake ta tashi ya yi ma dakin Fati tsinke.

Tana tsane gashin kanta da tawul ya bude mata dukkan hannuwan sa bayan ya aje babyn a cikin katifar sa.
Chapter 21 · 0% Book details