← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 35

Sashe 9

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata ganin kowa da mutunci ban Isa in nuna mata kuskure ko shawara ba shine na ke son gani a gabanta ka fada mun idan Kaine ka daure mata......

Wallahi bani da masaniya.

Kuma me yasa tun farko Baki fada min ba ......saboda Ina tunanin ko hada bakunta ne Shi yasa Amma na lura galari ne da daurin gindi....wurin wa?

Na rantse da Allah ban sani ba.

Ke Ummi kinji abinda ta ce haka ne?

Ta yatsina fuska, eh saboda Ni ko a gidan mu ba saba dafa abincin gandu da......what?

Nan gidan ku ne?

Da sauri ta kalleshi.

Ya zaburo na ce Nan gidan ku ne?

To bari kiji in fada Miki Nan gidana ne matukar kina son Zama Dani wallahi sai kinbi abinda nake so da abinda na tsara.

Waye zakiyi ma gadara kice gidan ku?

Idan gidan naku kike so sai a maida ki kije kiyi abinda kike so Amma anan matukar kina son Zama to ya Zama wajibi kibi abinda nake so.

Bazan taba daukar raini da wulakanci ba ai nasan halinki na ga take taken ki na rashin tarbiyya da tsageranci idan nayi la'akari da yanda kike datsa mun magana many times.

Ya nuna ta da yatsa wallahi ki taka a sannu......Amira dai juyawa tayi abinta.

Ya kirata Amira tana juyowa tace abinda ya kawo ni kenan idan itama tana da nata korafin Ina jiranta.....tayi ficewarta.

Amma ke wallahi Baki da wayau Ummi.

Da kin San Hali irin na Amira da kin lallabata Kun zauna lafiya.

Kin Aure mata miji Kuma kin dawo kina wani hauka......

Gori zaka mun?

Ai ba ni na kawo kaina ba.......

An Miki gorin.

Wallahi matukar kina son Zama Dani cikin Jin dadi sai kinbi Amira Kun zauna lafiya.....fuuuuu ya tashi ya shige daki ji kake gammmmm.

Kwalla suka zubo mata, zuciyarta tayi mata kunci wanna masifa dame tayi Kama?
******************
*Federal University dutsinma*
Sun fito lecture 9-11 kenan aka aiko registration officer dinsu na kiranta.

Babban mutum ne ana yawan Kira mishi kirki da mutunci.

Tana ta faman tunani ko lafiya?

Bayan sun gaisa ya mata fatan alkhairi sannan yace yaji dadin gajin result dinta da Kuma yanda ta Sami shaida a department na tare mutunci amatsayin ta na budurwa Kuma ita kadai mace musulma a ajin.

Sannan idan har tana da wata matsala kada tayi kasa da guiwa ta je ta sanar dashi in shaa Allah zai taimaka.

Tayi godiya sosai, ta koma aji dayake suna da wata lecture ta 11-1 sannan suyi test 2-4.

Sadeeq babban abokin Anwar, Wanda kowa yasansu tare tun aji daya, ya hangota yace mutumen ga fa bilky can .

Yayi kamar baiji Shi ba miskilin........
*Zainab wowo*..
ayi hakuri da kadan pls
*WA ZAI FURTA?*
0
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.

Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Kinfi Alawiyya farin jini unex ta hannun damata ( Hussaina Nasir )* Allah yaba kauna. *Alawiyya*
*********************
*Federal University dutsinma*
Tana isowa ya tashi yabar gurin.

Haushi ya kamata ganin zai dizga ta bayan Kuma yasan cewa wurin Shi tazo.

Sai Shan kamshi yakeyi yau ta rasa dalili.

Ta kalli sadeeq yau me akayi wa abokin ka ko Yan wulakancin ne bisa Kai.?

Yayi murmushi to wa ya sani.?

Sadeeq Yana da kokari Shima sosai musamman bangaren calculation ya iya Math sosai da sosai.

Tayi murmushi kyaleshi don nace zamu zauna test tare ne yake faman hade rai.

Murmushi kawai sadeeq yayi.

Suleiman na zaune gefen ta, tace sadeeq kara nuna mun nan please ta bude littafi ( Bilkisu kenan ba girman Kai indai maganar karatu ne ), ya danyi Yar dariya bari in Kira Miki mutumen ki kada.......bana so kyaleshi kawai nunan.

Tare da Suleiman ya nuna musu sai ma ta ga cewa yafi Anwar iya koya lissafi Shi Kuma yafi iya theory ( labaran banza ).

Yana shigowa ajin ya gansu tare da sadeeq ya Kara hade rai, wani haushi ya turnukeshi ji yakeyi kamar ya rufesu da duka su biyun.

Zai gitta sadeeq ya rikoshi malam zo ka koya mata.....kyaleshi banso ta fada a hasale.

Baka ga sai wani Shan mur yakeyi ba simply don nace Zan zauna test kusa dashi?

Mtsew ta balla mishi harara.

Duk kunya ta kamashi, saboda Shima fa bai San dalilin fushin nasa ba,
Gaban sa ya fadi kaddai fa kishin yarinyar nan yakeyi.

Yayi saurin kawar da tunanin yadanyi tsaki a hankali.....

Ke bana son Sheri, yaushe ma na ganki da har Zaki mun wannan shaidar.

Eh Mana, Ina ma ka ganni ai baka so ko ido mu hada kana ta wani muzurai......mtseew ya finciko sadeeq tashi munafuki.

Ya zauna kusa da ita kamar ya ingije Suleiman yakeji , kawai baya son raini ya shiga tsakanin su.

Zaka karya nine?

Ya mishi banza..., Ita ma bai Kara mata magana ba.

Suleiman dai na gefe ta juya tana mishi magana......idan na wanko ga Anwar ka wanka kada kayi kasa da guiywa....ya kyalkyace da dariya ita ma dariyar tayi.

Ya Kara hade Rai....yarinyar nan ma ta daukeni Dan iska Amma ba laifin ta bane Suleiman zanci ma uwa......akan me?

Wata zuciyar ta bukata.

Yayi saurin kawar da zancen ya maida Air piece dinsa a kunne.

Ya ajiye littafin sa ya fita waje.

Kowa nata karatu Amma Shi ba yanda zaka ganshi da littafi.

Handsome and intelligence guy amma girman Kai da wulakanci sun bata Shi.

Vivion dake zaune gaba na ta fada tare da kallon uchechi.

Ai ya Raina kowa don Yana da kokari.

Ga kyau Kuma ko?

Eh, Amma baya birgeni saboda gadarar sa, jiya munyi ta kiransa yaki daukar waya nida su faith.

Hmmm mu samun sa mukayi dazun after lecture muna son ya koya Mana Amma kowa ya kasa Masa magana........

Maganar ta makale ganin Yana dawowa.

Ashe malamin nee gani ya taho.

Ko Zama baiyi ba ta nuna su uchechi gasu Nan suna son ka koya musu amma sun kasa tambayar ka......sai ke Mai Baki Zaki tambayeni?

Idan abun ya damesu ki bari su fada Mana.

Zata Kuma magana ya nuna mata hannu alamar ta duba ga malamin nan ya shigo.

Sadeeq na bayansa.

Ta fiddo paper zata rubuta suna yayi saurin daukewa ya rattaba nasa sunan ya wani hade Rai.

Ta kura mishi ido Baki bude.....gashi Bata da wata.

Ko wa ya dauke jakar sa....malamin ya fada.

Ya dauko jakar ta ya saka littafinsa Suleiman ya Miko nasa a saka mishi da wayar sa kawai ya Mike ya saka tashi wayar yakai jakar can gaban malamin.

Ita Bata San me yayi ba, Amma Shi Suleiman din yaji haushi sai dai Yana uchechi ta saka mishi a tata jakar.

Sadeeq kuwa dukewa yayi Yana sumke dariya.

Bilkisu tayi zugum tana zare ido Anwar ya kwace takarda.

Tana tsoron tayi magana ya canza mata wurin Zama.

Ko ajikin Anwar tuni ya Fara rattaba number sa bayan ya rubuta suna da course code.

Suleiman ya Ankara Ashe biyu gareshi.

Ya Miko mata.

Wani sanyi taji ta balla ma Anwar harara sosai sannan ta Fara rubuta suna.

Gaba daya ajin yayi tsit!

Tana rubuta suna taga Anwar ya fiddo wata takardar ashe daman Yana da ita.

Haushi ya Kara kamata shin me take nufi da akoreta sit din ko meye?

Nan da nan ta Kara kulewa.

Har malamin ya gama raba question paper Bata gama duminiyar Jan layi da rubuta suna ba.

Lokacin da ya bada umarnin a Fara kowa ya bude takardar Amma sai wutar kowa ta dauke saboda yanda ya mako muguwar tambaya Mai sarkakkiya.

Sadeeq taji na magana a hankali, Anwar wannan 35 din zamuyi amfani da ita kuwa?

Ya kada Kai alamar a'a.

Yawwa na gode.

Bilkisu tayi zugum, Suleiman ya zungurota alamar ta iya?

Ta girgiza Kai ya ce to kawai tayi ta kwafo musu na Anwar.

Ganin ya Fara rubutun tayi saurin maida hankali don samun abinda zata tsira.

Kamar injin haka yake rubutun zu..zu..zuu kafin tayi layi hudu har ya juya , haushi ya turnuketa bai jira ta gama?

Wannan wace irin mugunta ce?

Nan da Nan ta zuciya kawai sai ta ci gaba da rubuta shirme.

Gara naci zero da in yi naka ....ta fada cikin zuciya.

Kafin kace kwabo har ya gama ya janyo wata sabuwar takardar, ya canza biro black ya ci gaba da rubutu, sakamakon ta farkon da ya Fara da blue biro.

Tana kallon sa ta wutsiyar ido ko ya Turo mata wacce ya Gama da ita ta rubuta sai ma ya sanyata kasan tashi , idanun ta har ruwa ruwa sukeyi saboda fushi .

Wallahi Ni da Anwar har abada au Ni zai ma rashin mutunci?

Duk inda ka waiga kowa sai mazurai yakeyi an kasa rubuta abin kirki.

Tana kallon sa ya gama kawai yasa hannu biyu a kirji.

Kamar tayi ta tsunkulinsa takeji don takaici.
*stop writing*, ya Fara karbar wadanda ke gaba layi layi........ai kamar jira akeyi ajin yau dauki gungunai.

Jin haka kawai taga ya dauro mata takarda bisa tata.

Sunanta, number, course code.....da komai da komai.

Ta zaro ido Wai Daman biyu yayi tawa da tasa?

Tayi saurin kallon sa, ki soke wannan shirmen da kikayi kisa mistake.

Ta kalli takardar ita ce ya Fara solving da blue biro.

Suleiman ya Fara kunno Kai zai Fara kwafa , malamin har ya zo wurin su, duk suka Mika.

Shiru Suleiman din yayi yama rasa meye zaiyi don takaici, Tabbas yasan don Shi Anwar yayi haka.

Ta kalli Suleiman din cike da damuwa ka gama kuwa?

Wallahi banyi komai ba ya fada Yana kakaro murmushi,
Innalillahi.....

Ta juya zata ma Anwar magana Ashe har ya bar class din.

Ta waiga ta Kara waigawa Amma Ina tuni yabar shiyyar class din ma.

Kayi hakuri , ta juya tana ma Suleiman magana.

Nima wallahi har na sadakas, ashe rubuta mun yayi.

Kai Anwar karshe ne wallahi.

Murmushi kawai yayi.

Ai kaga da ya barni na kwafa har kaima kayi.....kayi hakuri Suleiman.

Haba ba komai wallahi.

Ya fada Yana Yar dariya.

Haka suka fito duk jikinta wani iri.

Kai Anwar case ne.
Chapter 9 · 0% Book details