Sashe 31
Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fine , ta fada tare da wuce Shi ta koma class din.
Duk aka kawar da fuska ganin ya biyo bayanta, samm bata lura ba Bata Kuma ji takunsa ba.
Littafin ya fada can karkashin desk ta kutsa can ciki ta Kuma duka tana kokarin dauko Shi, ya shigo sit din ya zauna, ita kuma tana ciki.
Dagowar da zatayi taji ta fada bisa kafar mutum ta mike da sauri innalillahi....
Wai kanka daya Anwar???
Ta daka mishi tsawa.
Idan baki so na Miki abinda Kika tsana ki zauna silently muyi magana wallahi idan Kika kuskura anan zan Miki abinda......
Bazan zauna ba bani wuri in wuce.
Naki na bayar ko Zaki daukeni da tsiya ki fitar?
Me yasa kike da gardama Bilkisu???
Kai Kuma me yasa baka da zuciya?.
Yayi murmushi nima Ina neman amsar nan wallahi.....
Ta ja tsoki kanka akeji bani wuri.
Ya kalleta alamar ba wasa yayi baya da hular sa , kin san Allah idan Baki zauna ba Zan daura ki a bisa cinyata ki zauna in kuma rikeki har sai na gama maganar da zanyi ko bazan iya ba?
Tayi shiruuuuu, sai Kuma ta zauna saboda tasan karamin aikin sa ne sai dai idan ya aiwatar daga baya ya bada hakuri.
Ya bita da ido Yana murmushi.....
Ta Kara tsuke fuska Ina sauraron ka ba ka tsareni da ido ba......
Me yasa Kika tafi Kika barni jiya?
Saboda ka gane baka gabana bana son wannan shisshigin, Kuma na Kara fahimtar fakai bana son kana taba ni na tsani hakan .
Kin tabbatar bana gabanki?
Ta kalleshi shekeke Zan ma karya ne don Ina tsoronka ko kana nufin......
Ina nufin mufeeda ce ta Kara Bata Miki Rai ko?
Mufeeda?
Mtseww a'a ka manta.
Idan ba ita bace me yasa Kika hasala sosai Kika tafi Kika barni?
Saboda ka rike ni na kuma fada maka bana so.....
Me yasa ke bazaki daina abinda nima bana so ba?
Ajiyeni kayi?
Ko kana iko dani da zaka Sanya mun doka kace kuma dole sai na bi?
Kiyi hakuri, ya fada a hankali.
Tayi sokoko ta kasa ci gaba da masifar.
Ya tsareta da ido, Dan Allah kiyi hakuri naji nayi kuskure bazan Kara ba I'm sorry please.
Tayi shiru,
Bana son fadan nan wallahi, bana son kina wannan tada jijiyoyin kina fushi dani bana so ko kadan please kiyi hakuri shikenan ko?....
Ba shikenan ba, sai ka mun alkawarin bazaka Kuma taba ni ba sannan.
Yayi shiruuuu, gaskiya ban yi alkawari ba amma Zan kiyaye.
Ya wuce ko?
Eh, ta fada a hankali.
Mun shirya?
Ta dan harareshi.
Yayi Yar dariya.
Mun shirya ko?
Um, ta ce tana murmushi.
Hmmm, Bilkisu kenan kina yarda Kika ga dama.
Karfe nawa Zaki kawon tuwo?
5, ta ce .
Lokacin na gama mutuwa da yunwa ko?
Ba abinci dare zakaci ba?
Waya fada Miki?
Shi zanci a matsayin lunch.....
Tuwon???
Yayi Yar dariya yes!
Hmmm,
Zaki kawon irin two din nan?
I'll try.
Ta fada a hankali.
Waye Zaki Aiko ko nine Zan turo?
Zan kiraka idan na gama dai.
Ya Mike tashi muje.
Ga book din ta Mika mishi .
Yayi Yar dariya daman ke nake bukata ba Shi ba......
Ta zaro ido what?
Ya Kara yin dariya ya ce Ina nufin ke nake so kizo inyi magana dake ba littafin ne a gaba na ba.
Tace hmmmm.
Suka jera suna tafiya.....
Tana tsallaka titi sadeeq ya karaso suka wuce.
Ta zagaya can baya wurin Mai nama ta siyo tsoka Mai kyau ta Shani kilo daya.
Tana shiga ta cire hijab ta Fara hada Miya...( Duk kudi irin nasu Bilkisu baisa anyi sake da koya Mata girki ba ) har catering school tayi ga karance karance da tambaye tambaye saboda girki na daya daga cikin abinda take so a rayuwarta.
Ta shirya miyar kuka Mai Rai da lafiya, naman yayi ruguf a ciki wurin Aisha ta Samo kukar da daudawa saboda bata dasu Kuma Bata Kai ga ta siya ba, anan daman take siye.
Duk wacce taji kamshin sai ta leko.
Tana gamawa ta daura tuwon bai wani dauki lokaci ba, karfe daya da kwata ta kullashi a leda, ta janyo sabbin coolers manya cikin kwali Wanda batayi amfani dasu ba daya kawai take amfani da ita karamar tana zuba Miya.
Ta jera tuwon guda Sha biyar aciki.
Ta zuba Miya ga Mai bi Mata duk naman ta kwashe musu kaf!
Ta bi da manshanu saboda bata rabo dashi ita ma'abociyar taliyar hausa ce dahuwar daudawa Tasha manshanu.
Ta kwalala mishi ta rufe.
Ta jera a basket ta Sanya mishi gwangwanin biscuit biyu cikin wadanda ya siya Mata da lemuka kala kala, ta dauki basket din da 200 ta fita.
Napep ta tsaida tare da mishi kwatancen hostel.....
Zan kirashi ya fito sai ya karba sunan sa Anwar.....
Anwar?
Ya zaro ido...
Anwar din zai fito ya karba?
Ta banka mishi harara ka San sa ne?
Ni kuwa na sanshi an bani abinci na Kai mishi kwanaki nafi awa banga kowa ba na Kira abokin sa da aka bani number sa Koda yaji zancen nawa ya kashe waya bai Kara.....
Malam zaka Kai mun sakon Nan ko na nemi wani?
Zan Kai Hajiya Amma idan bai karba ba Ina Zan ganki saboda wadancan kayan har Yanzu suna gidan mu......
Kaga compound gashi can???
Ka ce Bilkisu kake nema ta ajiye mishi basket din ta bashi 200 ta juya kawai....
Ya kalleta a yamutse wahalallu.....
Ta kanga waya a kunne tana Kiran sa.....
Barci yakeyi kasa rika Kuma yanajin dadin barcin.
A hankali wakar *Because you love me* ta Fara tashi ta cylindion.
Yayi firgigi saboda Bilkisu kadai keda ring tone din.....
Hello ya fada cikin muryar barci.
Ina hanya Zan kawo maka tuwon na kusa karasowa na sameka bakin gate din ku kada ka barni Ina jira......ta kashe wayar.
Idanun sa suka bude tangaran ya bi fuskar wayar da kallo.....
Ya Mike zumbur ya zura jallabiya ya fice da silifas kafarsa.
Dai dai tsayuwar Mai napep din Yana hango napep yanufe ta da sauri Yana lekawa.....
Kai ne Anwar?
Sai kawai yayi murmushi watau yarinyar nan dabara tayi mishi don ya fito?
Ya kalleshi eh, tare da Mika hannu ya karbi basket din.
Yasa hannu aljihun jallabiya ya fiddo 500 ya Mika mishi....
Ta biya yallabai.
Yayi Yar dariya to in mayar kenan baxaka Kara ba tunda na fiddo?.....
Yayi charaf ya karbe Yana fadin wazai mayar da alheri?.
Na gode yaba napep wuta Shi Kuma ya nufi hostel Yana murmushi.
Ya bishi da kallo Yana jinjina Kai.
Yanda suke fama da student wurin neman ragi da amsar chanji amma ga wani na kyautar 500, ita Kuma ta biya 200 zuwa kawai.....
Wurin Nan akwai magana ya ce kafin ya chilla keken titi.
Sadeeq nata barci bai motsa ba.
Yasa kafa ya Kai mishi harbi....
Tashi Dan ubanka Bilkisu ta Mana girki.....
Zumbur ya Mike Yana kallon basket din....
Yayi dariya wallahi tuwon ne ta kawo .
Yunwa sukeji Daman, sadeeq ya Fara kwashe lemukan Yana ajiyewa kasa, sannan ya fiddo coolers din, kamshin manshanu ya buge dakin Anwar ya hadiye wani tsinkakken miyau ya gyara Zama .
Baiwar Allah hada biscuit ta debo da lemuka......
Tana so ta rage su ne sun Mata yasa Anwar ya katse Shi Yana murmushi.
Sun kwashi tuwon sosai musamman Anwar kulli hudu suka Bari.
Amma fa yarinyar ta iya girki in har itace tayi....
Ita tayi nasan bazata ba kowa yamun ba ya janyo waya .
Hello ta fada tana Yar dariya.....
Ni Kika mayar gaki nan zuwa ko?
Ta kyalkyace da dariya....
Tuwon nan yayi dadi fa ga Sadeeq nan Yana lasar kwano....
Shi na Bari Yana lashewa karya yakeyi ya fada da karfi.
Ta tuntsure da dariya.....
Na gode sai na maido kwanonin Allah ya biya thank you so much Bilkisu Mai gadon zinari...
Ya fada Yana dariya.
Ta ce hmmm.
You and this your hmmm.
Bye wanna baf.
Ya kashe wayar.
Haka kawai taji ranar ta Mata dadi tana nishadi.
Wunin ranar wani nishadi takeji.
Akan hanyarsu ta dawowa daga masallaci isha'i take ba Aisha labarin wayar da sukayi cewar yaci tuwon.
Kamar daga sama suka ga mutane gewaye dasu hada maza.....
Gabansu ya Fadi suka tsarata ainun Aisha tayi karfin hali tace lafiya?
Mufeeda suka gani ta fado gabansu tana taunar chingam.
Ta kalli Bilkisu ke karamar Yar iska ce wallahi....
Ni zakiyi ma karuwanci?
Akan Anwar har kisan Kai Ina iyayi na rantse da Allah ta daga hannu zata kwada Mata Mari akayi charaf da hannun aka rike Shi ta baya....
Kowa yabi hannun da kallo zuwa inda aka Kama don suga waye?
Anwar ne yasha boyel fari kansa da hula kube ya murzata irin sa hular kanawa sai kamshi ke tashi, hannunsa dayan rike da basket........
*ZAINAB DAHIRU WOWO DUTSINMA*
*KAUNAR KI AZIMUN CE Ina yinki over RUKAYYA BAKO DANBATTA* *ZAINAB WOWO NA JIN JINA MIKI ALALH YA SHIRYA ZURI'A AMIN*
A ringa mun uzuri, Ina zuwa aiki, Ina da miji Ina da Yara kafin na Fara rubutun na fada I won't be able to post all the time na Fadi haka saboda Ina da hidindimu.
Alawiyya ciwon ciki
*WA ZAI FURTA?*
1
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.
Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*RUKAYYA BAKO DAN BATTA i love you so much, remember this always*
***************
*Federal University dutsinma*
```Ya juya hannun da karfi, wallahi duk ranar da wannan hannun ya yi gigin taba Bilkisu sai na karya shi, nima akanta Zan iya kisa```.........
Ya wurgar da hannun.
Sannan ya kalli wadanda ke tsaye *What the hell are you doing here?* Ya daka musu tsawa......
Suka Fara darewa, mufeeda ta juya zata tafi ya fizgota..... ``` Bata hakuri```.......
Tayi saurin kallon sa, Jin haka yasa kawayenta Suma suka Fara yin baya,
Bakiji abinda na fada ba?
```ki Bata hakuri ko Kuma wallahi....```
Ta fizge hannunta, bazan bayar ba.....
Ta wuce da sauri kamar zata tashi sama.....
Aisha ta rike hannun Bilkisu tamau.
Ita kuwa kanta a kasa kawai tayi shiru......