← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 35

Sashe 6

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta Dan waiga ta hango Suleiman can baya an cillashi sai zare ido yakeyi.

Duk Wanda ka kallo zakaga ko Yana zufa ko Yana ta raba ido.

Kije kiyi submitting...ya fada kasa kasa ta ce toh.

Kowa sai kallonta yakeyi Yana mamakin yanda zata bayar da wuri haka, Wasu na tunanin kawai ta gaji ne da zama kamar yanda Suma suke zaune, tafi mintuna talatin kafin wasu tsirara suka Fara fitowa duk Wanda ya fito idanu jawur ana tsinar malamin kusan kowa ya sadakas da kawai faduwa zaiyi course din saboda rashin iya amsawa.

Suleiman kawai take jira ya fito sai kuwa gashi Yana ganinta yace, Bilkisuuu.....

Yau naji wuta wallahi Allah dai ya kyauta Amma question biyu kawai nake da tabbaci cikin sauran.

Tabbb....wallahi ni Allah ya taimakeni Anwar ya bani duka Wanda ban sani ba....hada question one?

Eh Mana.

Wai da gaske kike?

Wallahi kuwa.

To Ina Jin keda shine kawai kuka amsa ta don ko su chinyere gasu can suna cewa Basu gane ba.......Allah dai ya kyauta ta fada tare da cewa sai gobe ta ruga hango Anwar yayi hanyar *Gate* Yana ta faman sauri.

Anwar.. ta kwada mishi Kira, yasan za a rina Shi yasa yaso ma kada su hadu.

Ya Dan tsaya Yana murmushi , ya jarabawar Bilkisu ya fada Yana latsa waya.

Hmmm jarabawa yau Allah ya rufa man asiri bacin Kai ai Dana shiga uku.

Na gode na gode Allah ya Kara ilimi......Daman ka iya course din sosai haka?

Naga yanda ake ta kuka dashi Kai komai ka amsa.....hatta jamilu ma naga naka yake kwafa ( copying ).

Murmushi kawai yayi yace ba damuwa.

Ya wuce kawai.

Ta bishi da ido.

Anwar...ta Kara kwada mishi Kira.....ya juyo wallahi na gode kaji?

Sai kawai ya kyalkyace da dariya ya juya abinsa.

Taji dadi sosai da sosai a Ranar domin course din kadai kowa ke kuka dashi wannan semester din.

Hutun ya kasance dogo akalle ankwashe watanni biyu a gida kafin a dawo aji biyu.( Su Bilkisu an Fara manyanta ) wannan karon suna gida result ya fita inda take da 4.22 ta Dan sauko kadan saboda ansha wahala matuka Shi Kuma Suleiman Yana da 2.72 Amma ya Sami carry over daya.

Sun koma da makaranta da sati biyu akayi *convocation* tare da bayar da kyaututta ga first class da over all.

Bata halarci wurin ba.

Saboda ba kowa ya maida hankali ga taron ba.

Hakan yasa Anwar zuwa tare da karbar five pointer award da Kuma overall student na aji daya da suka gama.

Kamar munafuki ya karba sim sim sim yayi saurin barin hall din ganin babu alamun Yan ajin su ko wani Wanda ya sanshi.

Ashe Suleiman yana wurin.

Ba karamin mamaki yayi ba watan Anwar shine *Hamza Yusuf* din da ake nema cikin class Amma wallahi sai ya fadawa Bilkisu.................
*************
*KADUNA RIGASA*
Yana ta mamakin yanda ummi ta mishi text tana son ganin sa alhalin bata taba hakan ba.

Yana zaune babban falon gidan nasu an cika gaban sa da kayan ciye ciye da lemuka kamar kullum ta shigo tana ta faman Bata rai .

Ya kalleta tana ta faman karairaye karairaye......Amarya bakya laifi ko kin kashe Ahmad ( Babban yaron sa ) ya fada cikin zolaya Yana Yar dariya hannun sa rike da samosa mutumen shi Yana ci.

Banga alama ba, ta fada tana taunar cingam.

Ya kalleta jin maganar ta fito gatsal....

Kamar Yaya?, Ya bukata.

Kamar yanda kaji.

Kamar yanda naji?

Ya maimaita cike da mamaki kafin ya ajiye guntun samosan bisa plate ya tattara hankalin sa duka wurin ta.....me ke faruwa ne ummi?

Tayi shiru!

Dake nake magana...me ya faru?

Ta gyara Zama, Ina ce apartment din da kayi sabo Ni ka gina mawa Amma labari yazo cewa Aunty Amira ta koma.......

Ke ya daka mata tsawa.

Nan da nan ya harzuka, Ni na fada Miki Ina Miki gini?

Gabanta ya fadi tayi tsuru tsuru, kinji?

Munyi dake Ina Miki gini?

Okay ita da Zaki aure Mata miji Bata kawo mun matsala ba sai kece Zaki fara kawo mun tsirfa?

Saurara da kyau ya Mike tsaye Yana nuna ta yatsa wallahi matukar kina son Zama dani tare da Jin dadi sai kin daratta Amira kin mun biyayya kin Mata bazan dauki sakarci ko kadan ba.

Dukkan ku Ina sonku to dole kowace tabi ra'ayi na, idan Kika saki na gane kina da matsala to wallahi zakiji ba dadi.

Mtsew ya buga tsaki ya wuce.......ta yi zuruuuuu tana zare ido lallai ta gwada Bata ji dadi ba.

Kwallah suka zubo Mata.

Ta buga ma babbar yayar su waya domin ita ce abokiyar shawarar ta .....salati ta kamayi ubanwa ya aike ki?

Ai kinyi sauri bari zakiyi sai kinje gidan yasan dadin ki lokacin yazo hannu tukun Amma Yanzu ai lallaba matar sa yakeyi tunda ya Mata laifi.

Ki bari Zan baki ahawarwari idan na shigo gobe.

Tun daga ranar Bata Kara Sanya Shi a ido ba.

Tuni a Mata hudubar kada ta saki ta dauki raini ga matar sa Kuma idan ta a gidan ta Sami damar juya Shi yanda zata amshe ragamar komai.

Babu yanda ba a yi dashi ba ko kamu ayi yace bai son bidi'a ba Dan komai ba kada ma akirkiri partyn Amira taji ba dadi.

Ranar walima akayi mashi Sha Tara ta arziki hada mota.

Yana falon sa zaune yaji marokiya na sanarwa.

Shima ya Mike ya kirawo marokiyar ya bada makullin mota kirar *GLK* baka 2019 model ta kusan miliyan Tara yace yaba Amira ayi sanarwa.

Nan dangin Amarya kuwa suka Fara surutai............

Ko ajikin sa.

Dangin ango dana Amirai kuwa suka Fara rangada guda suna tayata Murna.

Hakan ba karamin harzuka Amarya da danginta yayi ba.

Nan suka Kara hure Mata kunnen wallahi sai ta tashi tsaye Dan kwato ma kanta yanci.

Kuka takeyi wuiwui.

Kafin karfe shida gida ba kowa duk an tafi.

Ana gama sallar isha'i ya ja Amarya zuwa sashen Amira don yi masu huduba.......
*Ayi hakuri da typing error please yanayin typing din ne saboda kawai ta WhatsApp nake yi Kuma gaskiya bana bi idan na Gama kawai nake turawa.
*Daga zainab wowo*
*WA ZAI FURTA?*
0
*TUKUICI NE GA AUNTY RABI ALLAH YA KARA ARZIKI DA RUFIN ASIRI*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki.... blood sister khadija Dahiru wowo miji na gari I pray my besty*
*DAYA TAMKAR DUBU AL'AMEEN ZUBAIRU* TANNY ALLAH YA RAYA MIKI YARON NAN YA KARA MISHI KYAU DA KWARJINI
*Federal University dutsinma*
Tunda aka dawo bai yarda sun hadu da Bilkisu ba har suyi wata magana.

Tana ta kokarin su hadu Amma yaki yarda.

Suna tsaye ita da su favour bakin ajin da zasuyi darasi ta hango Suleiman na taho wa, tun daga nesa suke ma juna dariya saboda Yanzu sun Zama tamkar *Wa da kanwa*, Anwar har yazo ya wuce ta gaban ta bata ganshi ba amma Shi Suleiman man din ya hango shi.

Yana karasowa malamin Shima ya iso haka suka rankaya zuwa aji.

Ko Zama Yanzu kusan tare sukeyi.

Har Yan class din sun Fara lura da shakuwar su.

Ya fakaici idon malamin ya Fara mata magana kasa kasa.

Wai Bilkisu kinsan Hamza Yusuf din say ake nema ajin nan Anwar ne?

Ta zaro ido *Anwar*?

Eh wallahi.

Jiya gaba na ya amshi award din first class da Kuma overall award ina kallon sa yayi saurin boyewa ya bar hall din da sauri.

Ta rike baki.

Innalillahi, wallahi sai na mishi magana naga wannan semester din ma tunda muka dawo sai wani shareni yakeyi.

Hmmm, ai da yake kece, Amma Anwar inba ke ba waye ke mishi shigar kawara duk makarantar Nan.

Kinsan girman kansa, jiji da Kai da kuwa maida kowa banza yasa aka tsane Shi wallahi ya cika gadara.......

Duk yaji dashi nikam daga yau wallahi ya shiga uku dani.

Ba abinda nake nema wurin sa inba karatun ba.....ta katse shi.

Hmmm Hana wallahi nayi mamakin *Business finance* din last semester, bana fada maka cikin mintuna da Basu wuce talatin ba ya gama kusan questions 4 kowa na kuka da question one amma Shi duka yayi. *B* fa gareni course din Kuma wallahi C A da 22 na shiga......ohh ni *Balky* ai wallahi ya shiga uku dani.

Suleiman man dai sai dariya yakeyi yace idan kin kwaso wurin sa Kya ringa koya mun....tabbbb tare zamu je kyaleshi ai wallahi sai na fitine Shi ga wannan semester din kurar ta tafi ta aji daya.

Daya ke Anwar din Yana ta gefenta sai kawai ta yi ta kallon sa.

Tun bai lura har ya fahimci tana kallon sa.

Ya Dan juyo suka hada ido ta balla mishi harara Shi Kuma sai ya kawar da Kai Yana murmushi kawai.

Haka sukayi tayi da sun hada ido sai yayi murmushi ita Kuma ta harareshi.

Yana ta sake sake cikin Rai *Kuma yau me nayi Ni Hamza* bana iyawa rigima da fitinar Yarinyar can.

Ya kawar da Kai bai yarda sun Kara hada ido ba har aka gama.

Hankalin ta na kansa yana mikewa itama ta Mike.

Abinka ga namiji kafin ta sunkuya ta dauki jaka har yabar ajin.

Da gudu tabi ta kofar baya kawai sai dai ya ganta gaban sa.

Gaban sa yayi mummunan faduwa Amma miskilancin Anwar bai yarda ta gane hakan ko a fuska ba hasali ma sai yayi Yar dariya *Hajia Bilkisu an tashi lafiy?*
Ta rike kugu To yau Allah ya Kama ka, Ashe Kai ne *Hamza Yusuf*........

Har ga Allah ya Dan razana.

Amma a zahiri sai kawai yayi dariya duka kumatunsa suka lo6a ....inji wane makaryacin?

Ya fada Yana dan waige waige kada sauran Yan aji masu fitowa suji,
Wallahi Kaine *Hamza Yusuf*....

Ta fada tana hararar sa.

Tana matukar bashi dariya saboda ko gida bai taba samun Wanda ke mishi magana Kai tsaye Babu shakka ba irin Bilkisu.

Yadan Sha mur Yana Dan zare mata ido ke ni bani bane ya gitta zai wuce .....Tasha gaban sa da sauri tare da ware hannuwa ba inda zakaje sai ka fada mun wanene jiya aka bashi kyauta ya boye ya gudu?......tuni hankalin mutane ya dawo kansu an Fara fahimtar meke faruwa.

Ya zaro ido.....

Ke ni bani bane.....

Wallahi Kaine.

Naji nine yanzu meye kike so?
Chapter 6 · 0% Book details