← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 35

Sashe 17

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yan aji sai zolayar sukeyi jiya yaji tsoro baizo class ba kada a mishi wanka yana ta dariya da yazo zasu hada ido sai ya kawar.

Duk taji babu dadi.

Ana Gama lecture wasu suka shigo alamar venue din su ne.

Fitowa sukayi, ajin dake hade dashi ba mutane sosai Yana tsaye bakin taga tace Anwar muje Nan naga ba kowa.........

Anwar let's snap please Helen ta karaso tare da dafa kafadarsa.......

Wani dadi ya ziyarce Shi yace anzo wurin.

Ya kalli Bilkisu okay jirani Ina zuwa.

Kawai suka Fara hotuna.

Kamar jira akeyi sai ko wace ta taso wasu ma wucewa zasuyi ga Anwar da farin jini
Nan da Nan hankalin Bilkisu ya tashi ta kasa daurewa ganin yanda suke faman rikeshi wasu na kwanciya kafadar sa.

Ta shiga ajin idanun ta duk sunyi ja.....

Yafi mintuna talatin tana zaune ta ma kasa tashi suk tana hangensu ta taga.

Sadeeq ya karaso maigadon ya naga kinyi zaune baku Fara ba?

Eh, hotuna yakeyi yabar Ni Nan kamar sakarai, ta fada a wahale kamar zata kurma ihu.

Malami ya shigo yace ku fita zamuyi darasi......

Haka suka fito tare da jingina jikin icce ita da sadeeq har lokacin hotuna sukeyi ko kallon inda take baiyi ba.

Sadeeq ko zamu je ka nuna mun Dan Allah?

Ta fada Rai bace........

A 'a ki jira ya Gama kinsan halin mutumin....wallahi yau Kam bana so ko da kuwa yazo.

Tohhhh..... sadeeq yace kafin ya Kara magana sai ga Anwar din.

Bilkisu muje.

Ta kalleshi kallon da ya gwammace bugu dashi sannan tace bana so kaje kawai.......

Duk akayo musu ratai da ido.

Nan da Nan ya hasala don yasan a rina iyakar rainin wayo yarinyar nan ta daukeshi sakarai,
Saboda me Baki so?

Ya bukata a hasale....

Ina ce hoto ne a gabanka, ko?

Ina jiranka mintuna kusan talatin.....Kai ma abokina meye haka.

Zanci ubanka sadeeq...ya daka mishi tsawa.

Kada Allah yasa taso waya rasa?

Don kinga Ina lallabaki naje nayi hoton me ya hana kizo ayi dake?

Ko Zaki hanani ne?

Sadeeq zai Kara magana ya nuna Shi da yatsa a hostel zamu hadu zanga ubanda ya tsaya maka kaima......duk suka zaro ido lallai fa da gaske yake.

Sannan ya kalleta kada Allah yasa kiso ke Kika rasa........

Ya wuce fuuuuu ya fada wani class ya zauna Rai bace kamar zaiyi hauka idanun sa sunyi jawur.

Bilkisu ta rasa inda zata Sanya kanta, kuka zatayi ihu zatayi, itama nata idanun sukayi ja tare da kawo ruwa kamar zatayi kuka abin yazo kaina?

Hakan take ta nanatawa cikin zuciya.

Sadeeq ya kalleta hankali tashi, wallahi fada zamuyi dashi tunda Kika ji ya rantse.......

Ta zaro ido fada?

Hmmmmm Baki San halin Anwar ba.....

Sai akwai tabar Shi nan ta wuce class din da taga ya shiga....

Yana zaune ya hade Kai da table.

Ta zauna kujerar gabansa, ta Kira sunan sa,
Anwar!..

Ya dago da sauri sai da gabanta ya Fadi ganin yanayinsa.

Ta daure ta Kura mishi ido zuciyarta kamar zata fito amma ta daure kada tayi sanadin raba abokai .

Ta Fara magana a hankali.....

Ba ruwan sadeeq cikin maganar nan, kada laifina ya shafeshi duk abinda zakayi mishi kayi mun Amma kada ka Sanya Shi ciki kayi hakuri ka kyaleshi .......bazanyi hakurin ba.

Ya fada kamar zai mareta.

Duk ajin akayi shiru ana kallonsu,
Ya daga murya, ke har Zaki ce na Bata lokaci Baki so na koya miki?

Ni idan naje wurin malamai su koya mun korata sukeyi wani lokacin sai na kwashe fiye da awa daya sannan suce in tafi in Basu wuri, bana zuciya gobe sai na koma sai ke daga Yan mintoci Zaki nemi kiyi mun wulakanci cikin jama'a?......

Naji kayi hakuri,......

Bazanyi ba nace ki tashi ki bani wuri.....gabanta ya Fadi.

Ta daure ta hadiye kwallan dake son taruwa a idonta tace sadeeq nake nufi kayi.......

Bazanyi hakurin ba ya Mike, idan ke bazaki tashi ba ni na tafi.....kawai yabarta wurin.

Na shiga uku ni Bilkisu ta fada.

Tashi tayi tabar class din don kwallar sun kasa tsaiduwa.

Ni Anwar zaiyi ma wannan wulakancin?

Ni Anwar zai dizga?

Ni Anwar zaiyi ma gorin karatu?

Me yasa tun farko na bashi fuska?

Idan sai Anwar ya koya mun karatu zanci jarabawa billahil azim na hakura da degree har abada.

Biji biji take ganin hanya....ba abinda kanta keyi sai sarawa, kaicho na ni Bilkisu na kyale Anwar har abada tallahi ko kallonsa bazan karayi ba.....ta bude daki ta fada bisa katifa sai kuka.........

Hankalin sa yafi nata tashi, kamar mahaukaci ya Isa daki Anas ne kwance ya fada bisa katifa Anas na shiga uku nayiwa Bilkisu wulakanci.

Ya zaro ido me ya faru.?

Yarinyar nan kureni tayi yau, na rasa ta inda Zan bullo mata.....naji me ya faru.

Ya Mike kamar mahaukaci.......laifinta ne nasan gobe zata Kara bani hakuri.

Zamu shirya .....ya fice dakin.

Duk duniya Yanzu Babu Wanda takejin tsanar say ranta irin Anwar ko sunan sa Bata so a fada ta fita batunsa Amma kullum cikin kuka take.

Kwananta biyu daki kwance ta kasa zuwa lecture saboda Bata kaunar Kara ganin sa.

Shi Kuma jira kawai yakeyi tazo ta Kara bashi hakuri su dai dai gashi Yana ganin ya zubda ma kanshi class matukar ya kirata a waya, abinda bai sani ba har ta goge no.

Sa cikin wayarta.

Abu kamar wasa kusan sati Bata zo school ba, sai dai kullum tabi dakuna ta karbi note tayi.

Ranar laraba ta Kama kwananta tara rabonta da school Shima tazo ne dole saboda za'ayi C.A Kuma course din da tafi tsoro.

Dadi ya kamashi yasan dole yau ta nemeshi.

Yana zaune Yana koya masu Helen ta shigo gabansa ya Fadi ganin irin ramar da tayi though Shima ya Dan fada.

Layin da yake Bata kalla ba ta Isa can baya, Damian please help me here ta fada a hankali.....

Ashe bai iya uwar komai ba nan da Nan hankalin Anwar ya tashi ganin ana koya Mata wrong.

Helen ta zungureshi ga fa Bilkisu.....

Eh na ganta, tana fushi dani ne Kinga taje Damian na koya Mata hauka.

Mtsew ya buga tsoki.

Ya kasa ci gaba da koya ma Helen din.

Damian na gamawa tabar class din sai lokacin test ta dawo.

Tana shigowa ta hango sadeeq ta Isa wurin Shi.......

Alhamdulillah dama Ina ta addu'ar kada a riga ni.

Yayi murmushi kawai, tare suka zauna ya Bata ta kwashe hankalin Anwar na kansu kamar zai haukace.

Tana gamawa taje tayi submitting tayi tafiyarta daki Koda Anwar din ya fito bai ganta ba ya Kara hasala.......

Sadeeq na fitowa ya Fara surma mishi Zaki har Yana yunkurin dukansa Wai ya zauna tare da Bilkisu test.......

Tirkashi.

Ayi hakuri da kadan...
.

Zainab wowo ce
Juma@ mubarak don't forget to receive suratul kahfi
*WA ZAI FURTA?*
1
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.

Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
************
*KADUNA RIGASA*
Tun daga bakin gate yake jiyo kamshi, mamaki ya cika Shi, shin ko yayi batan lissafi ne gidan Amira yake ba Ummi ba?

Tana tsaye cikin Riga da skirt na leshi tasha ado ya shigo.

Da gudu ta rungumeshi yaji wani tsammmmmmm......

Anya Ummi ce?

Nan danan ta Fara sabon salo.

Shigowa yayi kawai ya ajiye jaka ya wuce wurin Amira sannan ya dawo Amma inaaaa tuni hankalin ya karkata........

Bayan yayi wanka, ta zauna tana bashi abinci kamar yaron goye tun a daki da ya motsa sai ta bashi hakuri yanzun ma tana bashi abincin tana Kara lallashi duk ya sukukunce ya rikice.

Ya kalleta wallahi Ummi Ina sonki, kawai halayenki ne suka Sanya mun ko kwanto a zuciya Shi.......ta rufe bakin da chokaci ta debo pepp
soup, sorry my love zaka ga changi I promise......

Ai na ga changi wallahi please keep it up.......

Amira Bata Sanya Shi ido ba sai bayan isha'i ta gama kulewa ta Kai karshe.........
**************
*Federal University dutsinma*
Kowa yasan sadeeq baida fitina, murmushi kawai yayi yabarshi a wurin yana babatu.

Sai kawai ya Fara fushi dashi.

Cikin bacin rai sadeeq ya samu Anas, Yana fada mishi abinda Anwar din yayi mishi Kashi na biyu akan Bilkisu.

Yaja guntun tsaki, kayi hakuri sadeeq wallahi *So* ke wahalar dasu duka for now ka bashi time zai nemeka.

Tun daga ranar Bilkisu ta koma sadeeq ke nuna mata, sun kyale Anwar.

Hankalin Anwar yayi matukar tashi ga exams na karatowa, hanya ma idan ta hango shi canzawa takeyi.

Ya rasa inda zai saka ransa.

Ko kallo bai isheta ba.

Idan ta zo school amma tana komawa daki zata ci kukan ta tayi ma'ishi.

Yanzu fa kowa ya fahimci an bata Bilkisu da Anwar.

Tsalle da Murna mufeeda ta ringa yi.

Tana zaune class za'a yi lecture ya shigo.

Yana ganin ta yayi saurin shiga sit din zai zauna kusa da ita......

Sai da ya karaso gaf!

Daman can karshe take sai kawai ta kwashi kayanta ta dora waya a kunne , helllooo....yes inajinki.

Tayi waje kamar me amsa wayar gaske.

Tana fita tayi jimmm sannan ta dawo tare da canza layi ma gaba daya.

Ransa ya baci, hankalin sa ya Kara tashi, kowa ya fahimci abinda tayi.

Sam ta rage fara'a in kaga tana dariya to tare take da Suleiman.

Ana gama lecture ya tsaya bakin kofa yasa hannu duk Wanda zai fita sai ya mishi magana, tana ganin haka ta yi zamanta, Shima ya ayyana a ransa wallahi yau Kam sai dai su kwana haka.

Masu shigowa da masu fita kowa sai ya mishi magana sannan.

Ta dawo gaban sit suna magana da chinyere, tayi sa'a ya juya suna magana da wani dan aji daya da alama bayani yakeyi mishi har ya manta ya saki hannu Yana magana cikin nuni da hannu....tayi wuf, ta wuce ko alama bai lura ba sai da tayi nisa ya waiga class din da sauri ya tabbatar lallai ita ce.........wani mugun tsoki yaja tare da dunkule hannu ya daki bango har yaron ya tsorata.

Cikin tsawa yace yaron ya bace mishi da gani.....

Daki ya tarar da sadeeq nacin abinci.
Chapter 17 · 0% Book details