← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 35

Sashe 22

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya daga kai, idan kin gaji go and submit.....

Bata San ta mishi wata uwar harara ba......shin nashin zata bayar amatsayin tata?

Dukewa yayi Yana Yar dariya yaci gaba da rubutu.

Sit biyu ne tsakanin ta da Suleiman tana son daga mishi na Anwar Amma sunyi nisa.

A hankali aka Fara submitting...... invigilator din nan yazo yayi tsayi tagar kusa da su.

Anwar na gamawa kawai ya Mike yaje yayi submitting yayi signing out ya fice.....

Kaiii Anwar karshe ne.

Ta kasa tashi.

Har sai da akace time out....stop writing, aka bi ana karba......

Ta saki ajiyar zuciya a hankali sannan ta mike taje tayi signing out.

Yana can zaune bisa taga.....

Ya kura ma kofar fitowar ido.

Tare suka jero da Suleiman....

Bilkisu yau Nasha wahala Allah dai ya kyauta.....

Bilkisu kinyi duka ko?

Naga Anwar aka maido miki.....Helen ta dafa kafadarta.

Tayi murmushi eh.

Suleiman yayi karaf, da kyar na amsa question one *b* da question three *a*.

Sai na tafi question 4 na buga mishi kame kame ya Allah kasa ko *e* mu Samu na gaji da carry over wallahi....ai Bata da dadi ta fada tana Mai jajanta mishi.

Wallahi Suleiman *Anwar* dan rigima ne Wai kasan Shi yamun jarabawa yayi submitting Ni kuwa yaban tashi na bayar?

Ya zaro ido ban gane ba.

Ta bashi labari...yayi dariya yace *Hmmm* kawai.

Yana ta kallonsu...ji yakeyi kamar ya je ya Shakure Shi.

Na Miki Barka wallahi Allah ne ya duba Miki.

Wallahi kuwa Alhamdulillah ai jiya na kwana du'a'i wallahi saboda daman na tabbatar Ina ruwa.......

Karaf suka hada ido dashi.

Ya bata rai,....Ina zuwa Bari na karbo wayata wurin Anwar.......

Okay sai gobe Nima zanje waje wani ke jirana.

Ya wuce, saboda yasan ba dawowa zatayi ba dan Yanzu.

Kun gama?

Idan baku gama ba kije gashi can zai tafi.....Anya ba kishin Suleiman Anwar keyi ba?

Ta fada a zuciya.

Shiru kawai tayi.

Baki da lokaci na?

Ta kalleshi, wallahi duk ka sauya Mani, Yanzu Abu kadan sai ka Fara fada kana sako Suleiman, Yana fada mun yanda yasha wahalar exam ne shine fa ka ganmu.......

Bana sonji.

Kina son fada mun cewa kowa baisan Shi din saurayinki bane.?

Zatayi magana ya Mika Mata wayarta, ungo idan daddy ya tambayeki kice wayar ba chargy ta kwana saboda na kasheta b4 ya Kira don't know what to tell him.

Fishi kayi?, Ta ce ba tare da ta karbi wayar ba.

Akan meye zanyi fushi, Ina abinda ya dameni, na Isa in rabaki da Suleiman ne while Nima albarkacin sa nakeci na........ *Anwar*.....

Ta Kira sunan sa.

Ya kalleta,
Wallahi ka canza, bana Jin dadin abubuwan nan har ga Allah.

Magana takeyi kamar me Shirin yin kuka.

Yayi shiru kawai,
Amma kayi hakuri idan na bata maka Rai shikenan ko?

Naji karbi wayar ......

Ta danyi murmushi ta Kai hannu.

Kina Sanya attachment?

Da sauri ta kalleshi, ya kura Mata ido....

Ta sunkuyar da Kai Allah ya sawake ban taba ba......

Gashin ki ne haka?

Haka me?....

Daman ka karbi wayar ne don ka man kwakkwafi kazo ka addabeni da tambaya?

Ya bushe da dariya......

Me yasa anan bakya sa ko gyale bare ki kwatanta saka wando mu gani........

Juyawa tayi ta Fara tafiya, ya dirko da sauri ya bita....Ina zakije?

Yasha gabanta....

Dan Allah kiyi hakuri na daina.

Hmmm, ta ce.

Na ce na daina ko?

Shikenan, bani wayar.

Tafiya zakiyi?

Eh, tace,
Suka jera suna tafiya,
gobe ne last paper kuma morning ana fitowa Zan gudu.........

Nima gobe Zan tafi.

Ta fada mishi.

Haba, Abuja ko sokoto.

Tayi Yar dariya Abuja.....

Shikenan na Sami lift har gida ke zanbi ko?

Ance Kano kike kawa jirgi Yar gayu .........

Tayi Yar dariya.....inji wane magulmacin.?

Ke fada mun Zaki tafi dani na shirya ko.....

Shatar mota zanyi fa ba zuwa akeyi daukana ba.......

Shatar mota?

Eh,
To kawai ki Bari mubi motar gidan su sadeeq idan anzo......Kai nifa bana son rabe rabe.....

Ba damuwa nida sadeeq daya ne kada ki damu we are now family.

Shikenan Zan fadawa mommy yanda tace .......

Ya watsa hannu fine.

Ta harareshi Kai wallahi Anwar din Nan ka fiye yanga kamar mace......

Ya tuntsure da dariya a'a kin manta nine Bilkisu.

Barci kawai kowannen su keji.

Koda suka suka rabu gado kowa yabi lafiya..........

Shako wuyansa yayi suka yi bayan daki.....Kai lafiya ....Wai Anwar kana da hankali kuwa?????

Warning Zan maka wallahi tallahi idan kayi kuskure *you are dead* ya mishi nuni da yanda a wuya.

Da Bilkisu zamu tafi gobe na fada Mata Kai zamubi idan ka saki ka nuna Mata inada alaka da tafiyar you are sorry Dan ubanka.

Zan ma Umar waya in mishi bayanin komai......

Kaji ko?

Naji banza....sakarni toh.

Yayi murmushi.

Good and fine.

Wace karyar ka shirga Mata?

Ya tabe baki wallahi bance Mata komai ba Kuma nasan bazata tambayeni ba.....

To kaja ma Umar kunne wallahi......bai da matsala.

Kuma wannan karon Shi kadai zaizo ba wani security saboda Kai zaka zauna gaba nida Bilkisu a baya ......

Dan ubanka ni oga Kuma a gaba?

Eh, Kai zakayi arranging hakan.......mtsew naji.

Cikin kwanciyar hankali tayi wa mommy bayani.

Tayi Mata nasiha da addu'a , ganin Bata boye Mata hakan ba, (munafunci ga yaro Shi keda ciwo).

Umar yasan dakin su, can ya biya aka Sanya musu kayansu kafin ya karaso cikin makarantar.

Suna fitowa ya tareta Yaya?

Ta ce ta shirya.

Haka suka biya ta dauki jakar ta suka wuce.

Sadeeq ne oga ya kame a gaba.

Shida ita baya.....

Ya kalleta.

Kinga WhatsApp????

Tayi murmushi eh,
Zamu ringa chatting kinji?

Toh,
Ko Baki da time?

Me zai hana......

Good, ya fada.

Kinyi break?
....tambayo.

Ta fada a zuci.

A zahiri tace Nasha tea.

Tea?

Umar akwai abinci motar nan?

Eh, yalla.......

Yayi saurin datse maganar ya canza da cewa, Yana daga Nan baya.....

Sadeeq ya juyo Kai bana son hauka abincin nawa zaka cinye?

Bilkisu zata ci ko zaka Mata rowa ne......Ni na koshi ma ta fada tana Yar dariya.......

Au Bilkisu waa nakeyi I tot koshine keson ci.

Ya yunkura ya dauko cooler sadeeq ya Miko mishi spoons biyu, yabude.....kamshi ya buge motar...

Gasassun kaji ne da soyayyen dankali da kwai.

Ya kalleta kici ....

Tayi murmushi.....na gode.

Wani kallo yayi Mata....bakici?

Ta tabe baki Alhamdulillah.

Ya daga kafada, kufa wadannan an Saba haduwa ko?

Wurin mu ne sabbin zuwa ya waxgi kaza ya Fara ci.

A hankali a hankali yaci ya koshi tana kallonsa ........Kai namiji baida kunya ita Ina zata iya Shan ko ruwa a nan?.

Ya Mika ma sadeeq ungo......

Miko mun maltina Mai sanyi gaban ban......Ashe Yar cooler ce ta ruwan sanyi dankare da lemuka .......

Ya kalleta me zai Miko Miki?

Ta girgiza Kai na koshi......

Ke kuwa Dan Allah hajiya Kisha ko Mai sanyin ne.......Kyaleta umar tana tsoron kada mu saka Mata baliyan.......

Ta zaro ido....yasha mur...... sadeeq bani maltinar Nima......

Ungo wannan Kisha Ni ta isheni. .....ya Miko mata tasa.

Kurba biyu tayi da kyar, ya tsareta da ido.....ko kadan baijin kunya ko nauyin kallonta, taci gaba da rikon ta.........tana jujjuyawa.
.........

Kina tunanin Suleiman ne?...

Wohohoho Kai kuwa a Rana sau nawa kake ambaton Suleiman a rayuwar ka Wai meye ya tsare maka?.

Inba tunanin sa kikeyi ba Kisha.....na koshi ne kaima ka kasa shanyewa bare Ni?

Kuna da Yan uwa a Kano?

Um, um....

Ni ban ma taba zuwa Kano ba sai ta dalilin karatun nan.

Da gaske?

Allah kuwa.....

Kai Dan asalain Kano ne?

Yayi murmushi ciki da bai kuwa.....ya bangan ka da tsagen kanawa ba?

Yayi Yar dariya, daga kaina aka daina gidan mu kinsan nine auta gidan mu muna da yawa.....

Ya sunan anguwar ku?.

Keda Baki San Kano ba Ina ruwan ki da sunan anguwar mu kuma?.

Eh, Ina son sani.

Yayi Yar dariya ni ba cikin garin Kano nake ba kauyen Kano karkashin karamar hukumar *Rano* kin San wani gari *Dagama*?

Nope, ta fada.

Yayi Yar dariya.

Suna shiga Kano ya ce a tsaya ya sauka.

Ya Dan fita can gefen hanya.....ya Kira Alhaji Mubarak a airport.

Hello an Gama komai?

Ya rusuna, angama Allah Shi taimakeka.

Yawwah.

Ya shigo motar da sauri, Umar airport muje Airport da sauri please.......

Ta kalleshi zakewa?????

Shi Dan karo sai instruction yake badawa tun dazun.

Tun daga bakin gate ake Basu girma.

Ko kadan Bata kawo wani Abu a ranta ba.

Ya tokare bakin kofa zan koma mota, sadeeq sune Yan gari zasu raka ki har ciki......

Toh, na gode sai munyi.

Sai Yan waige waige kamar marar gaskiya......zamuyi chat kinji?

Tayi murmushi ba damuwa.......

Manyan mutane biyu ta gani sun zube gabansa Allah Shi taimakeka Barka da sauka.........

Ya zaro ido ita Kuma tabi fuskar sa da kallo........

Alawiyya ma na gefe...
*ZAINAB WOWO*
*WA ZAI FURTA?*
1
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.

Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*For Gaje Abu*
Alaweez
Ana mugun tare.
*Ya Allah ka Kara Mana katangar karfe da masu bakinciki damu* *Hassada ga Mai rabo taki ce duk Wanda Allah ya tarfa ma garinsa nono wallahi ko ana mazuru ana shaho sai yasha* masoyana ga taku
***************
*KADUNA RIGASA*
Tayi zaune falon suna labari da hajiya bayan ta sako doguwar hijab.

Ta kawo Mata lemu da naman kaji......gidan Alhaji shamsu naje shine na biyo ni in ganku tunda Shi ya kwammace yayi ta kullenku da ya barku zumunci.

Murmushi tayi kawai.

Ya kuke ba wata damuwa dai ko?

Babu damuwa, ta mike tsaye bari na Kira ummin ku gaisa.

Da gasken gaske hankalinsa ya tashi sha"'awar Amira ta addabeshi.

Da farko yaji haushin kwalelen da ta mishi amma da ya tuna haramcin yin haka saboda ya shiga hakkin Ummi, sai ya bata uxuri.

Ya shiga toilet dinta yasa ruwan zafi ya warwatsa a jiki saboda ya Sami sauki, sannan ya fito.

Zaune suka tarar dashi suna labari da hajiar, ya kasa dauke idonsa daga Amirar duk inda tayi idanun sa na kanta har Ummi ta Shaka.

Koda suka raka hajiyar Sashen Amirar ya koma.

Ya riko kugunta wallahi gobe sai kin gane kurenki......
Chapter 22 · 0% Book details