← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 35

Sashe 8

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk sukayi shiru.......Amira ya muku?

Ta dago Kai umm hakan yayi ko Ummi?

Ta Dan yatsina fuska ..um.

Da kyau!

Maganar abinci Kuma duk Mai aiki ita zatayi abinci, Ummi tsarina a gidan Nan ko Ina Nan ko bana Nan karfe Sha biyun Rana ya zamanto kin Gama abinci saboda Yara da masu gadi da Kuma sauran mutanen gidan.

Bana son kwauron abinci a ringa dafawa a wadace, tun daga safe har dare.

Amira zata Miki bayanin quantity din idan Kun zauna.

Ba wacce zanbi dakin ta lokacin kwananta duk ranar aikinki Zaki sameni sashena ban yarda da raba kwana ba Koda munyi fadan soke soken wuka.....

Ya kalli Ummi wannan shine tsarina.

Duk wacce nayi ma laifi kafin ta tsiri yin fushi dani ta Fara sanar Dani idan har nayi bisa kuskure Zan bata hakuri, idan Kuma akasin haka Zan Fadi dalilina.

Duk Mai bukatar abu ta tambayeni Kai tsaye domin nine mijinku, idan anzo muku da magana akaina ku Fara sanar dani da Kuma Wanda ya kawo maganar ku fadan wanene.

Idan cikin ku wata keson haddasa fitina ta kawo muku gulmar daya to ku tsaidata ku kirawo wacce ake maganar kusanya ta maimaita a gabanta zakuyi maganin munafukai.

Ina fatan duk kun gane?

Wacce keda magana tayi.....duk sukayi shiru.

Ya Mike Ummi jeki Ina zuwa......kamar jira takeyi ta Mike.

Ya Mika wa Amira leda uwargida ga taki kazar.......wayar say tayi Kara ya ganka a kunne hello........na'am hajiya.....Nan ta fahimci mahaifiyarsa ce.

Ya yahuto ta da hannu alamar tazo ta rufe kofa zai fita Yana ci gaba da tafiya.

Yana fita ya Sha kwana ya latse wayar daman fakaitar idon ta yayi ya latso wakar saboda Shi baisan yanda zai mata bankwana ba. ( Namiji?.....)
Tana rufe kofar ta duke a wurin tafara kuka na ban tausayi....( Kishi kumallon mata.....)
Ina bada hakuri Dan Allah.......
*zainab wowo ku muku fatan alkhairi*......
*WA ZAI FURTA?*
0
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.

Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Kinfi Alawiyya farin jini unex ta hannun damata ( Hussaina Nasir )* Allah yabar kauna. *Alawiyya*
*Federal University dutsinma*
Tun lokacin da Bilkisu ta siya ma Anwar break abun ya mishi tsaye cikin Rai saboda karon farko daya taba karbar kyauta daga hannun wani ko wata bayan iyayen sa.

Wasu mutanen basa raina alheri ko kadan hakan yasa Anwar yaji Bilkisu ta shiga ransa farat daya ba don Yana sonta ba ko makamancin hakan sai dai lura da yanayin takun yarinyar, Bata da Jaye Jaye kuma baya tunanin zatayi yawan surutu.

Ita kuwa tuni ta fitar da abun a ranta saboda bata dauki hakan da tayi da wani girma ba, kawai she feel like making him happy kamar yanda ita ma ta kasance cikin Jin dadin bayar da lokacin sa gareta ya koya mata karatu .

Ya kasa sukuni ganin lokacin yakeyi baya gudu duk wadanda keson Karin bayani ya Basu hakuri sai zuwa dare, yanayi Yana duba agogo da Kuma wayar sa Koda zata Kira, me yasa ni ban karbi wayar tata ba?

Mtsew yaja guntun tsaki, uku na bugawa ya kasa hakura kawai yayi wanka ya shirya cikin kananan Kaya gayu yayi sosai, uku da ashirin ya Isa makaranta, anata Kiran sallar la'asar hakan yasa Shi wucewa masallaci.

Lokacin da aka fito sallah uku da hamsin, ya kura ma wayar sa ido kamar ya rotsata da kasa, shin Wai bazata kirani ba?

Bummmmm......ta fada daga bayansa alamar tana son bashi tsoro.

Ya tuntsure da dariya lokaci guda Kuma zuciyar sa ta mishi sanyi, Ni Zaki ba tsoro?

Ko kin dauka kowa irin ki ne matsoraciya?

Tayi murmushi kawai, Yanzu na fito masallaci Ina Shirin kiranka na hango ka........

Ba wani baki da niyyar kirana tun yaushe Kika karbi wayar ba sai ki yi mun ko flashing bane don Nima nayi saving taki?

Suka jera suna tafiya,
No need....kawai na barta ne sai lokacin da Zan Kira.

Bana daukar wayar da bansan no.

Ba so better call me to save yeye.

Ta kyalkyace da dariya yabi fararen hakoranta da kallo.......Ni ce yeye?

Ya mata banza kawai.

Karo sukayi da Dr Dan Musa akan hanya, ta gaida Shi Anwar kuwa ko kallo ya wuce abinsa, ya bishi da kallo cikin bacin Rai laifi biyu gashi suna tare da Bilkisu sannan Kuma gashi baya gaida Shi kusan sau hudu kenan suna haduwa Anwar din na watsin kasa kasa dashi, don akwai lokacin ma da suka hasu banki Anwar din ya kalleshi ya watsar ba tare da ya gaida Shi ba.

Ya kuta cikin Rai zaka ci ubanka, ya kalli Bilkisu sai Ina Kuma haka kuna da evening lecture ne?

A'a zamuje karatu ne Anwar zai mun bayani.

Wanene Anwar?

Ya bukata, Hamza Yusuf wancen ta nuna Shi da yatsa Yana tsaye gaba kadan Yana ta faman latsa waya da alama ita yake jira, Au wancen Dan iskan yaron Mai girman Kai Wanda ya Raina mutane?

Ta zaro ido......raini Kuma sir?

Ya harareta kawai ya wuce abinsa yabarta tsaye.

Ta bishi da kallo tana mamakin me ya hada Shi da Anwar din domin tasan Shi mugu ne ana kuka dashi a department.

Me ya hada ka da Dr Dan Musa?

Ta karasa inda yake tsaye da sauri.

Ya kalleta cike da mamaki.

What the hell are you talking about.

Meye zai hadani dashi kuwa inba Yanzu da ya ganmu tare ba.......kada ka mishi fassara, yace ka Raina mutane and this is the second time I hard about something like this a bakin lecturer.

Me yasa baka gaida Shi ba Yanzu Kuma kaji na gaida......saboda baya gaba na.

Malama stop interrogating me about those idiots...... idiot?

Anwar kanka lafiya kuwa?

Bai tanka mata ba har suka zauna wani class.

Ki fiddo littafin da zamuyi.

Bazan fiddo ba ....me yasa malamai ke cewa ka Raina mutane Kai kowa ma daukar ka yakeyi ka Raina kowa......Amma ai ke kinsan ban Raina ki ba ko?

Hasali ma tsoron ki nakeyi to meye zai dameki?

Ya karasa maganar Yana Yar dariya .

Ba wani... ai su malaman ka.....

Bilkisu me yasa kike kirkiro unnecessary problem ki dorawa kanki?

Meye abin dagewa anan Wai?

Sun Dade basu kirani da Dan rainin hankali ba so what?.......sai suyi maka mugunta a result,
Basa iyawa ki daina damuwa......

An Gaya ma na damu ne?

Kai ba a Isa a fada ma kana kuskure ba ka gyara.?

Ta dunga balbala mishi masifa.

Hannunsa duka biyu ya goya a kirji tare da tsareta da ido Yana mamakin.

Meye abin hakikancewa anan?

Ita meye nata aciki?

Wai me yasa take kokarin shiga harkarsa ne ma?

Ya sha mur Yanzu kin kirani anan ne don ki nemi rigima ko kuwa karatu zamuyi?

Cos I'm tired of it already.

Ya janyo littafin dake gabanta bari mu Fara ...........

Gab da magariba suka gama, tare suka taho yana ta binta, har suka karaso kwanar gidan ta, lokacin ne ta kalleshi zaka bini ne?

Ashe kin gane , ya fada Yana murmushi....

Tabbb da ka ci na jaki kuwa muyi maka ihu Kato.

Wannan karon dariya yakeyi sosai nine katon?

Eh Mana namiji a gidan mata.

Kin San ma'anar katoa hausa kuwa?

Ta kalleshi eh Mana gashi na fada kato namiji kamar Kai......barawo ake ce ma Kato fa ni barawo ne?

Kai Ni dai bance ba kada kamun fassara.

Test din gobe ina bayanka please.

Da gaske kike?

Allah kuwa......

Okay ba damuwa.

Kiyi man flashing nayi saving no.

Ki Mana.

Zan kiraka anjima kada ka damu ai na ce Zan karanta abinda mukayi inda na manta Zan maka waya ka tuna?

Ke ban yarda ba kirani Yanzu.

Allah Zan kiraka kaji na rantse.

Sai da safe gashi can an Fara Kiran sallah.

Kina korata ne?

Me yasa like zaune a off campus bakya son hostel?

Hakanan Ina da kyankyamin toilet maganar gaskiya Kuma Ina son privacy in ma life.

Kai me yasa kake son zaman hostel?

Kar na Zama Dan iska Shi yasa a off campus mata zasu dameni Yanzu ma Yana iya......harara ta balla mishi sannan ta buga tsoki kaji dasu can, sai da safe..............

Bilkisu....

Bilkisu...

Bilkisu.....

Amma inaaaa tayi shigewar ta gida ta kyalesa.

Yayi murmushi yarinyar rigimammiya ce wallahi.

Kut!

Wai ni Anwar yau mace tayi wa tsoki banji haushi ba shin Wai wanna yarinyar wacece ita?
**************
*KADUNA RIGASA*
Tunda suka Fara raba kwana matsaloli suka Fara kunno Kai daga bangaren Ummi, duk ranar girkin ta sai ta Mila tasha iska take data abinci wani lokacin sai dai Amirar ta dafa ma Yara indomie ko su Sha oat ko wani simple food, tun abun baya damun Amira har ta Fara Jin Yan aikin gidan kansu sun Fara korafi.

Gashi baya nan yayi tafiya.

Ranar da ya dawo kuwa akayi sa'a dakin amaryar yake.

Bayan sallar isha'i Yara sunyi barci ta sameshi acan.

Yana kishingide bisa kujera ita Kuma tana saman kafet tana chatting......dukkan su ta kalla sannan ta watsar.

Ya Dan zabura Amira yau kece anan?

Lafiya dai ko?

Domin bai taba ganin ta sashen ba idan Yana nan wata kila ko tana zuwa sai idan baya nan ne.

Zuwa nayi in tambayeshi ka, Kaine ka Sanya matar ka ta ringa yin abinda taga dama gidan nan?

Ya zaro ido Ni?

Me tayi?

Ta zaburo Au karata.....ya daka mata tsawa idan Kika Kara magana bakin auren ki wallahi kada ki dauki mutane Yan iska ke gidan ku ba manya ne?

Abinda kikeyin mun daga ni sai ke Ina shanyewa idan Kika ce zakiyi gaban jama'a kece Masha wuya.

Amira me ya faru?

Zo ki zauna.....

Ba Zama ya kawo ni ba.

Ina so in sani cewa Kaine ka ce matar ka ta ringa Mana horon yunwa a gidan nan?

Daman ka sanya doka ne na Mai miji tayi girki don ka fifita daya?

Tun zuwan Ummi gidannan a duk lokacin da aka ce kasa kafa kayi tafiya to mu da abinci sai taga dama Yara har sai sun Fara kuka sai dai a nema masu wani abun.
Chapter 8 · 0% Book details