← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 35

Sashe 24

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baya jin turanci ko kadan ya figi hannun sa kazo mu je ka tukani in tuka ka kowa ya Rama ma kowa sannan in tafi......

Sai kawai Anwar din ya bushe da dariya....Ni yau na hadu da matsala.

Hajiya ta Sanya musu ido kawai da tsiya ya fidda Anwar din.....

Ta kalli labaran da ya kawo keken.....yaron can dole ya Zama abokin Anwar saboda zasuyi dai dai........

Shi yasa na tsani karatun kasar waje Ina so yayi anan yasan duniya.......

Arziki irin na yaron nan Yanzu Yana da hadari a gareshi.......

Hayaniyarsu take jiyowa suna ta wasa.

Da abu yayi dadi a mota aka Kai sadeeq har gida da sabon keken sa da ma tsohon Basu da nisa sosai.

Mahaifansa sukayi ta godiya, tun daga ranar kullum sadeeq sai yaje gidan su Anwar wasa su hau Keke, shillo kamar kananan Yara.

Shakuwarsu yasa Anwar din kawai yace a maida su school daya suka dauki nauyin karatun sa.

Abin mamaki tun a lokacin sai Anwar din ya ringa mishi kandakun kada yaje Yana bada labarin gidan su.

Aka ba iyayen sadeeq jari Mai tsoka Banda taimako da zakka sannan hatta Kaya sutura Anwar ke ba sadeeq tun Yana bashi kwance har ta Kai Shima nashi ake siya mishi.

Suna girma Anwar na Kara miskilanci sadeeq Kuma na Kara lakantar sa ciki da bai.

Yana ss 2 ragamar dukiyar sa kaf!

Ta dawo mishi mafi karfin kasuwancin yafi karfe a *Dubai* sai ya kasance da anyi hutu yake tafiya sadeeq Kuma ya tsaya Nan Yana wasu ayyukan.

Ko kadan Anwar baida fahari.

Ko a Dubai yasha Kira cikin yaransa yayi acting as shine Anwar din wajen wata Hulda idan tazo.
......

Babu kasar da baya zuwa da sunan kasuwanci.

Shi yasa da jarabawa ta fito ya cike Nigeria jihar katsina Kuma, don ya na son surveying area din ciki da bai, saboda suna da karancin kasuwa a katsina matuka......

Jiragen sa shidda sannan ya na da share a Abu Dhabi airlines suna bayar da hayar jiragen su.

Anwar hamshakin Mai kudi ne Amma duk duniya ba abinda ke birgeshi irin ya boye Identity dinsa Yana acting as normal person hakan na saka Shi nishadi Shi yasa karatu kasar waje bai taba birgeshi ba yafi so yayi cikin normal mutane cewarsa masu kudi naturally suna da wani abnormality Wanda basu fiye sanin hakan ba........

Duk wani taimako da ake bayarwa makarantar fudma daga miliyan daya zuwa sama Anwar ne ba tare da an sani ba.

Yana da tausayin talaka, Abdul Mai shop yasan Anwar masu kudi ne saboda kyautar da yakeyi mishi na ya Kara jari Kuma ya mishi mugun kashedi Koda wasa kada ya fadawa kowa.

Yana da gadara haka ya tashi fil azal............
*wannan kenan*
Falon cike da mutane ya shigo duk suka Mike Allah Shi taimakeka.......

Wayarsa tayi Kara , *Bilkisu ce* da sauri ya daga Ranki ya Dade Kun sauka?

Um, gashi ma har na Kama hanyar gida....good nima shigata gida kenan mun biyata gidan su sadeeq....Ayyah, ka Kara mun godiya ga sadeeq Allah ya Kara arziki.....Baki da matsala.

Zamuyi waya Anjima please.

Okay bye....ta latse wayar.

Ya kalli Alhaji murtala.......

Yallabai yau ka dawo ne?

Ya rusuna Allah ya Kara ma daraja eh wallahi.

Yayi Yar dariya Dan Allah idan Kun ganni da jama'a ku daina irin haka bana so Kun San haka, za a ringa kallona bani da tarbiyya matukar Ina tsawatawa Kuma tabbas bana Jin dadin hakan......kuskure ne ayi hakuri in shaa Allah......

Ina takardun jirgin da ake gyara Jidda??

Ya Mika mishi file gashi.............

Sai karfe shidda da Rabi ya shiga ciki.

Tana zaune bisa abun sallah ya shigo........

Yaro da akidar manya....tsohuwar ta fada.

Yayi dariya hajiya tuwo zanci akwai ko?

Eh, ........

Ya Mike a hada mun kafin na watso ruwa na gaji yau Zaki Sha labari.....

Tana kwance bisa kafar mommy falo kiransa ya shigo......ta daga hello Anwar.

Ranki ya Dade......ya gajiya?

Ba gajiya yasu mamah?, Ya danyi jimmm, kafin yace Hajiya lafiyarta kalau,
Ohhh, hajiya yake Kiran mamansa?

Yasu mommy ya katseta.

Ga mommy nan kusa dani...Ina gaisheta please.

Tana amsawa.

To meye labari?

Labari na wurinka ni na iya labari ne?.....mommy ta zameta tare da mikewa...

Ki koya Mana sai ki bani.

Me yasa gidanku babu hayaniya ko yaran sunyi barci?

Auwal da musbah ne suna can dakin su.

Ke Kuma kina makale da mommy ko?....

Tayi Yar dariya ai ta tashi ma ta shiga ciki.

Ya Kano din?

Kauyen Kano dai? gamu ciki ya fada Yana dariya.

Ta ce hmm.

Zan Fara fita kasuwa gobe kin San talaka baya Zama......kana kasuwanci ne?

Eh, Ina bin wani ubangidana Ina mishi tsaron shago cikin sabon gari a garin Kano......kin San kasuwar sabon gari?

Naji dai ana fada.

Okay toh can.

Tausayin sa ya kamata.......rashi bai hanashi gadara da izzah ba, Mai Hali baya barin halinsa....kinyi shiru.

To Allah ya bada sa'a ka samo kudi da yawa Wanda zamuci biscuits next semester....ya kyalkyace da dariya ni Zan siya Miki?

Kwarai kuwa a rama wa kura aniyarta nima sai na ci kudin ka next semester.....hahahaha ya Kama dariya.

Naji Zan dage na samo da yawa.

Ke me Zaki kawo mun tsaraba?

Abinda kake so,
A'a kawai ki dai kawo man ko menene.

Hmmm, tace.

Ko bazan samu ba?

Zaka samu in shaa Allah.

To me Zaki kawon?

Ka fada Mana me kake so?

A a bani da zabi.

To shikenan ka jira zaka gani.

Na gode.

In kyaleki haka ko?

Okay gudnight ta kashe kawai.......

Ya doka tsoki jira takeyi ne?

Yarinyar nan tafini
gadara wallahi.

Washe gari bai Sami kansa ba ko kadan, abubuwa sun taso, ba shiri karfe shidda ya bar kasar......

Yanayin abubuwan sai da ya kwana biyu bai samu yayi magana da Bilkisu ba.

Ta nemeshi a waya har ta gaji.

Da ta Kira sai a Fara nata faransanci Ashe France ya tafi ya Kuma chanza layi.

A Rana ta biyu ana ta meeting a katon office din sa Kira ya shigo through WhatsApp ya kalli turawanya ce kowa yayi shiru,
Ya daga...

Hello Bilkisu....

Duk kasuwar ce wayar ka Bata shiga?

Ina Kira sai wani yare ko ka Sanya Ni voice mail ne?.....

Voice mail Kuma ?

Yayi dariya kiyi hakuri wasu kayukane muke shiga Saro tattasai Kuma ba service wurin kiyi hakuri muna lissafi da Mai gida anjima zamuyi chatting......

Hakan kuwa akayi tun Sha daya suke chatting har kusan biyun dare.

Amma ita dashi lokutan sun banbanta.....

Daga ranar kuma bai Kara samun lokaci sunyi magana ba.

Fushi tayi Bata nemeshi ba, Suleiman kuwa duk bayan kwana biyu sai ya nemeta sun gaisa.

Ranar da zai baro France aka mishi waya zasuyi meeting Abuja da managers din, *Next, ShopRite da Sahad*
Dole sukayi landing Abuja.

Motoci shidda kebin bayan tasa biyu na gaba.

Saboda tafe yake da nashi mutanen.

Ko a cikin motar waya kawai akeyi.

Bayan an gama meeting din suka zagaya ta kofar shiga ShopRite wurin ice cream security sai kyarma sukeyi yau ga Anwar......

An cunkushe kofar an tsaida masu shiga.

Ya Kira Angelina suna magana.........Ai sai ku bamu wuri mu wuce ko?

Da sauri ya waigo *Bilkisu ce* rike da iyayen ledoji..........
*Ayi hakuri a hankali za a ji yanda labarin ya ke da yanda zai Kare* Banda sauri please mubi komai a hankali.

Zainab wowo ce
*WA ZAI FURTA?*
1
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.

Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*****************
*ABUJA NIGERIA*
........

Ya juya da sauri ya kalli Anjelina Yana magana kasa kasa.....

Jeki ce su bude kofa ta fita da sauri...

Ta rike kugu tana ta faman masifar su bude kofa zata wuce.

Ya juya a hankali, yana kallonta ta wutsiyar ido.

Matsattsar doguwar Riga light pink ta saka da Dan karamin gyale fari iya wuya, kafarta cikin dogayen takalmi....

Anjelina na fada musu sukayi saurin bude Mata.....

Ta bude baki iyyehhh ikon Allah yau Allah ya kawo mu ShopRite shiga da izini fita haka..... mtseww ta buga tsoki ta wuce.....

Ya tuntsure da dariya....yarinyar can wata Rana sai ta janyo mun rigimar da za a daureta.

Ya fito a hankali Yana leke duk aka bishi da ido..... yallabai lafiya?

Yayi murmushi Ina zuwa ya fita da sauri.

Tana faman zuba kayan bayan mota.

Ya fiddo waya da sauri ya kirata, ya lafe bayan wata mota.

Ta zumburo Baki kafin ta dauka alamar tayi fushi ya kyalkyace da dariya Yana hangenta.

Sai yau ka tuna dani?

Allah ya Baki hakuri ayyukan ne sunyi yawa Kuma kinsan kauye service din waya sai a hankali... always excuses mtseew.

Yayi murmushi kiyi hakuri ai Yanzu na dawo gari Daman wasu Kaya ne muka siyo......

Naji dan kasuwa, Ina wuni......ta fada tana kokarin shiga mota ya musu nuni da hannu, alamar motar can zasu bi.

Ya manta ma da abinda ya kawo Shi,ya Abuja kina Jin dadin ki fa.

Hmmm kawai tace.

A hankali Yana janta da labari suna bin su a baya har suka je gwarunfa a road *111* gidan yake flat 4 Nan ne gidan su Bilkisu.....

Next week fa za a koma school nasanka da Kara kwanaki wannan semester din ka Kara Alalh sai munyi fada......

Amma dai ba ranar da aka koman Zan dawo ba ko?

Na Kara ko sati biyu.....daya dai wallahi Nima ranar Zan dawo......

Ya kyalkyace da dariya Hajiya kice kawai kina neman lift Kuma matsalar ba tare da Sadeeq nake dawowa ba Mai rabo ni har na gayyaci wasu.....mtsew a a ka manta... shikenan kayi zamanka....ta ajiye wayar daidai lokacin da motar ke kutsa Kai cikin gate din gidan.

Ikon Allah har taji haushi?......

Kamar yaje gidan yakeji Amma baya so yayi hakan Yanzu.

Komin dare yake son komawa kano, haka suka juya Yana waigen gidan.

Bai kirata ba, ya Bari sai zuwa anjima........

Suka kura ma jaridar ido, daddy yayi murmushi ai yaron nan ne wallahi.

Na fada Miki kinki yarda Amma Bari Bilkisun ta dawo muji cikakken sunan sa a bakinta Amma tabbas prof.
Chapter 24 · 0% Book details