← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 35

Sashe 4

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa sai kallonta yakeyi Yana mamakin yanda zata bayar da wuri haka, Wasu na tunanin kawai ta gaji ne da zama kamar yanda Suma suke zaune, tafi mintuna talatin kafin wasu tsirara suka Fara fitowa duk Wanda ya fito idanu jawur ana tsinar malamin kusan kowa ya sadakas da kawai faduwa zaiyi course din saboda rashin iya amsawa.

Suleiman kawai take jira ya fito sai kuwa gashi Yana ganinta yace, Bilkisuuu.....

Yau naji wuta wallahi Allah dai ya kyauta Amma question biyu kawai nake da tabbaci cikin sauran.

Tabbb....wallahi ni Allah ya taimakeni Anwar ya bani duka Wanda ban sani ba....hada question one?

Eh Mana.

Wai da gaske kike?

Wallahi kuwa.

To Ina Jin keda shine kawai kuka amsa ta don ko su chinyere gasu can suna cewa Basu gane ba.......Allah dai ya kyauta ta fada tare da cewa sai gobe ta ruga hango Anwar yayi hanyar *Gate* Yana ta faman sauri.

Anwar.. ta kwada mishi Kira, yasan za a rina Shi yasa yaso ma kada su hadu.

Ya Dan tsaya Yana murmushi , ya jarabawar Bilkisu ya fada Yana latsa waya.

Hmmm jarabawa yau Allah ya rufa man asiri bacin Kai ai Dana shiga uku.

Na gode na gode Allah ya Kara ilimi......Daman ka iya course din sosai haka?

Naga yanda ake ta kuka dashi Kai komai ka amsa.....hatta jamilu ma naga naka yake kwafa ( copying ).

Murmushi kawai yayi yace ba damuwa.

Ya wuce kawai.

Ta bishi da ido.

Anwar...ta Kara kwada mishi Kira.....ya juyo wallahi na gode kaji?

Sai kawai ya kyalkyace da dariya ya juya abinsa.

Taji dadi sosai da sosai a Ranar domin course din kadai kowa ke kuka dashi wannan semester din.

Hutun ya kasance dogo akalle ankwashe watanni biyu a gida kafin a dawo aji biyu.( Su Bilkisu an Fara manyanta ) wannan karon suna gida result ya fita inda take da 4.22 ta Dan sauko kadan saboda ansha wahala matuka Shi Kuma Suleiman Yana da 2.72 Amma ya Sami carry over daya.

Sun koma da makaranta da sati biyu akayi *convocation* tare da bayar da kyaututta ga first class da over all.

Bata halarci wurin ba.

Saboda ba kowa ya maida hankali ga taron ba.

Hakan yasa Anwar zuwa tare da karbar five pointer award da Kuma overall student na aji daya da suka gama.

Kamar munafuki ya karba sim sim sim yayi saurin barin hall din ganin babu alamun Yan ajin su ko wani Wanda ya sanshi.

Ashe Suleiman yana wurin.

Ba karamin mamaki yayi ba watan Anwar shine *Hamza Yusuf* din da ake nema cikin class Amma wallahi sai ya fadawa Bilkisu.................
*************
*KADUNA RIGASA*
Yana ta mamakin yanda ummi ta mishi text tana son ganin sa alhalin bata taba hakan ba.

Yana zaune babban falon gidan nasu an cika gaban sa da kayan ciye ciye da lemuka kamar kullum ta shigo tana ta faman Bata rai .

Ya kalleta tana ta faman karairaye karairaye......Amarya bakya laifi ko kin kashe Ahmad ( Babban yaron sa ) ya fada cikin zolaya Yana Yar dariya hannun sa rike da samosa mutumen shi Yana ci.

Banga alama ba, ta fada tana taunar cingam.

Ya kalleta jin maganar ta fito gatsal....

Kamar Yaya?, Ya bukata.

Kamar yanda kaji.

Kamar yanda naji?

Ya maimaita cike da mamaki kafin ya ajiye guntun samosan bisa plate ya tattara hankalin sa duka wurin ta.....me ke faruwa ne ummi?

Tayi shiru!

Dake nake magana...me ya faru?

Ta gyara Zama, Ina ce apartment din da kayi sabo Ni ka gina mawa Amma labari yazo cewa Aunty Amira ta koma.......

Ke ya daka mata tsawa.

Nan da nan ya harzuka, Ni na fada Miki Ina Miki gini?

Gabanta y
a fadi tayi tsuru tsuru, kinji?

Munyi dake Ina Miki gini?

Okay ita da Zaki aure Mata miji Bata kawo mun matsala ba sai kece Zaki fara kawo mun tsirfa?

Saurara da kyau ya Mike tsaye Yana nuna ta yatsa wallahi matukar kina son Zama dani tare da Jin dadi sai kin daratta Amira kin mun biyayya kin Mata bazan dauki sakarci ko kadan ba.

Dukkan ku Ina sonku to dole kowace tabi ra'ayi na, idan Kika saki na gane kina da matsala to wallahi zakiji ba dadi.

Mtsew ya buga tsaki ya wuce.......ta yi zuruuuuu tana zare ido lallai ta gwada Bata ji dadi ba.

Kwallah suka zubo Mata.

Ta buga ma babbar yayar su waya domin ita ce abokiyar shawarar ta .....salati ta kamayi ubanwa ya aike ki?

Ai kinyi sauri bari zakiyi sai kinje gidan yasan dadin ki lokacin yazo hannu tukun Amma Yanzu ai lallaba matar sa yakeyi tunda ya Mata laifi.

Ki bari Zan baki ahawarwari idan na shigo gobe.

Tun daga ranar Bata Kara Sanya Shi a ido ba.

Tuni a Mata hudubar kada ta saki ta dauki raini ga matar sa Kuma idan ta a gidan ta Sami damar juya Shi yanda zata amshe ragamar komai.

Babu yanda ba a yi dashi ba ko kamu ayi yace bai son bidi'a ba Dan komai ba kada ma akirkiri partyn Amira taji ba dadi.

Ranar walima akayi mashi Sha Tara ta arziki hada mota.

Yana falon sa zaune yaji marokiya na sanarwa.

Shima ya Mike ya kirawo marokiyar ya bada makullin mota kirar *GLK* baka 2019 model ta kusan miliyan Tara yace yaba Amira ayi sanarwa.

Nan dangin Amarya kuwa suka Fara surutai............

Ko ajikin sa.

Dangin ango dana Amirai kuwa suka Fara rangada guda suna tayata Murna.

Hakan ba karamin harzuka Amarya da danginta yayi ba.

Nan suka Kara hure Mata kunnen wallahi sai ta tashi tsaye Dan kwato ma kanta yanci.

Kuka takeyi wuiwui.

Kafin karfe shida gida ba kowa duk an tafi.

Ana gama sallar isha'i ya ja Amarya zuwa sashen Amira don yi masu huduba.......
*Ayi hakuri da typing error please yanayin typing din ne saboda kawai ta WhatsApp nake yi Kuma gaskiya bana bi idan na Gama kawai nake turawa.
*Daga zainab wowo*
WA ZAI FURTA??
0
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( maman Ibrahim) Allah ya shirya Miki zuri'a ya Kara arziki*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD KO DA YAUSHE*
*DOMIN KU AUREN FARI FANS ANA MUGUN TARE*
*Federal University dutsinma*
Semester tayi nisa komai yayi zafi har Yanzu Bilkisu bata Sami sakewa ba, karatun Yana mata mugun wahala, ahankali take bin su chinyere suna nuna mata abubuwa duk Wanda ta fahimci Yana da kokari zataje don Kara fahimtar abinda ya shige mata.

Su Anwar sune Yan baya ga komai, ya biye wa mashiririta yaki nuna ma kowa Shi din Mai kokari ne, masu karyar suna da kokari sai ya kwantar da kanshi Yana Jin yanda suke kwabar bayani musamman idan akazo gun lissafi.

Hankalin sa a kwance duk C.A din da akayi shine overall, Yana amsa sunan Anwar a zahiri ba Wanda yasan Shi da Hamza Yusuf a badini.

Fahimtar halin Bilkisu na rashin girman Kai yasa Shi suke gaisawa da ita sama-sama Yana son kulla mu'amula da ita Amma Yana ganin hakan a gareshi zai zubda mishi aji.

Ita kuwa a gareta Sam bai ma gabanta ko kadan idan an hadu a gaisa idan ba a hadu ba Bata ko tunanin sa.

Shine ma sau da yawa take Dan takura tunanin sa kadan kadan.

Ta Dan Fara sakewa da su chinyere saboda ta lura sune masu kokarin ajin, takan zauna tayi tunanin akwai department din da yakai Economics barin wuta duk makarantar?

Sau da yawa tana tunanin Anya ba hausa ko Islamic zata koma ba?

Ta gama tsorata da makarantar musamman yanda taji ana bada carry over, probation da Kuma withdraw.

Takan yi tunanin ai ita abun kunya ne gareta ta sami Koda carry over din ne ma hakan yasa ta Kara dagewa tana Kara naci cikin karatun ta musamman da jarabawa ta karato kullum tana library ko Kuma tare da su chinyere tana Kara koyon karatu.

Saura kwana hudu su Fara jarabawa misalin karfe hudu na marece tana zaune wani class tana faman karatu yazo wucewa kunnensa like da air piece har ya gitta said yaga kamar ita, yayi jimmm Yana tunanin ita ce ko gizo idanun sa keyi Masa kamar kullum?

Kamar kada ya dawo sai Kuma dai ya koma don tabbatarwa .....ita din daice tana ta faman Mimi da baki ya kyalkyace da dariya lokacin daya kunna Kai ajin hankalinta naga littafi har yazo ya zauna kusa da ita....tayi firgigi cike da tsoro ko da taga shine bata San lokacin da ta balla mishi harara ba.....yayi murmushi afuwan matsoraciya duk wadannan mutanen meye zai kamaki da rana gatse gatse haka?

Ya karasa maganar Yana janyo littafin ta gaban sa, meye kike karantawa ayi mun bayani.

Haushi ya turnuketa domin karatun ya Fara shigar ta sosai gashi yazo zai rikita ta, Tasha mur tare da janyo littafin Dan Allah karatu nake zaka rikitani ka tashi ka bani wuri.....bazaki koya mun ba?

Nima Yanzu ai nake karantawa ta fada cikin fada fada, yayi murmushi it's alright go ahead and read ya sunkuyar dakai kawai bisa desk din.

Ta ci gaba da karatun ta ba tare da ta Kara bi ta kansa ba.

Idan ta karanta sai that bude can karshen littafin ta rubuta haka haka Yana ta lura da ita duk ta dage bakin Rai bakin fama Nan da nan ya gane hadda ce takeyi.

Yana so ya mata bayani Amma ya rasa ta inda zai Fara......

Tana son kamshin turaren sa ainun Anwar Dan gayu ne matuka Yana daukar wanka gashi kyakkyawa.

Kamar ta karanci zuciyar say ta Dan karkato Dan Alalh wannan kalmar me take nufi?

Ta sungo mishi littafin a gaban sa.

Daman tun zaman sa kusa da ita ya kashe music din hakanan wayar ke jikin kunnen sa.........yayi kamar baiji me tace ba har sai da ta kalleshi sannan ya Dan zare wayar daga kunne Shi ala dole baiji me tace ba ya dan kalleta Shima kina magana ne?

Cewa nayi me wannan kalmar ke nufi?

Ta nuna mishi da yatsa ....yabi hannun nata da kallo Yana kallon Zara zaran yatsun ta ya ce bari muji sentence din, Ya fada mata ma'anar kafin yace kin gane course din nan ne?

Ta Dan bata rai to gashi dai Ina karantawa......

Ya Kara janyo littafin gaban sa ya budo shafin farko......
Chapter 4 · 0% Book details