Sashe 19
Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallo yayi ma sadeeq ya watsar.
Ni kakeyi ma wannan Dan iskan kallon?
To Suleiman zuwa yayi ya fada Mana ya shawo Kan Bilkisu tace ta hakura zaku koma normal.......zumbur ya Mike...
Are you serious????
Ya galla mishi harara na ban sani ba kaga wulakancin da kayi mashi da yazo ko kallo......forger about that please ta hakura????
Anas yaja dogon tsoki sai kaje ka fada Mata ka kusa mutuwa.....
Ya kyalkyace da dariya a'a ka manta mutuwar nayi.
Eh Mana, Kuna ta wahalar da kanku a banza.......
We are just friends jor what are you talking about???
Ai maganin sa Bilkisun, nifa yarinyar ta bala'in birgeni wallahi ta nuna mishi ita din ta daban ce......Anas ya fada Yana Kara doka mishi harara.
Ya lumshe ido ya koma ta baya ya kwanta...ku yau kuka San Bilkisu ta dabance ko?
Duk suka dunkule hannu suka Kai mishi duka ... sadeeq yace asirinka dai ya tonu munafuki.....ya Kara bushewa da dariya.
Washegari suna da exam 3, karfe biyu ta fito library jikin wata bishiya bisa kujera ta Kira Suleiman......
Hello ka shigo?
Eh, kina Ina ne?
Ina ta wajen library wallahi na kasa game wannan last part din, zo kamun dalla dalla please.....
Okay Ina zuwa.
Ashe tun karfe tara suna tare da Anwar Yana koya musu a class, ya kalleshi cikin kosawa.......Yaya?
Dariya yayi kafin yace, last part din nan ne bata gane ba take so na nuna......tashi muje ya Mike.....
Anas ya kalleshi Dan uwarka mu Kuma fa ?
Ya dalla mishi harara ku gane ...yayi waje.
Daga nesa ta hangosu , tayi saurin boyewa bayan bishiya sannan ta saka wayar ta Airplane mode.
Tana kallonsu sai safa da marwa sukeyi amma ta boye.
Har kusan uku saura kwata sannan ta hangosu sunyi hanyar class din da zasuyi jarabawar.........
Watan Suleiman kiranshi yayi ko?
Ta buga tsoki.
Lokacin da ta Isa har sun zauna invigilators sunzo, ta shiga...idon sa na kanta, Koda wasa Bata yarda ta kalli inda yake ba, Suleiman na bayansa ya Dan gyara alamar ta zauna sai kawai ta wuce kamar bata lura ba.
Ana gama jarabawar, tayi saurin submitting tabar shiyyar.
Suleiman na fitowa ya kamo hannun sa, kaga ta tafi ko?
Murmushi kawai yayi.
Abu kamar wasa har saura exam uku su gama amma Bata yarda sun hadu ba.
Ya Sami Suleiman kamar zai mishi kuka yace shifa bai gane ba.
Dole ya sameta yace Dan Allah tayi hakuri ta saurareshi.
Tasha mur, au ni zan sameshi bashine zaizo yaban hakuri ba?......
Ohhh toooo kiyi hakuri zaizo, ta wuce abinta tabarshi wurin saboda yama bata haushi.
Suna rabuwa ya Kira Anwar din yace tace Shi baida bakin bata hakuri ne?
Gaban sa ya Fadi.....Anya zai iya tunkarar ta Yanzu Kam har ga Allah tsoron ta ma yakeyi.
Haka ya kwana dardarce, ko barci kirki ya kasayi da ya tuna sai ya yi firgigi ya tashi zumbur.
Jarabawar ta safe ce, farar shirt ya saka Mai kwala tana da ratsin ja, da farin jeans sai jar facing cap.
Agogon hannun sa kirar *Rado* baka .
Ya rufe ido da makeken glass dinsa Baki. ( Anwar akwai kyau da iya wanka ).
Ba abinda gabansa keyi sai faduwa Anya zai iya mata magana?
Duk inda ya gitta sai an kalleshi ya wanku iyakar wanka sai kamshi ke tashi.
Yana tsaye jikin taga ya hangota sun taho tare dasu Aisha sai faman dariya sukeyi.
Ya bude littafi kamar Yana karatu amma ita kawai yake kallo.....tana matsowa kirjinshi na Kara bugawa.....kafin ta iso har invigilators sun iso, dole ya shiga hall din ya zauna.
Yana Zama tazo zata wuce yasa kafa tun daga nesa ta hango abinda yayi sai kawai tabi dayan layin.
Ya rigata fitowa, Banda faduwar gaba har Yar kyarma ya Fara lokacin da ya hango tana fitowa.
Ta zukunna gaban Helen tana fadin .....duba mun wannan shin sune characteristics din nan?.......
Kamar daga sama taking yace *Bilkisu*........
Gabanta ya bada rasss!!!
Maganar ta makale Mata.......ya Kara kiranta a hankali Yana tsaye bayanta..... *Bilkisu*...........Zainab wowo ce
Ayi hakuri da kadan
*WA ZAI FURTA?*
1
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.
Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
****************
*KADUNA RIGASA*
Ranta a bace amma Sam hankalinsa baya kanta sauri sauri yakeyi daman tun da ya iso an shigo Mata da tsarabun da yayo.
Gabanta ya fadi, wannan rawar kafar ta mecece?
Ta daure ta dan boye fushin ta, kafin tace : Wai lafiyar ka kuwa?
Yau ka dawo sai Yanzu ka shigo nan Kuma kana ta wani sauri sauri........
Nan da Nan guiltiness ya kamashi, ya Fara Yan kame kame.....
Nan da nan ta gano bakin zaren tayi murmushi ko hada gajiya halan?.....
Ya kakaro murmushi gajiyar ma ce gaskiya.
Gaskiya ne.
Ta Mike , mu kwana lafiya kaje ka huta......wuf Shima ya Mike Daman jira yakeyi yayi waje Yana fadin Allah ya tashe mu lafiya.
Ta bishi da ido kawai, lallai namiji akala ne, ta kuta zaka gane kirenka ka gama kwanakin ka dawo...amma zanje in ga kalar wainar da ake toyawa.
Ummi nada tsawo Kuma doguwa ce tafi Amira .
Ita kuwa Amira irin Dan jikin Nan gareta Mai kyau da tsari, kallo daya Kai kace ummi keda Yara biyu ba ita ba.
Tana gyara jikin ta don ko tsakanin Ahmad da almustapha shekara biyar ne.
Ta bashi kamar mintuna arba'in kafin ta saka bakar jallabiya matsattsa tabi jikinta da turaren da ya fi so ta nufi sashen sa don ta San Yanzu suna can.
Ta danna karaurawa, ummin ce ta zo ta Dan leka.....ta kalleshi tare da yin Yar dariya *Yaya Amira* ce.
Oya bude ya fada Yana kishingide Yana Shan kankana.
Ummi na sanye da dogon wando jeans ya matse ta da Yar matsattsar Riga kanta ba kallabi ta yi kitso shuku Wanda ta daure da katon ribom saboda karancin gashi .
Ta kalli ummin sama da kasa sannan ta danyi murmushi sorry for disturbance please.....laaa ba komi karaso ciki.
Ya tashi zaune Yana Yar dariya Amira Yaya?
Tayi Yar dariya.....zuwa nayi in ji ka siyo mun book din nan kuwa dazun na mance in tambayeka......ohhh yes, Yana mota Bari na dauko Miki........ya yunkura..
A'a barshi kawo key din na dauko Yana ta wajen Ina?
Wurin Mai tuki jikin kofa Yana Nan....Ummi dauko key din.
Ta Mike.
Ya Kura Mata ido, Yana son tayi shigar doguwar Riga, wannan kamshin zuwa akayi ayi mun kwalele?
Good and fine, ta ce cikin zuciya, sannan tayi murmushi ta ce hmm kawai.
Kinji?
Gobe zanje kasuwa Dan Allah da safe ba dadewa zanyi ba, Zan biya gidan Salma.....me akeyi gidan salmar?
Ta dan mishi warrrr da ido, zumunci......duk sai ya diririce, Ni Zan kaiki ko?
Ta Dan Kara farrr da ido tare da Yar dariya, lokacin da Zan fita bana tunanin ka tashi cos by 8 nake son zuwa kasuwa Kuma Kai ba ma'abocin son zuwa kasuwa bane.....Zan biki please.
Saura kadan ta tuntsure da dariya yanayin yanda yayi maganar.
Ta danyi murmushi.....Ummi ce ta fito da key.
Ta mike Bari na dauko book na.
Ya bita da ido Ummi ta dankara mishi harara Amma Sam bai lura ba.
Bude tabar kofar tana dawowa Bata shigo ba ta tsaya bakin kofa....ga key din Ummi, ....wuf ya Mike Bari na karbo.
Tana daga waje ya hada da key din da hannun ya rike in fito goben muje?
Nooo, kaga Ummi zata ji haushi kayi hakuri ka bata full time dinta don nima turn Dina.....ya murza hannun da karfi.
Tayi Yar Kara, ya dawo Yana dariya......
Ummi kamar zata fashe amma ta daure ta cije duk da haka sai da ya danga chanji amma sai kawai ya share.
Butique ta tafi, ta siyo rantsattsun English wear sabbi hada three quarters wando da skirt da crazy jeans.
Har ta dawo wajen Sha daya bai fito ba.
Ta fada wanka Yara sun tafi islamiya tahfeez, ta kulle kofar ciki tabar Mai aikin ta kitchen tana fita ta kofar baya.
Amira nada gashi sosai, kanta kananan kalaba ne duk sun zuba bisa bayanta wani sky blue crazy ta saka da wata crazy riga Mai hannu daya nononta kawai rigar ta rufe kasan ta Kuma bazace, ta cikin Bazar kana hango cibinta.
Kamshi kawai ke tashi gidan.
Sha biyu saura ya fito, motar ta kawai ya gani yasan ta dawo.
Ya nufi bangaren nata don agaisa.
Tana Jin motsin sa ta ruga daki ta dawo rike da littafi kamar me karatu ita a dole bataji shigowar sa ba.
Mutuwar tsaye yayi ya kusa sarkewa da miyau sai kawai taji Yana tari.....ta dago Kai da sauri irin ta razana din nan.......
*****************
*Federal University dutsinma*
.....Ta kasa dagowa ta amsa, jikinta ya Fara Yar kyarma.
Helen ta kalleta, Anwar na Miki magana...
A hankali ta juya kamar Mai ciwon wuya , idanun sa cikin glass Yana Dan murmushi........
Minti biyu.
Ya fada kafin ya juya ya Fara tafiya can nesa wurin parking motoci.
Ta Mike jikinta duk ya mutu tabi bayansa.
Jingina yayi da mota hannuwan sa duka cikin aljihu ya kura Mata ido.
Kanta a kasa ta karaso fuskar ta babu yabo ba fallasa.
Ta kasa magana....
Ya Kara nutsar da idanun sa gareta yace: Ranki ya dade ya exam din?
Ta danyi murmushi kadan Alhamdulillah...Ina kwana.
Lafiya Lau, na Aiko a Baki hakuri kina ta ba mutane wahala kince dole sai nazo da kaina to gani nazo.
Ta Kara kasa da Kai tana murmushi...... ban taba tunanin zakiyi fushi haka dani ba ko kadan.
Tayi shiru dai,
Har kiranki nayi da sallah without knowing u deleted my number.......
Shikenan dai ya wuce.
Ta fada a hankali.
Kin tabbatar ya wuce?
Mun shirya?
Sai kawai tayi Yar dariya saboda yanda yayi tambayar kamar wani karamin yaro.
Yabi fuskar da kallo......
Ji yakeyi kamar ya kamota ya rungume...
Yayi murmushi kinji mun shirya Yanzu ko?
Eh,
To na gode, Zan kiyaye daga yau Allah ya Kara Baki hakuri shikenan ko?
Um, tace a takaice.
Ina zakije yanzu?
Gida Zan tafi.
To muje na rakaki .....