← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 35

Sashe 23

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai Ina Kika saki Kaya haka bayan nasan ke ba ma'abociyar su ba ce?

Inji waye?

Ina ra'ayi Kaine naga kamar basa birgeka.......wallahi Ina so.

Da kin tsaya dazun tabbas da ba kiss kadai zanyi ba...........

Maganar ta makale ganin Ummi ta banko kofa kamar an biyo ta....
**************
*Federal University dutsinma*
......Malam ba Wanda kake tunani bane get lost....

Ya bude baki zai Kara magana ya fiddo mishi idanu I said get lost ya fada cikin tsawa..........

Wai Kai baka girmama manya ne?

This is not your business mutane fa Yanzu kasar nan a firgice suke kamar.....kamar kowa ya haukace irin ka?

Da sauri mutumen ya kalleta, sai kawai ya tashi yabar wurin.

Ya kamata kasan darajar mutane fa......naji kiyi hakuri go....ya Mata nuni da baki.

Kana korata ne don na Fara fada maka gaskiya.......

Bilkisu muje...... sadeeq ne ya karaso da sauri.

Sadeeq kayi ma Anwar fada abunsa ya Fara wuce gona da iri ta Yaya zai ringa yi wa magidanta tsawa babban mutum mai kima......

Dan Allah kiyi hakuri ban karawa...ohhh my God.

Ya akayi ne?

Inji Sadeeq.

Ta juya suka jera suna tafiya tana magana cikin fada fada, Shi ya raina kowa, mutum da kimarsa yayi mishi magana mistakenly it might be ya mishi Kama da wani ne Wai kaga wulakancin da ya mishi?

Haka kawai ya janyo ma kansa dauri a banza........

Kiyi hakuri Zan Kara mishi nasiha don Anwar Kam sai dai nasiha ba fada ba.

Suna wucewa ya saki ajiyar zuciya.......

Ya ruga mota.

Yana Zama ya kirata a waya, kamar bazata dauka ba tana kokarin hawa jirgin bayan sun rabu da sadeeq.......

Hello...fly mode Zaki Sanya wayar ki Kuna landing in the next 40-50 minutes I'll call..okay?

Naji, thank bye....ta latse wayar.

Yayi dariya, Bilkisu rigima.
.......

Yana bude mota ya shako wuyansa.....Dan ubanka me yasa kakeyi Mata boye boye?

Ya kyalkyace da dariya,
Wane babban mutum ne kayi ma wulakanci a gabanta......

Wallahi su Alhaji murtala ne kasan Shi ya cika shisshigi Ina Jin saukarsu kenan.

Ya zaro ido?

Shi ka yankwana???

Kwarai kuwa......anjima idan yazo lissafi Kuma fa me zaka ce mishi?.

Inaaaa bazan bashi fuska ba yasan bana son haka gaban mutane.

Ya kalleshi, jirgin kayan nan fa ya iso tun last week, jibi zanje Lagos nayi clearance a Fara distribution.......

Masha Allah.

Amma me yasa baka son Bilkisu tasan Kai wanene?

Yayi murmushi saboda Suma suna da kudi Kuma......

Kuma ubanwa??.....

Ko makaranta kaki nuna ko Kai wanene Wai me yasa kake haka?

Yayi Yar dariya, Kuma fa yarinyar ta gane Zan masifa amsa questions irin lokacin da tasan ni first class ne.

Kana son Bilkisu ko Anwar?.....

Ya kalleshi bana son irin wannan tambayar taka na Fara gajiya da ita, saboda ka kasa fahimtar baka da amsarta Yanzu......mtseww nonsense.

Ya Kai mishi duka.

Tarihinka Zan Bata Dan ubanka, Zan fada Mata Kai din wanene.....

Da kayi nadama irin Mai ban tausayin nan wlhi.

Sadeeq din suka Fara ajiyewa sannan so gida unguwar makil da jama'a Yan maula kofar gidan ba masaka tsinke .........
*TUSHEN LABARIN*
Babban gida ne a Kano, Alhaji Hamza hamshakin Dan kasuwa ne Wanda aka sani ko'ina a fadin duniyar.

Yaranshi shidda hudu Mata sai biyu maza.

Matansa uku, Allah bai azurtashi da yawan yaran ba,sai yawan dukiya.

Ta farkon hajiya maimuna keda Yara hudu, maza uku mace daya, ta biyun Allah bai Bata haihuwa ba hajiya Jamila, sai karamar keda Yara biyu mace daya namiji daya Kuma Wanda ya kasance Auta a gidan watau mahaifin Anwar (Alhaji Yusuf ).

Ya tashi cikin tsana da tsangwama ta Yan uwa, ganin hakan yasa mahaifiyar Shi ta maida hankali ga karatunsa fiye da harkar kasuwanci.

Babu Wanda mahaifinsu bai jaraba ba cikin yaransa maza 3 Amma dukkan su sai da suka ha'ince Shi.

Yusuf bai da lokaci ma bare a kwatanta kullum Yana makaranta.

Ya gama jarabawar aji shidda suna jiran sakamako mahaifin su Allah yayi mishi rasuwa daga ciwon ciki.

Nan da nan rikicin rabon gado ya taso.

Aka raba rabo na son zuciya.

Cikin gidajen da suka gada shida Yar uwarsa da mahaifiyar sa suka koma can wata unguwa.

Allah ne gatanta shine jigonta.

Ya ce zai ci gaba da kasuwanci kawai tunda ga jari sun samu.

Nan da nan ya Fara fita China Yana saro turaruka Yana rabawa manya manyan shaguna a garin Kano.

Tun Yana tsayawa Kano kadai har ya Fara kaiwa kaduna, zariya......wasa wasa sai ya bulla har Lagos, Abuja da sauran wurare.

Arziki Kashi........

Nan da nan ya Kara da cosmetics, takalmomi, jakunkuna.....Kai kayan masarufi........kafin kace kwabo Yusuf ya taso da zafi....hakan yasa mahaifiyar sa bata duba karancin shekarun sa ba tace lallai sai yayi aure.

Bai da ko budurwar ma saboda bashi da wannan lokacin.

Itace ta nemo mishi diyar kawarta Yan asalin Yola Fulani basa ko hausa cikin gidansu, lokacin duka bai wuce shekara ashirin da biyu ba.

Shekarar su daya cif da Aure aka haifi Anwar.....bayan ta haifeshi kuma tace ga garinku nan Shi bai San mahaifiyar sa ba.

Tunda ga lokacin ko maganar Aure baya so.

Anwar ya tashi hannun kakarsa, Yana Dan shekara 2 bayan an yaye shi yayar babansa Aunty murja tayi Aure.

Ya kasance gidan daga Shi sai kakarsa mahaifinsu ba mazauni bane sai Yan aiki dake kula dasu suna musu dawainiya.

Duk Yan uwansa arzikin ya tsiyace sun dawo karkashin sa.....

Cikin kankanin lokaci ya nunka mahaifinsu kudi linkin baninkin.

Yan uwan cutarsa sukeyi amma kullum kudin kamar ana Kara musu taki.

Ya mallaki kaddarori iyaka, kamfunna a Nigerian ba inda baya dashi komai Yana shigowa dashi Kuma ana yi na cikin gida.

Anwar na primary school ya Kara Aure, ba hausa Amma mazauna saudiyya yarinya Mai hankali da sanin ya kamata.......watansu uku da Aure hatsarin jirgi ya rutsa da Alhaji yusuf.

Anji mutuwar sa a kasa Baki daya, sanarwar rasuwar ya barar da tayin cikin Amarya.

Illahirin dukiyar Anwar da kakarsa suka gaje ta, Nan take ta ce ta yafe ma Anwar komai na mahaifinsa amma nata na mijinta a fiddo Mata, haka akayi kuwa aka Bata ta karawa yarta murja.

Kafin marigayin ya rassu Yana yawan fadawa mahaifiyar sa amintattun mutanen sa da wadanda ke cutarsa.

Baya boye Mata komai.

Cikin amintattun hada Alhaji murtala ( wadanda suka hadu da Anwar airport ), shine kan gaba wajen Jan ragamar kasuwancin.

Tsaron shaguna aka ba wasu daga cikin macuta.

Allah da nashi iko, sai ya dubi maraitar Anwar ya Kara bunkasa dukiyar........

Yana j.s one wata Rana an dauko Shi school sun shawo layin gidan su kawai suka ga yaro gabansu da Keke......da karfi suka taka birki ji kake kuuuuuu....

Yaron ya Fadi da karfi lokacin da keken ya daki motar Kan ya karye tayar ta lauye....Shi Kuma ya karya musu madubi ya karci motar.

Anwar na kwance bayan sit, yaki ko motsi tunda yaga abinda ya faru ya kishingida bai Kara dagowa ba.......

Drivern ya fita mutane suka taru sosai, ihu kawai yaron keyi Yana kururuwa wallahi sai an biyashi keken sa, kowa yasan laifin yaron ne amma sai aka goya mishi baya.

Shurun tayi yawa hakan yasa Anwar din fitowa, ya kalli Umar driver yace ya akayi?.......

Sai kawai yaron ya cakumo wuyan Anwar, na rantse da Allah ban sakin sa sai an biyani kekena........

A hasale Anwar din ya kalleshi cika ni ko Kuma wallahi in maka mugun duka anan...ya fizge tare da ingijeshi yayi taga taga.....Nan Yan unguwa kowa ya Fara darewa an San Hali.....

Ya Kara shako wuyansa.....

Umar yayi wuf ya fizgeshi......

Sai abun ma yaba Anwar dariya.

Keken nawa yake?

Koma nawa yake wallahi sai kun biyani, don ba inda zakuje ya babbake hanya Yana ware kafafu.

Shigo muje .....Akan wannan shegen keken.....wani nushi ya Kai mishi a gefen fuska, Nan da Nan suka rukume fada...kichaaa...kachaaaa.

Mutane suka yo kansu da gudu.......kowane sai haki yake.

Yau naga bala'i Kai wane irin Dan iskan yaro ne?.......

Mugun bugu Zan maka, wallahi na gane fuskar ka matukar ka Kuma zagin keken Nan sai nabarka kwance saboda zufar ubana ce....ita wannan motar zufar uwarka ce da ka fado Mana ko baka ga ka Mana barna muma......

Sunfi awa ana abu guda daya Anwar yace Basu biya Shi Kuma ya hanasu tafiya......har hajiya ta Kira waya taji shiru.

Hankalin ta a tashe ta fito......

Tasa aka iso da ita wurin da ake rigimar .

Yaron ta kalla lokacin da ta iso tace zo muje a siya ma wani keken....ta kalli Umar saka wannan mota......Yanzu naji magana...ya figi hannun Anwar zo muje tare kada a yaudareni.......suka fada motar hajiyar da tazo ciki.

Anwar na shakkar hajiya baya kaunar bacin ranta duk duniya.

A motar yaji tana waya..... hello Yanzu Yanzu Aiko da sabon Keke Mai inganci na Dan samrayi sa'an Anwar .

Suna shiga Anwar yayi saman bene da gudu cikin bacin Rai.

Suka zauna falo Shi da ita.....ta kalleshi ya sunan ka?

Yace *sadeeq* da sauri.

Babanka ya siya maka ne?

Eh, ya zumburo baki cewa yayi idan nayi na daya a makaranta zai siya mun, yau kwananshi biyu fa da saye!.

Tayi murmushi.....to ba sai ya Kara siya maka wani ba idan yaje kasuwa?......ai ba a kasuwa yake yin faskare ba nan kusa da gidan mu ne kullum.....dai dai Anwar na saukowa bene....ta ce innalillahi faskare yakeyi?

Eh, shine yayi ta tarawa ya siyo mun keken.
........hansa'u!!!!!!!

Ta kwala ma cikin Yan aikin Kira.

Da sauri ta karaso, kawo ma yaron nan abinci.

Ya washe baki Yana Murna,Nan da Nan Anwar yaji tausayin sa musamman da aka kawo abincin yanayin yanda yakeci.

Ya tashi kawai yabar gun.

Da gudu Anwar din yayo baya cikin firgici jin ihu ba kakkautawa........Ashe sabon keken ne aka shigo dashi..

Kawai ya dunga buga tsalle Yana ihu da rawa.....

Da hajiya da Wanda ya kawo keken sukayi ta dariya......

Kai Wai baka da hankali ne ?

Ya daka mishi tsawa ka bani tsoro a banza wajen hauka......Allah ya baka hakuri Yanzu ko duka na kayi bana ko kallon ka...mtsew ya yi hanyar daki.

Ya ruga ya kamoshi.....zo muje mu dana tare kafin na tafi a titin cikin gidan Nan...... serious ya kalleshi...are u mad?
Chapter 23 · 0% Book details