← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 35

Sashe 20

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A'a barshi kawai na gode, ta katse shi tare da yin gaba abinta.

Ya bita da kallo baya so ta tafi ko kadan.

Ya hura iska.... nawaoooo yarinyar nan miskila ce ta karshe.

Wani sanyi zuciyar ta keyi mata, tana zuwa daki ta fada bisa katifa ta rungume filo ta maida idanu ta rufe a hankali.

Su Anas suka bushe da dariya, ya cire glass Yana hararar su , Helen na bayansu, tana so taji yanda akayi.

Munafuki sai kace yau neman shiri zakayi Shi yasa tun karfe biyar ka yo wanka kana faman shiri.

Mtsew yaja guntun tsaki, suka jera suna tafiya.

Ya kalli Helen din dake kokarin jerawa da su yace ke kuma lafiya kike faman binmu?

Kamar za ta nutse dan kunya, ta juya kawai ta koma......

Sadeeq ya harareshi wallahi ka daina dizga mutane haka Anwar.

Ya maida glass din a idon sa, inba gulma ba ubanwa zatayi cikin mu?

Kasan tun dazun ina tsaye da Bilkisu hankalin ta na nan?

Kayi mamaki ne?

Inji Anas.

Waye bai San ta mutu kanka ba......

Ban san abinda kuka mayar dani school din nan ba.

Ko wace jik and jak Sona takeyi?

Mtseww kada kusanya inci ubanta da kyau fa.

Mufeeda ma ta gama haukanta ta shafan lafiya bare wata arniya.......

Kada ka taba yarinyar mutane arnan can sun fika hauka.....

Ko in gwada?

Muga cikin mu wa ya darar ma wani?
.......Anas ya zaburo Kar ka Soma wallahi.

Babu ruwanka da ita baka San tana yi ba kawai ka ci gaba da nuna Mata baka ganeba.

Naji!

Ya fada a takaice.

Yaushe zaka Mana bayanin Economic of production?
4, yace a takaice.
4, Kuma?

Eh, saboda zanje wani wuri da daddare.......duk suka kalleshi.

Yanzu barci zanyi, 4 Kuma sai muyi zuwa magrib ko bai muku ba?

Amma ai yau ba ball ina zakaje ne?....

Murmushi kawai yayi.

Suka Kara binsa da ido.

Wai lafiya?

Ya bukata Yana Yar dariya.

Ina zaka je muka ce?

Wanda zai bini ya shirya ban hanaku ba.....

Duk sukayi shiru, suna kallon kallo.

Ya kyalkyace da dariya wallahi ku munafukai ne...... sadeeq ya Kai mishi duka wallahi baka da gaskiya.

Ya kyalkyace da dariya.

Mashin daya suka hau.

Dakin acike bai samu ya yi barcin ba daga wannan sai wannan, ya gaji matuka.

Shi ba koyawa ko bayani ke baya son yi ba, cin lokacin sa da akeyi ke sanya Shi kosawa.

Sai da yayi wanka sannan ya Fara shiri cikin farin boyel ya dauko hudaddun takalma ya saka na fata *masarati*, yana cikin sharce gashi suka shigo.

Duk suka zaro ido.....

Ya fiddo turaruka ya shiga fesawa kusurwa kusurwa, lungu lungu.

Sadeeq ya kalleshi *Anwar Ina zaka je?*
Bai ma kowa magana ba ya Mike, har ya Kai bakin kofa ya waigo ku bakwa ganin karuwa da danta baku tambayi ubansa ba.
*Zance Zan je*.......

Ya fice da sauri suka Fara surma mishi zagi.

Yana tafe Yana tunanin Yanzu kuwa Yana zuwa ya tarar tana tare da wani to ya zai yi?

Ya tofar da miyau, Wai kada abin ya Zama gaskiya.

Mashin din Salim, roba roba ya karba.

A bakin gidan yayi farking ya kafe mashin din tare da Zama saman Shi kamar kujera sannan ya Kira wayar ta, tana kwance da Yar shimi ta barci rike da littafi tana karatu wayar tayi Kara........

Tunanin ta mommy ce.

Ta muskuta, Ba tare da ta kalli screen din ba tace.

Mommy.....

Mommy Kuma?

Ya bukata.

Ta zaro ido tare da kallon fuskar wayar sai akwai ta mayar a kunne....still Baki mayar da no.

Ta ba ko?

Ya hakuri Ina wuni?

Gani waje Ina jiranki.......

Waje Ina?

Kofar gidan ku.

Na shiga uku.....Bata San a fili ta fada ba sai da taji yace.....zuwan nawa ke da shiga uku?

Ta zaro ido.

Duk ta diriri ce.

Ko baki maraba dani na juya?

Ina zuwa...

Ta fada a hankali.

Jikinta yana ta Yar kyarma.

Ohh ni Bilkisu ko lafiya?

Sauri sauri ta shirya ta zumbula hijabi har kasa ta fita.

Kallo daya tayi mishi tsikar jikinta ta tashi Yarrrr....

Anwar a manyan Kaya????

Tayi murmushi kunyar duniya ta kamata gabanta ya dunga faduwa tana zullumin me ya kawo Shi?

Ya tsareta da ido, yaki magana.

Ta dago Kai sai ta zumbure baki ta maida Shi kasa.

Yayi murmushi, haushi kikeji nazo saboda ba Suleiman bane ko?

Kallon sa tayi da sauri , ya Sha mur!

Kin tsaya kina ja mun class kamar irin nazo zancen nan.

Dariya tayi.

Yanzu dai Ina wuni, me ya kawo ka cikin tsohon Daren nan?

Yayi murmushi, zance nazo can baya na biyo mu gaisa ko ban kyauta ba?

Gabanta ya fadi, ta dan tsuke fuska.

Hmm.

Ko ban kyauta ba?

Kayi daidai.

Ke baki iya tarar bako?

Ko haka kikeyi wa Suleiman idan yazo?

Suleiman again?

Ta ce cikin zuciya.

Wai meye kake ta fadin Suleiman......

Ba Kya so long sunan sa na fada kada gabansa yayi ta faduwa?.

Ikon Allah ta fada.

Eh Mana.

Gashi kin kasa sauraron kowa sai shine ya shirya mu.......

Baka ji dadin hakan ba?

Ya Dan harareta meye tsakaninki dashi?

Ki fada mun sirrin.....

Anwar rigima kazo muyi ko kuwa zuwa kayi mu gaisa da gaske?

Duka biyun nazo yi.

Karatu nakeyi.

Nasan kayi covering gobe ka Fara ansar extra sheet ina page 2 ina zare ido......

Suleiman zai Baki amsa....

Na shiga uku.

Ta fada tare da kallon sa.

Yasha mur, ko ruwa bazaki bani ba da gaske......juyawa tayi kawai.

Ya bita da kallo.

Kwalin fresh milk ta fito da Shi da cup a hannu, gashi amma ba sanyi.

Ya karbi kofin ya Mika Mata alamar ta zubo mishi.

Ya tsareta da ido sai Yar kyakkyarwa takeyi.

Nayi kyau da manyan Kaya?

Ta tuntsure da dariya......

Yau naga ta kaina.

Shima dariyar yayi, to naji kin ki yabawa .....

Ta dalla mishi harara ita wacce kaje gurinta Bata yaba bane?.

Ya Kai kofin bakinsa yasha kafin yace, ta yaba tayi comments kema kiyi naki.

Har zata ce ni budurwar ka ce sai Kuma tayi shiru kada yace *Eh* tafi so *YA FURTA* Da bakin sa.

Me yasa baki WhatsApp?

Hakanan.

Bai yiwuwa , saboda duk Mai hankali baya abu babu dalili.

Me yasa bakya yi?

Allah kawai bana son abun da zai daukar mun hankali daga karatun nan.

Muga wayar.......ta kalleshi.

Ya nutsar da idon sa cikin nata tayi saurin kawar da Kai.

Kada Inga text din Suleiman?

Bazan shiga can ba......ta Mika mishi da sauri, yayi murmushi.

Zan dawo Miki da ita gobe ya saka aljihu.

Meye password din?

Ta zaro ido, Daddy na kirana every asubah..... don't worry I'll talk to him meye password din?.

Dan Allah ka bani saboda.......

Saboda Suleiman bazaiji dadi ba?

Sau nawa nake ganin ta a hannun sa?

Wai lafiyar Anwar kuwa meye Yanzu magana daya sai ya ambaci Suleiman????

Na rantse da Allah sau biyu ne, Kuma duk chargy ya kaimu ya Kuma karbo.......

Yasha mur meye password dinki?.

Gabanta ya Fadi duk ta rikice saboda ANWAR ne password din.

Ya kalleta wallahi wurina wayar Nan yau zata kwana Kuma sai kin fada mun password din..........

Zainab wowo ce
Ayi hakuri da kadan.

An dameni da cigiya
*WA ZAI FURTA?*
1
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.

Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Godiya ta musamman ga :*
*Mowa ( maimuna Nasir )*
*Hauwa'u, ( mum khady nima Ina kaunarki matuka*
*Da masu mun waya, text da kirana direct ku sani cewa zainab wowo Bata Raina masoya wlhi Ina kaunar ku sosai*
*Unex*
***************
*KADUNA RIGASA*
Ta dan rike kugu tana Yar rangwada....

Mura kakeyi haka?

Wuffff....

Ya riko kugunta, kece Zaki Sanya mun ita Yanzu, Ina Kika Sami kananan Kaya haka?

Sai faman shinshinarta yakeyi ya nutsar da kansa cikin wuyanta.

Tayi wani juyi tare da mayar da fuskar ta gab da tasa saboda ya sunkuyo tayi warrrr......

Kawai taji ya hada bakin sa da nata......

Fittt... ta fizge.

Ta danyi baya tare da buga wani makirin tsalle rigar tayi sama cikinta ya fito fili.....

Kanka qalau kuwa?

Ya yunkura zai Kara chafko ta tayi baya tana Yar dariya idanunsa sun kada sunyi jawur....

Ya kalleta kamar Mai Shirin yin kuka *Dan Allah ki tsaya bani da karfin binki ko'ina*.......

Amma kasan ba anan kake ba ko?

Ya langwabar da Kai, please one kiss....

Tabbb wlhi Haram.

Ta fada tana wata karairaya.

Ya kura Mata ido duk hankalin sa ya tashi....

Amira kada ki hadu da fushin Allah ki tsaya....

To Yanzu.......

Charaf!

Taji ya damke ta cikin taku daya.

Yana riketa ana dukan kofa da karfi.

Kafin yayi wani motsi ya jiyo muryar hajia ( mahaifiyar sa ) tana fadin Amira ko Bata ciki ne?.

Ya buga wani uban tsoki ya ingijeta ya wuce bedroom dinta da sauri.........
***************
*Federal University dutsinma*
It seems like baki da gaskiya fa!.

Ya fada tare da tsareta da ido.

Ta dake ta kalleshi Yanzu dai Wayata ce zaka tafi da ita ko?

In shaa Allah, ya fada Yana murmushi.

Wai meye zakayi da wayata ne Anwar?, Bincike......., Ya fada Kai tsaye Yana kallonta, tayi shiruuuuu.......

Naji Zan baka, kawo na goge abu daya shikenan....menene?

Wallahi dana goge Zan baka hoto ne.....hoton Suleiman?

Ta doka tsoki Wai Kai komai Suleiman??????

Eh, ai kema komai shine....mtsewww to ba nashi bane nawa ne.

Kiyi hakuri bazan Baki ba don Ina son ganin hoton.

Ta Sha mur bani da Riga ne, Shi yasa da best Aisha ta daukemu muna cin abinci akwai hotuna da yawa nawa sai ka gaji da gani amma wannan bana son ka ganshi.......Ni Kuma naji Shi kadai nake son gani ma .....ta zaro ido.

What?

Cikin fushi ta juya gara ta nade tabarmar kunya da hauka... shikenan sai da safe ka cinye wayar ko kaje wurin Yan gyaran waya su bude.....dawo dawo....zo ...zo..zo please.

Gashi zo ki goge ya fada da sauri Yana fiddo wayar daga aljihu.

Ta kusa sakin dariya Amma ta daure ta Mika hannu okay bani.
Chapter 20 · 0% Book details