Sashe 2
Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana tsaye duk an rufeshi ana mishi surutai sai dariya kawai yakeyi tazo ta raba ta wuce ya ringa satar kallon ta har ta kule.....
*****************
*KADUNA RIGASA*
Amira kiyi hakuri wannan auren da zanyi ki daukeshi amatsayin kaddara wallahi wallahi bazan taba wulakanta ki ba don girman Allah kiyi hakuri ki daina wannan kukan......baban Ahmad Dan Allah ka fita ka bani wuri wallahi ko ganin ka bana sonyi na tsaneka da dukkan wannan rayuwar.....ya zukunna na tuba na rantse Miki da Allah ba zanyi auren nan don in wulakanta ki ba mu daukeshi matsayin kaddara Amira kiyi hakuri nasan ban kyauta Miki ba, ta Mike tsaye yaudarar maza wacece ban sani ba?
Haka kuke cewa Amma wallahi ka zalunceni ka cuceni kaci amanar kauna.....kada kice haka na rantse da Allah har gobe Ina kaunar ki.....karya kakeyi baka kaunata da baka ga wata har ta birgeka kake kokarin kawo ta gidan nan ba.
Shima mikewar yayi bacin Rai zaisa ki Fadi haka Amma Ni nasan wallahi ba haka bane Amira kiyi hakuri laifi ne na riga nayi na tuba Dan Allah kiyi hakuri.....mtsew ta wuce nabar maka dakin tunda Kai bazaka tafi ba.
Tabar Shi Nan tsaye.
Ya dafe Kai kwalla suka zubo mishi Shi kansa yasan Yana kaunar Amira Kuma baida niyyar Kara aure, matsalar kanwar abokin sa ce yasan kaunar da yarinyar keyi mishi tun Yana saurayi da farko Yana ba yarinyar fuska ba tare da Yana tunanin zata iya like mishi haka ba, kowa yasan suna tare Yanzu idan yace bazai aure ta ba kamar yanda abokin nasa ya bukata lallai zasu Bata.
Ya zauna bisa gefen gado ya dafe Kai dole in lallaba Amira har ta sauko tabbas bazan yi auren Nan ba matukar Bata cikin kwanciyar hankali.
Ya kwashe kusan kwana biyar Yana faman lallashi kafin ya shawo kanta hakan yasa Shima ya Sami sukuni da kwanciyar hankali.
Nan da Nan suka Fara hidimar aure shida ita .
Ya dauketa suka tafi Kano hado lefe, ya zauna gefe yace to ki Fara zabar lesuka , tayi jimmmmm kamar zata ce dauko mun Yan dubu uku da dari biyar sai Kuma wata zuciyar ta kwabe ta da cewar kisa tsoron Allah ga wannan lamarin bazaki taba tozarta da wulakanta ba.
Ta Fara ma lesussukan kallo tana tambayar farashi har aka kawo na karshen masu kudin daga dari suka Fara, ta ce nawa za a Sanya ne?
Yace yanda duk kike ganin ya Isa ni Dan kallo ne, ta dunga darzo manya manyan lesussuka tana warewa idan ta dauki red Shi sai ya dauki pink ko maroon, haka sukayi tayi har aka Gama da suturu aka koma kayan shafa da kalmomi.
Sun kashe kudi yafi miliyan uku sannan suka je gurun jakun Kuna da akwattai nan ma aka darje kusan set takwas ta daukar ma Amarya pink shi Kuma ya dauki sky blue.
Bata kawo komai cikin ranta ba, tana ta addu'o'i na Kara karfin guiywa kamar yanda mahaifiyarta ta Bata shawara.
Ita dashi aka Kai lefe, gidansu yayi wa Amarya sabon gini kusa da nata, sai dai yafi nata kyau nesa ba kusa ba saboda tsarin yabanbanta.
Sati daya saura bikin ta dawo gidansu da maraice ta tarar an fitar da kayanta duka anata fenti tayi tsaye turus, sai gashi ya fito daga gidan amaryar yace shigo kiga anyi wa Amarya jere Amira.
Gabanta ya bada Ras!
Da karfi ta daure tana yake tabi bayansa, na mutu.....kawai na mutu...abinda take nanatawa kenan cikin Rai ganin dukiyar da aka lafta gidan.
Sai dai kwalla su cika idanunta tayi saurin mayarwa ganin yanda yake ta zakwadin nuna mata ko'ina.
Jikinta yayi mugun sanyi ya kamota suka zauna babban falon Wanda suka Fara wucewa, Amira ya naga jikinki kamar yayi sanyi?
Ta Dan kakaro murmushi ba komi tana faman sunkuyar da kai, yayi kasa da murya ki aminta Dani Amira tunda Kika kwantar da hankalinki tare da kwantar mun da nawa wallahi na Miki alkawarin bazan taba watsa Miki kasa a ido ba, yanda mutane suka zuba Ido suga wata baraka Basu gani ba Yanzu daga wurin ki ba wallahi bazan taba bari su gani ba.
*Wannan gidan naki ne bana amarya ba* ita gashi can ana mata fenti kayanki gasu can ana sakawa mota za a Kai wa su *Umma* ( mamar ta ).
Tayi saurin dago Kai Amma suna hada Ido sai ta rushe da kuka.....ya rungumota kiyi hakuri na Miki laifi I knew!
Ita kanta Bata San ya sunan kukan da takeyi ba Yanzu.
Amma Tasha almwashin zata Kara daurewa taba maradda kunya har sai taga iya gudun ruwansa though har yau ta kasa aminta da kalaman sa tana ganin kamar yaudara ce irin da mazan yau.
Ya sungumeta zuwa dakin da Basu shiga ba Nan taga ikon Allah duk yafi dakunan kyau da girma yafi ko'ina Jin kayan alatu sannan taga akwatunan da ya saya jere sky blue yace kema ga lefenki can.
Kece shaida Babu abinda na banbanta sai kala.
Ahmad da Almustapha ma nasu na tafe gobe anmun waya sun zama ready.
Ta kankame Shi ta saki wani irin kukan Dadi.....kayi hakuri abinda na maka wallahi bazan taba watsa maka kasa a ido ba.....ya Kara rike ta nasan haka Amira kiyi hakuri.
Tuni labari yakai gidan su Amarya Nan da nan maganganu suka tashi wasu na cewa ta Gama dashi wasu na cewa tsoronta yakeyi surutai kala kala har Amarya takai ga ta harzuka.........
Turkashi a tsumayi diyar Aunty Rabi (mamn ibrahim) kada a manta a ringa Sanya mun ita cikin addu'a Allah ya Kara mata yawancin kwana ya shirya Mata zuri'a da rufin asiri.
Har Yanzu babana ma Yana bukatar addu'a Allah ya bashi lafiya yaba maman mu ladar jinya.
Ni din dai ce Zainab Dahiru wowo maman Abdullah
WA ZAI FURTA??
0
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( maman Ibrahim) Allah ya shirya Miki zuri'a ya Kara arziki*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD KO DA YAUSHE*
*DOMIN KU AUREN FARI FANS ANA MUGUN TARE*
*Federal University dutsinma*
Semester tayi nisa komai yayi zafi har Yanzu Bilkisu bata Sami sakewa ba, karatun Yana mata mugun wahala, ahankali take bin su chinyere suna nuna mata abubuwa duk Wanda ta fahimci Yana da kokari zataje don Kara fahimtar abinda ya shige mata.
Su Anwar sune Yan baya ga komai, ya biye wa mashiririta yaki nuna ma kowa Shi din Mai kokari ne, masu karyar suna da kokari sai ya kwantar da kanshi Yana Jin yanda suke kwabar bayani musamman idan akazo gun lissafi.
Hankalin sa a kwance duk C.A din da akayi shine overall, Yana amsa sunan Anwar a zahiri ba Wanda yasan Shi da Hamza Yusuf a badini.
Fahimtar halin Bilkisu na rashin girman Kai yasa Shi suke gaisawa da ita sama-sama Yana son kulla mu'amula da ita Amma Yana ganin hakan a gareshi zai zubda mishi aji.
Ita kuwa a gareta Sam bai ma gabanta ko kadan idan an hadu a gaisa idan ba a hadu ba Bata ko tunanin sa.
Shine ma sau da yawa take Dan takura tunanin sa kadan kadan.
Ta Dan Fara sakewa da su chinyere saboda ta lura sune masu kokarin ajin, takan zauna tayi tunanin akwai department din da yakai Economics barin wuta duk makarantar?
Sau da yawa tana tunanin Anya ba hausa ko Islamic zata koma ba?
Ta gama tsorata da makarantar musamman yanda taji ana bada carry over, probation da Kuma withdraw.
Takan yi tunanin ai ita abun kunya ne gareta ta sami Koda carry over din ne ma hakan yasa ta Kara dagewa tana Kara naci cikin karatun ta musamman da jarabawa ta karato kullum tana library ko Kuma tare da su chinyere tana Kara koyon karatu.
Saura kwana hudu su Fara jarabawa misalin karfe hudu na marece tana zaune wani class tana faman karatu yazo wucewa kunnensa like da air piece har ya gitta said yaga kamar ita, yayi jimmm Yana tunanin ita ce ko gizo idanun sa keyi Masa kamar kullum?
Kamar kada ya dawo sai Kuma dai ya koma don tabbatarwa .....ita din daice tana ta faman Mimi da baki ya kyalkyace da dariya lokacin daya kunna Kai ajin hankalinta naga littafi har yazo ya zauna kusa da ita....tayi firgigi cike da tsoro ko da taga shine bata San lokacin da ta balla mishi harara ba.....yayi murmushi afuwan matsoraciya duk wadannan mutanen meye zai kamaki da rana gatse gatse haka?
Ya karasa maganar Yana janyo littafin ta gaban sa, meye kike karantawa ayi mun bayani.
Haushi ya turnuketa domin karatun ya Fara shigar ta sosai gashi yazo zai rikita ta, Tasha mur tare da janyo littafin Dan Allah karatu nake zaka rikitani ka tashi ka bani wuri.....bazaki koya mun ba?
Nima Yanzu ai nake karantawa ta fada cikin fada fada, yayi murmushi it's alright go ahead and read ya sunkuyar dakai kawai bisa desk din.
Ta ci gaba da karatun ta ba tare da ta Kara bi ta kansa ba.
Idan ta karanta sai that bude can karshen littafin ta rubuta haka haka Yana ta lura da ita duk ta dage bakin Rai bakin fama Nan da nan ya gane hadda ce takeyi.
Yana so ya mata bayani Amma ya rasa ta inda zai Fara......
Tana son kamshin turaren sa ainun Anwar Dan gayu ne matuka Yana daukar wanka gashi kyakkyawa.
Kamar ta karanci zuciyar say ta Dan karkato Dan Alalh wannan kalmar me take nufi?
Ta sungo mishi littafin a gaban sa.
Daman tun zaman sa kusa da ita ya kashe music din hakanan wayar ke jikin kunnen sa.........yayi kamar baiji me tace ba har sai da ta kalleshi sannan ya Dan zare wayar daga kunne Shi ala dole baiji me tace ba ya dan kalleta Shima kina magana ne?
Cewa nayi me wannan kalmar ke nufi?
Ta nuna mishi da yatsa ....yabi hannun nata da kallo Yana kallon Zara zaran yatsun ta ya ce bari muji sentence din, Ya fada mata ma'anar kafin yace kin gane course din nan ne?
Ta Dan bata rai to gashi dai Ina karantawa......
Ya Kara janyo littafin gaban sa ya budo shafin farko......
Kin San fa abun duk labari ne Kinga.......ya Fara mata bayani a hankali ahankali Nan da nan ta Fara fahimta sosai saboda bayanin nasa duk da hausa yake mata.