← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 35

Sashe 15

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana tsaye ya harde hannu duka biyu a kirji.

Manyan Kaya na mishi kyau matuka, ya Kura Mata ido kamar zai cinyeta.

Ta karaso kanta kasa, Ina wuni.....ban amsawa.

Wai Bilkisu me kike nufi ne?

Me Kika fadawa su daddy akaina?

Ta dago Kai me fa, wani abu ya faru?

Komai ma ya faru gashi kince dole nazo mu gaisa ya Mika Mata kudi Kinga bayan Wanda aka ba su sadeeq ga nawa Kaya Kuma nacan an ajiye mun kamar.....to meye ne ba kyauta bace?

Ya kalleta, Kuma only me?

Ta daure fuska Ni ban gane abinda kake nufi ba......

Meye Kika fada ma iyayenki a kaina?

Simple question.

Ta gyara tsayuwa, sun San cewa Kaine kake koya mun karatu Kuma Koda yaushe Ina Basu labarin karatun da mukayi.....ya akayi daddy yasan bana shiri da malamai?

Ta zaro ido wallahi bamuyi wannan maganar ba.

Kin tabbatar?

Ta balla mishi harara na maka ta kudin ka.

Ya kyalkyace da dariya, to ai abun ne ya bani tsoro,
Mtsew ....tayi tsoki.

Mun shirya ko?

Tunda na amsa Kira na Kuma bada hakuri Nima ayi hakuri na gaji da fadan Nan wallahi.

Mun shirya ko?

Ya Kara maimaitawa Yana murmushi,
Ta yi Yar dariya eh,
Good, Dan Allah kiyi mun godiya sosai na gode.

Ba komai.

Sai gobe.

Korata kikeyi?

A'a bana son dai a Kira magriba kana Nan ko?

Hmmm, kawai kin koreni sai anjima ya Dan juya kamar yayi fushi.

Allah ya baka hakuri ka dawo ban koreka ba.....ya juyo Yana murmushi tunda kin bada hakuri kin tsira.

Zan kiraki please.

Ta juya.

Kinji?

Na ce toh.

Tuni magana ta Game ko'ina akan zuwan iyayen Bilkisu Kuma anga Anwar a wurin.

Hankalin mufeeda yayi mugun tashi ta dunga bala'i a daki.

Tare da Shan alwashin dole ta gyarawa Bilkisu Zama ta Kuma ja mata kunne akan Anwar.

Sha daya da kwata na dare ya kirata.

Labarin kayan da aka kawo mishi da makudan kudin da aka bashi yake lissafa Mata sanannan yadanyi Mata bayanin course din da zasuyi gobe.

Sha biyu ta wuce suka ajiye.

Su sadeeq sunyi sunyi yayi confessing akan Bilkisu Amma amsar kamar kullum itace, *baku da hankali*
Kowa yayi mamakin ganin su rumi rumi.

Sai karfe hudu suka gama lecture.

Duk ta gaji tana tafiya da kyar kawai taji anfinciko hijabin ta.......jira karamar Yar iska.

Kafin ta Ankara sun Mata zobe.

Ta kallesu daya bayan daya tace *Anzo wurin* cikin zuciya.

Lafiya?

Ta bukata tana musu kallon up and down.

Ko zamuji na jaki ne tukun?

Ko Kuma Ni ko?

Wallahi tallahi duk Yar iskar da ta Kara ja mun jiba sai naci kutumar........ke banza...mufeeda ta katseta.

Wani kallo ta wurga Mata nice banza?

Eh kece banza ko Zaki Rama ne?

Akan meye Zaki kirani banza?

Saboda Anwar..!

Wallahi idan Baki fita harkar sa ba Zaki......Zaki fiddani karatu FUDMA?

Ta bukata.

Amma ke a matan ma rakiya kikayo, ai mace idan ta cika mace namiji binta yakeyi ba itace ke bin sa ba.

Kije ki tambaya Dani da Anwar waye ke bin wani?

Ko an fada Miki dashi da Babu suna da banbanci a wurina?

Karatu ma da mukeyi Shi ke rokona da inzo ba Ni ce ke makalewa ba.

Ta fiddo waya ta latso missed calls.....ta nuna Mata fuskar wayar kalla ki gani.....don haka wallahi tallahi sai kinyi Dana sanin kirana banza......ta ingijeta ta wuce , gigin yasa jamcy ta Kai hannu zata rikota ji kake faaass....

Ta wanka Mata Mari , Marin da ya janyo duk illahirin masu wucewa da wadanda ke zaune sannan ta daga murya....duk wacce Kuma take ganin ita Yar Tasha ce tazo ta yi gigin kwatanta abinda tayi ko a nemi wata ta Rama Mata......

Bilkisu lafiya meke faruwa?

Suleiman ta gani.

Tayi murmushi cike da takaici duka na suka zo yi saboda inji tsoro in daina karatu da kula Anwar .

Duka?

To bisimillah kuzo ku dake ta wallahi summa tallahi da na karya hannun yarinya ko waye ubanta....duk suka juya suna gunguni, yace:, Yan iskan karya.

Muje kyalesu.

Suka jera.....

Haushi ya kamata lokacin da ya Kira taki daukar wayar.

Tasan akan maganar test din *GST* ne.

Yasan cewa ta tsani CBT,
Ya buga tsoki, duk duniya Babu Mai Sanya mishi ciwon Kai irin Bilkisu.

Bakin Auditorium din cike da dalibai abinka ga general course.

Tana can gefe ta makure sai faman karatun past question takeyi, Shi kuwa sai wurge wurgen ido yake ta inda zai hangota,
Mufeeda na can jikin bedi sun Kura mishi ido.
.......Wai Daman kina Nan?

Yanzu naga Anwar Yana nemanki nace bamu hadu ba, Aisha ce ta karaso rike da past Q din itama.

Yana Ina?

Gashi can....

Ta Mike , okay jirani Ina zuwa.

Yana hangota ya nufo ta.

Tayi kamar Bata ganshi ba ta nufi inda su mufeeda.

Ya biyota.......ke nake nema fa tun dazun kin Kuma hangoni kina neman sharewa........

Da karfi ta finciko mufeeda tare da bankada ta kusa dashi har yayi saurin ja da baya ganin zata fado jikinsa.

Ya zaro ido.....ita Kuma ta juyo a hasale ta Kara maida keyar ta tare da nuna ta da yatsa.......Ni agabansa Zan Miki *warning*
Ko a Yanzu wakika ga yabi wani cikin mu?

Tuni an musu zobe ana kallon ikon Allah,
Ta daka Mata tsawa nace ubanwa Kika ga yabi wani cikin mu?

Na tabbatar tun dazun ya ganki anan Amma bai nemeki ba saboda haka kece *BANZA* Gashi nan nabar Miki Shi duniya da lahira idan kina bukata Ni karatu ya kawoni ba shashanci da bin maza ba don haka idan kina son sanin wacece Bilkisu please try and confront me again wallahi you'll regret it for the rest of your life useless fool.........

Kawai ta bi cikin mutane ta wuce abinta.

Zainab wowo ce dai
*WA ZAI FURTA?*
0
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana.

Amin.*
*Wallahi tallahi inajin dadin masu kirana da mun text WhatsApp musamman don jinjinawa Aunty Rabi dayi Mata addu'a da masu yiwa mahaifina addu'a na gode Allah yabar kauna my fans my pride ana mugun tare irin sosai dinnan*
*Arziki irin na Aunty Rabi kowa ke fata Wanda zaka ba kowa ba arziki irin nasu o'e ba daga mu sai 'ya'yanmu
Wanda ya tsargu dashi nake*
_Wayata na bani matsala wallahi Shi yasa bana update da wuri_
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Ke ta tabance UMMI MAMAN KHAIRAT DA ZARAH, makwabciyar Alawiyya Ina godiya*
*Unex*
( Babu kamar ki ).
*Alawiyya Ina Kara godiya fa Allah yabar tare Allah yabarki da malam ya tsone idon munafukai*
*AUREN FARI FANS*
one love well.
*INA CIGIYAR MZ*
***************
*KADUNA RIGASA*
Tabbas Ummi Taji uwar bari,
Ta zabga uban tagumi, competition zanyi da Amira wallahi dole in ajiye wannan jahilcin in kwatar ma kaina yanci.

Mutane dake cewar duk namijin da yayi sabuwar Amarya uwargida ta Zama banza yau na karyata hakan, naga inda year gida ke fin Amarya daraja da kima.

Tun kafin inzo gidan Nan yakeyi man gargadi akan matarsa, ban Kara tabbatar da hakan ba sai da nazo, Bata laifi, bata gundurar sa.

Ya Zama wajibi Nima nabi hanyar da tabi don mallakarsa.

Ranar ya koma aiki, tunda ya tafi tana bangaren Amira suna fira, abin ya bata mamaki ganin ba wani alamun sauyi daga fuskarta, ta sakar Mata jiki suna ta fira Mai dadi ( ba abinda yafi Zama lafiya dadi, abinda mutane suka kasa ganewa kenan ).

Ta Dan muskuta Aunty wata alfarma nake nema wurin ki.

Ta kalleta cikin natsuwa sosai kafin tace Ina jinki ummi.

Wallahi Aunty na rasa gane Kan Abban Ahmad ko wane lokaci duk abinda nayi Ni Kam ban iya ba.

Kinga ko abinci na dafa mishi idan na kawo mafi yawa fushi yakeyi yabarshi a wurin Koda kuwa nayi abinda yake so.

Idan Kuma na sameshi daki...........ohhhhh na fahimci zancen ki.

Ta katseta tana Yar dariya.

Baya Miki korafin Baki da kula?

Wallahi yanayi Aunty.

Yawwa, kin gane, Shi mutum ne Mai son kula gaskiya.

Misali: wurin abincin da kike korafi, Shi yafi so idan Kika kawo mishi abinci ko ki zauna kuci tare, ko Kuma ki zauna kusa dashi yanaci Koda kuwa kin koshi, ya tsani ki bashi abinci kibar wurin.....ke abinda ma yafi so Bari in fada Miki shine ki na bashi da kansa.

Ya tsani lokacin da yake zaune dake ki maida hankali akan waya ko kallo ko wani abu saboda Shi mutum ne Mai tsananin son kula.

Ko a kwanciya ya tsani mace tayi mishi tabababaaa Nan da Nan sai ya harzuka.......gabanta ya Fadi...tohhh wannan dalilin ke sawa kullum sai sunyi rigima?

Ikon Allah.

Ta yi shiru dai, taji Amira ta shiga ranta sosai ganin ba bakin ciki ba Jin zafi ta zauna tana Mata irin wannan bayani Mai tsada Wanda ta tabbatar idan ita ce bazatayi hakan ba.

Kunya ta kamata sai kawai ta sauko bisa kujera.....Dan Allah Aunty Amira kiyi hakuri abubuwan da nayi a baya wallahi hada zuga irin ta mutane Amma Yanzu na gane........Dan Allah tashi ki zauna ba komai.

Shawarar da Zan baki shine ki kuji fitar da sirrin auren ki ga ko wanene wasu ba shawarar kwarai zasu Baki ba, ko meye kiyi keda mijinki ba Wanda yaji ya gani ko wace Kika gani gidan aurenta wallahi hakuri takeyi.

Shi Aure 90% hakuri ke raya Shi sauran 10%din ne ilimi da soyayya.

Saboda haka Dan Allah ki zauna mu fahimci juna tunda kaddara ta hada mu ba kanmu aka Fara ba iyayenmu da kakanni duk haka muka gansu Kuma zamansu lafiya ba don Babu kishi ba sai don hakuri da hangen nesa.

In shaa Allah Aunty Zan kiyaye Allah yayi Mana jagora..........
Chapter 15 · 0% Book details