← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 35

Sashe 5

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin San fa abun duk labari ne Kinga.......ya Fara mata bayani a hankali ahankali Nan da nan ta Fara fahimta sosai saboda bayanin nasa duk da hausa yake mata.

Haka haka har ya gama mata littafin.

Taji dadi sosai da sosai ta fadada fara'ar ta ohhhhh Ashe ka Gama covering komai ko???.......a'a fa nima kawai na gane darasin ne lokacin da yake bayani a class.....Amma wallahi ka iya bayani saboda har kafi malamin ma iyawa....ya danyi dariya tinda na Miki bayani da hausa ko?

Ta kyalkyace da dariya yabi fuskar ta ta Yana Kara kallo ta bude jakar ta to Dan Allah ka gane wannan math din?

Ta fiddo littafin.

Dariya kawai yake cikin Rai Amma a zahiri yadan basar.......ya kalli littafin, gaskiya ban iya Shi ba Amma ki bari yau sanje dakin wani dan aji hudu ya koya mun gobe sai mu hadu in nuna Miki......da karfe nawa?

Ta katse shi, Yayi murmushi duk lokacin da kike so goben....... 8:00am Zan jiraka anan.

Ya zaro ido 8?

Gaskiya sai dai 4 saboda barci bazai barni na fito da wuri ba.

Kamar zatayi magana sai Kuma ta fasa ta ce Allah ya kaimu lafiya tare da janye littafin yabi Dan karamin bakin ta da kallo har ta sunkuya.

Ta Mike tana kokarin sagala jaka ta kalleshi tana murmushi Dan Allah ka koya da kyau Zan jiraka anan din goben in shaa Allah.

Yace ba damuwa.....see you then.

Ta wuce.

Yabi ta da kallo kamar ya rufa mata baya amma Shi kansa yasan bazai iya hakan ba ( saboda gadara ).

Zuciyarta Fara fes!

Ta isa daki taji dadin bayanin Anwar matuka.

Washe gari tana fitowa masallaci ta wuce class din kamar yanda sukayi alkawari, ta fiddo wani course theory ta Fara karantawa kafin ya iso.

Ta nayi tana Dan kallon taga tare da duba agogon wayarta har kusan hudu da arba'in.
*Anwar* kuwa Yana can Yana shakar barci abinsa sammm ya manta da maganar su.

Allah ya taimaketa kawai sai ga su chinyere sun shigo karatu Suma Kuma cikin sa'a statistics din zasuyi solving sai kawai tayi joining suka Fara.

Tana yi tana tunanin watakila Anwar bai iya bane Yana Jin kunyar zuwa....ta tabe baki to meye na karyar zaije ya koya bayan yasan bashi da wani kokari....mtsew taja guntun tsoki.

Bai farka ba sai shidda saura ya tashi a hargitse ga takaicin lokacin sallah ya shige ga Kuma tunanin sabawa Bilkisu alkawari da yayi.

A gurguje ya watsa ruwa yayi sallah ya fito da sauri.

Ya shawo kwana ita Kuma ta fito ajin zata tafi.

Tana hango Shi tayi sauri bi ta dayan side din tabayan azuzuwa tayi hanyar fita gate sauri sauri.....tana tunanin watakila Yana can Yana faman koyo don yazo ya birgeta..tayi tsoki to karya tame ne?

A hargitse ya shiga ajin sai wurge wurgen ido yakeyi girman Kai da nuna Isa sun Hana ya tambayi su chinyere ko sun ganta.

Rai bace ya fita Nan ya Fara bin azuzuwa neman ta.

Helen ta tabe baki I don't like this Anwar honestly....

Mtsew don't mind idiot abeg inji chinyere Nan gulma ta tashi.

Ya cika girman Kai da nuna Shi wani ne, baya yi ma kowa magana sai abokansa uku.

Surutai kala kala saboda Shi din Daman baida farin jini a class din tun zuwansu Wai ya cika fadin Rai da gadara.

Tunda ga ranar bai Kara Sanya Bilkisu a ido ba yayi neman har ya gaji gashi baida no.

Ta bai Kuma San Wanda zai tambaya ya bashi ba haka Kuma baisan accommodation dinta ba hostel take ko off campus.

Wasa wasa abun ya Dan dameshi.

Ranar da zasu Fara jarabawa da yake ta karfe uku ce tun biyu saura yake hall din Yana so ya ganta, ita kuwa tun 8 tana library sai biyu da Rabi ta fito bayan tayo sallah.

Kansa sunkuye baiga shigowar taba har ta zauna bayansa.

Lallai Anwar ka kyauta shine ka shanya ni rannan ko?

To kayi dai dai ta fada tana faman hararar sa .

Da sauri ya dago Kai zaiyi magana kenan invigilators suka shigo tare da fadin everybody out..ta rigashi fita, ko da aka Fara shiga ma tayi saurin fadawa don Zama gaba gaba.

Alhamdulillah jarabawar ta mata dadi ainun domin duk abinda ta karanta suka fito.

Ita ce ta biyar din bayarwa ( submitting ) bata jira kowa ba tayi masallaci don gabatar da la'asar saboda lokacin biyar da kusan ashirin.

G
Haka semester din ta kare ba tare da sun Kara haduwa da Anwar ba, ko kadan Bata yarda su hadu tasan karya zai shirga mata don kare kansa.

Shi Dan garin Kano ne ita Kuma Abuja mahaifinta ke aiki Amma asalin su Yan katsina ne.

Washegarin da suka Gama jarabawa tabar garin Anwar kuwa karfe biyar na ranar yabar dutsinma.

Hutun baida tsawo sati biyu akayi aka dawo.

Sun dawo da sati daya aka saki result a *portal* Murna tsalle ga Bilkisu saboda ta cinye ko wane Bata da carry over ko daya ga point dinta 4.33
Hakan ba karamin dadi yayiwa Yan gidan su da iyayenta ba.

Anwar kuwa 5:00 dai dai ya samu saboda duka courses din da sukayi goma Sha daya ko wane *A* yaci.

Yaja bakin sa ya tsuke.

A cikin ajin kowa nata fadin result din sa daga Mai 4 point sai masu 3 point da abubuwa.

Duk Wanda ya tambayi Bilkisu sai ta ce lafiya Lau ne ni Daman carry over ke bani so to ban samu ba.

Bata yarda ta fada ma kowa result dinta ba.

Tana zaune an gama lecture din wani mugun malami ta kura ma dan rubutun da tayi ido tana nazarin ya zata ci jarabawa da Dan wannan rubutun?

Suleiman ya mata sallama.

Suleiman matashi ne Shima a cikin ajin Mai natsuwa da son addini babancin say da Anwar yafi Anwar saukin Kai da yarinta.

Ya zauna kusa da ita bayan ta amsa sallamar Dan Allah Hajiya Bilkisu na kasa bude portal dina ya akeyi ne?

Tayi murmushi Ina wayar taka in nuna maka?

Wallahi daki na barta ki nuna mun da taki.......hankalin Anwar na kansu haka kawai sai yaji ya tsani Suleiman karon farko a rayuwar sa.

Ta fiddo wayar tare da tambayar sa password da matric number.

Portal din na budewa ta Mika mishi wayar kaga inda zaka Danna.....

Ya danyi dariya to bude Mana ai ba komai don kin gani.

Ta kalleshi tana mamaki saboda tasan Portal sirrin dalibi ne ba kowa kake yarda ka nuna mawa ba.

Ya Kara Yar dariya ki bude ba komi.

Ki gane mun Ina da carry over?

Ta ce to a sanyaye tana mamakin irin warda da yayi mata farat daya zuciyar ta cike da Jin dadi tare da ganin kimar say da mutunci.

Kaiiii....ta fada tare da zaro ido ka Fadi accounting.

Sai kawai yayi murmushi nasan za'a rina sai wane?

Ka Fadi GST English Shikenan.

Nawa ne point dina?

Ta duba can kasa tana warware ido.....

Okay gashi Nan 2.65.

Ta kalleshi, amma Suleiman me yasa ka yarda dani haka?......Au kin San sunana kenan?

Ya fada Yana kallonta cike da mamaki, tayi murmushi eh Mana nasan sunan ka Suleiman.

Ina fatan ke dai lafiya lau ko?

Sai kawai ta budo mishi portal din ta tace kaga nawa.

Ya zaro ido kaiiiiiii......

Ta danyi murmushi Amma bana son Dan Allah ka fadawa kowa result dina.

Ya Jin jina Kai in shaa Allah Zaki sameni Mai rike sirrin ki, amma Bilkisu kinyi wuta da yawa fa!

Ta yi Yar dariya kawai.

Allah yasa albarka.

Kiban no.

Ki dan Allah ko da wani Abu Yana tasowa Kuma idan bazaki damu ba Zan ringa matsowa kina tasar Dani inda ban ganewa.

Ba matsala ga number rubuta........

A harzuke Anwar yabar class din tunda ga ranar sai kawai yayi baya da ita ko gaisuwa baya son suyi cikin kankanin lokaci ta Saba da Suleiman ta fahimci Yana da saukin Kai bashi da girman Kai sannan Yana da addini tare da daratta mutane.

Ko da ya gane Bilkisu nada kokari sai ya like mata ko C.A zasuyi Yana manne kusa da ita baya yarda tayi mishi nisa.

Ko kadan Bata da mugunta duk amsar da ta kakare mishi zata bashi ya kwashe tsaf!.

Akwai wani course Mai matukar wahala gashi three credit unit ne Kuma calculation Mai rikitarwa kowa Yana Jin course din.

Anwar yayi burus da ita Yana Jin kowa na kokawa Amma ya ki nuna ya iya.

Kwana takeyi karatu da salloli, Ranar jarabawar course din ana ta jera layi kawai malamin yace ta zauna can, hankalin ta ya tashi ganin ya cillata gaba don yau baya take son Zama saboda ta Sami taimakon wani.

Tana Zama sai taga Anwar ne a gaban ta, ita dai kawai sai addu'a takeyi tasan yau sai Allah da malaman gari.

Tambayoyi bakwai be a amsa biyar tambaya ta farko dole ce gata da 'ya'ya har goma.

Saura kadan ta kurma ihu saboda duka tambayoyin guda daya ne kawai ta sani itama theory ne ba calculation ba.

Idanun ta suka kawo ruwa, taga tunda Anwar ya duke bai dago ba, hall din yayi tsit!

Ta yi zugummm, zuwa can kawai ta Fara amsa wacce ta sani.

Mafi yawancin malaman dake tsaron nasu duk sun maida hankali wurin Yan baya.

Haka ta dunga rubutu Dan Allah yasa ta Sami Koda *E* ne a course din ta wuce wurin.

Tana gamawa tayi zugummm kawai tana fargaba.

Yadan waigo kadan ganin malaman basa kusa yace kin iya question one naga tana da wahala fa.

Tayi kasa da murya wallahi question 4 kadai na iya cikin bakwai din nan ga Shi ta farkon naga 30marks ne.

Ya dan gyara zaman sa kadan tare da kango mata booklet din sa yace kiyi sauri ki kwasa.

Habaaaaa.....ga bilkiyda saurin rubutu gata very smart.

Duba daya sai ta kwaso layi biyu.

Cikin sauri ta gama shafin tace juya....Shi kansa yayi mamaki yace ke duba da kyaufa kada kiyi shirme.

Wallahi na gama ka juya kawai.

Haka ya bata dukan sauran question hudun da bata iya ba.

Sai da ya tabbatar ta Gama tsaf sannan yaci gaba da amsa Shima question 4 din da tace tayi.
Chapter 5 · 0% Book details