← Book details Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 35

Sashe 14

Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin cika zafi yaran nan yanda suke tsoron ki koni basa tsoro haka meye abin fada ga shekaru irin nasa ma abinda yafi haka yi zaiyi.

Hmmm, kawai tace.

Ya finciko ta......zo in koya Miki yanda ake ba miji amsa idan yayi magana ba hmmm ake cewa ba.........dai dai ita Kuma ta turo kofa ashe bude yabarta lokacin da ya shigo.

Yana kokarin Kai bakinsa ga nata sukaji an turo kofa itace tayi saurin zamewa tunanin ta ma ko Yan aiki ne.

Tuni idanun ta sun gane Mata.....me ya kawo ni?

Wace kaddara ta aikeni?

Na gano ma kaina Ni Ummi........gabanta ya dinga halbawa da karfi da karfi.

Ita Bata karaso ba, Bata Kuma juya ta koma ba.

Gashi ya rike Amirar gammmm yaki saki, sai kichiniya takeyi amma ya riketa tamau .

Dole ta hakura ta kalleta, ki karaso daga ciki Mana Kika yi tsaye bakin kofa.

Bai dago Kai ba Yana ta wasa da hannun Amirar yace idan wani abu kike bukata me zai hana ki Kira waya?

Shiru dai tayi har ta zauna bisa kujera tana facing dinsu amma ta kasa Kara maida idanu ta kalli takaici.

Tayi shiruuuuuuuuu, sai Kuma kwallah sharrrr, duk motsin da takeyi idon Amira na kanta saboda tana ta mamakin zuwan nata.

Ganin zubowar kwallah yasa ta zunguro shi,
Ya maida Kai gefe Ummi lafiya dai ko?

Ita kanta tasan kukan da biyu takeyin sa, kasa ta sauko ta Fara magana a hankali,
Aunty Amira kiyi hakuri Dan Allah Akan abubuwan da suka faru sharrin shaidan ne, in shaa Allah hakan bazai Kuma faruwa ba......Ayya Ummi ba komai ya wuce.

Ta fizge hannun ta bari in zubo Miki abinci......um um na gode ta mike.

Ina zakije toh?

Ki zauna muyi fira.......ya Kara hade fuska ya tsuke.

Ta Dan tabe baki , a'a barci nakeji da wuri sai ko zuwa gobe haka.

Har kofa ta taraka, kafin taja kofar.
.........

Gaskiya abinda kakeyi ko kayi Abban Ahmad wallahi baka kyauta ba, Shi ido ba mudu ba yasan kima.

Ka rikeni gaban Ummi ai wannan cin fuska ne.

Ya kalleta sosai.......makaho idan Yana Kashi in har ba'a zungureshi ba to bazai gane ana kallonsa ba.

Yarinyar can abinda take nuna mun tun kafin in aureta dole in bita in Mata yanda takeso ita bazata bi ra'ayi na ba.

To Ni da ita wake auren wani?......duk da haka Yanzu kaga.....kiranta mukayi?.

Inba kilibibi da tsugudidi ba me ya kawota Yanzu?

Ba a haka......ke naji.

Tayi murmushi....

Ita Amarya ai Bata laifi.

To wannan dai tanayi.

Naji dadin zuwan ta yau din wata kilan ta Dan Sami darasin kula da miji idan ita din Mai hankali ce.

Ya Mike idan kin Gama sallamar Yara Ina jiranki.
*Ummi* taci kuka kamar ranta zai fita, tabbas ya kamata tayiwa kanta karatun ta natsu.

Ashe ita sunan tana Aure Amma har Yanzu Bata San meye Jin dadin Aure ba, ta goge hawayen da ke shatatowa, dole in kwantar da kaina inci arziki in barshi inda yake saboda tabbas idan naki abinda yake so nice Masha wuya.............
******************
*Federal University dutsinma*
Shigowar su Aisha ya bata damar neman mafita.

Ita kanta ma tana son ya zo su gaisa amma bazata iya kiransa ba.

Text ta tura mishi.
_Kaxo ku gaisa da su daddy yanzu_.

Wayar na hannun sa Yana kallon film.

Zaune ya tashi zumbur.

Sadeeq ya kalleshi lafiya?

Ya jefa mishi wayar.

Anzo wurin Dan ubanka sai kaje ka gabatar da kanka.

Munafukan banza Kun tsaya sai ba juna wahala kukeyi.....mtsew malam ban wayata.

Ya jefa mishi.

Wani text din ya Kara shigowa ... _zasu tafi in d next 30 minutes so hurry up and come_
Kara jefa ma sadeeq wayar yayi.

Kai seriously fa ...ya fada Yana zaro ido.

Ya tuntsire da dariya sai ka tashi ka tafi.

Ku dai tashi mu tafi wallahi bazanje Ni kadai ba.

Kasan dai rashin zuwan Nan kuma wani problem din ne.

Anas ya Mike zumbur Tabb ku tashi mu tafi rigima dame ta cimma kurege.
........

Ya kallesu sai faman canza Kaya sukeyi, yayi murmushi wallahi Yan iska ne ku.

Kaman zakuje biki?

Sadeeq ya jefo mishi wani farin boyal malam saka mu tafi...

Ya Mike idan Kun Gama mu je banson shirme.

Duk sukayo mishi chaaaaaa wallahi sai ka canza Kaya Dan ubanka da wannan hug din zaka je?

To meye aciki?

Kana hauka ne?

Ku daine mahaukata, Kun zauna Kuna ta faman wata kwalliya kamar zakuje daurin Aure.

Yayi hanyar waje.

Anas ya finciko Shi, kasa manyan kayan nan kada muci ubanka.....kici kici suka Fara kokawar cire mishi riga.

Ba arziki ya cire su.

Sukayi juyin duniya yasa hula kube yakiya dole suka hakura sai dariya yakeyi masu duk sun Sha huluna.

Daddy ya Fara mikewa Zan jiraku waje ku karasa kada muyi dare.......

Tuni su Aisha sun rufo mishi baya don barin Bilkisu ta gana da mommy.

Mashin din muhseen roba roba suka amso.

Sadeeq ne driver, Anas tsakiya Anwar karshe.

Suna shawo kwana sadeeq ya kurma zagi ashar, wancen muguwar motar fa?

Dai dai su daddy na kunno Kai sai dai ji sukayi Anwar ya dire da yake ba gudu sukeyi ba.

Ga Anwar nan kuwa inji Aisha.

Murmushi daddy yayi, nesa kadan sukayi parking.

Tare suka jero su uku.

Wata irin faduwar gaba yakeji wacce bai taba Jin irinta ba, duk suna durkushe lokacin da suka karaso.....Barka da rana.

Idanu su Aisha suka bude duk girman Kan su?

Ya fadada fara'ar sa ya Mika musu hannu, Assalamu alaikum duk Wanda suka gaisa sai ya dago hannun alamar ya Mike tsaye har yakai ga Anwar,
Wani shocking yaji duk illahirin jikinsa ya dauka dai dai lokacin ne Kuma Bilkisu da mommy suka fito.

Ta danyi dariya to mommy ga Anwar can .

Da sauri ta Fara waige waige Yana Ina?

Gashi can daddy ya rike hannun sa.

Tunda ya dago daddy bai saki hannun sa ba, ya rikeshi gamm suna Yar tafiya hakan yasan su sadeeq da Aisha stepping back kadan suna bin bayan su.

Sai murmushi yakeyi Yana sunsunne Kai.

Daddy ya kula dashi tsaf!, ( Abinda bai sani ba yasa an kishi bincike kaf akansa tun lokacin da Bilkisu tace wurin Shi take daukar karatu ).

Ya karatu?

Alhamdulillah!

Ya fada,
Kana fama da rigimar Bilkisu ko?

Yar dariya kawai yayi, har lokacin yaki yarda su hada ido dashi.

Ai kullum labarinta Anwar, ko an Kara wani fadan ne?

A'a ya fada Yana murmushi.

Ta ce Kai Dan Kano ne ko?

Eh, ya ce har lokacin fuskarsa ta kasa daina murmushi.

Me yasa baka jituwa da malamai?

Lokacin ne ya Dan saci kallon daddyn ta gefen fuska....

Ya kasa amsa tambayar.

Ganin haka yasa yaci gaba da cewa, mutunta malamai akeyi ana gaishesu, wasu akasin hakan duk kokarin ka sai sunyi maka mugunta.

Haka ne!, Anwar din ya fada a hankali.

Sai a kiyaye kaji ko?

In shaa Allah.

Yace.

A bakin mota suka tsaya.
..........ga Anwar ga Anwar , tun daga nesa mommy ke fada tana dariya.
( Na shiga uku ni Hamza ).

Ya fada cikin zuciya.

Duk su sadeeq suka gaisheta Bilkisu na gabatar dasu.

Ya yunkura zai zukunna don gaisheta daddy ya rikeshi, ku gaisa a tsaye kamar yanda sunna ta koyar.
......ya akayi Kika gane shine Anwar?

Daddy ya tambayeta Yana murmushi.

Balky ta nuno min Shi lokacin da mun fitto.

Idanun ta na kansa Shima Yana son kallonta Amma ya kasa.

Su Aisha sukayi bankwana suka juya, Shima ya saci kallon su Anas alamarr su ware lokacin dasu daddyn kema su Aishar bankwana da nasiha.

Sai dariya sukeyi mishi daga nesa.

Daman tun da suka taho da daddy din suke mishi dariya ganin duk yanda ya dabarbarce.

Anas yace munafuki kaga duk rashin kunyarsa yaki sakewa Kuma don sun dauki mutane Yan iska Basu so a gane suna son juna.

Anas ne ya matso ya Dan rusuna zamu koma hostel Allah ya tsare hanya......

Amin Amin ya zaro envelope ya Mika musu.

Har lokacin hannun daddy na cikin na Anwar.

Ya kalli Anwar tafiyar ku daban ko?

Ya Dan sunkuyar da Kai tare muka zo.

Ohhh, to su tafi sai mu ajiyeka......

Ba Anwar din ba ita kanta Bilkisu tayi mamakin hakan.

Ya kalli Bilkisu ba abinda kike bukata Kuma?

Tace eh.

Okay muje kada dare yayi suka bude mota.

Lokacin ne ya Sami hada ido da ita.

Ya sakar mata murmushi sai kawai ta harareshi ta juya.

Gaba ya shiga Yana nuna hanya.

Allah dai ya baku sa'ar karatu ya kareku daga dukkan sharri.

Yace Amin
Dan Allah kusa tsoron Allah ga dukkan al'amuran ku Anwar kada kuci amanar iyayenku, kaji ko ?

In shaa Allah mommy.

Ya fada.

Yayi matukar godiya lokacin da suka ajiye Shi daddy ya umurci driver ya sauke mishi sauran kayan dake boot , sannan ya Mika mishi envelope Mai kauri.

Yayi godiya sosai.

Aka Fara sauke Kaya, cartons din lemuka , ruwan roba, carton din indomie, oat,Madara family size 3, corn flakes, biscuits kala kala,Dan kalin turawa cikin buhu, plaintain, kwai Crete hudu,fresh milki, gasassun kaji, kilishi, soyayyar miyar naman rago, dambun Daman kaji, fanka Mai chargy ( Daman Yana da ita ), sabon carpet kato Mai laushi da turaruka.

Cikin kwalaye aka jero kayan.

Yabi kayan da kallo kafin ya Kara
komawa bakin tagar motar yadan rusuna, Angode Allah ya Kara arziki Mai albarka ya bada lafiya da tsawancin kwana.

Duk suka amsa Amin Amin.

Ya daga musu hannu Allah ya kiyaye lokacin da driver yaja mota, gaban hostel din cike da mutane Shi kawai ake kallo saboda motar da ta janyo hankalin kowa.

Da gudu su sadeeq suka karaso.

Ya kallesu ku shiga da kayan Nan zanje in ga Bilkisu......kawai ya tsaida mashin ya koma..............Tana ta faman shirya kayan Jennifer ta shigo, Bilkisu Anwar want you......ta kalleta da sauri Anwar?

Yah, he's out side......

Tana fadar haka ta fice abinta.

Ikon Allah, lallai ni ta bance , duk FUDMA kuwa akwai macen dake juya Anwar kamar Ni?.

Wallahi Bata taba tunanin zaizo ba lokacin da tayi mishi text despite fushi da rashin daukar wayarsa, Wai me yasa Baya mata fushi da gadara da Kuma wulakanci kamar yanda ya Raina kowa?.

Hijabi ta saka ta janyo dakin.
Chapter 14 · 0% Book details