Sashe 25
Wa Zai Furta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hamza yace mun lokacin da na saka ayi binkice Kan dabi'un sa da irin rayuwar da yakeyi makarantar......
Da gudu ta shigo, mommy na samo cheese din kuwa.......
Ba sallama?
Assalamu alaikum...ta fada tana dariya.
Gardama mukeyi da dadyn ku akan Anwar meye cikakken sunan sa?
*Hamza Yusuf Hamza*......
Duk suka kalli juna shida ita da sauri,.....
Ta zaro ido lafiya?
Yanzu Ina fitowa ShopRite ya kirani kuwa.....yace me?
Duk suka hada Baki.
Ta tabe baki gaisawa kawai mukayi da yake kwana biyu bamuyi magana ba ya ce sunje kauye siyo ma ubangidan su wasu Kaya.....
Nace damuwata ya koma school da wuri kada ya barni da tararrabi inyi ta zare ido saboda idan Yana kusa da anyi ban ganeba ya mun bayani shikenan.....
Aikin meye yake?
Daddy ya Kara bukata......
Daddy hoooo nace maka wani yake mawa fa tsaron shago sukeyi a sabon gari market...this is what he told me na.....
Tohhhhh, ai Yanzu muka fahimta.
Jeki ciki abinki.
Kin yarda Yanzu da maganata?
Ta zaro ido shine da gaske wallahi.....baya son fada Mata Shi wanene Kuma makarantar ma badda sawu yayi.
Ba tace first class din ma boyewa yayi ba?....
Tabbas.
Yayi murmushi, shikenan mu Sanya su addu'a Kar ki saki Koda wasa ki sanar da ita, wata kila Yana da dalilinsa nayin hakan....
Hmmm.
Tace duk jikinta yayi sanyi tana Kara maimaitawa a zuciya *Hamza Yusuf Hamza bushara* Shi ne *Anwar* ikon Allah.
Karfe biyun dare ya sauka Kano.
Bai Sami kwanciya ba sai uku saura, Shi yasa ya makara washe gari wurin tashi.
Sha biyu saura ya farka tun bayan da yayi sallar asubah ya koma.
Ko juyin farko batayi ba ya mirgina ya janyo wayarsa.......
Cikin magagi ta dauka hello.......shine Kika ajiye mun waya jiya ko?.
Hmmm, ina kwana.....
Duba agogo ki gani Sha biyu ta wuce kike faman ina kwana.
Ina labarin Suleiman,
Lafiya Lau.
Shi Dan wane gari ne....Ina ruwanka ta fada tana tashi zaune.
Yayi murmushi lallai dai Kam, babu ruwa na.
Next week result zai fito waye zai Miki registration?????...
Suleiman nake turawa kudi Yana mun.....kenan yasan password din portal dinki....why not?
Shine ni ban sani ba?
Tayi dariya kawai.
Kinji?.
Nawa ka samo kasuwar?
Nawa ne share na Kuma?
Ya kyalkyace da dariya....sai nazo zamuyi lissafi.
Ehee, hakan ya kamata.....tana so tace mishi suyi video call tana Jin nauyi.
Sun kusa awa kafin suyi sallama.
Tunda ya dawo Kano ayyuka sukayi mishi sauki a Rana sai suyi waya sau hudu, chatting kuwa Koda yaushe suna online.
Ya rasa inda zai Sanya kansa da tayin Yan mata.
Sati daya da komawa Bilkisu ta koma, Shi Kuma yace Mata sai satin sama, Amma duk Rana daya suka dawo Yana son Bata surprise ne banbancin shigar dare sukayo sosai don lokacin da suka zo dutsinma daya saura na dare.
.......ya kalli s
adeeq an dawo fagen fama.
Suka kyalkyace da dariya.
Sadeeq ya Kara langabe Kai ka dubi girman Allah ko roba roban ne ka sai Mana muma wannan semester din......
Allah ban saye ka Bari kawai muyi ta aro muna 3 in1 hakan Yana matukar birgeni da saka ni nishadi......mtsew..kada Allah yasa ka siya mugu, ya wuce.
Ya bishi Yana dariya, inba kaiba Bilkisu duk duniya Yanzu kunfi sanyani ciwon Kai.
***************
*Federal University dutsinma*
Hutun ya amshe ta, tayi kiba ta Kara yin jawur, Bata son zuwa lecture din Dr Richard munafuki saboda ta tsane Shi.
Kuma Yana iya bada test idan yaga ajin ba mutane.
Milk lace ne ta saka Yana da ratsin flowers orange dinkin Riga da skirt, sannan tabi da doguwar hijab.
Agogo kawai ta daura sai zoben azurfar da ke hannun hagu.
Tafiya take kanta a kasa, wani haushi take ji har cikin zuciyar ta idan ta tuna class din yau ba Anwar.
Ga mamakin ta ajin cike fiye da rabi duk an dawo.
Daga nesa Helen ke ihu oyoyo Bilki beauty....
Tana Yar dariya tana Kara sauri tare da ware hannu suka rungume juna.
Kinje America ne irin wannan fresh haka?....
Ta tun tsure da dariya suka fada aji........
Karaf sukayi tozali, ta zaro ido Anwar??????
Ya sakar Mata murmushi kawai, wani dadi ya ziyarce ta kamar ta ruga ta rungume Shi takeji, ya Kara kyau shima yayi haske, tayi kasa da Kai kawai tana murmushi.
Tana Shirin Zama ya taso...
Helen move, ya janyota da hannu ya fiddo ta sit din, Shi kuma ya zauna.
Wani mugun kishi ya turnuketa ta kalleshi a hasale ji yanda ka wani kamata ba ka iya cewa ta wuce ko ta gafara dole sai ka cacukumota?
Ta Kara sa maganar tana maka mishi harara......
An Kuma dawo fa, yau din nan har na Fara tabka laifi?.
Au hakan da kayi daidai ne???
To ka je Kama kadaddabeta Anwar mtseww ta doka uban tsoki.
Ya dafe Kai, ohhh my God, naji ban kyauta ba kiyi hakuri bazan Kara ba shikenan ko?
Kinji?
Naji, ta fada.
Ina tsarabata?
Ya Mika Mata hannu.......
Tana daki na yi tunanin baka dawo ba.
Jeki daukon Ina jiranki.
Kana jirana a Ina?
Lecture din Kai zaka mun?
Ai ba zai zo ba Yanzu ya Aiko kafin ya karaso......
Mtsew mutumen nan baiyi ba wallahi.
Tashi muje in baka......ta mike.
Ya shafa Kai da hannu, kije ki dauko mun Ina nan ki dawo.
Inje in kuma dawowa?
Eh, Mana.
Idan na biki muka je kina bani zaki gudu......ta yi Yar dariya in gudu kamar wata marar gaskiya?
Eh, nidai jeki dawo Ina Nan.....
Me zakayi anan din?
Jiranki zanyi kawai har ki dawo, a a idan na tafi ka gama sai ka biya ka karba kawai.....wallahi bazan karba ba kuwa, ki je ki dawo akwai labarin da Zan baki.
Ta koma ta zauna, mu gama labarin tukun sai mu tafi tare ka karba.
Ya kalleta better.....
Ina Suleiman Shi bai dawo ba?
Wallahi ban sani ba.
Yasu mommy?
Lafiya Lau.
Meye Kika siyo mun tsaraba?
Tayi Yar dariya kana sauri ne?
Ka jira zaka gani Mana.....
Ina salalar business dina?
Ba kince zamuje na siya Miki abinda kikeso ba?
Tabbas, Amma dole inji dumus Kuma.....ya kyalkyace da dariya har Yana dukan table....Yan aji duk suka maido hankalin su sai dai ba Wanda kejin me suke cewa.
Watau kiji dumus......
Ta kalleshi tana murmushi eh Mana.......
Ashe da gaske ka dawo....
Sukaji magana daga sama kwatsam, duk suka dago *Mufeeda ce* tsaye tana murmushi Tasha wanka.....
Ya Dan Sha mur kamar bashine ya Gama dariya Yanzu ba....
Eh na dawo ya kike?
Qalau, ya hutu?
Lafiya.
Dan Allah kazo minti biyu Ina son magana......
Kodai ki Bari sai anjima ko Kuma ki fada anan.
Anjima yaushe.
Evening may be.......
To anjiman zamu hadu, ta juya ta wuce....
Mikewa tayi,
Ina zakije?
Ya bita da idanu.
Ta tsuke fuska, daki.
Saboda mufeeda tazo?
Ta dalla mishi harara ta Isa ta koreni ne?
Idan Bata Isa ba ki zauna to, ko don kinji nace Mata anjima?
Wallahi don ta kyaleni Ina zata ganni anjima din?.....
Na sani?
Ai zata maka waya ko baka zo ba ko?
Wallahi na Miki alkawari bazan dauki wayar ta ba ko da ta kirani.
Kiyi hakuri zauna.......
Ta koma ta zauna.
Ya kalleta Yana Yar dariya, saurayin ki ya shiga uku don kina da kishi sosai da sosai.
Tasha mur batayi magana ba.
Wayarsa tayi Kara, Yana dubawa yaga Alh.
Murtala.
Ya mishi text cewar zai Kira anjima.
Ya kalleta, haka shima Suleiman kike saka mishi doka da horashi Akan kula Mata?
Murmushi kawai tayi tace humm.
Ina ruwana da su?
Kawai bana son raini ne?
Kiyi hakuri Zan Mata fada sai ta ringa Baki girma........
Ta kalleshi, ya gyara fuska alamar ba wasa.
Cikin semester din nan Zaki fiddamun gwana cikin su, Aure nakeso gaskiya.....
Saura kadan ta dora hannu a ka.
Ta ce hmm.
Ko bazaki fidda mun ba?
Ta daure ta cije ba tare da ta kalleshi ba tace cikin su wacece tafi birgeka?
Yayi jimmm, ai ruwan ido bazai barni na tantance ba, wace kike ga tafi?
Ta harareshi ban sani ba ta Mike Ina da aiki daki......
Ya gumtse dariya shima ya Mike.
Suka jera kamar ta kwasa a guje tabarshi agun takeji.......
Kin San rayuwata Ina son mace wacce Bata da tsoro, .....,..ai shikenan bani ciki kawai, ta fada cikin Rai saboda nikam kamar farar Kura nake don tsoro.........Mai kyau, Mai ilimin addini, wayayya, fara Mai dogon hanci, Mai tsawon gashi, Yar gayu.......shin Wai ni Yanzu Ina ruwana kake ta faman lissafo mun kaje can ka Nemo Mana....
Yayi Yar dariya ke nake fadawa irin wacce zaki nemo mun.....
Mufeeda kaje na zabar maka mufeeda ita ce keda duk qualities din da ka zayyano......
Ya Kara gintse dariya mufeeda ba Fara bace Kuma Bata da gashi dogo attach........
Har ma ka sani?
Ta zaro ido.......
Eh, Mana kowa ma yasan haka tana boye gashin ta ne?
Mtsew....sai kaje sadeeq ya Nemo maka......
Ke Zaki Nemo.
Tayi murmushi ikon Allah dole ne?
To ai kece babbar kawar tawa ko?
Kema sai in taya ki zabe......Ni an mun miji.....
Ya bazga uban tuntube saboda tashin hankali saura kadan ya Fadi tayi saurin tarewa kamar zata taba Shi tace subhanallahi sannu....
Ya Mike idanuwan say duk sun Fara chanzawa daga farare zuwa jajaye.....
Da gaske an Miki miji?
Ya fada Yana gyara takalmin sa, ta kakaro murmushi ta ce aikuwa dai Ina da Wanda Zan aura......
Bai Kara magana ba har suka je kofar gidan.
Ya tsaya kansa juyawa kawai yakeyi, ta fito da Yar karamar leda ta Mika mishi ga tsarabar.....ya kasa Sanya hannu ya karba.
Ta kura mishi ido ya sunkuyar da Kai kasa kawai.
Lafiya dai ko?,
Yayi shiru.
Gabanta ya Fadi......
Anwar lafiya?
Ta Kara fada a hankali .
Ya dago Kai, kirjinta ya buga duk ya wani gigice yayi kicin kicin da rai, ya sunan Wanda Zaki aura?
Ta kalleshi........
Wai shine abinda ya sanyaka damuwa......
Ya Mata wani kallo dole ta kawar da Kai saboda ta tsani kallon banza da rainin wayau.......
Akan meye zai dameni?
Tayi murmushi to naga ka chanza lokaci guda.......
Kaina ne yake mun ciwo.
Ga tsarabar.....ta Mika mishi ledar.
Ya juya ajiye wurin ki Zan karba......
Wallahi bai yiwuwa.
Ina ce shine dalilin biyo ni.